← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 68

Sashe 7

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya kilishi tace" 'yar wajan Maryam cefa,da wanne samarin zaki had'ata?,inaaa! bade 'yanbiyu naba,har abada babu had'i, yanda kika gantannan kullum haka take yawo tana nunawa mutane jiki,ita ga tantiriya,kuma uwarta ce take koya mata komai,idan na kuskura nabari yarinyar nan ta auri d'ana aina kashe kaina, tun yanzu ma kafin ayi mata aure bad'ala iri-iri uwarta take koya mata,to inaga anyi aure? tana saka irin wannan kayan yanzu,idan tayi aure kuma wanne iri kike tunanin zata saka?kinsan 'yar maiduguri ce uwar, idan 'yarta ta auri dana kuma ai shikkenan sai yanda aka min dashi, kiduba kigani de yanda tashiga tafita a wajan malamai da bokaye saida tarabani da 'yanbiyu nah,basu Isa suzo gidan nanba saide kiga sunje part dinta sun tare,Ashraf ma dayazo shekaran jiya danyaga na tsaye masa ne, na Kuma saka masa ido,amma da abinci ma Infad'a miki saide yaci awajanta, to inda nakejin dad'i sauqina d'aya,yarinyar bata gabansu duka su biyun, musanman ma ARYAN...."

Cikin sauri Hajiya Mariya ta katse ta" ke dakata matar Alqali,wai kina nufin yarinyar nan ce 'yar wajan Maryam tagirma haka?"

Hajiya kilishi tace"hmm ai Ina ganin ikon Allah Hajiya Mariya,itace wallahi,ai kallon tsoro kikai mata,bakiga uban nonuwan taba"

Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"to aikuwa matar Alqali tun wuri kitashi tsaye,inba hakaba kiyiwa kanki sakiyar daba ruwa..."

Cikin sauri Hajiya kilishi tace "wa?, Allah yatsare ni,ai har abada babu alkhairi a tsakanin ta da 'yanbiyu na,to Ina alkhairi ga yarinyar da batayi gadon haihuwa ba? Ita kad'ai uwarta tahaifa daga ita babu qari, ita kuwa bana tunanin ma idan tayi auren zata haihu, tunda batayi gadon haihuwa ba,to waima INA UBANTA?, har zuwa yanzu mude bamu ganshi da idonmu ba"(😳🙆🏻‍♀️tofa)

Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"tabdi, aikuwa matar Alqali saiki dage,kuma kisawa 'ya'yanki ido sosai, kinsan maza da jarabar tsiya,da gane-gane, suna qyalla ido idan suka ganta shikkenan,musanman idan wannan dirin nata ya rud'esu,kina zaune saide kiji Ashraf yana cewa shizai aure ta shima Aryan yana fad'in shi zai aure ta...."(😂)

Hajiya kilishi tayi ajiyar zuciya tace"kada ubangiji ya nunamin wannan baqar rana....to Hajiya Mariya ai bakisan wani abuba,gaba d'ayansu su biyun fa har yanzu basuda tsayaiyar budurwa,abun har tsoro yake bani, shekaru sunata tafiya sunqi aure, musanman Aryan, shi bashida magana, bansan yaya zaiyi yasamu mace ba"

Hajiya Mariya tace"tokode baqar aljana ce ta aure shi?"

Cikin sauri Hajiya kilishi tace"aiko farar aljana ce dole zaiyi aure shima ya ajiye zuri'ah"

"wannan gaskiya ne" cewar Hajiya Mariya, daga nan tarakota get dinsu na farko, sannan tadawo.

******

Da daddare Mamy tagama cin abinci suna zaune afalo gaba d'ayansu, yayanta dake maiduguri Alhaji Mustapha yakira wayarta, bayan sun gaisa yace"Maryam yaronki ne yasani wannan waya, kinganshi nan zaune tun yamma yazo yasani agaba lalle saina kiraki nafada miki shifa yanason Mawahib,yace nafada miki yanason ayi masa izni yafara zuwa wajanta zance "

Mamy tayi murmushi,tasan cewa yayan nata bashida wani da namiji Sai guda daya, sauran duka mata ne, cikin Jin dadi tace"Nabil kenan,yanzu nice nazama haka awajansa? bazai Iya kirana yafadamin da kansa yanason Mawahib ba saide yasaka kakirani kaida kanka Yaya?"

Gaban Mawahib ne yayi wata irin faduwa Jin maganar akanta akeyi,dama Yaya Nabil sonta yake shiyasa taga kwana biyu yana matsa mata da magana idan tahadu dashi a chat?
Bata gama tunanin datake ba taji Mamy tana cewa"a a, batada kowa Yaya, amma Nabil aina gida ne,Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa rabon sa ce"

Bayan sungama wayar,cikin jin dadi Mamy ta Kalli Alhaji Isah tace"Abban Mawahib kaji wai Nabil din Yaya Mustapha ne yace afada mana yanason Mawahib"

Abba yayi murmushi ya Kalli gefenda Mawahib take zaune kamar ruwa ya cinyeta,cikin tsokana yace"yanmatana wai zaki aure shi kigudu kibarmu?"

Cikin kunya tatashi da sauri tafice daga part din nasu, tatafi wajan Nabiha.

Alhaji Isah yayi murmushi yace" To Alhamdulillah, gaskiya naji dadi sosai, Nabil ai yanada hankali,zansamu su Yaya inyi musu maganar,shima saiki fada masa yazo suyi magana shida Mawahib din,idan sun sasanta kansu shikkenan, idan Allah yayi auren dashi,saita qarasa karatunta adakin mijinta"

Mamy tayi murmushi tace"hakane,amma gaskiya ni naso ace saita kammala karatunta sannan zatayi aure,banason irin neman aure da wurin nan,duka-duka ma nawa Mawahib din take?shekara goma sha takwas Alhaji wanne irin aure ne wannan zasuyi?"

Abba yayi murmushi yace"wanne karatu Maryam?yaushe tafara karatun? ko level two bata shiga bafa yanzu tasa qafa a karatun,kicire wannan tunanin aranki inde harshi Nabil din zai barta tayi karatunta ai Alhamdulillah, batun shekaru kuma bawata matsala bane,tawani fannin ma gara hakan, mijinta zai koya mata soyaiya da kansa, sannan kuma kinsan abinda mu iyaye mukeso akan yayanmu qaddara tana zuwa ta sauya shi,kiga abinda mukeso din bai faruba, ke kinaso ace tagama karatu, taqara shekaru, sannan tayi aure,nikuma abinda yake Raina shine naso ace ta auri Yayanta CAPTAIN ARYAN,dukansu dagashi har ita Ina musu sha'awar junansu"

Gaban Mamy ya yanke yafadi,cikin sauri tace"Alhaji kadena wannan maganar Dan Allah, Allah yasa Nabil din yazame mata mafi Alkhairi"

Cikin Sanyin jiki Abba ya amsa mata da "Amin"

******

Tana zuwa dakin Nabiha tace"Nabiha nadena zuwa wajanki daga yau, ke bakida aiki saiki ki shige daki ki dauki wayarki,gaba daya kin manta dani"

Cikin murmushi Nabiha tace"to yi haquri,nadena, shikkenan? meyake faruwa naganki yanzu goma saura?"

Saida ta yatsina fuskarta sannan tace"kinsan me?wai Yaya Nabil ne yasa kawu Mustapha yayiwa Mamy magana wai yana sona"

Nabiha tanajin haka tagyara zama tace"ke dan Allah?"

Mawahib tace"wallahi,Nina rasa yanda zanyi,gaskiya ni bana sonshi,amma zan aure shi kodan Momy kilishi, idan tadena ganina ai shikkenan, bazata sake fada mana magana nida Mamy naba"

Nabiha tayi ajiyar zuciya tace"hakane kam, amma gaskiya nide Mawahib nafi miki sha'awar Yaya Ashraf,saboda naga kamar yana ra'ayinki"

Cikin sauri Mawahib tazaro idonta(😳) tace"Rufamin asiri Nabiha,inani Ina 'ya'yan Momy kilishi?,sannan kuma yamin girma,banason tsoho, gara yaro dan ashirin dawani abu"

Nabiha tayi murmushi tace"lalle yarinyar nan, Yaya Ashraf ne tsoho? to bari Kiji wallahi irinsu akeso,sunfi yaran Iya soyayya....wallahi innice ke ko,yanda Yaya Ashraf dinnan yake kulaki,wallahi sainayi soyayya dashi Inga Yaya Momy kilishi zatayi,Yaya Captain nede dama bamu Isa mugwada hakan ba" (😂)

Mawahib tace"Nabiha ko amafarki bana fatan nayi soyaiya da 'ya'yanta, zama lafiya aiyafi zama dan sarki"

Haka suka dinga tattauna zancen har shadaya nadare,sannan Nabiha tarakota, sukai sallama

******

Washegari tun kafin tatashi daga bacci Nabil yakira ta yakai sau biyar tana bacci bata dauka ba,kuma wayar tana silent, saida tatashi taga messages dinsa dayawa,kusan guda hudu, duka babu wanda bai zuba mata kalaman soyaiya ba,kasancewar ta farin shigan soyaiya tafi minti ashirin tana daga kwance tanata aikin karanta saqonnin nasa,daga baya kuma tatashi tayi wanka ta shirya ta futo ta gyara musu gidan,bata dade da gama aikin ba Mamy tadawo kasancewar yau juma'ah da wuri take dawowa,sai bayan ansauko daga sallar juma'ah sannan Nabil yakira ta,sun dade suna waya tun Mamy tana mamakin Mawahib harta dawo ta daina ganin yanda take magana qasa qasa ita Ala dole da saurayi take waya, da abun ya isheta saita Kalle ta tace"Mawahib kije daki kiyi wayar mana"(😂)

Babu musu tawuce dakinta,saida sukazo sallama dashi ne sannan yake fada mata zaizo gobe,me takeso yataho mata dashi, ta nuna masa batason komai, daga qarshe sukai sallama.

Saida daddare take fadawa Mamy Yaya Nabil zaizo gobe,Mamy tayi murmushi tace"Allah yakawo shi lafiya"

Washegari da sassafe taje tatashi Nabiha daga bacci,cikin Jin dadin bacci Nabiha tace"dan Allah Mawahib ki barni nayi bacci na"

Mawahib tace"kitashi dan Allah Yaya Nabil ne zaizo anjima, yamin waya yana hanya wallahi"

Cikin sauri Nabiha tatashi zaune tace"wai daga maidugurin zaizo?"

Tace"eh,bansan me zanyi masa ba,nahada masa drinks kawai yayi?"

Nabiha tace"haba Mawahib,ya mutum zaizo tundaga maiduguri amma mu bashi lemo, kinsan me? fita zamuyi muyo cefane muyi masa girki mai dadi, kinsan yau momy kilishi ce zatayi girki ba Mamy ba bare muce zamu bashi abincin gida,kuma wallahi momy kilishi abincin gargajiya takeyi, kawai kije kifuto muje driver yakaimu kasuwa muyo cefane mudawo"

Mawahib ta jinjina kanta tace"eh hakane kuma,to bari inje in shirya, kema kitashi dan Allah"

Cikin sauri suka shirya suka fita,driver yakaisu suka siyo abinda suke so, sannan suka dawo gida, suna dawowa ko zama ba suyi ba suka fada kitchen, kasancewar kayan maqulashe suka hada masa nan da nan suka gama kafin ma ace Hajiya Kilishi ta shigo kitchen din, Mamy de taga anata jera girke girke afalo cikin ranta tace"ikon Allah,zamani kenan"

Sai wajan qarfe uku na yamma yazo,kasancewar sa ba baqo ba a gidan yasa kai tsaye Mawahib ta shigo dashi falo,saurayi ne matashi bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba.

batayi kwalliya mai yawa ba,kawai light makeup tayi,tasaka riga da siket na leshi,tayafa mayafi dan madaidaici mai kyau, bayan sun gaisa ta gabatar masa da kayan ciye ciye, babu kunya yaci abunsa sosai, sannan takira masa Mamy suka gaisa, Mamy tadan dade a zaune tana tambayarsa 'yan'uwanta mutanan maiduguri, sannan ta koma daki tabarsu shida Mawahib din.

Cikin nutsuwa yafara yiwa Mawahib magana cikin sigar jan hankali domin kuwa ya lura bata taba soyaiya ba,a hankali a hankali harya dinga janta da zance harta sake dashi,nan da nan ya dinga sakata dariya sai gashi tun kafin yatafi taji ya kwanta mata arai kasancewar sa mutum mai barkwanci, maisata nishadi.
bai dade sosai ba yace zai tafi, kasancewar tafiyar akwai nisa,sai a lokacin takira masa Nabiha suka gaisa,dazata tafi yadauki 5k yabata, Nabiha tayi masa godia sosai, sannan tatafi, ita kuma Mawahib suka qarasa tattauna wa sannan ta futo zata rakashi,sunzo get nafarko ya kalleta yace"to Amarya ta,zan tafi,sai yaushe kenan?"

Kalmar daya fada ta amarya ta, itace tasa Mawahib dariya,har dimples dinta suna futowa, adede lokacin musa megadi ya budewa Ashraf get yasako hancin motarsa ciki,dasu yafara cin karo,tun daga nesa ya hangota tana yiwa wani qato murmushi, lokaci daya yanemi annurin fuskarsa yarasa,ko gama daidaita parking baiyi ba yafuto daga cikin motar ya nufi get na biyu,fuskar nan tasa a murtuke, Mawahib data dago daga dariyar datake lokaci daya tayi ido biyu dashi, mamaki ya kamata,kode Yaya Captain ne yadawo? to ai kuma idan shine yadawo dole zata sani,da tuni qofar gidansu ma yacika da jama'ah, to meyasamu Yaya Ashraf yayi irin wannan daure fuskar?gaba daya saiya koma mata Yaya Captain sak.
Chapter 7 · 0% Book details