← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 68

Sashe 15

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana zuwa falon yaga babu kowa sai qarar TV datake yi,zama yayi acikin daya daga cikin kujerun falon yayi tagumi hannu bibbiyu tareda zubawa tv ido,amma azahiri ba kallon yakeba,ya lula ne cikin duniyar tunani, saida yagama tunani yaga bashida mafita sannan yasaki ajiyar zuciya, yajuya gefensa anan yaga wata yar madedeciyar brezia akan kujera, ya qarewa breziar kallo ya yatsina fuska,yasan aikin Mawahib ne,ya kalli qoqon breziyar yana tunanin yanzu boobs dintane yake cika duk wannan qoqon? bazai iyuba, saide in cuko take,duka duka nawama take dazata saka wannan? dama duk ciko ne,za'a bawa dan'uwan sa fake,shikuma Ashraf duk ya rangauce jiyake abubuwan ne (😲🙊)

Adede lokacin Mamy tafuto daga dakinta taga Captain yana kallon brezia,mamaki ya kamata meyake damunsa ya zauna shi kadai anan yana tunani?

Cikin sauri taqaraso wajansa ta zauna tace"Captain meyake faruwa ka zauna anan kana tunani?"

Shiru yayi yakasa bata amsa,harta fitar darai ba zaiyi magana ba, sai can kuma yace"Babu komai"

Mamy tayi shiru tana tantama aranta tabbas akwai damuwa,akwai abinda yake damun Captain, tajuya ta kalli breziyar Mawahib data sameshi yana kallo, ta qwala mata kira....

Tana daga cikin dakinta ta amsa tafuto da sauri,tana sanye cikin riga da wando,sai hula mai girma data saka akanta, kwata-kwata baka ganin baiwar dogon gashin kanta, wandon na jeans ne sai kuma rigar yar qarama mai launin ja,hips dinta yacika wandon taf... sai rawa sukeyi, cikin sauri Captain yadauke idonsa daga kanta.

Mawahib tana qarasowa falon ganin Captain a zaune tayi tunanin Ashraf ne,shiyasa tad'an saki ranta tayi murmushi har dimple dinta suna futowa tace"laa Ya Ashraf yaushe kashigo?"

Binta yayi da kallo cikin ransa yace"dama tana murmushi?"(🤔)

Kafin yayi magana Mamy tace"banason shashanci Mawahib,dauke wannan abar daga anan...yayun nakima har gobe kin kasa ganesu"

taqarasa maganar tana yi mata nuni da breziyar ta dake gefen Captain,sai a lokacin Mawahib tashiga taitayinta,tanajin furucin Mamy tasan cewa toba Yaya Ashraf bane, Yaya Captain ne,nan take tashiga hankalin ta,tasa hannu ta dauki breziyar ta sum-sum takoma cikin dakinta.

Mamy ta kalli Captain tace"muje daki?"

Babu musu ya daga mata kai,tatashi tayi gaba shikuma yabiyo bayanta har cikin d'akinta, suna zuwa ta zauna abakin gadonta shima ya zauna, ta kalleshi dakyau, cikin sigar lallashi tace"meyake faruwa? wani abunne yasake ya faruwa kuma?"

Bude bakinsa yayi zaiyi mata magana amma saiya kasa,saboda raunin da zuciyarsa tayi,ahankali yadora kansa akan kafadarta,babu wata-wata yasaki wani irin kuka (😳🙊🙆🏻‍♀️)

Gaban Mamy yayanke yafadi, ta tabbatar akwai babbar matsala, Captain da kuka? yaushe rabon dataga yana kuka? zata Iya cewa tun suna yara

Ajiyar zuciya ta sauke tadora hannunta akan lallausar sumar kansa tafara shafawa, sannan tamaida hannunta kan gadon bayansa tafara bubbugawa alamun lallashi, batace dashi uffan ba, saida tabarshi yayi kukan, yaji sauqin rad'ad'in dayake damunsa, sannan tad'agoshi daga kafad'arta tace"fad'amin meyake faruwa?"

"Anty Ma-my....su Daddy ne sukace zasu saka mana rana jibi,nikuma banason auren"

Mamy ta lumshe Idonta tabude, sannan tace"yanzu Captain banda shagwa6a kawai saboda bakason aure saika fara kuka?meyasa bakason auren?,ko akwai yarinyar dakake so?"

Cikin sauri ya girgiza kansa sannan yace"ni babu yarinyar danakeso Anty Ma-my"

Mamy tace"to meyasa?"

Duk da gabansa yana faduwa hakan bai hanashi baiyana mata gaskiya ba,may be zai samu shawarar dayake nema a wajanta,kai tsaye yadago kansa ya kalle ta sannan yace" SABODA INADA AURE"

Cikin sauri Mamy tace"What...?"

(Ina ganin ikon Allah ni Amina😂
kowanne irin matsayi abokiyar shawara zata koma bayan Aryan yagano itace sirikar tasa? 🤔

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Taredashedar biya ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub ✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 19&20*

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Captain Aryan yayi shiru yana kallonta ganin yanda ta tsorata takuma d'auki zafi akan maganar,to inaga Momy kilishi Kuma?

Cikin tashin hankali Mamy taci gaba da fad'in"innalillahi...to garin Yaya hakan tafaru? meyasa kayi hakan Captain?"

Ahankali Captain yafara yimata bayani tiryan-tiryan yanda abubuwa suka faru harya gama sannan yace"ni bansan Yaya zanyi da Momy ba"

Mamy tayi firfita da hannunta alamun garin yafara yimata zafi tace"Hasbunallahu wani'imal wakeel, toshi mahaukacin inane zaiyi ma aure babu sanin iyayenka?"

Captain Aryan yayi shiru yakasa bata amsa

ganin yayi shiru hakan yasa ta fahimci bashida amsar dazai bata, tasaki ajiyar zuciya tace"wannan ba maganar daza'a yi shiru bane,maganar aure aita wuce wasa,zanje In samu Yaya kilishi Infada mata komai"

Cikin sauri Captain yace"a a Anty Ma-my,kada kisake yin wani laifin a wajanta, zan fad'a mata"

"to Ashraf yasani ne?"

"A a ban fad'a masa ba"
tace"toka sameshi kafad'a masa,kuje kusamu Daddynku da Yaya kilishin kufad'a musu komai "

Cikin gamsuwa ya girgiza mata kansa alamun amsawa, sannan yatashi yafuto daga dakin itama tabiyo bayansa gaba daya jikinta yayi sanyi,qwaqwalwar ta tatsaya cak tarasa gane tunanin me zatayi....

******

Abba yana zaune afalo yana ganin labarai,ya kalli Mamy yace"kiramin Ruqayya"

Mamy tatashi tashiga d'akin Mawahib a lokacin tana zaune akan sallaya tana karatun qur'ani, Mamy ta kalleta tace"kizo"

Saida takai qarshan ayar datake karantawa sannan tarufe qur'anin tafuto, tana zuwa ta zauna cikin ladabi tace"Abba gani"

Alhaji Isah Yadauki remote yarage qaran tv sannan yace"gobe muke shirin saka ranar ku keda Ashraf,Ina fatan de babu wata matsala ko?"

Kafin Mawahib tayi magana Mamy tace" Alhaji matsala ta nawa kuma? nifa dakun bar wannan maganar tazauna tajira Nabil din har zuwa lokacin dazai shirya"

Abba ya gyara zamansa sosai Yajuya yana kallon Mamy yace"saboda me? shi jinin nawa ne bakya so 'yarki ta aura kinfi son taje ta auri d'an d'an'uwanki?"

"bahaka bane Alhaji"

Cikin zafi Abba yace"to menene Maryam?tunda munkira yarinya jiya kuma ta amsa mana da bakinta tanaso to meyasa zaki dauko wata maganar kuma?"

Mamy tace"Alhaji, kaida kanka kasan cewa uwar yaron nan bata qaunar hadin nan,tunda Mawahib take cikin gidannan banta6a ganin Yaya kilishi tayi mata kallon arziqi ba,tayaya ne inaji Ina gani zan bari adauki yata qwalli daya akaita wajan Yaya kilishi bayan nasan cewa idan akwai wadda Yaya kilishi ta tsana a duniya to baiwuce nida Mawahib ba?"

Abba yace"Okay to yanzu hukuncin da muka zartar nida Yaya Alqali shi zaki warware kenan saboda kina taqama Ruqayya 'yarki ce?"

Mawahib tanajin haka idonta yaciko da qwalla,bata ta6a ganin Mamy da Abba suna sa'insa ba,sai gashi akanta hakan tana faruwa,ahankali tatashi tabar wajan takoma dakinta tana share hawaye

Mamy ta kalli Abba tace"Amma wanne irin hukunci ne wannan?,bayan kunsan abinda yake faruwa saboda me zaku hada aurensu? nide Alhaji bana maraba da wannan auren,idan kuma kuka dage sai kunyi tozan tattara kayana nabar muku gidanku"
Tana fadin haka ta miqe zatabar wajan.

Abba yace"to aikuwa dagake har Yaya kilishi,baku Isa kuhanamu abinda mukai niyya ba,idan kuma zaku fara toga wajan nan"

******

Da daddare suna d'akinsu,Ashraf sai waya yake da abokansa na wajan aiki yana fada musu very soon zai zama ango

Captain yana zaune agefen gado yana kallonsa, saida yabari yagama yin wayar sannan yayi ajiyar zuciya yace"Ashraf"

Ashraf dayake tsaye yana danna waya yadago yace"ya'akayi?"

Cikin damuwa Captain yace"magana zamuyi"

Mamaki yakama Ashraf,yadawo kusada Aryan ya zauna sannan yace"meyake faruwa? Ko wani abune yakema ciwo?"

Captain ya girgiza kansa yace"Ash...inada damuwa,narasa yanda zanyi inyi magana dasu Momy,but nayi maganar da Mamy, tace insameka muyi magana dakai sannan muje mufad'awa su Momy komai"

Ashraf yace"meyake faruwa? fadamin "

Cikin damuwa yace"Ash nifa anbani mace..."

cikin rashin damuwa Ashraf ysce"nasani ai,koba Asalamiyya ba?"

Captain yasaki dan qaramin tsaki sannan ya lumshe idonsa yabude yace"inama maganar serious kana min zancen wata Asalamiyya ni banma san yarinyar nan ba,Ina nufin inada aure Ash"

Cikin sauri Ashraf ya kalleshi yace"kana hayyacinka kuwa?"

Captain Aryan ya kalli Ashraf cikin damuwa yace"da gaske nake,anbani mace"

Cikin sauri Ashraf yace"to Aryan kode kafara shan wani abu ne bansani ba? tayaya zakace min kanada aure in yarda? yaushe kayi aure? kuma a'ina?"

Cikin sanyin jiki Captain Aryan yace"niba ni nayi ba,qaqaba min akayi,har yanzu bansan yaya yarinyar take ba,shi kansa wanda yamin auren bansan ko waye shiba"

Ashraf yace"mekake san cewa?"

Captain Aryan ya kwashe komai tun daga farko har qarshe ya fadawa Ashraf, sannan yaci gaba da cewa"bawai damuwar haihuwa ce tasa nake tunani ba Ash,wannan maganar auren ne,bansan ta'ina zan fara yiwa su Daddy maganar ba,nikuma gaskiya banda ra'ayin yin mata biyu,shiyasa nashiga damuwa,idan nayi shiru hakan yana nufin zasu sake daura min aure da Asalamiyya,bayan itama waccen yarinyar bansan yaya take ba,kaini yanda banason kowacce yarinya ma inde nasake had'uwa da mahaifinta banason damuwa gaskiya zan sakar masa 'yarsa...."(🙆🏻‍♀️)

Lokaci daya gumi ya wanke fuskar Ashraf,cikin sauri yasaka hannunsa ya goge sannan ya doka tagumi hannu bibbiyu(🙉)
Yayi shiru yakasa magana.

Captain Aryan yaci gaba fa fadin "kuma ni gaskiya bazan Iya tunkaran Momy da wannan maganar ba,kuma banason su sake liqa min wata yarinyar, gaba daya narasa yanda zanyi da raina,Ash... inaji araina dama banzo gida ba,kwata kwata wannan zuwan nawa bashida dadi,komai ya lalace min, kamar a film nake ganin komai yana faruwa akaina"
Ya qarasa maganar sannan shima yayi tagumi hannu bibbiyu kamar yanda Ashraf yayi.

Har zuwa lokacin Ashraf yayi shiru yakasa magana,shi kansa daba shine hakan tafaru dashi ba,gabansa faduwa yake, toshi kuma Aryan din yaya yakeji kenan?

Cikin rashin qwarin gwiwa Ashraf yace"tunani na yatsaya cak,bansan ma yaya zamuyi ba, amma abinda yafi kawai mu fadawa Daddy gobe,shidin yad'anfi Momy sauqi "

Captain Aryan yadaga kansa alamun amsawa sannan yasamu yacire tagumin da yayi yajuya ya kwanta tareda rufe idonsa badan yanajin baccin ba.

******
Chapter 15 · 0% Book details