← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 68

Sashe 48

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan shagwaba tasakar masa,ya lumshe idonsa yabude,sannan cikin dabara yasake bata tasha, ya ajiye sauran tareda kwantar da kanta a qirjinsa, yana shafa kanta,sun dad'e ahaka har bacci ya dauketa me nauyi, saida ya tabbatar tayi bacci sannan ya kwantar da'ita, ya sunkuya yadora bakinsa akan lips dinta,yayi kissing dinta, sannan ya futo daga dakin.

Yana futowa yaga falon babu kowa,cikin sauri yafice yanufi dakinsa yayi wanka sannan ya rungume fillo a qirjinsa ya lumshe idonsa yana tunanin ta har bacci ya dauke shi.

Washegari takama Monday,tun asuba Captain yake faman kiran wayarta yanajin yanayin jikin nata, ta kuma tabbatar masa ta warke ras.

Saida gari ya waye sannan yashiga part din,tare sukai breakfast shida ita da Mamy da Abba,tanajin yanda yake ta6o mata qafarta da tasa qafar ta qasan table din dasuke zaune, amma saita maze bata nuna komai ba, saide tadan kalleshi kad'an sannan ta kawar da kanta.
Abba yatashi zai tafi aiki, Mamy ma tayi shirin tafiya asbiti tadauki abincin su Hajiya kilishi, Abba zai fara kaita asbitin takai musu abincin, sannan ya rakata wajan nata aikin sannan shima yawuce nasa.

Su kadai suka bari afalon,hakan ba qaramin dadi yayiwa Captain ba,domin kuwa suna tafiya yasaka ta a jikinsa, ahaka suka wuni,banda shagwa6ata babu abinda yakeyi,bai tafi asbiti ba sai yamma dede lokacin da Mamy ta dawo kenan, bai yarda yabarta ita kadai a gidan ba,acan asbitin ya tarar da Ashraf,basu dawo gida ba sai dare kamar kullum.

haka rayuwar gidan Alqali ta kasance har tsawon sati daya,tsawon wannan lokacin Mama Sadiya ce me zama da'ita,Mamy kuma kullum zata kai musu abinci sannan tawuce aiki,zuwa wannan lokacin jikinta ya warware sosai,saide rama irinta rashin lafiya kafin jikinta yagama komawa daidai.

Azaman Aryan da Mawahib kuwa babu abinda ya sauya,bai ta6a tunanin neman haqqinsa awajan taba,koda yaushe kokarin ganin ya kyautata mata yake,kuma bai ta6a jin haushinta dan taqi baiyana masa menene acikin zuciyar taba.

yau aka sallamo Hajiya kilishi,mutane sai sintirin zuwa gidan suke ana yimata yajiki,gaba daya sanadin wannan rashin lafiya yasa Hajiya kilishi ta sauya kamar wanda aka sauya ta,tazama shiru shiru kamar ba'ita ba,cikin ranta kuwa tsantsar nadama ce take damunta,dama ance baka gane masoyinka sai kana halin jinya,tunda Maryam tazo da yarinyar nan cikin gidan Alqali shedan yake kitsa mata abubuwa marasa kyau cikin ranta, bayan babu abinda yarinyar ta tsare mata,ubangiji ya nuna mata Ishara akan danta Aryan mafi soyuwa aranta,Allah yahada aurensa da Mawahib, duk da haka bata saduda ba,ajiyar zuciya ta sauke bayan tagama tunani ta Kalli Ashraf da Aryan dasuka sakata agaba Ashraf yana zaune aqasan kujera yana game awayarsa Aryan kuma yana zaune agefenta akan kujera yayi shiru.

Kallonsa tayi tace"Baba na kamar kanada damuwa, meyake faruwa?"

kallonta yayi yana shakkar yimata maganar abinda yake ransa, cikin sanyin jiki yace"Momy dama inaso zanyima yarinyar nan lefe ne"

Cikin sauri tace"Mawahib?"

Kansa ya sosa yace"eh Momy"

Tace"kuyi musu mana,nima akwai wasu kayan awajena,idan kun gama sai ahadasu gaba daya"

Ashraf yadaga kansa ya kallesu yace"Momy to guda nawa zamu siyo?"

Hajiya kilishi tace"toku bawa Maryam kudin saita hado muku komai mana"🤭

Ashraf yace"shikkenan ma, yafi sauqi"

Captain Aryan ya6ata fuskarsa cikin shagwa6a yace"Momy...gaskiya nide gara kihada min da Kanki"

Hajiya kilishi tayi murmushi tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi,au bazaka bawa surukar ka tahada muku gaba daya ba? yanzu Baba na inani Ina shiga kasuwa? ita Maryam din de itace yar zamani duk zata sako muku abinda yadace, amma tunda baka so toka bawa Sadiya saita hadoma"

Cikin sauri yace"eh zan bata"

Murmushi tayi tajashi jikinta tana shafa kansa.
Adede lokacin Alqali yashigo falon, yana ganinsu yayi murmushi yakalli Hajiya kilishi yace"Kilishi maman biyu,kede kawai burinki kisa yaranki a gabanki kina lailayasu kamar jarirai"

Ashraf yayi murmushi yace"Daddy Aryan takewa haka,shine yaro"

Cikin sauri Captain Aryan yadago kansa daga kafadar Hajiya kilishi yace"waye yaron? Momy kidena bari yana cemin yaro"
Hajiya kilishi tace"yazan masa ne Aryan? kutashi muje kurakani part din Maryam"
Alqali yayi murmushi yace"lafiya deko?"

Cikin sanyin jiki tace"ai harda kai zamuje Alhaji,zan sake bawa Mawahib haquri,tunda gashi an sallamoni nadawo gida"

Gaba dayansu su ukun kallonta sukai cikeda jin dadi,Ashraf yayi wulli da wayar hannunsa yace"muje Momy"

Cikin jin dadi suka nufi part din Mamy gaba dayansu.

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

******

Mamy ta kalli Mawahib tace"tunda Yaya kilishi ta warke nasan kun kusa tafiya ko?"

Mawahib da hankalinta yake kan waya tace"wallahi bansani ba Mamy,banyi maganar dashi ba"

Mamy tace"to kafin kusa ranar tafiya saiki fara zuwa wajan gyaran jiki,nayi magana da Hajiya Balaraba,saiki fada masa zaki fara zuwa gobe,kona kwana biyu ne a miki kafin kutafi "

Tace"to Mamy zan fada masa"

"magungunan dasuke wajanki wanda na aiko miki sun qare ko?"
Mawahib ta kalleta,sai yanzu nema da Mamy tayi mata maganar magani sannan ta tuna da maganin da Matar Captain Habib tabata,yana cikin Jakarta,ta kalli Mamy tace"duka na shanye,turare ne bai qareba,yana can"

Mamy tace"to turaren babu qamshi ne? ko bayaso kina amfani dashi?"

Murmushi tayi tace"Yaya Captain din? besan ma Ina amfani dashi ba"

Mamy ta jinjina kanta daga haka bata qara magana ba,saide tunanin ta yagama bata Mawahib da Captain babu abinda yata6a hadasu, idan kuwa sunyi mu'amular aure toda kanta zata nemi maganin saboda yanada kyau sosai,idan taga Aryan din yana rawar jiki akanta lokacin da zata nemi wani ma babu wanda yasani.

Adede lokacin su Hajiya kilishi suka shigo falon,cikin farinciki Mamy ta kallesu tana tashi tsaye tace"sannunku da zuwa,Yaya meyasa kika taso keda bakyajin dadi aida kinmin waya nata so"

Hajiya kilishi tace"A a jiki ai yayi kyau Maryam,babu komai wallahi"

Mamy ta kalli Mawahib tace"kawo musu ruwa"
Sannan ta kalli Alqali cikin ladabi tace"Yaya Bissmillah"
Zama yayi a kujerar, sukam su Ashraf tuni sun zauna,Mawahib takawo musu ruwan takoma zata dauko lemo Hajiya kilishi tace"Mawahib dawo ki zauna,Maryam kibarta ta dinga hutawa mana"
Cikin sauri Mawahib ta kalli hajiya kilishi sannan ta nemi waje ta zauna, Mamy ta sunkuyar da kanta qasa tanata mamakin Hajiya kilishi.
Hajiya kilishi tajuya ta kalli Mawahib tace"Mawahib wajanki nazo, zuwa nayi nasake yimiki godia akan taimakon dakika min a asbiti,haqiqa naga aya,kuma na dauki darasi,inaso ki yafemin duk abubuwan dasuka faru abaya, Sharrin shaidan ne,kiyi haquri kiyafemin kodan mijinki Aryan"

gaba dayansu sai jikinsu yayi sanyi,Alqali yayi shiru yana sake godewa Allah acikin ransa, ashe yana raye zaiga irin wannan ranar, kafin yagama tunanin sa yaji Mawahib tace"babu komai Momy, nayafe miki"

Hajiya kilishi tace"Allahu Akbar,haqiqa ni kilishi Naga ikon Allah,rayuwa kenan,Allah ya miki Albarka Mawahib"
Ahankali Mawahib tace"Amin"
Hajiya kilishi tajuya takalli Mamy tace"Maryam kiyi haquri,daga yau namiki alqawari insha Allahu bazaki sakejin wani tashin hankali awajena ba, abubuwan dasuka faruwa Dan Allah na roqeki ki manta dasu, ki daukeni amatsayin yayarki daga yau"
Cikin farinciki Mamy tace"wallahi babu komai Yaya, yawuce, Allah yayafe mana baki daya"

Cikin farinciki Hajiya kilishi tace"nagode Maryam"
tajuya tasake kallon Mawahib da kanta yake qasa tace"Mawahib...? Allah yabaku Zaman lafiya "

Cikin jin kunya Mawahib tatashi tawuce dakinta, Captain Aryan yayi murmushi yabita da kallo.

Sun dan jima afalon,har Abba yadawo ya gansu,shima yazauna sukaci gaba da firarsu gwanin sha'awa, sannan Alqali ya rufe musu taro da Addu'ah suka tafi nasu part din.

Da daddare suna zaune a dining itada Mamy bayan sungama cin dinner,tadauki wayarta tatura masa saqo "Yaya Captain inaso gobe zanje wajan gyaran jiki"

Alokacin da saqon yashigo wayarsa yana wajan Mama Sadiya yana fada mata irin kayan lefen dayake so a hadowa Mawahib,saqon nata yaduba yagani yayi murmushi, sannan yayi mata replay yace"send me your account number"

tura masa tayi sannan ta ajiye wayar,Mamy tafuto daga dakinta tabata magani a cup tace"ungo shanye kiban cup din"

Ganin yanda Mamy ta tsareta yasa babu musu ta shanye maganin sannan tabata cup din.

Alert ne yashigo na dubu dari cikin wayarta, mamaki ya kamata, ta nunawa Mamy alert din tace"Mamy nafada masa shine yaturo min wannan kudin"

Mamy tace"har dubu dari? lalle Captain gyaran jiki yakeso dakyau"

Mawahib taturo bakinta gaba tatashi tawuce dakinta cikeda shagwa6a, Mamy tayi murmushi takira Hajiya Balaraba tafada mata bayan gyaran jikin ayi mata hadin magunguna masu kyau hadin amare ta zaunar da'ita tasha komai agabanta, yanzu zatayi mata alert.

Hajiya Balaraba tanajin zancen alert tasan Mamy ba wasa,cikin tabbaci tace"karki damu Hajiya Maryam,ai tunda kin kawo ta wajena kingama komai,inde nayi mata gyaran jikin nan ko mijin ta kasa ganeta zaiyi,sannan zanyi mata hadin nafi qarfin reni,ina tabbatar miki daqyar mijinta zai iya kallon wata yarinyar amatsayin mace,saina sata ta gigitashi banida sasssauci ta wannan fannin"

Mamy tayi murmushi tace"to shikkenan saita zo,zakiji alert yanzu yanzun nan"

Daga nan sukai sallama Mamy tawuce daki,tana jiran zuwan Abba Ashraf yakirata awaya yake fada mata maganar lefensa, suka tattauna abinda zasu tattauna sannan sukai sallama

Kamar yanda Mamy ta tsara washegari tun sassafe Mawahib tabar gidan,tatafi gidan Hajiya Balaraba,bata dawo ba sai yamma lis,tun aranar yau din Mamy tafara ganin canji,farar fatar Mawahib din taqara yin fresh,kasancewar tana dadewa bata dawo da wuri ba, hakan yasa tana zuwa gida take kwanciyar ta tayi bacci,Mamy tana lura da shige da ficenta kokadan taqi bata damar da zata hadu da Captain,tafi son agama yimata gyaran jikinta tsaf,sannan ta tattara ta sukoma Abuja.

kwananta biyar tana zuwa kuma yaune qarshe,tana dawowa tawuce part dinsu cikin kasala saboda kwana biyu wannan magungunan da ake bata yasa take yawan jin feeling ajikinta.

Acikin kwana biyar dinnan su Mamy suka gama hada komai na lefe, apart dinsu Nabiha suke ajiye komai wajan Mama Sadiya.

******

Hajiya kilishi ta Kalli akwatunan dasuke gabanta guda ashirin,tace"wanne ne na Mawahib?"
Chapter 48 · 0% Book details