← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 68

Sashe 35

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri tadawo hayyacinta,tasaka bayan hannunta ta goge hawayen,sannan tagyara zamanta,shiru sukai duka su biyun,kusan minti biyar sannan yaga sai ajiyar zuciya take, cikin aji kamar baison magana yace"kiyi shiru, keba matar soja bace?"

Cikin sauri ta kalleshi cikin ranta tana tunanin sunan daya fada mata, matar soja.

ganin tana kallonsa yasa shima yajuyo yasake fuskantar ta dakyau sannan ya Kalli cikin idonta mai kama dana mejin bacci yace"yes...kizama jaruma, kidena tsoro, ba komai akewa kukaba,lalle Anty Ma-my na haquri,haka take haquri da kukanki? bakece kike murna zakije gida ba? yanzu nabaki za6i guda biyu,koki zauna a gidan mij...mijin...mijinki, kokuma kano"
Yafadi sunan mijinki din a daqyar kamar yana shakkar fadar hakan, sannan yadauki handkerchief din daya ajiye mata ya dorashi akan cinyarta, yatashi yafice daga dakin gaba daya,Mawahib tabishi da kallon mamaki, dama yana doguwar magana haka?
gidan mijin ta?
Yana nufin yayarda kenan yanzu shine mijin?

tashi tayi tashiga toilet tayi wanka,tasake gyara kanta, sannan takoma kan gadon ta ta kwanta tayi shiru tana tunanin rayuwar aurenta, ita kuma tata qaddarar kenan Uwar miji bata qaunar ta,wayarta ce tayi qara taduba taga Mamy ce, saida tayi ajiyar zuciya sannan tace"Mamy"

Mamy tace"Na'am, ya hanya, kun sauka lafiya?"

Cikin sanyin jiki tace"lafiya kalau Mamy,munzo tun dazu"

Mamy tace"to Alhamdulillah,Allah yahuci gajiya,kidinga haquri de,Kici gaba da yiwa mijinki biyaiya,kina ganin de abubuwan dasuke faruwa,kuma kun tafi bamuyi sallama ba,dakin tafi da gumbar ki ai,nace Anty Kulsum ta aiko miki wata daga maiduguri,saide idan anyi sai abayar akawo miki"

Yatsina fuska tayi tace"wai Mamy maganin menene?"

Cikin basarwa Mamy tace"kawai magani ne,ko a barshi kar akawo?"

Cikin sauri tace"A a kikawo min, yanada zaqi sosai, ni dayan ma banasha"

Mamy ta girgiza kanta tace"kici gaba dasha yanada amfani,gobe qawata zatazo taganki, tare muke aiki da'ita anan daga baya sai suka dawo Abuja"

Tace"to Allah yakaimu Mamy"
Daga nan sukai sallama.

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

*******

Da daddare tasake wani wankan saboda yanayin period datake ciki,tafuto tashafa mai sannan tafeshe jikinta da turare Kala Kala,tasaka wata irin shedaniyar rigar bacci,wadda kake hango farar fatar jikinta,qirjin rigar bashida girma sosai hakan yasa tayi mata daidai madaidaitan nashanunta suka cika rigar,tagyara kanta sannan ta daure shi, tana tunanin ya kamata ace taje wajan wankin kai,batajin yunwa saboda yanayin damuwar datake ciki na Hajiya kilishi, saide ta samawa Yaya Captain wani abun marar nauyi,futowa tayi daga dakin Sai zuba qamshi take, tasauko tanufi kitchen,a lokacin yana kwance a doguwar kujera yadora computer asaman cikinsa yana browsing,baiga futowar taba sai qamshin ta yaji, kafin yadaga kansa harta shige kitchen, ko minti talatin batayi da shiga ba, tafuto hannunta daukeda plate wanda tadafa masa indomie da dafaffan qwai,yana daga kwancen tunda tafuto daga kitchen yazuba mata ido yana binta dawani irin mayen kallo, kwata kwata yakasa janye idonsa akanta,har itama ta tsargu da kallon nasa, cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa sannan ta qaraso gabansa ta ajiye masa plate din tace"gashi"

Computer ya ajiye sannan yatashi zaune ya Kalli abincin yace"banaci"

Cikin sauri takalleshi, yadaga girarsa daya yace"Anty Ma-my tasani, banacin indomie banacin dafaffan qwai, saide Ashraf..."

Cikin sauri tatashi tadauki plate din tace" bansani ba,zan dafa wani yanzu"

Captain Kam baiji meta ce ba, saboda gaba daya tunda tafara magana yazubawa dan qaramin bakinta ido yana kallo,saida yaga bata wajan sannan yadawo cikin tunanin sa,Yasaki wani irin numfashi yabi hanyar kitchen din da kallo,kasa haquri yayi, ahankali yatashi yabi bayanta zuwa kitchen din, yana zuwa ya tsaya abakin qofar kitchen din yaharde hannunsa a qirjinsa yana qare mata kallo,yanda take girkin birgeshi takeyi,tanayin komai a nutse babu sauri bare gaggawa, kasancewar dare ne yasa ba zatayi abu me nauyi na, Banana pancake tafara hada masa,tadauko Zuma ta ajiye agefe tana so idan tagama tazuba masa zuman akai.
kallonta yake har lokacin,fuskarsa babu fara a kamar de kullum,tunani yake meyasa duk lokacin datake kusa dashi yakejin komai yana masa daidai?(😲)
Baisan dalilin hakan ba,amma yana fatan ace ba sonta yakeba, kunyar Ashraf ma kadai ta isheshi, tayayama za'a ce sone? tayaya zai fara sonta? no kawai sabo ne(🥺)
Ajiyar zuciya yasaki,
kamar daga sama taji yace"dame zan tayaki?"

Cikin sauri tajuya a tsorace,bai damu da tsoratar tataba yatako ya qaraso wajanta yatsaya dab da'ita.
Lokaci daya ta rikice,yana ganin yanda hannunta yake karkarwa,cikin rawar jiki tace"nagama"

Tafadi hakan gabanta yana faduwa,zuman ta dauka zata zuba yasaka hannunsa ya kar6a, sannan yazuba son ransa,suka futo daga kitchen din, tana gabansa, yana bin bayanta idonsa akanta.

Suna zuwa falo bata zauna batawuce sama,wannan baqin halaiyar na Yaya Captain yanasa ruwan kanta yatsaya cak,yana ruguza mata duk wani kuzarinta,tana zuwa daki ta kunna esi sannan tashige cikin lallausan bargonta ta lumshe idonta.

Harta haye sama akan idonsa,saida yadena ganinta sannan yasauke numfashi tareda shafa sajen fuskarsa, yafara cin pancake din,yadauki wayarsa yakira Ashraf, yana dauka yace"kasamu kanka Kenan,shiyasa kasamu damar kirana"

Murmushi yayi yace"nasamu kaina bayan brother na ya ku6utar dani, Momy rigima,yakuka qare?"

Ashraf Yasaki dariya yace"kasan mene? Wallahi karka Kira Daddy,dan sunji komai, wayar nan a speaker Daddy yace nasaka, Kuma dukansu sunji yanda mukai dakai,wallahi kasa kallonsu nayi marar kunya kawai"

Cikin sauri yace"what? yasalam,shikkenan magana ta qare, amma Anty Ma-my de bata bata wajan ko?"

Ashraf yace"tana nan wallahi,to ya zasuyi? share kawai,yanzu de kafara murna munkusa zama Daddy's,Nabiha tanada ciki"

Captain yace"wow kace qwallo tashige...."
Gaba dayansu sukasa dariya.

Ashraf yace"Ina Mawahib,ka lallashe ta sosai, tasha kuka"

coffee din gabansa yasha kadan, sannan yace"yanzu tawuce daki, shiyasa nasamu damar kiranka, datana nan nasan kallonta bazai barni inkira kowa ba, bansan meke damuna ba Ash...,idan tana tare dani inajina cikin jin dadi,zuwa wannan lokacin acikin hayyaci na nake komai,but..idan naci gaba da ganin yarinyar nan, bazan Iya riqe kainaba..."

Ashraf yayi dariya yace" ai tun lokacin danaga ka'iya kallon idon Momy kace mata saki babu kyau,daga Nan nasan cewa kakamu,wallahi sonta kake"

Captain dayakai pancake bakinsa cikin sauri ya ajiye fork din hannunsa yace"kai a a, tayaya?,bahaka bane,niba sonta nake ba"

Ashraf yace"to menene?, Aryan katsaya ka nutsu, ka fuskanci rayuwar aurenku,maganar gaskiya so guda dayane Kuma kanason Mawahib"

Sumar kansa ya hargitsa da hannunsa daya Wanda bai riqe wayar dashi ba,ya runtse idonsa tareda fadin "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un....,tayaya?, meyasa nayi wannan saken?,tayaya yarinyar nan taci galaba akaina?"

Ashraf yace"to menene aciki? nasan bakai ne kayi dacen mata kadai ba, itama tayi dacen samun miji nagari,ka riqe matarka,kasameta kafada mata kana sonta"

Cikin rashin sanin abunyi kamar wani yaro yace"kenan sai Infada mata Ina sonta?"

Ashraf yayi dariya yace"emanah,kafada mata"

Yace"tayaya? bazan iyaba Ashraf..."

Ashraf yayi ajiyar zuciya yace"Aryannn,ka nutsu mana,kaifa Sojane,a 6angaren soyaiya ma inaso Kaci gaba da zama soja,kayi yaqi akan soyaiyar ka harsai kasamu abinda kakeso,karka bani kunya Kai namiji ne,karka koma Kaine kake tsoron Mawahib a yanzu,ka tunkareta...."

Jin kalaman Ashraf yasa yaji qwarin gwiwa a jikinsa,cikin sauri yadauki coffee din gabansa, shida bayason zafi a wannan Karon bai damu da zafin dayake dashi ba yadaga duka ya shanye, sannan yafara maida numfashi yace"insha Allah, zanyi yanda kace"

Cikin farinciki Ashraf yace"kokaifa"

Daga nan suka kashe wayar, Captain Aryan yadoka tagumi hannu bibbiyu,gaba daya ya manta dawani pancake dayake gabansa,Kenan duk alamomin nan da yakeji akanta shine soyayya? wato yanmatan dayake qwacewa Ashraf abaya duk ba sonsu yakeba,yanzu ne zai fara soyayyar kenan, tayaya zaija hankalinta gareshi?
tayaya zai birgeta?
tayaya zai Iya kallon idonta yafada mata yana sonta?
tayaya zai goge laifinsa a wajanta???

(irin wannan quations tsaya na tambayoma fan's din Amnah 🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub✍🏻[7/13, 5:41 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Washegari da sassafe tatashi tagama aikin komai, tayi masa breakfast tabarshi a dining sannan takoma dakinta tayi wanka tashirya,tafuto Sanye cikin doguwar riga ta material dinkin bubu mai fadi,tayafa dan madaidaicin mayafi taruqo yar qaramar handbag dinta a hannunta, bazaka ta6a cewa tanada aure ba, sakkowa tayi qasa Sai zuba uban qamshi take, a lokacin yana zaune a dining yanacin Yam kebabs din data hada masa, saikuma kunun gyada, tana sakkowa yazuba mata ido yana kallonta, fuskarsa ba'a sake takeba,harta qaraso inda yake idonsa yana kanta, yana kallon yanda taci gayu kamar zataje wajan dinner,Kuma ga jaka a hannunta, saida tazo dab dashi sannan Yasaki ajiyar zuciya ya janye idonsa,zama tayi a daya daga cikin kujerun dining din sannan tayi qasa da kanta tace"ina kwana"

Kallanta yayi qasa qasa, sannan yace"lafiya" yazuba mata ido yanacin abincin yana aikin kallonta,jinsa yake cikin nishadi duk da bamagana suke ba,wani irin dadi yakeji aransa saboda ganinta ta tabbata kenan dai son yarinyar nan yake.

Mawahib da kanta yake qasa a hankali tadago kanta ta kalleshi,cikin sauri ya janye idonsa akanta saide ya makaro, tariga ta kamashi yana kallonta,bata damu da kallon ba saboda tasan cewa ba komai bane danya kalletan,tasan daga kallon de babu wani abu,ahankali tabude dan qaramin bakinta tace"Yaya Captain...dan Allah idan babu damuwa inaso naje a wanke min kaina"
Tunda tafara magana yazubawa lips dinta ido yana kallo,har wani lumshe idonsa yake yana sake kallonta,cikin jin dadi yace"kishirya muje nakaiki"

Cikin sauri ta kalleshi tace"aina shirya,nagama komai"

fuska babu fara'ah kamar kullum ya girgiza kansa yace"kikoma ki sauya shiga,idan kingama ki sameni a Mota"
Chapter 35 · 0% Book details