← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 68

Sashe 13

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhamdulillah....anan nakawo qarshan free page's dina, duk meson cigaban littafin MAWAHIB, yabiya naira 500 kacal👌🏻

Yanzu kwamacalar tafara,akwai rikici agaba kala kala duk a gidan Alqali, koda kudinka saida rabonka 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

Insha Allah zaku dinga Samun posting biyu arana,wani lokacin kuma posting daya, kamar de yanda mukai daku a SHAHAAB, sai kunzo 🙏🏻

Zaki turo 500 ta wannan account din 👇🏻

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub✍🏻[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 78*

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Bayan sunfuto daga dakin kai tsaye wajan payment sukaje Alhaji Ma'aruf yabiya kudin komai harda na magunguna ta hanyar atm dinsa, sannan suka futo daga asbitin,Alhaji Bala ya dubi abokinsa yace"Alhaji Ma'aruf kana ganin abinda ka zartar kuwa babu matsala? idan mahaifiyar yarinyar tayi mata aure fa? sannan idan yarinyar tana soyaiya dawani kuma kai karaba wannan soyaiyar ai kamar da cutarwa aciki"

Alhaji Ma'aruf yace"ni ina ganin wannan ba matsala bane,koda RUQAYYA tana soyayya dawani dole zatayi haquri tabarshi ta rungumi wannan sojan,saboda shi d'a na halak dole zaiso mutumin daya taimaki mahaifin sa,zan kira MARYAM Infada mata abinda na yanke"

Alhaji Bala yace"to shikkenan Alhaji Ma'aruf,Allah ya shige mana gaba"

******

Kasancewar jirgi suka biyo hakan yasa cikin sauri suka qaraso asbitin,gaba daya mazan gidan ne suka taho cikinsu harda Hajiya kilishi datake kuka wiwi,Mamy ce kawai bata taho ba itada Mama Sadiya,amma dukansu sun taho.

Suna shiga asbitin d'aid'aikun mutane suketa kallonsu,ganin yanda Hajiya kilishi take kuka har lokacin babu tantama zakayi tunanin mutuwa aka musu.

Sojojin dasuke tareda Captain suna ganin zuwansu Alqali suka musu iso zuwa dakin da Captain din yake, suna shiga Hajiya kilishi ta rungumesu shida Ashraf din gaba dayansu tana kuka, gaba daya saita bawa mazan gidan tausayi.

Alqali yayi gyaran murya yace"Kilishi kukan ya'isa haka,tunda yana raye to Alhamdulillah,Allah zakiyi wa godia"

Yajuya ya kalli Sojojin yace"muje wajan likitan"

Cikin sauri suka juya suka rakasu har office din likitan,da Alqali da Alhaji khaleed da Alhaji Isah,su ukun dukansu suka shiga office din likitan,Bayan sun gaisa Alqali ya kalleshi yace"likita,mune iyayen yaron nan da aka kawo muku wanda yasamu harbi"

Cikin girmamawa likita yace"Sojannan?"

Alhaji Isah yace" qwarai shi,ya ake ciki ne dangane da jinyar tasa? shikkenan babu damuwa zamu Iya tafiya dashi yanzu sai acigaba da kula dashi a asbitin mu nacan?,kokuma zamu sake barinsa ne yasake warwarewa?"

Cikin mamaki Likita yace"ikon Allah,wai dama wancen mutumin ba shine mahaifinsa ba?"

Alhaji khaleed yace"wanne mutumi?"

Mamaki cikeda fuskar likita yace"mutumin daya kawo shi,nayi tunanin shine mahaifinsa shiyasa ma nayi masa bayanin komai"

Alqali yace"kai likita,mune iyayen Captain Aryan,kayi mana bayanin meyake faruwa"

Likita yayi ajiyar zuciya yace"wato abunda yake faruwa shine....."

Nan take yasake yimusu bayani kamar yanda yayiwa Alhaji Ma'aruf.

Lokaci daya gumi ya rufe Alqali,Alhaji Isah mijin Mamy yacire hular kansa yafara firfita da'ita,Alhaji khaleed ne ya dinga maimaita salatin Annabi a fili, sannan yasamu qwarin gwiwar yiwa likitan magana yace"yanzu likita menene abunyi? zamu Iya fitar dashi qasar waje ne a nema masa lafiya kokuwa akwai wani abu wanda zaku iyayi basai anfitar dashi ba?"

Likita yace"Alhaji no need ace anfitar dashi wata qasa saboda duk maganin dazai buqata munada shi anan qasar,sannan zamu dorashi akan magani idan yafara shan maganin lokaci zuwa lokaci yana mu'amular aure da matarsa to zai gani idan Sperm dinsa yazama normal kamar yanda yake abaya,idan har yadawo normal to zai Iya samun ciki da matarsa,idan kuma yaga yanayin Sperm din bai sauya ba,to dole zaici gaba dashan maganin sa"

Alhaji khaleed yace"likita Captain Aryan bashida aure,tayaya zamu gane ya warke idan yafara shan maganin sa yanzu?"
kai tsaye likita yace"saikuyi masa auren,kuma Ina baku tabbacin inde yafara shan maganin akan qa'ida kamar yanda nafada muku,to insha Allah bazai dauki dogon lokaci ba zai warke"

Alhaji khaleed yasaka gefen babbar rigarsa ya goge gumin fuskarsa, sannan yace"mungode likita,yanzu zamu Iya tafiya dashi ne?"

Likita yace"Why not?"

Daga nan sukai masa godia suka futo daga cikin office din jikinsu a sanyaye.

Daga waje Sojojin suka tsaya,su Alqali suka qarasa cikin dakin, Captain Aryan yana ganin yanayin jikinsu yasan cewa sunji komai, Alqali yanemi waje ya zauna, Alhaji khaleed da Alhaji Isah suna tsaye,Hajiya kilishi data kama yaranta ta riqe duka su biyun kamar za'a qwace mata su, cikin sanyin jiki ta kalli Alqali tace"Alhaji.....yana ganku jiki a sanyaye? lafiya?"

Alqali yayi ajiyar zuciya yace"akwai matsala kilishi,yaron nan yasamu matsala......"
nan take yabata labarin komai kamar yanda likita yafada musu.

Tun kafin yagama yimata bayani take hawaye harya gama,amma bai fada mata yanda sukai da likitan akan shawarar daya basu ta batun auren Aryan dinba,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta share hawayen idonta tace"hasbunallahu wani'imal wakeel,Ina ganin ikon Allah ni kilishi,wacce irin masifa ce wannan Alhaji?"

Alhaji Isah yasaki ajiyar zuciya yace"Yaya kilishi kiyi haquri,kowanne bawa baya Iya kaucewa qaddarar sa,Ina ganin kutashi muyi shirin tafiya kawai"

Adede lokacin shima doctor yashigo dakin, shida Ashraf sune suka fara qoqarin kamashi,cikin muryarsa kamar bayaso yace"zan'iya Doctor"

Dakansa yatashi kamar ba ciwo ne a jikinsa ba,suka futo yabawa Sojojin sa umarnin suwuce Abuja kawai,zai taho daga baya, cikin girmamawa suka sara masa, sannan suka wuce, sukuma gaba dayansu suka nufi Airport suka dauki hanyar dawowa gida

Tun kafin su koma gida labari ya Isa unguwar kowa yaji abinda yafaru,suna sauka kuwa sukaga mutane sun tattaru abakin get din gidan gaba dayansu ire-iren wanda yake yiwa Alkhairi ne idan yazo, sosai mutanan sukai musu jaje tareda addu'ar Allah yakiyaye gaba,sun dade a bakin get din, sannan suka samu nasarar shiga gida.

Agidan ma kai tsaye suka wuce part din Hajiya kilishi, Mama Sadiya da Mamy da Nabiha nan take sukaje sukai masa sannu,amma Mawahib bataje ba,suma su Mamyn dasukaje Hajiya kilishi ko d'ago ido batayi ba bare ta kalli inda Mamy take.

Tun safe dasuka zo Captain Aryan yayi shiru baya cewa um bare um um, saide in anyi masa Addu'ah Allah yakiyaye gaba yace Amin, daga haka babu qari, iyayen nasa sun lura yana cikin damuwa,sai suka dauki hakan amatsayin maganar rashin haihuwar sane take damunsa,abunda basu saniba shine maganar haihuwar kokad'an bata damunsa tunda ba cewa akai gaba daya har abada bazai sake haihuwa ba, yanasa ran shima zuwa gaba idan Allah ya qaddara zai iya haihuwa shima,maganar auren nan ce kawai take damunsa, yarasa wazai fad'awa yaji dad'i ko zai samu shawarar data dace.
tun saukar su Hajiya kilishi bata zauna ba,dakanta tadafa musu abinci shida Ashraf takuma hanasu fita ko nan da can,sai yamma Ashraf yaje dakinsu yayi wanka sannan yadawo falon wajan Aryan.

Ya zauna ya kalli Captain Aryan dayayi shiru kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, yace"muje daki kayi wanka?"

Kafin yayi magana Hajiya kilishi tace"bari inhada masa ruwan wankan a toilet dina saiya shiga yayi"
tafadi hakan tana shigewa cikin dakinta,Ashraf yabi bayanta da kallo tareda murmushi yajuyo ya kalli Captain Aryan yace"d'an autan Momy"

Captain Aryan baice komai ba Sai idonsa daya lumshe kawai

Batafi minti biyar ba tadawo tace"Ashraf rakashi yayi wankan"

Sai a lokacin ya bude lumsassun idonsa yace"zan'iya Momy"

Daga nan yatashi ya shige dakin nata,yana shiga yawuce toilet yacire rigar jikinsa zai fara wankan.

Hajiya kilishi ta dubi Ashraf dake zaune agefenta tace"dauko masa kayansa Ashraf"

Kafin Ashraf yatashi sai qara suka jiyo daga toilet din Hajiya kilishi
Cikin sauri Hajiya kilishi ta nufi dakinta tana fadin"Aryan lafiya?meyasa meka?"

Yana daga cikin toilet d'in cikin shagwa6a yace" Momy zafi ruwan...."

Ashraf yasaki d'an qaramin tsaki yafice daga dakin,yayi tunanin ma faduwa yayi shiyasa yashigo d'akin aguje(😂)

Hajiya kilishi ta dafe kanta da hannunta(🤦🏻‍♀️)
tace"Aryan anya hardakai akai training din aikin nan naku kuwa?"

Yanajin abinda tace yayi shiru, badan yaso ba haka ya runtse idonsa yashiga ruwan,cikin ransa yana jinjina zafi irinna ruwan.

Da daddare suna d'akinsu shida Ashraf,Captain Aryan yana zaune akan gado dagashi sai gajeren wando,wandon yanada laushi sosai hakan yasa mutum zai Iya ganin shacin komai(🙈)
Baqin gashin dayake faffad'an qirjinsa ya kwanta luf asaman farar fatarsa,Ashraf kuwa yana sanye cikin kayan bacci wata doguwar riga mai kyau.
Yazo bakin gadon ya zauna kusada Captain Aryan sannan yace"wai damuwar ce har yanzu? banajin dad'in yanda kake yawan tunanin nan Aryan,idan de magana ce akan haihuwa bagani ba, sai indinga haifo mana yaran"
Captain Aryan yayi shiru yana tunani,kwata-kwata ba wannan ne damuwar saba, tunanin aurensa yake baisan yaya zai fadawa su Momy ba.

Ashraf yaga yayi magana amma kamar ma Captain Aryan din baya tareda shi,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yaja fillo ya kwanta agefen Aryan din,Captain Aryan kuwa yanata tunani saida yadawo daga duniyar tunanin nasa sannan ya kalli Ashraf yace"yanaga kaima kayi shiru? tunanin me kake?"

Ashraf ya kalleshi yace"Ina tunanin abubuwan dasuka same mune dagani har kai cikin kwana biyun nan,kaiga qaddarar data sameka,nikuma Momy batason aure na da Mawahib,shekaran jiya fa anyi tashin hankali a gidan nan, inata kiran wayarka bata shiga,qarshe ma Daddy har marin Momy yayi"

Cikin sauri Captain Aryan yace"mari kuma? tome ta masa?"

Cikin sanyin jiki Ashraf yace"hakane,kayi haquri kayafemin nasa Daddy ya mari momy,amma yanzu dasauqi rashin lafiyarka yasa wancen rikicin ya kwanta,amma gaskiya Ina cikin damuwa,yanzu Momy bazata barni in auri yarinyar danake soba kenan?,wai ashe ba uncle Isah ne ya haifi Mawahib ba,Ina tunanin akwai abinda yafaru a gidannan wanda bamu saniba lokacin da muka fita karatu, kuma babu wanda yasanar damu, idan ba uncle Isah ne ya haifetaba waye mahaifinta to? yaushe Anty Mamy ta haifeta awani wajan kuma duk bamu sani ba?,amma ni koma waye ya haife ta inason ta ahaka"

Captain Aryan yayi shiru bayan yagama Jin labarin da Ashraf yabashi,to Mawahib ma dasuke gida daya Momy tatashi hankalin ta tace baza'a aure taba,inaga shi da ko yarinyar ma baisaniba?🤔

Cikin damuwa yasaki ajiyar zuciya sannan yace"naka mai sauqi ne Ash..."(😂)

Ashraf dabai fahimci me Captain yake nufi ba cikin sigar tambaya yace"kamarya?"

Kafin Captain Aryan yayi magana Mamy tashigo dakin bakinta daukeda sallama, suna ganinta suka saki murmushi, Ashraf yace"Anty Mamy kece?"
Chapter 13 · 0% Book details