← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 68

Sashe 51

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin jiki Mamy ta 6oye damuwarta, saboda kar mutanan gidan suyi tunanin wani abu,tace"A a Yaya,Captain yamin text ne yace inzo indubata"

Cikin tsananin mamaki Hajiya da bata kalli inda wayarta take bama bare taga saqon da Captain yaturo mata na sallama tace"kamarya kizo? to ina yatafi?"

Mamy tace"anyi masa kiran gaggawa ne awajan aikin su"

Cikin 6acin rai Hajiya kilishi tace"zancen banza zancen wofi,ya za'ai yatafi yabar yarinya tana wannan ihun kukan?"

Bata jira amsar Mamy ba tatura dakin suka shiga atare,tun kafin su qarasa gadon sukaci karo da wandonta daya cillar dashi qasa,ga rigarta daya yaga acan gefe kusa da bedsheet din daya cire,Mawahib tana ganin Mamy tasaki wani irin kuka.

Hajiya kilishi kuwa tana ganin bedsheet din dayake qasa duk gashinan jini ya 6ata shi, ga idanun Mawahib sunyi jajir saboda kuka,saita dora hannunta akanta tasaki kuka, Mamy ta kalleta tace"haba Yaya kidena kuka mana"

Cikin kuka Hajiya kilishi tace"dole nayi kuka Maryam,wannan rashin imanin har ina?"
Mamy ta qarasa wajan Mawahib ta zauna ta rungume ta tace" ya'isa, yi shiru, kukan ya'isa haka"

Cikin kuka tace"Mamy zan mutu,"

Wannan Kalmar da Mawahib tafada itace tasake sa Hajiya kilishi fashewa da kuka, sai jijjuya kai take cikeda tausayi, Mamy ta dagata zata kaita toilet,anan taga jallabiyar Captain dinma datake jininta itama jini ya6ata ta,cikin sauri Mamy ta runtse idonta, takama jallabiyar tacire,Hajiya kilishi tayi sauri tawuce toilet tahada mata ruwan zafi.

Mamy Kuma takamata tace"tashi muje kishiga cikin ruwan zafi"

Cikin hawaye tace"Mamy bazan Iya takawa ba"

Hajiya kilishi ta qaraso da sauri suka kamata su biyun, suka kaita toilet, sannan Mamy ta sakata cikin ruwan zafi, tana shiga cikin ruwan tasaki wata qara zata tashi, saboda wanda Yaya Captain yasakata bekai wannan zafi ba, Mamy ta maidata ta koma tazauna, Hajiya kilishi ta goge hawayen idonta tace"duk yanda akai Aryan bai sakata acikin ruwan dumi yanda ya kamata ba saboda shi dama baya son ruwan zafi, gani zaiyi itama zafin zai mata yawa"

Mamy tace"toya za'ai Yaya,ai sai haquri"

Saida suka sauya mata ruwa sau uku,sannan suka kamota suka futo,Hajiya kilishi ce ta riqeta Mamy Kuma tasake gyara gadon sannan suka kwantar da'ita daga gefe,ahankali Mamy ta tsugunna ta bude qafafun Mawahib taduba wajan sannan ta miqe tsaye tace"dole sainayi mata dinki Yaya"

Hajiya kilishi tace"dinki? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ina ganin ikon Allah ni kilishi...."
saita saki kuka.

Mamy tace"Yaya kidena kukan nan kada mutanen gida suji"

Cikin kuka tace"ji na nawa Kuma Maryam? yanda ya haiqewa yarinyar nan waye acikin gidan nan zaice baiji ihun kukan taba? Aryan baya hayyacinsa,inajin maganin maza yasha"

Mamy tace"babu wani magani Yaya, tunda kikaga haka gardama ta masa,inda ta tsaya koda zataji ciwon bazai kai har hakaba,tayayane zata nunawa soja itama me qarfi ce?, bari inje daki in dawo"

Mawahib tanajin yanda suke tattauna wa,hawaye ne kawai yake zuba daga idonta.

cikin kuka Hajiya kilishi ma tafuto daga dakin tawuce part dinta, Mamy tabita da kallo kamar cewa akai Captain din yakashe Mawahib,ta girgiza kanta tatafi part dinta da sauri.

Hajiya kilishi tana zuwa falonta tazauna a kujera tadafe kanta tana share hawaye tareda ajiyar zuciya.

******

Abba daya dawo daga masallaci yanzu, ya Kalli Mamy ganin tana hada wata allura yace"meyake faruwa ne?"

Cikin damuwa tace"Alhaji yarinyar nan taji ciwo ne sosai,zanyi mata dinki"

Cikin sauri yace"subhanallah...kode zamu tafi asbiti ne?"

Tace"A a babu matsala zanyi mata komai, idan munje asbitin ma zasu dinga surutu ne suyi tunanin rape ne akayi mukuma muka 6oye"

Cikin sanyin jiki yace"yanzu tana wanne hali?"

******

Alqali da Ashraf suka nufo part dinsu, Alqali yana tambayar Ashraf "meyake faruwa kazo gida haka sassafe kabar iyalinka?"

Ashraf yace"naraka Aryan Airport ne"

Alqali ya kalleshi yace"eh naga yaturo min saqo dazu,yatafi Abuja,Allah yakaishi lafiya, shiyasa jikinka yayi sanyi kenan? Ashraf anya rayuwa zata iyu dahaka kuwa? inde dan'uwan ka zaiyi tafiya saika saka damuwa aranka? Ina Abuja Ina kano? idan kanason ganinsa basai kaje ba?"

Ashraf ya Kalli mahaifin nasu,shi kadai yasan inane Captain zai tafi,shi kadai yasan Ina aka tura qanin nasa.
Meyasa Aryan yabashi ruqon wannan babban alqawari?
tayaya zaiyi shiru da bakinsa shi kadai ba tareda iyayensu sun san cewa yaqi aka tura shi ba?
Dan Kar Daddyn nasu ya fahimci wani abu hakan yasa yasaki ajiyar zuciya yace"to Daddy insha Allah"

Alqali yace"yawwa kokaifa, Allah yayi muku albarka"

Kafin Ashraf ya amsa suka shigo dakin anan suka tarar da kilishi tana zaune tana share hawaye, gaban Ashraf yafadi kode taji labarin Ina Aryan yatafi ne?

Cikin sauri suka qarasa wajanta Alqali yace"Kilishi meyake faruwa?"

Cikin muryar kuka tace"Yakashe ta"

Ashraf yazaro idonsa waje(😳)
Yace"wa aka kashe?"

Tace"Mawahib,Aryan yayi mata kaca-kaca babu dadin gani,Ashraf Ina imanin dan'uwanka yatafi? yarinya qarama yakasa binta a sannu tun cikin dare muke jiyo ihun kukanta babu damar dauki,nabar su acan itada Maryam zata mata dinki bazan Iya ganin wannan a zabar ba"

Alqali ya zauna yace"dinki?"

Hajiya kilishi tace"dinki za'a mata,yarinyar duk ta rame dare daya abun tausayi ido duk ya kumbura"

Ashraf ya sunkuyar kansa qasa yana sosa qeyarsa,saboda maganar ta masa nauyi.

Alqali yace"amma yasan da wannan danyan aikin yatafi Abuja yabarta? Wanne irin aiki ne za'a yi da bazai jira gari yawaye yabawa yarinya kulawa ba kafin yatafi?"

Hajiya kilishi tace"ni ban yarda ma kiransa akai ba,nasan halinsa sarai kawai guduwa yayi saboda shi yasan abinda ya aikata"

Alqali ya girgiza kansa yace"Allah yarufa asiri,kitashi kihada mata tea saiki kai mata tasha"

Hajiya kilishi tatashi tsaye tanufi dining dinsu tana fadin"zaizo yasameni,wato shiga me qarfin doki"

Ashraf yasake yin qasa da kansa yana sosa kansa,yasan cewa yana magana zata rufeshi da fada tace ai tare suke qulla komai,bayan kuma hakanne tare suka qulla din. (😂)

******

Mamy da Mama Sadiya ne adakin wadda tazo yanzu saboda itama tun ihun farko tasan cewa gidan ba kalau ba, itace take miqowa Mamy abinda take buqata, ita
kuma Mamy tana mata dinkin,duk da Mamy tayi mata allura kafin afara dinkin hakan bai hanata jin zafi ba, saida mama Sadiya ta riqeta,Mamy tayi mata dinkin cikin nutsuwa.

Zuwa wannan lokacin Mawahib kasa kukan tayi, saide hawaye dayake zarya a'idonta,bayan angama Mama Sadiya tace"bari naje nahada breakfast sai akaiwa Abban Mawahib dinma tunda ke kina nan"

Mamy tace"to shikkenan,ai yau ba zanje asbitin bama,zanyi musu waya"

Mama Sadiya tace"ai abun da tausayi, bazai iyu abarta ita kadai ba"
tafadi hakan tana ficewa daga dakin.

Mamy ta Kalli Mawahib tace"kidena kukan mana"

Mawahib tana jinta tayi shiru,amma bata daina hawayen ba,saboda ita kadai tasan metake ji ajikinta.

Hajiya kilishi tashigo da tea a hannunta tace"kungama dinkin Maryam?"

"angama Yaya,gata nan kwance"

Tea tabata tace"toga tea me kauri nahado mata zataji dadin cikinta insha Allah"

Mamy ta kar6i tea din tace"to Yaya angode"

Hajiya kilishi ta Kalli Mawahib datake zubar da hawaye tace"sannu Mawahib,yarinyar nan kin adda azaba,kiyi haquri kidaina kuka,shima duk inda yaje zaizo yasameni"

Mamy ta Kalli Mawahib tace"kici gaba da kukan, idan ruwan hawayen naki yaqare sai naga da wanda zakici gaba da kukan,tun asuba kina kuka anyi lallashi anyi ban haquri kinqi kiyi haquri,kowa da haka yafara saide na wata yafi na wata, amma bazakiyi haquri ba kamar akanki aka fara kar6a budurci?"

Hajiya kilishi tace"um um Maryam...,kibarta tayi kukanta,irin wannan abun de, kuma acikin wannan gida,to akanta aka fara,saboda nima ko ubansa bai ganamin wannan azabar ba" (🙊)

Mamy tayi shiru ta dauki tea din tabata,a hankali ta kar6a tafara sha,kad'an tasha zata ajiye Mamy tasata ta shanye shi duka.

Ashraf ne Alqali yazo yaga jikin Mawahib din,dakin yaturo yashigo shida Ashraf, idon Ashraf yasauka akansu, yagansu sun sata atsakiya ga qafafun ta a bubbude ,kansa yadan sosa sannan ya sunkuyar da kansa yace"Anty Mamy Ina kwana"

"lafiya Ashraf,ya Nabiha?"

"tana nan kalau wallahi, yame jikin?"

Mamy ta Kalli Mawahib tace"gata nan sai langwai take jiki da sauqi,dauketa kakaimin ita dakina dan Allah,sai a rufe nan din"

Cikin sauri ya girgiza kansa yace"A a"

Hajiya kilishi ta kalleshi tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi Mawahib dince bazaka dauka ba?"

Kansa ya shafa yaqi cewa komai,Hajiya kilishi tayi ajiyar zuciya tace"ai shikkenan"

Mamy tayi murmushi tace"to Ashraf Mawahib datana da aure dabata aure ai qanwar ka ce"

Abba ne yayi sallama yashigo dakin ya shirya tsaf zai fita aiki, yagaida Hajiya kilishi, Ashraf ma ya rissina ya gaishe shi.

ya Kalli Mawahib yace"sannu Ruqayya"

Daga masa kanta tayi alamun amsawa amma batace uffan ba.

Abba ya Kalli Mamy yace"zanfita aiki Maryam, saina dawo"

Tace"to Alhaji Allah Yakiyaye hanya, ko zaka dauki Mawahib mukoma can?,Ashraf yaqi daukarta"

Abba ya kalli Ashraf yayi murmushi ya qaraso ya dauketa cak, suka futo daga dakin,Mamy ta Kalli Mawahib datake goge hawaye tace"bazaki daina wannan qananun kukan ba? aida kinyi shiru ganin ubanki ne yasa zakici gaba da kukan"

Hajiya kilishi tace"kai Maryam sai fada kike yiwa yarinyar nan dame zataji ne?"
ta kalli Abba tace"isah kaimin ita dakina,zanyi jinyarta"

Abba de yana jinsu baice komai ba yayi murmushi yajuya yakai Mawahib har cikin dakin Hajiya kilishi, sannan suka futo daga dakin.

Mamy tawuce dakinta tayi breakfast sannan tawuce kitchen tadafa mata farfesun kifi,takai mata,alokacin tana kwance da apple a hannunta tana karya ahankali,farfesun tabata taci sosai, sannan ta kalleta tace"babu inda yake miki ciwo bayan wajan dinkin ko?"

Idontane yacika da qwalla amma taqi basu damar zubowa tace"bacci nakeji kuma nakasa yi"

Mamy ta jinjina kanta, sannan tafuto taje part dinta tahado allurar bacci tazo tayi mata, ko minti biyar bata sakeba, wani irin wahalallan bacci ya dauketa.

Ta dade tana bacci har azahar, Hajiya kilishi data idar da sallah adakin tajuya tana kallonta tana azkar,hannunta ta daga zata fara Addu'ah taji Mawahib tana cewa "Yaya Captain zan mutu....kayi haquri,wayyo!!..."

tafadi wayyo din da qarfi tareda firgita tabude idonta.

Cikin sauri Hajiya kilishi ta ajiye carbin hannunta sannan tafara yimata magana tace"Mawahib..,kin tashi ne?"

Cikin idonta dake cikeda da bacci tace"um...." tareda lumshe idonta taci gaba da baccin.

Hajiya kilishi tasaki ajiyar zuciya tana girgiza kanta, lalle yarinyar nan tasha wahala a hannun Aryan,har cikin bacci ma yarinya tana firgita wacce irin rayuwa Aryan ya daukar wa kansa?
Mutane suna cewa ko awajan aiki ana cewa danta Aryan jarumi ne, bata tabbatar da hakaba sai yanzu,haqiqa taga jarumi ganin idonta(😂)
Chapter 51 · 0% Book details