← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 68

Sashe 34

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri Mawahib tadago kanta ta Kalli Captain Aryan,adede lokacin shima yadago kansa idonsu ya sarqe dana juna,cikin kamewa ya janye idonsa,ahankali itama tayi qasa da kanta bazatace ga yanayin datake ciki ba, itade tasan cewa batason sa,saide azaman dasuke gudanarwa na yanzu bazatace yanayi mata abinda bataso ba, daidai gwargwado yana bakin kokarin sa, soyaiyar sa cede bataji aranta har yanzu,cikin sanyin jiki ta sunkuyar da kanta qasa, tasan cewa tabbas wani abu yafaru.

Hajiya kilishi tace"Alhaji kasan de bana qaunar auren nan,kawai fin qarfina akayi,saboda haka idan de nice na haifi Aryan, inaso abani damata ta mahaifiyar sa d'ana yamin abinda nakeso"
Tajuya ta Kalli Captain Aryan da kansa yake qasa har lokacin yana tsugunne ko zama baiyi afalon ba, sannan taci gaba cewa"gashinan a zaune tun auren Ashraf na bashi umarnin yasaki yarinyar nan,idan yasan bai sake ta ba,to karya kuskura yasake kirana,amma saboda ban Isa dashi ba, shine yadaina kirana kwata-kwata yaza6i yazauna da wannan tijararriyar yarinyar akan yabi umarnina,kuma muddin Ina raye bazan ta6a daukan wayarsa ba saiya cikamin umarnina,gashinan a zaune, itama yarinyar gata nan a zaune yasaketa,uwarta taje ta aura mata mahaukaci..."

Mamy kanta yana qasa,tunda sukazo falon batadago kanta ta Kalli kowa ba,tana jira ne kawai Alqali yayanke hukuncin wannan aure,wani irin hawaye mezafi yazubo daga idon Mawahib, tasaka hannu ta share,ta tabbatar akwai abinda yafaru agidan yau,ta tabbatar anciwa Mamyn ta mutunci yau,meyasa Hajiya kilishi bata sonta? a gaban kowa da kowa taza6i taci mata mutunci saboda qiyaiya.
idon Ashraf yayi jajir qiris yarage yafara hawaye.

Wayar Captain Aryan tafara qara alamun Kira yana shigowa, yasaka hannu yayi rejecting kiran.
A'irin wannan lokacin bashida qwarin gwiwar daukan waya.
Kansa yana qasa bai dago ya kalli iyayen nasaba,saide yarasa dalilin dayasa yakejin mummunan faduwar gaba atare dashi.

Alqali yayi ajiyar zuciya yace"to kilishi ki kwantar da hankalinki,insha Allah yau wannan matsalar taku zatazo qarshe,dama can abinda yasa mukayi tunanin hada Ashraf da Mawahib aure, saboda wannan sa6anin dakuke samu ne keda Maryam, munyi tunanin idan danki, ya auri yarinyar Maryam,rikicin naku zaizo qarshe,kika nuna baza'a yi wannan aure ba, Kuma daga qarshe Allah da ikonsa Sai ubangiji yayi ikonsa akan Aryan,mukayi haquri bamu bashi umarnin yasaketa mu aurawa Ashraf itaba saboda Allah yariga yayi ikonsa,Sai muka kar6i tsarin Allah da hannu bibbiyu mukayi haquri muka bisu da Addu'ah,amma tunda har yanzu kin nuna bakyason auren,amatsayin ki na uwa,dole zamu baki damar ki,idan de har rabuwar auren shine kwanciyar hankalinki,to zai sake ta"

Mawahib tadaga kanta,tajuya ta kalli Captain Aryan taga kansa yana qasa baka gane yanayin dayake ciki, ta Kalli Mamy taga kanta yana qasa har yanzu, Mamy kuwa tariga ta saduda,tasan cewa auren Mawahib yaqare yau,qarshan cin mutunci de yau Hajiya kilishi tamata,tunda gashi agabanta za'a saki yarta,menene yafi wannan ciwo?
Menene amfanin zamanta awajan?
Ahankali tatashi tafice daga falon gaba daya,Abba bai hanata ba.

Alqali ya Kalli Captain Aryan yace"Aryan...kaji yanda mukai da mahaifiyar ka,tanaso kasaki Mawahib"

Captain Aryan yaji kamar an doka masa guduma akansa,cikin damuwa yadago kansa ya kalli Hajiya kilishi yace"Momy saki bakyau..."(🙊😳)

Gaba daya sai falo yayi tsit,maganar Captain tabawa kowa mamaki,a yanda suka sanshi da miskilanci dakuma sanin cewa baya son auren, ba suyi tunanin zai fadi wannan maganar ba.

Cikin Masifa Hajiya kilishi tace"haka Kuma ubangiji ya halasta shi, gatanan a zaune kasaketa"

adede lokacin aka sake kiran wayarsa akaro na biyu,yayi shiru ya runtse idonsa yarasa mayake masa dadi,yayinda Alqali yazuba masa ido yana kallonsa yanaso shi Aryan din da kansa yakawo musu qarshan wannan tashin hankali,Ashraf ya kalli halin da dan'uwan nasa yake ciki,yaga kowa yazuba masa ido yana kallonsa anason aga mezai yanke ,cikin sauri dabara tafado masa yadaga murya yacewa Captain "kaje kadauki wayar kadawo"

Cikin sauri yadago kansa ya kalli Ashraf,kallo daya Ashraf yamasa nan take Captain yadauki haske,cikin sauri yadaga wayar wadda take shirin katsewa tareda fadin"oga inajinka"

Sannan ya silale yabar falon.

Hajiya kilishi ta Kalli Mawahib ta watsa mata wani irin kallo,cikin sanyin jiki Mawahib tatashi tafuto daga falon idonta yana tsiyayar da hawaye,sai yanzu ne tasan dalilin kiran nasu, tana futowa daga part din adede lokacin Captain Aryan yagama maganar dayake awaya yajuyo,ahankali yatako yazo gabanta yatsaya,itama tana ganinsa ta tsaya tayi sauri ta goge hawayen idonta,zuba mata ido yayi yana kallonta yakasa cemata komai,yanda yaga hawaye a fuskarta ba qaramin ta6a zuciyarsa hakan yayiba,da'ace ya'iya lallashi da babu abinda zai hana ya lallasheta,baisan Yaya zaiyi da'ita tacire damuwar Momynsa aranta ba,wani 6angare na zuciyarsa ne yake zigashi akan ya rungume ta(🙆🏻‍♀️)
kallon compound din gidan yayi, ganin babu kowa hakan yasa ahankali yasake takawa gab da'ita har sunajin hucin numfashin juna,ahankali yasaka hannunsa ya rungume ta sosai a jikinsa har yanajin yanda tudun nashanunta suke ta6a qirjinsa,lokaci daya yafara sakin ajiyar zuciya kamar yaron daya shekara baisha nonon uwarsa ba,hannunsa daya rungume tan yafara motsawa yana shafa bayanta ahankali,hakan yasa Mawahib ta kwantar da kanta a faffadan qirjinsa tayi luf idonta yana tsiyayar da hawaye.
cikin wata irin muryar rad'a,data hadu da kasalar jikinsa sukasa muryar tasa tasake yin wani irin laushi,yadora bakinsa asetin kunnan ta yace"Sorry,are you ok?"

Adede lokacin Mamy tafuto daga part dinta zataje part din Hajiya kilishi sakamakon kiran wayarta da Alqali yayi,(🙆🏻‍♀️)
Kokadan basuji takun tafiyar taba,Mamy tana dago kanta ta gansu a wannan yanayin,gabanta yafadi,cikin sauri tajuya takoma part dinta.

Cikin kuka Mawahib tace"please kakaini wajan mahaifina,ni nagaji..."

Cikin sigar lallashi yace"kinaso mutafi?"

Cikin sauri ta daga masa kanta,yace"Okay let's go"
Yana fadin haka yakamo hannunta suka futo sukabar gidan(🙆🏻‍♀️)

Suna zuwa bakin get Captain yacewa driver "kaimu Airport"

Cikin sauri direba yabude musu Mota suka shiga yadauki hanyar Airport.

Mamy tajima afalo hannunta dafe da qirjinta, wacce irin rashin kunya su Aryan suke da ranar Allah kuma a filin tsakar gida basa tsoron a gansu? kasa fita tayi saita window ta leqa,taga basa nan, sannan tafuto takoma falon Hajiya kilishi,har lokacin suna nan a zaune yanda suke,Alqali ya kalli Ashraf yace"ina Aryan din yakene? baigama wayar bane har yanzu? jeka kirashi haka"

Ashraf yatashi ya futo ya dudduba ko'ina bai gansu ba, yakoma ya zauna yace"Daddy ban ganshi ba"

Alqali yace"to Ina yayi? kirashi awaya kace masa muna jiransa"

Ashraf yadauki wayarsa yakira Aryan,wayar tana shiga yabawa Alqali yace"Daddy gashi tashiga"

Alqali yace"A a,sakata a speaker inaji"

Ashraf yabude waya kamar yanda Alqali yasa shi,saida takusa katse wa Aryan ya dauka, Ashraf tace"Aryan kana inane? tun dazu fa su Daddy suna jiranka"

Kai tsaye Captain Aryan yace"Ashraf gaskiya natafi..."(😲)

Cikin sauri Ashraf yace" Ina katafi?"

Captain Aryan yajuya ya kalli Mawahib datake gefensa tayi luf a jikinsa tana goge hawaye da bayan hannunta, sannan yayi qasa da murya yace"nakoma bakin aikina"

Ashraf yace"kakoma aiki kuma? Mawahib dinfa?"

Captain Aryan yace"gatanan muna tare,itace tace mutafi,damuwa zatasa mata ciwon kai Ashraf,daga zuwanmu har face dinta yarame,kafada musu mun wuce,ka nuna musu anmin kiran gaggawa ne a office"(🙆🏻‍♀️🙊😂)

yana fadin haka yakashe wayar,Ashraf daya saka waya a speaker duk mutanan falo sunajin abinda Captain yake fada saiya qame da waya a hannu yakasa dago ido ya Kalli kowa.

(asauka lafiya Captain😂🙏🏻)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/11, 7:47 PM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Kibiya ki karanta cikin salama,yafi sauqi akan abinda za'a barki da ubangijinki

Alqali yayi murmushi cikin kunya,ta tabbata de abinda yake zargi yagama tabbata,Aryan yanason matarsa,shiyasa yadauki wuqa da nama yabawa Yaron,tunda shine me aure saiya yanke abinda yake daidai,Alhaji khaleed yayi murmushin jin dadi duk dade maganar Aryan din shima tasashi kunya,Mamy tasaki wata irin asirtacciyar ajiyar zuciya,tana hamdala aranta

Hajiya kilishi tanajin abinda Aryan Yafada tadora hannunta aka ta rusa uban kuka tatashi tsaye tace"shikkenan....maryam kin cuceni,kingama da dana, wallahi bazan ta6a yafe mikiba sai Allah yayi mana sakayya dake"

Cikin kuka ta wuce dakinta tafara kiran yan'uwanta awaya tana fada musu abinda yake faruwa.

Alqali yayi gyaran murya ya Kalli Alhaji khaleed da Alhaji Isa yace"to Alhamdulillah,ban tauyewa kowa haqqinsa ba,Aryan ya nuna mata yanason matarsa,saboda haka Maryam karna sakejin anyi wani tashin hankalin dan Allah,Yara Kuma mubisu da Addu'ah Allah yabasu Zaman lafiya"

Gaba daya falon suka amsa da "Amin"

Alqali yasake dubawa ya kalli Ashraf da kansa yake qasa har yanzu,kawai jira yake yabar falon yakira Aryan yafada masa komai,yace"kai tashi kaje kadauki matarka kutafi gidanku,Allah yasauketa lafiya"

Cikin kunya ya sosa kansa sannan yace "Amin Daddy"
yatashi yafice daga falon cikin sauri, daga nan sukai Addu'ah taro yatashi.

******

Suna sauka agida tabude murfin motar tafuto idanunta sun kumbura saboda kukan datasha kafin su qaraso,kokadan taqi yarda tahada ido dashi.
bayanta yazubawa ido yana kallonta harta shige ciki, sannan Yasaki wani irin huci mai zafi, hannunsa yazuba cikin aljihun wandon sa sannan yafara takowa ahankali zuwa cikin gidan,yana zuwa falon yaga batanan,kai tsaye yabita sama batare da tunanin komai ba yatura yashiga dakin.
Tana zaune agefen gado ta jingina kanta da jikin gadon tafada duniyar tunani, batasan cewa hawaye ne yakebin fuskarta ba, wacce irin qiyaiya Momy kilishi take mata haka?
meyasa bata santa?
saboda ta kasance agola?
haqiqa maganar Nabiha tanakan gaskiya datace muddin tabari Yaya Captain yasaketa to daga ita har Mamy sun shiga ukun su.
qamshin turaren Captain data shaqa wanda kokadan batasan ya zauna akusa da'ita ba, shine yasa tatuno irin rungumar dayayi mata agida,dama shima ya'iya irinna yan film?
bata ta6a ganin hakan a zahiri ba,Sai gashi yau tagani akanta,ashe yadade yana mata Alfarma bata saniba,ashe andade dabashi umarni yasaketa shine yaqiyin hakan? tasan cewa baya sonta,Kuma bazai ta6a sonta ba,soyaiya bazata sa yaqi sakinta ba,
shin saboda Mamy ne yasa yaqi sakinta kokuma saboda mahaifinta?

ganin tunda yazauna yaga ko motsi batayi ba kawai tunani take tana faman hawaye hakan yasa yayi gyaran murya,sannan ya'ajiye mata wani farin handkerchief
Chapter 34 · 0% Book details