← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 68

Sashe 18

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya kilishi ma tanajin furucin Alqali tayi maza tazo bakin qofar tatare tace"Babu inda zasuje saiya saki wannan yarinyar"

Alqali yatashi tsaye yanufi qofar,Alhaji khaleed da Alhaji Isa ma suka Isa qofar, Alqali yasa hannu ya matsar da kilishi gefe,yakamo hannun Mawahib yasaka acikin tafin hannun Aryan,sannan ya kalli Aryan d'in yace" d'auki matarka ka koma bakin aikinka"

(Kai wata dramar Sai a gidan Alqali,yau Hajiya kilishi tana ganin ikon Allah tsagwaron sa😂😂)
mutara zuwa gobe🙏🏻

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub ✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Tsawar daya matane yasa tajuya cikin dakin da gudu tana sakin wani irin kuka mai ciwo.

Jakar kayanta data futo dasu daqyar,gaba d'ayansu guda ukun yadagasu da hannusa guda daya,ya watsa mata su cikin dakin sannan ya rufe kofar yajuya cikin dakinsa cikin damuwa,yana zuwa Yafada kan gadon sa tareda hargitsa sumar kansa yana Runtse idonsa, lokaci daya yaji wani ciwon kai yana neman kamashi, bayason damuwa kokadan.

Cikin kuka tajanyo wayarta takira Mamy amma takasa cewa komai banda kuka babu abinda take, daga dayan 6angaren Mamy tayi shiru tanajin yanda Mawahib take kuka,adede lokacin tana kitchen, tasaka hannu takashe gas din sannan tabar kitchen din takoma dakinta ta zauna, bata hanata kukaba saida tabarta tayi kukan sosai, sannan tace"ya'isah haka"

Sai a lokacin Mawahib takejan zuciya alamun taci kuka ta qoshi,Mamy ta dafe goshinta alamun damuwa, ta tabbatar akwai abinda yake faruwa a gidan yaran, cikin sigar lallashi tace"meyake faruwa?"

Saida tarage kukanta sannan tace"Mamy ni gida zan tafi,Yaya Captain zai kasheni,mugune...."

Mamy tanajin wannan furucin gabanta yafadi,tayi tunanin ko takurawa yarinyar yake ta 6angaren auratayya,to amma kuma tana shakku akan hakan,cikin rashin sani tace"mekike nufi? meya miki?"

Cikin muryar kuka tace"yana takuramin,ni banason yana shiga harkata,ni kawai kowa yayi rayuwar sa,amma saiya dinga cin zalina yana sakani Ina faduwa,ni Mamy nagaji bazan iyaba"

Mamy tasaki ajiyar zuciya,tayi tunanin matsalar ta wuce haka, ashe Iya haka ta tsaya,duk da tana cikin dakinta saida ta rage murya sannan tace"Mawahib, keda Captain gaba dayanku nasan halinku ciki dabai, babu wanda zai kawomin qaran dan'uwan sa acikin ku bangane waye marar gaskiya ba,kinyi masa laifi ne?"

Cikin muryar kuka tace"Mamy ni banyi masa koma ba,Ina goge kitchen ban shiga sabgar saba yazo yaje far min da goran ruwa,Ina shara yasamin qafa nafadi,menayi masa dazai dinga cutata"

Mamy tayi murmushi marar sauti,gaba daya cikin bayanan na Mawahib tagama gane cewa da niyya Captain din yayi mata haka,soyake ta kula shi amma Kuma taqi kula shi ta nuna masa itama miskilar kanta ce,tasan cewa tun yana yaro bayason raini,Ashraf ma daya bashi Yan awanni kokadan bayason yaji Ashraf yana cewa ya girmeshi yanzu saisu fara musu har aje Ana tambayar kilishi waye Babba,gaba daya su biyun daga Mawahib din har Captain din kowa Yana buqatar ajashi ajiki a lallasheshi,shide dama tun yana yaro tasan cewa bai iya lallashi ba bare tasaran zai lallashi Mawahib,Shima kansa lallashin yakeso.
Cikin nutsuwa tace"Mawahib mekika dauki aure ne?"

Saida taturo dan qaramin bakinta gaba sannan tace"to Mamy dole ne saiya shiga harkata? kowa yayi rayuwar sa"

Mamy tace"karna sakeji kin fadi haka, kina qarqashin ikonsa ne yanzu,Sai abinda yace dake, duk cikin bayanin ki banji inda kikace kin gaishe shi ya mareki ba,banji inda kikace haka kawai kina zaune yazo ya rufeki da duka ba,Mawahib tayaya zakiga yayanki bazaki gaida shi ba? Kuna rayuwa gida daya kubiyu dole zaki gaishe shi,dole zaki tambayeshi koda abinda yake damunsa, idan kinzo gidama Abbanki a ranar zai maidake"

"to Mamy dole ne hakan? ni banason shi, banason auren nan,dole ne sai nayi masa magana?"(🙆🏻‍♀️)

Kai tsaye Mamy tace"dole ne,kishiga hankalinki Mawahib banason shirme,kina tunanin zai zauna ya dinga lalla6aki ne kamar Abbanki? Kece zaki masa biyaiya kimasa abinda yakeso saboda aljannarki kike nema,daga yau, gaisuwa kullum safe da yamma,girki kullum Kuma ba Kala dayaba,shara kullum mopping kullum, kinji abinda nace? Karna sakejin wata matsala makamanciyar wannan kuma"
Qit....takashe wayarta, Mawahib ta Kalli wayar da idonta,itace zata tambayi Yaya Captain meyake damunsa? tayaya? mutumin da inde ta zauna kusa dashi jikinta yadinga karkarwa Kenan ta'ina taga qwarin gwiwar yimasa magana?.

******

Washegari da sassafe yadawo daga motsa jiki, yana Sanye cikin Riga wacce take hade da hula, sai dogon wando qafarsa tana Sanye cikin farin kambos,yana shigowa gida dadan sauran gudunsa adede lokacin Nabiha tagama share musu compound din gidan gaba daya,kallo daya yayi mata yadauke kansa, Nabiha dabata lura dashi ba,kamar daga sama taji yace"kikai min abinci anjima"

Bai saurari abinda zata fada ba yawuce ciki,cikin sauri tabi bayansa da kallo tasaki wani irin murmushi sannan ta wuce part dinsu.

Darana takai masa abincin kamar yanda ya buqata, tajuya zata futo yace"zonan"

Babu musu tadawo ta zauna aqasansa, shikuma yana zaune akan gadon su, ya kalleta batareda da damuwa ba yace"Nabiha nasan bakyason auren nan,dole ce za'a miki,toki kwantar da hankalin ki Nima banaso,bazan 6oye miki ba, idan nasamu yarinyar danake so zan aureta,kema nabaki dama daga Nan zuwa lokacin da za'a liqa wannan aure,idan Kinga wani Wanda kikeso, toki sanar dani namiki alqawarin dakaina zanje nasamu su Daddy Nafada musu a dakatar da maganar auren nan,idan Kuma yanzu ma kinada Wanda kikeso toki sanar dani,Sai afasa wannan hade-haden"(🙆🏻‍♀️)

Nabiha tayi shiru tafara tunani cikin sanyin jiki,itade tasan cewa tun tashinta ba kula wasu samari takeba,asalima yanda gidansu yake da tsaro da wahala kaga saurayi yazo yana Neman su,abinda tasani shine tatashi da soyaiyar Yaya Ashraf acikin ranta, komai yayi birgeta yake,saide shi hankalinsa yana kan Mawahib,yanzu idan ta nuna masa batada saurayi kamar zai dinga yimata kallon wacce aka liqa masa yadinga hantarar ta,cikin dabara tace"inada saurayi amma bai shirya aure yanzu ba,makaranta yakeyi"

Cikin farinciki Ashraf yace"Alhamdulillah,tokinga ta kwana gidan sauqi,idan Naga yarinyar danake so,zan aureta,kema duk lokacin daya gama makarantar kifadamin, zan sauwaqe miki kije kuyi aurenku"

Mamaki yakama Nabiha,yanzu harya yarda da wannan qaryar data shirya masa? tayaya zata yarda yarabu da'ita bayan ya aureta?
Cikin ladabi tace"to Yaya Ashraf nagode"

Cikin sauri Shima yace"ki godewa Allah, zaki Iya tafiya"

Babu musu tayi masa sallama tafuto daga dakin.

******

tsawon sati biyu Kenan Mawahib bata sake saka Captain a'idon ta ba, Bata futowa sai taji baya gidan,zata futo ta dauki lemo ko madara da biscuit takoma dakinta, Shima Koda wasa bai nemetaba,yauda daddare daqyar tagama cin biscuit din,saboda ya'isheta, Kuma Mamy tace ta dinga yiwa Yaya Captain girki, ita Kuma qyashin yimasa girkin take,amma dole gobe zatabi umarnin Mamy tayi,kodan cikinta ma, wannan cin biscuit din babu inda zai kaita,shiyasa tayi sauri tayi wanka sannan tasaka kayan bacci ta kwanta saboda tana son tashi da wuri tayi gyaran gida tayi girki.

Acan dakin Captain kuwa bayan yagama abinda zaiyi Shima yayi shirin bacci, wayarsa tayi qara yana dubawa yaga Ashraf ne, cikin sauri yadauki wayar, Ashraf yace"yanaga kadauki wayar da sauri haka? Aryan anya kuwa? Kode baka zama da matarka ne kullum Ina kiranka saikayi caraf kadauka kod'an irin Ina zuwa zan kiraka dinnan babu?"

Cikin taqaici Captain Aryan yace"dan Allah kadena min maganar yarinyar Nan Ashraf,ni gaba daya na manta da'ita ma,tunda nabata abinci shikkenan na sallameta"(😲)

Ashraf yayi murmushi yace"kayi haquri mana,koba dan itaba, kodan Anty Mamy"

Captain Aryan yace"yanzu haka zanyi ta zama da'ita Kenan? Banson ganinta wallahi"(🙆🏻‍♀️)

Ashraf yace"to ya zakayi? Nima wallahi banason ganin Nabihan nan,but ni matsala ta tawuce, nace Koda bayan bikinne zan sauwaqe mata ta auri Wanda takeso"

Cikin sauri Aryan yace"yes hakan yayi,Nima zanyi tunanin Yaya zanyi da yarinyar nan"

Ashraf yace"kaikam Mawahib aita zame ma dole,zaka saki yarinyar Anty Mamy ne Kuma kadawo gidannan kaje wajanta? aikai auren zobe aka muku,nine de bazan dauki wannan auren nasu ba"(😲)

Captain Aryan yace"alaqa ta da Anty Ma-my daban,wannan yarinyar Kuma banda alaqa da'ita, saboda ita har yanzu Momy bata daukan kirana"

Cikin sauri Ashraf yace"what...? Amma Meyasa baka fadamin ba?"

"bansan tadama hankali ne,nabari ne idan nazo bikinka Sai muyi magana da'ita"

Ashraf yace"to shikkenan Nima zan bata haquri kafin lokacin insha Allah,wajan aiki zan tafi gobe da sassafe Nima, but kafin nawuce zanje nakai mana dinkunan mu insha Allah"

Captain Aryan yace"nima kwanciya zanyi, zanfita aiki da wuri gobe,sauqi nama kwana biyu Bata damuna da wannan kukan nata.

Ashraf yayi murmushi sannan yace"Bye"

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

Sassafe tatashi ko dogon hijabin datayi sallah dashi bata cire ba,tafuto Kai tsaye tawuce kitchen tashareshi tayi mopping, sannan tafara shirya abincin breakfast, ta dauki dankalin turawa tahada Chip salad,da pancake, sai tea Wanda tasaka kayan qamshi aciki sosai,tayi sauri tagyara wajan dining table din ta gogeshi, sannan ta dauko abincin ta jerasu akai, takoma kitchen tasake gyara shi, gashi de bawani girkin kirki tayi ba amma duk qamshi yacika gidan.

tadawo falo ta share tafara mopping.
Chapter 18 · 0% Book details