← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 68

Sashe 26

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Captain Aryan kuwa uffan baicewa kawai girki yake kwasa,kafin kace me,daga macaronin, har farfesun sai gashi sun tashi dashi gaba d'aya.(😳)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Mutara zuwa yamma🙏🏻

Amnah El Yaqoub✍🏻[7/9, 5:59 PM] AMINA KABIR CAPS: *Page 24&25*

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki.

____

Alhaji Bala yadauki tissue yafara goge bakinsa yana cewa"masha Allah,Captain girki yayi dadi"

Captain Aryan dayake riqeda spoon a hannunsa yana nadama dama abincin bai qareba,yayi murmushi sannan ya ajiye spoon din yana shafa sumar kansa.

Alhaji Ma'aruf ya ajiye gorar ruwan datake hannunsa yadaga murya yanda Mawahib datake kitchen zata jiyoshi yace"Ruqayya kina inane, futo zamu tafi"

Cikin nutsuwa tafuto daga kitchen din,har lokacin taqi yarda ta Kalli Captain Aryan,Alhaji Ma'aruf da Alhaji Bala suka miqe, Shima Captain ya miqe, Alhaji Ma'aruf yasake kallon Mawahib da kanta yake qasa tana jan yatsun hannunta yace"Babu damuwa deko?"

Manyan idanunta me kama Dana masujin bacci irinnasa ta dago ta zuba masa ido sannan yace"Babu komai Abba"

Cikin Jin dadi yasaka hannunsa a aljihunsa yadauko rafar kudi Yan dari biyar biyar guda uku yabata yace "Ruqayya, girki yayi dadi sosai, ga tukwicin girkin ki, saiki bayar a ajiye miki"

Tanajin abinda yace tagane nufinsa,cikin ladabi ta kar6a tace"to Abba nagode, Allah yaqara budi"

Cikin jin dadi yace"Amin Ruqayya,Allah yayi miki Albarka,Allah yabaku Zaman lafiya"

Alhaji Bala dayake gefe yace"Amin,Amin ya Allah"

Mawahib taqaraso a hankali tamiqawa Captain Aryan kudin,yabi kudin da kallo aqalla zasu Kai dubu dari da hamsin,ya Kalli dogayen hannunta dasuka riqe kudin sirara dasu da tsawo gwanin sha'awa.

Alhaji Bala Yazuba musu ido yana kallon tsantsar dacewa awajan,yaga alama Ruqayyan har yanzu kunyar Captain take ji,dubada yanda taqi hada ido dashi tunda sukazo,da alama Captain din yadaga mata qafane bai gama cire mata kunyar amarci ba(😲🙈)

gyaran murya yayi,hakan yasa Captain ya kar6i kudin da Mawahib din take bashi,yasaka su cikin aljihunsa.

Alhaji Ma'aruf yafara tafiya suma suka biyoshi abaya, har suka futo harabar gidan sannan yace"to zamu wuce,zamuje gwarumfa mukwana,gobe dasafe zamu wuce insha Allah"

Captain Aryan yace"Allah yakaimu Abba"

Suna tsaye shida ita su Alhaji Ma'aruf suka shige cikin motar,direban Captain yaja suka tafi.

Har sukabar gidan,idan Mawahib yanakan motar,duk da bawani sabo tayi dashi ba, taji babu dadi dazai tafi,uba ubane ko Yaya yake.

Atare suka jiyo sai akai dace idanunsu ya hadu waje daya,cikin sauri ta janye idanunta tajuya ciki da sauri,Captain Aryan yabita da kallo hannunsa zube cikin aljihun wandonsa.

Washegari dasassafe tatashi kamar yanda tasaba,qafafunta tazubo qasa yayinda take zaune akan gado,kayan bacci ne ajikinta Riga da wando light pink,wandon dogo ne yayinda rigar ta kasance yar qarama marar hannu kamar shimi,kayan me santsi ne sosai ya kwanta a lallausar fatarta luf.

Tagumi tayi da hannu bibbiyu,tana tunani,Nabiha da Mamy ne take Samun sassauci awajansu,to suma sun dawo suna cewa ta kula da rayuwar auren ta,idan Yaya Captain yasaketa kodan gorin da Hajiya kilishi zata mata bata Isa ta tunkari kano ba saide Kai tsaye tanufi kebbi wajan mahaifinta,idan taje wajan mahaifinta batasan wanne hali zai shiga ba idan yaji ansaketa yanda taga yana farinciki jiya,gara ta sakawa kanta salama ta rungumi aurenta tayi zaman aure kamar kowacce mace tunda tasan saki de babu maganar sa tsakanin ta da Yaya Captain,tasaki ajiyar tareda cire tagumin datayi,dole de akeso ta zauna da wannan mutumin,zata sauke duk wani haqqi nasa,idan an tilasta mata zama dashi ai baza'a tilasta mata tasoshi ba.

Ahankali tayi miqa,sannan tasauko daga gadon,tasan ai yau ba aiki,ba lalle yatashi da wuri ba,hakan yasa ta dauki dan qaramin mayafi siriri ta daura akanta ta wuce toilet tayi brush,sannan ta wanke fuskarta tarufe toilet din,sanin yana bacci yasa batareda tunanin komai ba tafice ahaka,yau ko hijabin babu.
Kitchen tawuce tafara tunanin abinda zata dafa,bata saniba idan ta dafa dashi zaiji ko bazai ciba,tasan na jiyama datayi wa su Abbanta baici ba, tunda shide tunda suke zamansu ko sau daya beta6a cin abincin taba,wata zuciyar tace da'ita kiyi komai domin sauke haqqin dayake Kanki,ko awajan Allah kin fita.

Ajiyar zuciya tasaki,ta dauki wayarta ta kunna data tafara browsing tana ganin ire iren abincin sojoji Wanda yake qarawa sojoji lafiya yagina musu jiki,datar ta rufe sannan tafara qoqarin girkin.

cikin kwanciyar hankali tafara girkinta tana qarfafawa kanta gwiwa akan Wanda takewa girki saboda baso take ba,tursasa kanta kawai take, cikin sauri take komai dan tagama da wuri takoma sama tayi wanka.

Girkinta yayi nisa qamshi yafara baiyana,adede lokacin yagama gym yadawo gidan,yana Sanye cikin gajeren wando da yar qaramar Riga wadda ta bayyana qaqqarfar surar jikinsa,kamar yanda yasaba idan yadawo zai shiga kitchen yasha ruwa,yau ma yana shigowa falon Kai tsaye yawuce kitchen, tun kafin ya qarasa yaji wani daddadan qamshin girki yana tashi,hakan ya tabbatar masa tana ciki,cak yaja ya tsaya abakin qofar gabansa yayi wata irin faduwa sakamakon kayan jikinta wanda yayi tozali dashi,wanda tsantsin kayan nata yasa kayan ya kwanta luf ajikinta kana ganin tsantsar dirin da Allah yamata.
tabashi baya batasan ya shigo ba,aikinta kawai take hankali kwance,shikuwa yazuba wa bajajjan hips dinta ido wanda yake dan rawa kad'an-kad'an saboda yanda take motsa jikinta wajan aikin,kamar da niyya take kadasu,zuciyarsa ce tafara zillo,yaji wani irin abu yana masa yawo tundaga qwaqwalwar kansa zuwa ilahirin jikinsa,gabansa ya tsananta faduwa yana so ya dauke idonsa daga wajan amma yakasa,mamaki yake wannan qanqanuwar yarinyar ce da wannan abubuwan? towai tayaya ta mallakesu?.

dankwalin kanta ya kunce yafado kafadarta,dogon gashinta data hadeshi waje daya shima ya baje, cikin sauri ta wanke hannunta sannan takama gashinta ta daure,tamaida dankwalin tarufe kanta, Captain Aryan dayayi mutuwar tsaye yabi dogon gashinta da kallo cikin ransa yake tambayar kansa to kode ba'ita bace?(🤔)

jiyayi yanayinsa yana sauyawa,marar sa tadan murd'a, ahankali yasaki ajiyar zuciya.
Cikin sauri tajuya cikeda tsoro tace"wayyo Allah na..."
tafadi haka cikin tsoro tana matsawa gefe,batayi tunanin akwai mutum a kitchen dinba,tana ganinsa ta lumshe idonta tareda sakin ajiyar zuciya,takalli ingarman jikinsa wanda yake a murde saboda d'aga qarfe,sannan takalli kayan jikinta cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa,tadaure fuskarta,taci gaba da aikin cikin sauri.

Ganin zata kamashi yana kallonta cikin sauri yanufi fridge yabude yadauki gorar ruwa guda daya,maimakon yafice daga kitchen din, saiya tsaya yaqi fita yafara qoqarin bude gorar ruwan.

Ta gefen ido ta Kalle haka kawai yau ta tsinci kanta da rashin fargaba dakuma tsoron sa,tunda tasan bayason auren itama bataso bataga amfanin daure mata fuskar dayake ba dukda dama hakan dabi'arsa ce, to amma itama gara takoya daga gareshi tadaure tata fuskar itama inyaso ayi wacce za'a yi, batare data kalli inda yake ba tace"ina kwana?"

Bai amsa mataba yad'ora gorar ruwan a bakinsa yafara sha,yana satar kallonta qasa-qasa.

Mawahib dataji bai amsa ba saitayi shiru taci gaba da aikinta saide duk ta takura saboda tsayawar sa awajan, tarasa menene dalilin tsayuwar tasa, duk saita kasa sauri kamar yanda takeyi kafin yashigo.

Saida yagama shanye ruwan tas, sannan yajuya yafice daga kitchen din.

Kai tsaye dakinsa yawuce ya watsa ruwa yafuto yana goge jikinsa,yana so yafita da sauri saboda yau babu aiki ogansa yamasa waya zasuyi ganawar sirri a Danjam hotel saboda wani qalubale dayake tunkaro su.

Jikinsa yake gogewa da dan qaramin towel amma ita yake gani a'idonsa lokacin daya ganta naked babu kaya,tsayiyun breast dinta suka fado masa,dan qaramin tsaki yasaki tareda jefarda towel din hannunsa, ya zauna akan gadon dagashi sai guntun towel din dayake daure a qugunsu,yadafe kansa da hannunsa cikin damuwa yake tambayar kansa meyake damunsa ne?

Wayarsa ce tafara qara, ba tareda yaduba yaga me Kiran ba yadauka yakara wayar a kunnan sa, daga dayan 6angaren Ashraf yace"A&M....."

Yanajin haka yagane tsokana ce take damun Ashraf din,wato Aryan da Mawahib,idonsa a lumshe yace"Ash kana lafiya"

Ashraf yace"lafiya,Ina Mawahib?"

Captain Aryan ya runtse idonsa,Ashraf baisan halin dayake ciki ba yarinya tasashi agaba tana masa gashi ta qarqashin qasa amma shi ita yake tambaya(🙊)

Cikin taqaici yace"bansani ba,bakada number tane?"(🙆🏻‍♀️)

Ashraf yayi murmushi yace"idan inada number ta inkirata inyi mata mene?"

Captain Aryan yace"oho"

Ashraf yace"kishi kake?"

Cikin sauri Captain Aryan yace"akan wa kenan zanyi kishin? wait....Ashraf, wai ita kakira kaji kokuma nika kira kaji lafiya ta?"

Ashraf yace"kaina kira"

wata irin ajiyar zuciya Captain yasaki sannan yace"yaushe zakazo?"

Ashraf yace"Ina zanzo Ina tareda wannan jarababbiyar yarinyar? tayaya zan tafi nabarta? Ina tafiya zata fara kuka nikuma inajin tausayin ta, saide kaikazo"(😲)

Captain yace"bazan Iya zuwaba Ashraf,gaba daya tsoron zuwa gida nake saboda Ina tsoron Momy"

Ashraf yace"to shikkenan idan nasamu lokaci zanzo ko daga wajan aiki ne saina qaraso"

Captain Aryan yace"nima idan nasamu lokaci inde bakazo dinba zanzo ok?"

Daga Nan sukai sallama, wayar daya gama da Ashraf itace tasa yarage tunawa da surar jikinta, harya samu nasara cikin sauri ya shirya cikin qananun kaya riga da wando yayi mutuqar kyau kamar ba gobe.

Wanka yayi da turare sannan Yafuto yana bulbula qamshi zuwa falo, adede lokacin tagama shirya komai na abincin zata koma sama tayi wanka,Koda wasa qin kallonta yayi saboda yana tsoro kar yaje gaban ogansa kuma asamu matsala(🙈)
yagama lura yau tashin hankali takeji shiyasa taqi saka hijabi, shikuma bai shiryawa wannan tashin hankalin ba,yana zaman zamansa nema take qarfi da yaji tasa azo ana abun kunya atsakani,shikuma bayason raini,kokadan hakan bazata ta6a faruwa ba.

ganin zai fice daga falon kamar yana sauri hakan yasa ta kalleshi tace"ga abinci"

Batareda ya kalleta ba fuska a daure yace"no,Ina sauri"

dan qaramin bakinta taturo gaba,Kenan duk wahalar da tayi tatashi a banza,ita kanta Batasan ya akai ba,kamar an qwato maganar daga bakinta saiji tayi tace"bakaci komai bafa.... "

Cak yaja yatsaya yaji yakasa fita,kuma yakasa dawowa.
Chapter 26 · 0% Book details