Sashe 17
Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read
Batare daya jira amsar Alhaji Isa ba yakashe wayar,kai tsaye wajan Abokinsa Alhaji Bala ya nufa,yafada masa abinda yake faruwa,daga nan suka wuce Airport domin tahowa kano, tun ahanyarsa ta tafiya Airport yake kiran Mamy,amma koda wasa bata dauki wayar ba, haka ya dinga kiranta har zuwa lokacin da jirgin su zai tashi sannan ya haqura da kiran.
******
"sister Maryam kina gani tun dazu ana kiranki amma kinqi dauka, kiyi haquri ki dauka mana ko marasa lafiya ne suke kira"
Mamy tayi ajiyar zuciya tace"Sister Bilkisa ba kowa bane yake kira Ma'aruf ne,me Ma'aruf zai fadamin? banason Jin muryarsa ko a mafarki"
Sister Bilkisa tayi murmushi tace"Sister Maryam nasanki da haquri amma bansan meyasa har yanzu kikaqi yafewa Ma'aruf ba,shekara nawa? yakamata ace komai yawuce, ki dauki wayarsa kiji dalilin kiran"
Cikin damuwa Mamy tace"bazaki ganeba,damuwar danake ciki ma ta'isheni basai nahada data Ma'aruf ba,mazajenmu sunacan agida suna kokarin saka ranar Mawahib dina da yaron Yaya kilishi,kwata kwata banason wannan hadin,bansan Yaya zanyi inhana faruwar hakan ba,amma muddin suka saka ranar nan to nima zan saka mana rana nida Mawahib saide su nememu surasa a gidan, maiduguri zamu tafi"
Sister Bilkisa tayi murmushi tace"kitafi kibar gidan aurenki saboda wata kilishi? haba Maryam karki bada matan maiduguri mana, kishiya bata koreki daga gidan miji ba sai wata can facala ce zata koreki? babu inda zakije zama daram a gidan Isah,ita de yarinya yanzu ne zaki samo mata hanyar guduwa, amma fa idan kinso"
Cikin mamaki Mamy tace"kamarya? mekike nufi?"
Sister Bilkisa tayi murmushi tace"kidauki wayar Ma'aruf kiji menene yake tafe dashi, daga nan kiji Ina yake da zama yanzu? dazaran yafada miki to ki hadawa Mawahib kayanta takoma wajan ubanta,hakan ai zaifi"
Mamy tayi shiruuu tana nazari akan maganar abokiyar aikin ta, sai can tace "kumafa hakane, ni kwata kwata ma bankawo wannan tunanin arainaba,saide Ina fatan ace zuwa yanzu Ma'aruf ya sauya halaiyarsa"
Tana gama wannan maganar ta kirashi,adede lokacin Alhaji Ma'aruf da Alhaji Bala saukarsu kenan a Airport din malam Aminu suna kokarin tare taxi,yana ganin kiran nata yayi sauri yadauka, cikin damuwa yace"Haba Maryam, me yayi zafi haka? amma ko babu yarinya a tsakanin mu ai zanci darajar kasancewata musulmi ki dauki wayata kiji abinda yake tafe dani ko? kinsan halin dana shiga saboda haka? Inda nasan gidan da kike aure wallahi da tuni kin ganni "
Cikin damuwa Mamy ta lumshe idonta sannan ta bude tace"Ma'aruf inajin ka meyafaru?"
Kai tsaye yace mata"ina Ruqayya? Inason ganinta"
Cikin mamaki tace"au dama kadamu da'ita ne?"
Alhaji Ma'aruf ya runtse idonsa, yace" Maryam, yanzu ba lokacin tone tone bane,inaso naga Ruqayya "
Mamy yace"Ina wajan aiki,Mawahib tana gida"
Alhaji Ma'aruf yacika da mamakin Mamy, har abada halinta mai kyau bazai canza ba,gashi de sunan mahaifiyar sa yarinyar taci, amma shi kai tsaye yake kiranta da sunan,amma gashi Maryam har wani suna daban tasaka mata,hakan yana nufin har yanzu tana ganin darajar mahaifiyar sa,tunda gashi ta kasa kiran sunan kai tsaye, yayi ajiyar zuciya yace"toki yi mata magana tahada kayanta gani nan zuwa"
Cikin mamaki Mamy tace"bangane ba"
Yace"idan mun hadu zanyi miki bayani,tahada kayan de zanzo har gida In dauketa"
Yana fadin haka yakashe wayar.
Sister Bilkisa tace"meyake faruwa kuma?"
Mamy tafada mata duk yanda sukai dashi, sister Bilkisa cikin mamaki tace"kode yaji labari ne za'a aurar masa da yarinya?"
Mamy yace"Ina zansani sister Bilkisa?amma bana tunanin haka gaskiya"
Sis Bilkisa tace"to ai zama bai ganki ba, ki kama hanya kije gidan, idan kunhadu dashi duk wacce za'a yi sai ayi"
Cikin sauri Mamy tace"to shikkenan"
Daga nan ta dauko jakarta, tacire dan qaramin hijab dinta na ma'aikatan asbiti, tasaka wani babban hijab me tsawo shima fari, sannan tanufo gida.
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼
******
Direban taxi yana zuwa inda aka yi masa kwatance ta waya yayi parking sannan yajuya ya kalli su Alhaji Ma'aruf yace
"Alhaji munzo"
Alhaji Ma'aruf yace"Okay nan suka kwatanta ma?"
Dan taxi yace"eh nan ne gidan Alqali"
Alhaji Bala yayi masa godia sannan yadauki kudi meyawa yabashi, bayan yatafi suka qarasa wajan Musa megadi Alhaji Ma'aruf yace"kashiga gidannan kace musu sunada baqi a waje"
Musa megadi yashiga ya'isar da saqon,nan take Alhaji khaleed mahaifin Nabiha yamiqe yabiyo Bayan Musa, yana zuwa ya gansu su biyu atsaye abakin get,yana ganin Alhaji Ma'aruf yaga kamar Mawahib atare dashi, Alhaji khaleed yamiqa musu hannu yace"baqin namu ne? sannunku da zuwa,ku qaraso mana,ku qaraso daga ciki..."
Alhaji Ma'aruf yace"to mungode"
Daga nan suka shigo cikin gidan, kai tsaye suka wuce part din Hajiya kilishi, har zuwa lokacin gaba dayansu suna nan a zaune,Hajiya kilishi kuwa takafa ta tsare tana so taga waye yayi mata katsalandan acikin rayuwar d'anta,Captain Aryan yana ganin Alhaji Ma'aruf yasaki wata irin ajiyar zuciya,Alhaji Ma'aruf kuwa cikin fara'ah yafara bawa duka mazan falon hannu suna gaisa wa, sannan ya zauna yamaida kallonsa ga Alqali ganin shine babba a cikinsu, yace"Alhaji kuyi haquri nasaku kuna jirana,ni Sunana Alhaji Ma'aruf,dan asalin jigar Kebbi,kuma nine wanda na aurawa 'yata Captain Aryan bisa shaidu da wakilai kamar yanda addini ya tsara,amma nayi hakanne badon komai ba saidon ganin nine silar dayasa yaron nan yashiga matsala,kuma inada tabbacin yata batazata ta6a yimasa gori akan batun haihuwa ba,amma...ina roqon ku da kuyi haquri kuyafemin, haqiqa nasan nayi kuskure,sannan yarinya ta na bashi ita halak malak, saide in shine yaga bata yi masa ba to zai Iya sauwake mata,amma amatsayina namai laifi Ina qara baku haquri amatsayin ku na iyayensa,idan har baku haqura ba to duk hukuncin dazaku min kuyimin inde zaku huce akan abinda na muku"
Alqali yayi shiru yanajin dogon bayanin da Alhaji Ma'aruf yayi,gaba daya sai jikinsa yayi sanyi,ada yayi niyyar yashiga qara tareda duk wanda yayiwa dansa aure ba tareda saninsa ba,amma bayan yaji bayanan mutumin sai yaji bazai Iya masa komai ba,yasaki ajiyar zuciya yace"to Alhaji Ma'aruf munji bayanin ka, kuma mungode, adade nayi tunanin ko duk abinda na mallaka zai qare to sai inda qarfina yaqare akan mutumin da yayi min auren d'ana, to amma bayan naji bayananka saina gamsu da maganganunka,haka ubangiji ya tsara masa,Allah yasa hakane yafi Alkhairi, yanzu Ina yarinyar take?"
Alhaji Ma'aruf yadauko wayarsa daga aljihu yace"bari nakira inji inane address din gidan sai muje daku a dauko yarinyar"(🙆🏻♀️)
Cikin sauri yadokawa Mamy Kira,bugu biyu Mamy data dawo daga wajan aiki tadauka, Alhaji Ma'aruf yace"gani akano, inane address din gidan"
Mamy tace"akawoka gidan Alqali,duk wanda ka fadawa yasan gidan"
Cikin tsananin mamaki Alhaji Ma'aruf yace"a a, gidan Alqali kuma? to ai Ina cikin gidan"
Yajuya ya kalli mutanan falon daduk suka zubo masa ido suna kallonsa yace"yanzu dan taxi yace mana nanne gidan Alqali, koba nan ne gidan ba?"
Ya qarasa magana yana kallon yan falon
Gaba dayansu sukace" Nanne"
Alqali ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"kafada musu suzo cikin gidan Alqali yanzu yanzu part din matar Alqali"
Alhaji Ma'aruf yacewa Mamy "to Ina cikin gidan Alqalin,gani ga mutanan gidan kuzo keda ita, Ina jiranku" yana fadin haka yakashe wayar
Mamaki yakama Mamy, kamarya suzo gidan Alqali? to Ma'aruf yariga yazo gidan kenan kome? waye yafada masa a gidan take?
Tadaga kanta ta kalli Mawahib datake tsaye a gaban tv tana qoqarin kashe kayan kallo, tana sanye cikin doguwar riga abaya mai kyau, tace"ke zomuje part din yaya kilishi"
Cikin sauri Mawahib tace"Mamy lafiya?, inaso ne inje gidansu Jiddah munyi waya tacemin zasu tashi sunkoma gombe dazama gaba daya"
Mamy tace"muje nace"
Babu musu tabiyo bayan Mamy suka tafi part din Hajiya kilishi,tun abakin qofar sukaga takalma dayawa hakan ya tabbatar wa Mamy mazan gidan suna ciki kenan, da sallama Mamy tashigo falon,Mawahib ma tashigo, gaba d'aya sai kallo yakoma kansu,cikin sauri Hajiya kilishi tatashi tsaye tace"Rainin hankali....idan an'isa in nutse anan,ni za'a rainawa hankali?"
Cikin tsawa Alqali yace"Kilishi meyake damunki ne?"
yajuya ya kalli Mamy dabai san dalilin zuwansu ba yace"maryam meyake faruwa?"
Kafin Mamy tabawa Alqali amsa Alhaji Ma'aruf yace"Alhaji ai itace wadda nayi waya da'ita yanzu,itace mahaifiyar 'yata Ruqayya wadda na aurawa d'anku Captain Aryan...."
Cikin sauri Ashraf yatashi tsaye yace"What....?"
Gaban Captain Aryan yayi wata irin muguwar fad'uwa,ya runtse idonsa afili ya furta "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,Hasbunallahu wa ni'imal wakeel...,ko ba'a fada masa wacece Ruqayya ba yasan Mawahib suke nufi tunda itace yarinyar Anty Ma-my"
Mamy tanajin furucin Alhaji Ma'aruf,saita tuna lokacin da Captain Aryan yake fada mata wani mutum yamasa aure da 'yarsa,ta tabbata de dolen dole sai yarta ta auri jinin Yaya kilishi, cikin tsananin damuwa tadafe kanta da hannunta (🤦🏻♀️)
Mawahib data gama rikicewa tana ganin abu kamar a film,cikin ranta tana fatan ace bade da'ita Ruqayyan sukeba, cikin rawar murya tace"Mamy meyake faruwa?"
Alhaji Ma'aruf ya kalleta, tsananin kamar datake dashi shine yasake tabbatar masa da cewa tabbas itace Ruqayyansa yace"Ruqayya nayi miki aure,na aura miki Captain Aryan nasan insha Allahu....."
Kafin yagama magana Mawahib takoma bayan Mamy da sauri ta rirriqeta,lokaci daya hawaye ya wanke mata fuska,jikinta yadauki rawa tafara girgiza kanta alamun rashin yarda
Hajiya kilishi ta kalli Mamy wadda har yanzu hannunta yana goshinta takasa dago kanta, cikin masifa tace"Maryam kinji dadi....wato dana nuna miki baza'a bawa Ashraf Mawahib ba saida kika koma kikai kutun-kutun kika liqawa Aryan ita, to billahillazi bazai iyu ba"
Tana fadin haka tanufi Captain Aryan wanda kansa yake sunkuye yanaji kamar a mafarki wannan abubuwan suke faruwa, tana zuwa takama hannunsa tatashe shi tsaye ta nuna masa Mawahib tace"gatanan saketa yanzu yanzun nan, maza yimata saki uku"(😳🙆🏻♀️)
Alqali dayake zaune yana ganin ikon Allah yayi murmushi ya kalli Captain yace"kai Aryan....dauki matarka kubar gidannan"
Mawahib tanajin wannan furucin tasaki ihun kuka ta qanqame Mamy tana cewa"Mamy zan mutu,wallahi banason sa,bagarama Yaya Ashraf dinba..."