← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 68

Sashe 67

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu musu tatashi ta dauki dan kayansu da tazo musu dashi, ta dauki Aryan yadauki Ashraf suka futo,itace agaba tana zuwa qofar daki taci karo dawata qatuwar kunama, cikin sauri tayi baya yace"Yaya Captain kunama"
Cikin rashin damuwa yace"ki dauketa mana"

Kallonsa tayi tace"haka kawai saika ce wanda nayi gamo zansa hannu na in dauki kunama?"

Kansa yashafa, sai yanzu yatuna ashefa ba Ashraf bane,ya kalli yanbiyunsa, sannan yazo yawuce tagabanta ya dauke kunamar, Mawahib ta matso da sauri takama hannunsa tace"ina kunamar? bata cijekaba?"

Baice mata komai ba yace"muje"

Kanta ta daga masa suka futo daga dakin,
alokacin gari harya gama wayewa safiya tayi, Hajiya kilishi tafuto zata shiga kitchen da flaks din tea a hannunta sai ganinsu tayi da yara a hannu, ga jakar pampers dinsu da sauran kayan buqata a hannun Captain, cikin mamaki ta tsaya tace"lafiya naganku sassafe? meyafaru?"

Kafin su bata amsa Mamy tafuto daga kitchen din da alama itace take qoqarin hada break fast, itama taja ta tsaya, babu kunya Captain Aryan ya kalli hajiya kilishi yace" Momy dama sun dawo wajanki ne,mun bakisu"(😂🙆🏻‍♀️)

Mamy tanajin haka ta kwashe da dariya, cikin sauri Captain da Mawahib suka juya, ganin Mamy yasa yayi saurin sunkuyar da kansa yana sosa qeyarsa.

Mamy ta qaraso wajansu takalli Hajiya kilishi tace"Yaya yanaga kin bude baki kina kallonsu, ko bakyason kyautar da'aka miki?"

Hajiya kilishi tace" Ina ganin ikon Allah ni kilishi, yanzu kai Aryan shine kasakota agaba kukazo kukawo min yara wato ni karna yi bacci ko?"

Mamy tayi murmushi ta kalli Captain da Mawahib tace"kafin kuyi aure kuyi bacci, bayan kunyi aure ma kuyi bacci, waye yace muku yanzu lokacin bacci ne? ai wanda kukai abaya kunyi Iya rabonku,banda shirme wannan qananun yaran ne za'a rabasu da uwarsu ace sun koma wani waje? toku bani tunda bakwa so"
Tafadi hakan tana meqa musu hannu, Captain da Mawahib suka hada ido,cikin sauri suka juya Sum sum suka koma dakinsu da yaransu.

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/22, 11:25 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Suna komawa daki Captain yayi tagumi hannu bibbiyu yana kallon yanda Mawahib ta goya Ashraf, Aryan kuma tana jijjigashi, wani irin tausayin tane ya kamashi, lalle in hakane Momy tayi qoqari, ahankali yatashi ya kar6i Aryan yafara jijjigashi yana zagaye dakin dashi.

Cikin kulawa tace"Yaya Captain kakawo shi saika kwanta kahuta"

Shiru yayi bai tanka mataba, tasake kallonsa tace"please"

Kallonta yayi yace"kidena fadamin sunan nan mana Honey"

Murmushi tayi tace"to Baby, Baby na kawo shi ka kwanta kahuta"

Sunkuyawa yayi yadora Aryan abayansa sannan yafara jijjigashi yace"da'inada damar dazan dauke ciwon naquda dana dauke miki Honey,meyasa rainon yaranmu zan barki kiyi ke kadai?"

Murmushi tayi cikin ranta tana jin yanda soyaiyar mijinta takesake nunkuwa acikin Zuciyarta, haka suka dinga lallashin yaran har sukai nasarar sakasu bacci sannan suka kwanta gaba dayansu sukai baccin.

Kwanan Captain Aryan uku agida sannan sukai shirin komawa Abuja,Hajiya kilishi tahada wa Mawahib kayan tsaraba sosai musanman abubuwan girki,Mamy tasake yimata nasiha akan kula da mijinta, bayan sun futo zasu wuce Mamy tayi mata sallama saboda gobe zata wuce maiduguri wajan bikin Nabil.
Ashraf da Nabiha ne suka rakasu Airport, saida jirgin su yatashi sannan suka dawo gida.

Da daddare suka sauka agida, gaba dayansu dakin Mawahib suka wuce suka gabatar da sallah sannan Mawahib tacire kayan jikinta tafara gyaran gidan, ganin yaran basa kuka hakan yasa shima Captain yazage sukai aikin tare, sai wajan qarfe tara suka gama aikin komai, kayan Yara ma suka adanasu inda yadace,batayi girki ba sai fita yayi yanemo musu abinci, sunacin abincin yaran suna gefen su kwance akan kujera, bayan sungama cin abincin tagyara wajan sannan tadawo falon, tun kafin ta zauna Captain Aryan yabata hannunsa, babu musu tasaka hannunta cikin nasa, yajata jikinsa tazauna akan cinyarsa, yayinda tadora kanta akan qirjinsa tayi luf.

Sunkuyawa yayi, yayi kissing dogon gashinta, sannan yasaka hannunsa ya sarqe musu hannun cikin na juna yace"Honey kode muyiwa Mamy magana asamo mana wadda zata dinga tayaki raino?"

Cikin sauri tadago kanta ta kalleshi tace"me raino kuma? haka kawai daga zuwa rainon yara takoma rainon mijina?"

Cikin sauri Captain Aryan yayi dariya yace"waye yace miki akwai wacce zataci gaba da raino na bayan ke?,Momy da Mamy sungama nasu, har abada kece zakici gaba da raino na nida yarana,Ina tausayin aikin dakike ne,kinashan wahala Honey..."

Kanta ta girgiza takama fuskarsa ta riqe tace"zanci gaba da kula daku har abada,bana fatan wata daban tashigo cikin rayuwar mu harta zama silar Samun sa6anina da mijina, Allah n daya bani su yasan zan kula dasune shiyasa,karka manta ubangiji baya jarabtar bawa da abinda bazai iyaba"

Kansa ya daga mata alamun gamsuwa da maganar tata,ahankali takoma cikin jikinsa ta kwantar da kanta akan qirjinsa, hannunsa yasaka yafara shafa dogon gashinta, yadaga kansa ya kalli yaransu da Mawahib tasaka musu kan fida a bakinsu sai tsotsa suke, dukansu idonsu biyu.

Mawahib tace"Baby da tuni nasa Mamy tamin allurar planning fa"

Cikin sauri ya kalleta yace"saboda me? meyasa?"

Dagowa tayi ta kalleshi tace"saboda munyi dakai mundena haihuwa"

Idonsa ya lumshe sannan yabude yace"yanzu de tayi miki kokuma bata miki ba?"

Kai tsaye tace"batamin ba"

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke sannan ya rungume ta yace"bazamu yi planning ba, insha Allah zanyi bakin qoqari na Inga nayi abinda yadace baki samu ciki yanzu ba"

Ajiyar zuciya tasauke tasake shige wa jikinsa, ahankali yafara shafa jikinta yana shaqar qamshin jikinta, cikin wata irin murya yace"Honey yarannan basa kuka yanzu,please inyi?"

Babu musu tadaga masa kanta, anan falon suka fara sha'anin su gaba dayansu sunfi ta daga hayyacinsu, Captain Aryan bai samu qwarin gwiwar daukanta zuwa sama ba, afalonsu suke gudanar da komai, yayinda tabar masa bakinsa abude itama tabude nata suka dinga zuba ihu San ransu, saida tafiya tayi nisan gaske, sannan yanbiyunsu suka fara kuka, Aryan ne yafara kuka shima Ashraf yafara, gaba daya yaran suka kaure da kuka sakamakon bakin fidarsu daya fice daga bakinsu, sai falon na Mawahib yakaure da kuka Kala biyu,yara suna kukan neman ceto, manya suna najin dadi, Koda wasa daga Mawahib har Captain babu wanda ya'iya yunqurin haquri da daya domin adauki yaran, suna jin kukan yaran sama sama,amma basu haqura da juna ba saida suka samu nutsuwa, Captain Aryan ya kwanta awajan yana sake maida numfashi, yayinda Mawahib tayi kokari tatashi zaune ta dauki yaran tafara basu nono, Captain Aryan kuwa idonsa a lumshe suke yana maida numfashi har lokacin, yana jin yanda take lallashin yaran amma yakasa Koda qwaqwqwaran motsi ne.

Washegari da safe Captain bai fita aiki ba, tun safe Mawahib take aiki saboda abokan Captain daza suzo domin ganin Yara, sai azahar sukazo sunji dadin yanda Mawahib ta karbesu, sunci sunsha sunyiwa Yara pictures, daga Nan sukai shirin tafiya inda suka ajiye wa yanbiyu kyaututtuka sosai.

Bayan sun tafi Mawahib tabar yaran wajan Captain Aryan tagyara gidanta tsaf,sannan tahau sama duk wani kayan sakawarta manya ta lodeshi waje daya, sai rigunan sallah data ware da hijabai na sallah, duk wasu manyan kaya datake amfani dasu ta ajiyesu sai qananun kaya saboda rainon yanbiyu.

Captain Aryan yashigo dakin hannunsa daukeda yaran, ya kwantar dasu a gadon shima ya kwanta, ya ajiye mata wasu kudi akan gadon,sannan shima ya kwanta.

Wayar Mawahib datake gefen Captain tayi qara,yadauka zai bata sai idonsa ya sauka akan sunan b me kiran, lokaci daya ransa yayi baqiqqirin tun kafin ta qaraso ta dauki wayar ya wullar da wayar akan gadon.
Mawahib ta kalleshi cikin mamaki ganin lokaci daya yanayinsa ya sauya, wayar ta kalla taga sunan Yaya Nabila yana yawo a fuskar wayar, ajiyar zuciya tayi ta dauka suka gaisa tayi masa ala Sanya Alkhairi akan aurensa sannan takashe wayar, tadawo gefen Captain ta zauna takama hannunsa ta riqe tace"meyafaru naga yanayin ka ya sauya?"

Cikin 6acin rai yace"oho"

Murmushi tayi tace"saboda Yaya Nabil yakirani?,bafa komai yacemin ba, kawai fadamin yayi cewa yayi aure yau,nayi masa ala Sanya Alkhairi shikkenan fa"

Cikin wata irin masifa yace"to saboda me zai kiraki? daya kiraki danme zaki dauka? saina futo fili nafada miki banason kina waya da wannan yaron sannan ne zaki fasa amsa wayarsa? cemasa akai bakisan bikinba? kokuma dole ne sai yaji muryarki sannan zai iya zaman auren?"

Mawahib ta girgiza kanta cikin damuwa,ashe yasan auren Nabil din amma koda wasa bai nuna mata ba,cikin damuwa tace" Yaya Captain Yaya Nabil yayanane fa"

Cikin sauri Shima yace"nima Asalamiyya ai yar'uwa tace"

Lokaci daya ranta ya6aci jin yakira sunan Asalamiyya,wayarta tabude ta bashi number Nabil din sannan tace"gashinan rufe number sa"

Babu musu ya kar6i wayar yayi blocking number Nabil sannan ya ajiye wayar.

Ta kalli kudin gefensa tace"wannan kudin menene?"

Murya ciki ciki yace"nakine"

Kallonsa tayi taga har lokacin baisa ki fuskarsa ba,tace"mekace?"

Cikin 6acin rai yace"nace miki nakine ha'a"

Dariya ce taso kamata,saitayi fuska ganin yanda yahade rai,cikin rashin sani tace"nawa kuma? yaushe nabaka kudi?"

"na Abbah"

Shine kawai abinda yace mata,lokaci daya ta dauki haske,wato kudin da Alhaji Ma'aruf yabata ne tun lokacin dayazo gidansu shida abokinsa harta bashi ajiya.
Murmushi tayi ta matso kusa dashi tadauki kansa ta dora akan cinyarta, ta sassauta muryar ta cikin sigar lallashi tace"fishin ne har yanzu?"

Shiru yayi yarabu da'ita, tasake sassauta murya tace" I'm sorry"

Cikin damuwa yajuya kansa gefe,tasaka hannu ta riqe kansa tace"me kakeso?"

Juyowa yayi yace"ke nakeso Honey"

Cikin jin dadi tace"amma kake fishi da Honeynka?"

Cikin shagwa6a yace"bakinsan menake soba?"

Murmushi tayi tadora bakinta akan nasa tafara kissing dinsa, ahankali yamiqo hannunsa yakama breast dinta,sun dade a wannan halin saida ta tabbatar yadena fishin sannan ta rabu dashi.
Chapter 67 · 0% Book details