← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 68

Sashe 59

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dare Captain Aryan yakoma gida tareda tarin kayaiyakin suna daya kawo mata,alokacin tana zaune afalo ta'idar da sallar isha'i kenan tana azkar,tana juyo qamshin turaren sa ta juya ta kalleshi tatashi da gudu tatafi zata rungume shi,rigar jikinta ya kalla wadda tayi mata kyau sosai anan yagane rigar daya siya mata a boutique ce yau tayi masa ado da'ita, cikin jin dadi yabude mata hannayen sa,saide kafin ta qarasa jiri ya debeta tazube awajan.

Cikin sauri yasaki ledar hannunsa yadauketa yasaka ta a jikinsa yafara tatta6a fuskarta yace"Honey...,Honey"

Yaji shiru bata amsa ba kuma fuskarta a rufe, cikin tashin hankali yasake ta6a fuskarta yace"Honey bude idonki"
nanma yaji shiru, cikin tsananin damuwa ya dauketa cak, ya futo yasakata a mota sannan yanufi asbiti cikin wani irin gudu.

(ga posting din safe Nan ayimin afwa yauba na yamma zan dan huta, nagode 🙏🏻)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Amnah El Yaqoub✍🏻[7/18, 10:14 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Asbitin dayake ganin likita nan yakaita,wata qwararriyar likita ta kar6eta, bayan taimakon gaggawa dasuka bata ta farfado,likitan ta dauki jininta da fitsarinta tatafi lab dashi.

Captain dake zaune agefe yakama hannunta yariqe yace"bakyajin komai ko?"

Kanta tagyada masa tace"banajin komai,dazun ma jiri kawai naji ya daukeni, sai dan zazza6i da nakeji"

Hannun nata yayi kissing yace"sorry..., zakiji sauqi kinji?"
Kanta tagyada masa alamun amsawa
Sannan ya sunkuya yasake kissing goshinta, yafara shafa kanta ahankali.

Likitan ce tashigo dakin tareda wani babban doctor, Captain Aryan yana ganinsa yatashi yabashi hannu suka gaisa, likitan ta kalleshi cikin farinciki tace"congratulation Captain,matarka tana daukeda juna biyu"

Mawahib dake kwance ta zaro idonta waje, cikin ranta tace ciki?

Cikin tsananin farinciki ya kalli doctor bakinsa a bude.
Doctor yayi murmushi yasake bashi hannu yace"masha Allah magani yayi kyau,Congratulation"

Cikin sauri ya girgiza kansa,wani irin hawaye yazubo daga idonsa,suna ganin haka suka fice daga dakin.
Juyowa yayi ya kalleta sannan yayi sauri ya goge hawayen idonsa ya zauna agefen gadon yadora bakinsa akan lips dinta yasakar mata kiss,tanajin yanda hawayen sa yake d'iga akan fatar idonta, ahankali tadora hannayen ta duka biyun a kansa tafara shafa sumar kansa, cikin sigar lallashi tace"yaya Capt..."

Cikin sauri ya rufe mata baki danashi yafara kissing dinta cikin nutsuwa,babu musu ta tafara maida masa martani,saida suka dauki lokaci me tsawo suna kissing junansu, sannan yazare bakinsa daga nata yace"nagode Honey,bansan da wacce Kalma zanyi amfani wajan gode miki ba, kingama min komai arayuwa,kinbani Kanki,rayuwarki,kulawar ki,bansan dame zan saka miki ba, kin zauna tare dani duk da kinsan cewa ba lalle ne kisamu Baby dani ba"
yafadi haka yana sake zubar da hawaye.

Cikin sauri ta goge masa fuskarsa sannan tace"kadena fadar haka,kaifa dan'uwana ne, kuma mijina,koda bazaka ta6a haihuwa ba zan kasance atare dakai har abada"

Cikin sauri yadaga mata kansa, sannan yadauki wayarsa yakira Ashraf, yana dauka yace"Ash..."

Ashraf yace"meyafaru kake kuka?"

Cikin sauri yace"Mawahib she's pregnant..."

Cikin tsananin murya Ashraf ya kalli Momy kilishi datake yiwa lil Aryan wanka yace"Momy Mawahib tasamu ciki"

Hajiya kilishi ta ajiye lil Aryan tasaki wata irin gud'a,tafuto compound din gidan tana fadin"Alhamdulillah....,Allah yabawa Babana lafiya"

Mamy da Mama Sadiya dasuke gyara kitchen saboda aikin suna da'aka yi, su naji mama Sadiya tafuto da sauri sunata farinciki, Mamy tayi murmushi batace komai ba, tana cikin aikin taga saqon Captain yashigo yana fada mata Mawahib tasamu ciki, wani murmushin tasake yi ta girgiza kanta tace"Allah ya sauketa lafiya"

tafuto daga kitchen din bayan ta qarasa aikin datake,anan ta tarar harda su Alqali a tsaye a compound din kowa yana maimaita magana daya.

Wuce su tazo yi Hajiya kilishi tace"Maryam dannaki fa babu zaman lafiya yakusa zama uba"

Mamy tayi murmushi tace"yaturomin text ya fadamin Yaya,Allah yasauketa lafiya"

Hajiya kilishi tace"Amin ya Allah,ai sai yakawo ta gida idan tagama laulayin cikin saita koma"

Ta kalli Ashraf yace"kiramin shi"

Alqali yayi murmushi yace"dakin barsu ai kilishi,shima zai Iya kulawa da'ita"

Cikin sauri Hajiya kilishi tace "a a Alhaji,Nabiha ma abinda yasa bance akawo taba saboda akusa take, amma wannan idan wani abu yasameta kafin muje ai komai yagama lalacewa"

Ashraf yabata wayar bayan Aryan yadauka, cikin farinciki yace"Ash..."

Cikin sauri Hajiya kilishi tace"nice Aryan,kanajina ko? kadauko Mawahib kakawo ta gida idan tagama warkewa saiku koma"

Gabansa ne yafadi yace"Momy gida kuma?,amma Momy she's fine fa"
Ya qarasa maganar kamar zai fashe da kuka.

Hajiya kilishi tace"Aryan haquri fa zakayi,laulayin ciki ai sai mace yar'uwarta,idan tanason dan abun sha'awa na marmari anan duk zamuyi mata koba hakaba?"

Cikin damuwa yace"Momy tuwo tafi so sai lemo,anan ma tanayi"

"tana laulayin ciki tana girki,tana kula dakai bazai iyuba,kaji abinda nafada ma"
ta qarasa maganar tana kashe wayarta.

Dafe kansa yayi da hannunsa yana salati cikin ransa, tayaya zai Iya rayuwa babu Honey?

har suka dawo gida jikinsa yana sanyaye,kasancewar dare yayi hakan yasa bata lura da yanayin dayake ciki sosai ba,sai washegari data gama bacci ta sauko qasa,ta ganshi ya zauna yana tunani,cikin jikinsa ta shige babu musu yafara shafa gadon bayanta.

Cikin kulawa yace"Honey kin tashi?"

Kanta tadaga masa sannan tasaka hannunta tadora akan kumatunsa guda daya tace"Baby meyake damunka?"

Cikin damuwa ya kalleta"Momy ce tace saina kaiki gida"

"gida kuma?,"

Kansa yagyada mata,bakinta taturo gaba tace"Gaskiya nide Baby um um,to tayaya zan dinga bacci bayan bakanan?"(🙈)

tafadi maganar cikin 6oye abinda yake ranta, saboda tafi son koda yaushe yana cikin yiwa shukarsa bayi.
maganar tata ta bashi dariya hakan yasa yayi murmushi,sai yanzu yagane dalilin dayasa takesan kasancewa dashi a kowanne lokaci,idan kuwa hakane yaji dadin abinda cikin nan yasata,Babynsa na cikinta ya kyauta wa babansa,haka kuma sai yanzu ne yasan dalilin cin tuwon ta.
yariqe fuskarta yace"toya zamuyi?mekikeso ayi yanzu?"

Cikin shagwa6a ta kalleshi"nide gaskiya saide muzauna acan hardakai"

Cikin sauri yabude bakinsa sannan yasaka dariya yace"Honey? ashe kuwa za'a samu matsala,kinsan meyasa nake cemiki Honey?"

Cikin sauri ta girgiza masa kanta.
Yadora kansa a kunnanta yace"saboda you're so sweet"

Cikin sauri tarufe fuskarta cikin kunya.
yadago kanta yace"zan nemi excuse idan anbarni saimu tafi gaba daya ko?"

Cikin sauri ta daga masa kai cikeda murna tasake rungume shi.

tunda Hajiya kilishi tayi masa maganar zuwan Mawahib take zuba ido taga shiru bai kawo taba har tsawon sati daya,acikin sati dayan daya qara kuwa banda shagwa6a Mawahib babu abinda yake, kasancewar itama batason tafiyar hakan yasa yayi biris da maganar Momy Kilishi,kawai sha'anin su sukeyi,Koda yaushe yana jiyar da'ita dadin datake so, saide duk lokacin dazatasha fruit kokuma wani magani shima bashi take yanasha duk da baisan na menene ba, shi kansa bayason tafiyar ta saboda shi kadai yasan meyake ji ajikinta,jiyake kamar zai rabu dawani sashin jiki nasa.

Saida sukai kwana goma bayan maganar Hajiya kilishi sannan suka shirya suka taho gida,ranar da sukazo part dinta suka fara zuwa,abinci ne agabansu ta zuba musu sunaci,Captain Aryan de sosai yakecin abincin sa,Mawahib kuwa kad'an takeci kana gani kasan batason abincin.

Hajiya kilishi ta kalleta tace"meyasa bakyacin abincin ne Mawahib ko bakya so?"

Cikin sauri tace"Momy cheese nakeso"

Cikin sauri Captain Aryan ya juya ya kalleta,cikin ransa yace yau kuma?

Mamy ce tayi sallama tashigo falon dawowar ta Kenan daga wajan aiki,tana ganin Mawahib tayi turus ta kalli hajiya kilishi tace"yaya yanaganta kalau kamar bame laulayi ba?naga tahada uwar qiba"

Hajiya kilishi tace"irin laulayina takeyi ai,nima lokacin danake laulayin su Ashraf kalau nake,zanci abinci na inqoshi,saide za6e, banida aiki saide inta za6ar abubuwa Inaci na kwadayi,itama gashinan yanzu daga zuwansu tace cheese takeso"

Mamy tayi murmushi tace"to Allah yaraba lafiya,bari insa driver ya siyo mata"
tajuya tafita,bayan sungama cin abincin zama sukayi Captain Aryan yadauki wayarsa yatura mata saqo, tagani tayi murmushi itama tamasa replay.

Suna musayar saqo Mamy tadawo da nbabbar ledar cheese gaba dayanta,Mawahib taja ledar tabude, sannan ta dauko guda daya tafara ci.

Captain Aryan yace mata "danbani"

Hajiya kilishi tace"karki bashi,yanzu haka a Abujan ma komai qwace mata kake kanaci"
Kansa ya sosa yayi shiru.

Mamy tayi dariya yace"Haba Yaya,yana qwace mata abunta shine zatayi wannan qibar? gashinan tana nema takamoni jiki"

Ashraf ne yashigo falon cikin farinciki yabashi hannu suka tafa yace"Boy kun qaraso kenan"

Captain Aryan yace"munzo tun dazu,Ina kabar wayar taka Ina kiranka baka daukaba"

Qyafta masa ido yayi,sannan yace"banga kiranba"

Captain Aryan yayi murmushi yasan cewa yanzu haka yana tareda matarsa,kuma hakanne domin kuwa yanacan dakin Mawahib inda Nabiha take zaune kafin ta zubar da wanka.

Zama yayi yafaracin abincin da suka rage, Mawahib ta gaida shi ya amsa,ya kalli Captain Aryan yace"amma zaka dade ko?"

Cikin sauri yace"no,da daddare zan wuce,zanbi jirgin qarfe takwas,na tambayesu amma babu damar hakan, akwai ayyuka dayawa"

Fira sukaci gaba dayi cikin farinciki, sannan Mamy tatafi part dinta,yayinda Hajiya kilishi taketa kallon Mawahib yanda takecin cheese kamar ba gobe,tatuna lokacin datake dauke da cikin su Ashraf haka Alqali zai sata agaba ya dinga kallonta tana faman cin gyada,ko ridi,saide duk lokacin data tuno baya tana sake jinjina wa irin qoqarin da Alqali yayi mata alokacin, saboda cikin yazo mata da jaraba,kullum suna daki itada Alqali suna abu daya,dasafe kafin yatafi aiki saiya yi mata zai fita,haka za'a dinga kiransa a kotu ana sanar dashi masu kawo qarafa suna jira(🙈).

Tasaki ajiyar zuciya tana fatan ace Mawahib nata cikin baisa mata wannan jarabar ba,saida taci cheese kusan guda biyar, sannan ta goge bakinta,ta dauke cheese zatakai kitchen din Hajiya kilishi ta kalli Ashraf da Aryan tace"bazakuci cheesenf ba?"

Ashraf yayi murmushi yace"A a,ci abinki Mawahib"
Hajiya kilishi tace"Ashraf kam nasan dama bazaici ba, amma shi de wannan dayan zaici, bashi qwaya daya kikai kitchen ki ajiye kayan ki"

Dariya Mawahib tayi ta dauki qwaya daya jal tabawa Captain Aryan,ganin qwaya dayan tabashi yasa ya harareta.
tana ganin hararar dayake mata tafara qoqarin maida abunta cikin leda(😂)

yana ganin haka yayi sauri ya qwace,daga nan suka fita shida Ashraf.
Chapter 59 · 0% Book details