← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 68

Sashe 52

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsawon sati daya Mawahib ta dauka Hajiya kilishi tana bata kulawa,acikin kwana bakwai dinnan kullum saita shiga cikin ruwan dumi haka bata aikin komai Hajiya kilishi tahana,zuwa kwana bakwai dinnan tagama warkewa ras,babu abinda yake mata ciwo,saide duk lokacin data tuno irin gumurzun da sukai itada Yaya Captain saita ji tsoro yasake kamata,idan ta tuna yana Abuja har wani nishadi takeji.

Hajiya kilishi Kullum saita gwada kiran wayarsa, amma bata shiga wayar tana kashe,haka Alqali Shima yakira yakira yaji shiru.

A6angaren Ashraf kuwa yafi kowa shiga damuwa saboda rashin samun Aryan awaya,idan yazauna yayi shiru ko agida ko awajan aiki maganar Aryan dince take fadowa ransa lokacin dayake cewa zamu tunkaresu, komu kashe ko akashe mu,idan ya tuno wannan furucin nasa saiya ji qwalla tacika idonsa.

Har yanzu bai fadawa kowa ga inda Aryan yatafi ba.
Haka sukaci gaba da nemansa har tsawon sati biyu, amma babu labarin Captain Aryan.

Alokacin Mawahib takoma part din Mamy tana rayuwa acikin dakinta,tsawon sati biyun nan tayi tunanin Yaya Captain zai kirata yaji awanne hali take ciki, amma taga shiru bai kirata ba,tunani tafara Anya kuwa soyaiyar dayake kuka yake fada mata yana sonta Anya da gaske ne? yasanar da'ita zaiyi tafiya amma wacce irin tafiya ce zatasa yakasa kiranta!?

ta dauki wayarta ta kirashi akaro na biyu tun aurensu,saide tana kira taji wayar akashe.

Haka tayi haquri tabari har zuwa yamma tasake kira nanma taji waya akashe, mamaki ya kamata Anya Yaya Captain lafiya kuwa? tasan cewa baya kashe wayarsa,cikin damuwa tafuto daga dakinta takira Yaya Ashraf tace"Yaya Ashraf yau tun safe Ina kiran wayar Yaya Captain amma bana samunsa"

Ashraf yayi shiru yana tunani to Mawahib sai yau takira Captain kenan,gyara muryarsa yayi yace"may be baida caji ne,zan kirashi zuwa anjima idan munyi magana saina fada masa ya kiraki"

Tace"to shikkenan"

Ta ajiye wayar jikinta yadan fara sanyi.

Hajiya kilishi kuwa ganin sati biyu shiru Aryan bai kirasu ba,kuma idan sun kirashi basa samunsa,hakan yasa hankalinta yatashi,da farko tayi tunanin saboda abinda yayiwa Mawahib ne yasa yakashe wayar yaqi kunnawa harsai sun huce,daga baya kuma dataga shirun yayi yawa daga nan tasan cewa akwai matsala.

Da daddare suna zaune da Alqali ta kalleshi tace"nikam Alhaji shirun Yaron nanfa yayi yawa babu waya babu wata magana qwaqwqwara akan ahaka"

Alqali yace"nikaina abun yafara damuna, yau satinsa biyu kenan, dazu munyi magana da khaleed da Isah, Isah yace zaije Abujan yagano to nahanashi zuwa saboda yanayin aikinsa, sai muka yanke zamu tura Ashraf yaje yagano mana ko lafiya.

Hajiya kilishi tasaki ajiyar zuciya yace"yawwa,amma shirun ai ya'isa haka,ko a wayar wani ai yakamata yakira mu idan tasa wayar ce bazai budeba"

Bayan kwana biyu Mawahib tana kwance a dakinta sai juyi take tana so tayi bacci amma kuma takasa, ko Yaya ta lumshe idonta shi take gani, kuma tasan rashin baccin nata baya rasa nasaba da yanda Yaya Captain din yasabar mata da kwanciya a jikinsa, wayarta tadauka tasake gwada kiran wayar Captain Aryan,taji waya a kashe,mamaki yasake kamata, shekaran jiya Yaya Ashraf yace zai masa magana, jiya ta wuni tana kira wayar a kashe,yauma haka.

Tashi tayi tanufi dakin Mamy tana zuwa tazauna jagwab akusa da'ita, Mamy ta kalleta tace"kekuma lafiya kikazo zaki sani agaba kifara min wannan jarababban kukan naki?"

Cikin damuwa tace" Mamy ba kuka zanyi ba, Kingani kullum idan nakira wayar Yaya Captain bata shiga,shekaran jiya nakira shi, jiyama, yauma haka,Mamy ke kunyi waya ne?"

Jikin Mamy yayi sanyi tace"Mawahib ai Captain yau sati biyu da kwana biyu kenan wayarsa a kashe,nikaina tun ranar daya tafi nake kiransa amma bana samunsa,babu ranar da zatazo tawuce ban kira Captain ba,tun tafiyar sa da kwana biyar danaji wayarsa a kashe jikina yabani ba lafiya ba,to babu wanda nafadawa saboda kada na tada hankalin iyayensa"

bakinta tabude cikeda damuwa sannan tasaki wani irin numfashi tatashi tafuto daga dakin kamar an tsikare ta, Mamy tabita da kallo cikin tausayawa dan da alama tunda Mawahib tafara nuna damuwa akan Captain haqiqa tafara sonsa ne.

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

Mawahib tana barin dakin Momy takoma dakinta tazauna a gadon tafara tura masa saqo Kala Kala,sannan taci gaba da kiran wayarsa, takira wayar har babu adadi, amma bata sameshi ba.

Har yamma tana kiran wayarsa amma shiru,daganan kuma jikinta yayi sanyi, gabanta yafara faduwa, tatuna lokacin dazai tafi, tatuna kalaman sa a gareta lokacin dayake fada mata cewa zanyi tafiya me nisa,bansan yaushe zan dawo ba, bansani ba zan dawo dinma kokuma bazan dawo ba, amma inaso kisani Ina sonki...
duk abinda kike buqata karki tambayi kowa ki tambayi Ashraf,koda bana raye ki kalleshi, kisa aranki kamar ni kike kallo ki yafemin....

tana gama wannan tunanin gabanta yayanke yayi wata irin faduwa,jikinta yafara karkarwa,a fili ta furta "Ina yatafi?"

Cikin sauri ta dauki wayarta takira Nusaiba matar Captain Habib abokinsa wanda sukaje gidansu suka kaimusu ziyara.

Tana dauka cikin tashin hankali ko tsayawa batayi sun gaisa da'ita ba tace"Aunty Nusaiba,dan Allah inaso ki turomin number Abban mufid zan tambayeshi naji Yaya Aryan ko lafiya muna kiran wayarsa bata shiga, koda yaushe a kashe"

Cikin mamaki Nusaiba tace"kamarya? Mawahib wai bakisan antura Captain Aryan wani daji zasuyi yaqi ba?"(🙆🏻‍♀️)

tanajin haka taqame a zaune tareda sakin wayar tata tafadi qasa,gabanta yayanke yafadi,hawaye yafara zuba daga idonta, tadora hannunta aka tasaki wani irin ihun kuka tace"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...."

Mamy datake kallo afalo, cikin sauri ta miqe tsaye tace"yau naga takaina yarinyar nan kode tahadu da matsalar aljannu ne?"

tatashi da sauri zata nufi dakin Mawahib Hajiya kilishi da mama Sadiya dasuka jiyo ihun nata suka fado cikin falon cikin sauri,Hajiya kilishi tace"Maryam Mawahib qonewa tayi ne da ruwan zafi?" (🙆🏻‍♀️)

Mamy tace"tana dakinta,nima Ina nan najiyo ihun nata"

gaba dayansu suka saka kai cikin dakin Mawahib,har yanzu hannunta yana kanta tayi baza-baza da gashinta tana kuka kamar mahaukaciya.

Mamy tace"Mawahib menene?, me aka miki?"

Cikin kuka tace"yaya Captain ne..."

Cikin sauri Hajiya kilishi tace"yakiraki ne? meyace miki?"

Cikin kuka tace"wai antura shi yaqi...,dama yacemin qila bazai dawo ba yatafi kenan...,Mamy dan Allah kice masa yadawo wallahi yanzu inason mijina zanyi masa duk abinda yakeso"(😭)

Hajiya kilishi tanajin haka ta jingina da bango tafara silalewa qasa zata zauna.

Cikin tashin hankali Mamy tace"yaqi kuma?"

(Sorry Mawahib 😥🙏🏻)
Mutara zuwa yammah🙏🏻

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/15, 4:20 PM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

*13&14*

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Mama Sadiya tace"ai bamuga ta zamaba kamata yayi a fadawa su Alhaji atashi tsaye da Addu'ah in saukar Alqur'ani za'a masa ma sai ayi, ko kwanakin baya dasuka tura shi ai yana Samun damar kiran waya kota minti daya ce"

Hajiya kilishi data silale awajan ta zauna tayi shiru kamar bata cikin hayyacinta, duk maganar da Mama Sadiya tayi kokadan bata jitaba, Mamy tacewa Mawahib "to ai Addu'ah zaki masa yanzu tunda de har anji inda yatafi"

tajuya ta kalli hajiya kilishi "Yaya kiyi haqiru,in Allah yayarda Captain yana cikin qoshin lafiya"

Cikin sanyin jiki Hajiya kilishi tace"rannan yacemin ankashe abokin aikinsa awajan yaqin....ina tsoro kar'akashe shi Shima "
tafadi hakan hawaye yana zuba daga idonta .

Mawahib tanajin haka tasake fashewa da kuka tadora kanta akan qwiwoyinta,sai yanzu ne take nadamar abubuwan datake masa abaya,sai yanzu ne take dana sanin meyasa takasa nuna masa soyaiya?

Fita sukai daga dakin Mamy da Mama Sadiya suka ruqo Hajiya kilishi datake ji kamar bazata Iya taka qafafunta ba,compound suka hadu da mazan gidan kowannensu yadawo daga wajan aiki,cikin mamaki Alhaji khaleed yake cewa"meyake faruwa ne?"

Mama Sadiya ta kalleshi "Alhaji yanzu Mawahib take cemana wai yaqi aka tura Captain tsawon wannan lokacin,gashi tunda yatafi Alhaji kana gani bamu ta6a Samun wayarsa ba"

Alhaji Isa dayake tsaye da brief case a hannunsa yace"yaqi? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, amma Captain yayi shiru yakasa fada mana? bari nakira Yaya"

Yadauki wayarsa yakira Alqali,yace"Yaya kana inane?"
Alqali yace"Ina tareda Ashraf zai shirya yaje Abuja"

Alhaji Isah yace"basai yajeba Yaya,kudawo gida akwai matsala"

Alqali yanajin haka suka juyo zuwa gida, afalon Hajiya kilishi suka tararda duka mutanan gidan banda Mawahib.

Ashraf yanemi waje ya zauna, Alqali ya kallesu yace"meyake faruwa? yanaga ana gogewa kilishi gumi?"

Alhaji khaleed tace"yanzu muke samun labari awajansu wai Mawahib tace musu antura Captain wajan yaqi"

Cikin sauri Ashraf yadago kansa ya kalli surukin nasa, Yaya akai Mawahib tasani?
tayi waya dashi ne?
Tayaya akai maganar tafita?

Alqali yanemi waje ya zauna yace"to akwai matsala kenan,to aini yanzu nake shirin tura Ashraf Abuja yaje yagano ko lafiya,toda ace yajema dada wannan mummunan labarin zai dawo kenan"

Alhaji Isah yace"idan munje masallaci anjima sai muyi magana da liman asaka shi cikin Addu'ah"

Mama Sadiya tace"Abban Mawahib nida cewa nayi mezai hana ko sauka ce ayi?"

Ashraf da kansa ke qasa yadago kansa ya kalleta yace"Mama nasa anayi masa sauka duk sati tun lokacin danaga yayi kwana biyar bai kirani ba"

Alqali yace"yafada maka maganar yaqin ne?"

Kansa ya sunkuyar yace"muna tare dashi aka masa waya lalle lalle yatafi Abuja dasafe, akwai abokin aikinsa dayake jagorantar sauran Sojojin ankashe shi,shine sukace kada ya6ata lokaci yaje yamaye gurbin wancen,naso nasanar daku tun ranar daya tafi, to amma yace nayi masa alqawari kada nafada muku saboda kada hankalinku yatashi"

Hajiya kilishi tanajin inda aka tura Aryan wani hawayen yazubo mata, shikkenan shima qila kashe shi zasuyi.
Chapter 52 · 0% Book details