← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 68

Sashe 21

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alqali dayake babban mutum ne Kuma Wanda yake mu'amula da mutane sarai yagane halinda Alhaji Sammani yake ciki,shikuma da hankalin sa bazai iyu yahada dansa aure dawani dangi na kilishi ba,shima kansa haquri yake da'ita tayaya zai sake qoqarin hada iri dasu?(😳🙊🙆🏻‍♀️)
abinda yasa ya amince mata da auren Asalamiyya afarko ma saboda tabar Ashraf ya zauna da Mawahib lafiya shiyasa Shima yace ya amince Aryan din ya auri Asalamiyya,amma yanzu tunda ubangiji yayi hukuncinsa yanda yakeso sai abar maganar Asalamiyya,Yara kuma suje gidajen su su qarata, acan saisu daidaita kansu.

Ashraf yanajin abinda Alqali yayanke yayi qasa da kansa yana tunani,shide Dama Mawahib yakeso, to Aryan ya aureta,maganar ta tariga ta wuce,amma Nabiha de baya sonta,tunda yake da'ita kallon qanwa yake mata, bai ta6a tunanin aurenta ba,Kuma yasan ta'inda zai 6ullo mata cikin ruwan sanyi zai sallameta.(🙆🏻‍♀️)

Alqali ya Kalli maqocinsa daya zama mutum mutumi zaune, sannan ya Kalli amininsa yace"ga abun saka Rana nan, ga mahaifin Nabiha nan, kusaka musu ranar daya dace, tunda su wadancan mutum biyun anriga an daura"

Nan take sukai abinda zasuyi, aka tsaida ranar auren Ashraf da Nabiha,sati biyar Masu zuwa,Ashraf yanajin haka yatashi yafice yabar falon cikin rashin damuwa saboda yasan abinda yagama qullawa aransa.
Alhaji khaleed yakira Mama Sadiya yabata umarnin takawo musu abinci,Nan take tasaka hijabin ta takawo musu abinci,already Hajiya kilishi takawo musu lemuka da ruwa,zata juya tatafi Alqali yace"dauki wannan goron kije ki rabawa dangin ki da sauran yan'uwa, nasaka ranar Ashraf da Nabiha ne"

Mama Sadiya taji maganar banbarakwai,Ashraf ba Mawahib za'a bashi ba? ganin mutumin daya Bata umarnin bawanda zata tsaya jayaiya dashi bane, Hakan yasa ta dauki goron tareda cewa "Allah ya tabbatar da Alkhairi"

Bayan tafita Alhaji Bala abokin Alhaji Ma'aruf,shine Yazuba musu abinci, sukaci su kasha kowa yana farinciki, Alhaji Ma'aruf yasaka hannu a aljihunsa yadauko rafar kudi dami daya,wadda zata Kai kimanin dubu Dari, yabawa Alhaji khaleed yace"Kudin sadakin Ruqayya ne,Wanda abokina gashinan a zaune Alhaji Bala shine yabiyawa Aryan, amatsayin sa na waliyinsa"

Alhaji khaleed ya kar6i kudin tareda godia,Alhaji Ma'aruf ya Kalli Alqali yace"inaso zanyi magana da Maryam da mijinta kafin muwuce"
Alqali yadauki wayarsa yakira Abba yace"inason ganinka kaida maryam"
Bayan wasu min tuna suka shigo shida Mamy amma idonta yayi jajir har yanzun kuka take, zama sukayi, Alqali ya kalleta yace"Maryam kukan ne har yanzu?"

Cikin kuka Mamy tace"yaya wannan mutumin ya cutar dani,Kuma ya dauki yata yamata aure babu sanina, bayan baisan wahalar taba, baisan cintaba baisan shanta ba, baisan Yaya take rayuwa ba"

Alqali yayi murmushin manya yace"to ayi haquri mana,Maryam shekara da shekaru ai ya kamata ace kin yafe masa haka ko?"

Alhaji Ma'aruf da jikinsa yayi sanyi yace"hakane Alhaji, haqiqa nime laifi ne awajan ta,acikin Zamana da Maryam zan'iya cewa nine na cutar da'ita,ashekarun baya banida wata sana'ah data wuce fashi da makami,da'ita nake cinyarda Maryam da mahaifiyata wadda ta Ruqayya taci sunan ta, kafin Allah yamata rasuwa,har Allah yabawa Maryam ciki ta haihu na sakawa yarinyar sunan mahaifiyata,bayan haihuwar ne Maryam ta kamani Ina waya taji duka sirri na,munyi tashin hankali da'ita, tace na daina nace wannan sana'ar tawa babu fashi, wannan dalilin ne yasa tace tona zaba kode in daina sana'ah nadena ciyar dasu da haramun mu zauna nida ita da yarmu, kokuma na sauwaqe mata, alokacin idona ya rufe da kudi, hakan yasa nace na zabi sana'ar fashi akansu, daga ranar Maryam ta dauke Ruqayya, bansake sanin Ina sukeba, saide number ta itace de bata sauya ba,lokaci zuwa lokaci Ina kiranta amma bata taba dauka, haka na haqura nadena kiranta,har kawo wannan lokacin Ina Nan Ina sana'ah ta tafashi da mamaki nariga nazama shugaba, kwanaki munje gidan wani Alhaji munyi masa fashi ban biya yarana kudin da suke so ba, wannan dalilin ne yasa suka hademin kai suka kawomin hari zasu kasheni, shikuma Captain Aryan yatemake ni, tunda naga dan mutane yana qoqarin rasa ransa akaina, daga ranar nayi tir da halina,naji na tsani kaina saboda Koda nake harkar fashi na niban yarda da kisan kai ba, bayan nabar asbiti naje duk wata dukiyata da nasan cewa ta fashi ce nakaita gidan marayu, gidan da zan'iya tunawa Kuma Natura musu kudin su tareda neman yafiyar su,a yanzu na daina wannan dabi'ar ta sanadin danku,sanadin danku na shiryu nazama nagari, yanzu Iya kudina na halak nake rayuwata dashi,wannan dalilin yasa ban nemi Ruqayya ba, saboda ban Dena fashi ba, idan na nemeta da haramun din zanci gaba da ciyar da'ita, Kuma nasan Maryam batason haka,yanzu da ubangiji ya nufeni da shiryuwa gashi nazo har gida na nemi yata amatsayinta na matar aure"

Dukkannin mutanan falon sukai shiruuuu Bayan sungama jin dalilin mutuwar auren Mamy,wannan ne dalilin dayasa taqi nuna musu mahaifin Mawahib kenan tsawon wannan lokacin.

Alkali yayi ajiyar zuciya yace"ikon Allah,Allah Mai yadda yaso,Allah de ya nufa Kaine zaka haifi Mawahib ba qanina ba, saboda auren ta na farko anan gidan muke da'ita,muna Zaman mu yau dadi gobe babu dadi Har na fitar da Ashraf da Aryan qasar waje karatu, to a wannan lokacin ne suka samu matsala da me dakina kilishi,alokacin Bana Gari munje meeting din Alqalai Abuja,to maganar gaskiya ni kaina shedane Maryam tanada haquri, to ranar ankaita maqura hakan yasa taciwa matata mutunci tarama abinda aka mata, to daga Nan qanina Alhaji Isah yamata saki daya,a ranar tabar gidan Nan tatafi maiduguri,Bayan nadawo nasamu labari nayiwa Isah wankin babban bargo, nasashi agaba mukaje maiduguri, muka basu haquri, sai mahaifanta suka bamu haquri cewa bazata koma ba, haka muka dawo gida duk jikin Isah yayi sanyi,Bayan tsawon watanni bamuji labarin taba,sai daga baya suka sake haduwa da Isah anan yaganta da yarinya, tafada masa tayi aure amma sun rabu da mijin,anan Isah ya nuna yanason tadawo dakinta saboda tsawon wannan lokacin bai sake aure ba,Maryam tace bazata aure shi tabar yarinyar taba, shikuma yayi mata alqawari zai riqe yarinyar kamar yarsa ta cikinsa, Isah ya sameni da maganar Nima na amince, to wannan ne dalilin dawowar ta gidan Alqali Akaro na biyu,gata han har yanzu muna tare"

Alhaji Ma'aruf yace"ikon Allah,dama can Allah ya qaddara saboda samun Ruqayya ne yasa tashigo cikin rayuwata ba"

Yajuya ya Kalli Mamy da kanta yake qasa yace"Maryam kiyi haquri, ki yafemin, sannan akwai kadarorinta dasuke wajena wanda nasiya mata da kudina na halak dakuma Wanda mahaifiya ta tabata kafin tamutu, idan komai ya Lafa zanje Abuja muyi magana da'ita, amma Dan girman Allah ki yafemin ki manta baya"

Mamy batace masa uffan ba, sai Abba ne yayi ajiyar zuciya yace"babu damuwa Alhaji Ma'aruf, Allah yayafe mana baki daya"

Gaba daya falon suka amsa da "Amin"
Daga Nan sukai shirin tafiya, suka sake musabahar rabuwa, gaba dayansu mazan suka futo domin yimusu rakiya, Mamy Kuma ta wuce part dinta, suna zuwa get nafarko adede lokacin direban dayakaisu Mawahib Airport yadawo, Alqali yasashi yasake daukansu Alhaji Ma'aruf suma yakai su Airport din domin tafiyar su jihar Kebbi.

******

Acikin jirgi suna zaune hankalin Captain yanakan window,tunani yake aransa yanzu shine aka hadashi da wannan jaririyar,shikkenan daga taimako taimako yazame masa masifa,?
Yatuna lokacin da suke zancen aurensu shida Ashraf har yana fadawa Ashraf cewa tayaya ne zaiyi aure baiyi komai ba a wannan ranar kamar wani kidahumi?
Shide yasan bazai ta6a neman wannan yarinyar da sunan mu'amular aure ba,ba ajinsa bace,bazai ta6a sunkuyar da kansa awajanta ba har abada bare har hakan yakaisu ga wata mu'amula ta aure,yanzu ta tabbata Kenan shine kidahumin,tunda gashi ga matar tasa amma saide kallo.

Wata zuciyar tace dashi idan hakan tafaru ma aiba haihuwa zakayi ba,saikasha magani sannan ne zaka gwada ko Allah zai baka haihuwar,idan kuwa saboda Mawahib zaisha magani gara ya tabbata babu haihuwa.(🙆🏻‍♀️)

kukan datake ne yadawo dashi daga dogon tunanin daya Lula,cikin tsawa yajuyo ya kalleta yace"kokimin shiru kona wanka miki mari...stupid"

Tsit,Mawahib tayi shiru, ita kanta jitayi ta nemi kukan tarasa Sai jikinta dayake karkarwa saboda tsawar daya mata.
Wanda yake zaune agaban kujerarsu yaji tsawar tayi yawa hakan yasa yajuyo ya kallesu, to ganin suna kama hakan ya tabbatar masa da cewa may be qanwar sace,danhaka baice komai ba Yajuya yaci gaba da karatun jaridarsa.

Suna sauka tabiyoshi abaya idanunta harsun fara kumbura saboda kuka,yana hango Sojojin dasuke jiran saukar sa kamar yanda ya musu text Yafada musu yanufi inda suke,suma suna ganinsa suka Sara masa, daya daga cikinsu yayi sauri yabude masa motar,ganinsa tareda mace yasa itama suka bude mata daya gefen tashiga,mamaki ya kamasu ganin ogan nasu tareda mace,Kuma tafiyar tasu kamar babu Shiri,babu jaka babu kwalliya gashi fuskar ogan nasu a daure, basu ga yana fara'ah ba bare a tambayeshi aji ko sunyi suruka ne.

Ahanya ma baice dasu uffan ba,sojan dayake Jan motar ne ya kalli Captain ta madubi yaga fuskarsa a daure yana kallon gefen titi, Yajuya yaga Mawahib itama kanta yana kan window, wannan ne Karon farko da tazo Abuja,amma tashin hankali yahanata kallon garin yanda ya kamata,Sojan ya daure yayi gyaran murya sannan ya Kalli Captain Aryan yace"Oga zamu wuce barrek ne kokuma muwuce gidanka?"

Saida yayi maganar gida sannan Yatuna lokacin dasuke fira da Ashraf yana nuna masa hadaddan gidan daya gina Har yana cewa yaso ace da matarsa zasu fara shiga,meyasa qaddarar sa take zuwa masa ajuye? meyasa yanda ya tsara rayuwar sa Bata zuwa masa daidai? yanzu duk yanda yakeji da sabon gidan Nan nasa hakan yana nufin tareda Mawahib zasu fara shiga Kenan? gashi ya debe komai nasa daga barek yamaida gidansa Dama yanda ya tsara shine yana dawowa yasauka asabon gidansa, cikin taqaici kamar Wanda aka qwato maganar daga bakinsa yace"gida"

Sojan da yayi masa tambayar Wanda harya fidda rai zai samu amsa cikin sauri Yajuya kan motar suka nufi sabon gidan Captain Aryan.

Dayan Sojan dayake zaune a kujerar me Zaman banza shine ya turawa wasu daga cikin Sojojin su text,sannan yamaida wayarsa cikin aljihunsa.
Chapter 21 · 0% Book details