← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 68

Sashe 30

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin damuwa tace"mezan cemasa Nabiha? aisaina zauna awajan ma bare yasake gasa min wata maganar,nabarshi yana can yana waya da Asalamiyya"

Cikin sauri Nabiha datake kwance tatashi zaune tace"kikace me? kinsan me kike fada kuwa Mawahib? wata shegiya takira wayarsa kika taho kika barsu sukadai?"

Mawahib tayi murmushi tace"to Nabiha menene aciki? tunda yana sonta saiya aure ta ai,ni sonsa nake? tayaya zan hanashi kula wadda yakeso?"

Nabiha ta girgiza kanta cikin fada tace"kina bani mamaki Mawahib,waiku sai yaushe ne zaku zubar da wannan makaman qiyaiyar dakuke yiwa juna? dan bakya sonsa hakan saiya baki damar dazaki bar mijinki kara zube kowacce bola ta kulashi? Idan zaki nutsu kiriqe aurenki dakyau toki nutsu,kinaso ko bakyaso babu saki a auren ku saboda gaba da baya adaure kuke,duk iyayenmu kowa yazubawa aurenku ido aga yaya yanayin zaman naku zai kasance? kisawa zuciyar ki salama kiso mijinki, saboda bazaku ta6a rabuwa ba, Yaya Captain bazai ta6a sakinki ba saboda Mamy, Yaya Captain bazai ta6a sakinki ba saboda Daddy Alqali,Yaya Captain bazai ta6a sakinki ba saboda mahaifinki,idan kika bari yasakeki ma kinsan haduwarki da Mamy,kinsan ba zataji dadi ba saboda kowacce uwa fata take Allah yazaunar da yarta lafiya a gidan mijinta,ga makaman yaqi a hannunki amma kin tsaya kina wasa da damarki,taqamar Momy kilishi de shine Yaya Captain din, kuma aure yariga ya dauru, saboda haka Ina baki shawara ki kama Yaya Captain da hannunki, idan kika riqe shi shine zaki zauna lafiya a gidanki, idan kikai wasa kukaci gaba da zama ahaka bai soki ba, Ina tabbatar miki wataran Momy kilishi tanayi masa maganar auren Asalamiyya to zai amince da auren ta, idan Yaya Captain ya auri Asalamiyya kuwa wallahi kin kade,watarana korarki zaiyi daga gidansa,kuma kidawo gida kusa da Mamy nanma taci gaba da gasa muku baqar magana,tana takura miki, ni bance kisoshi dole ba,amma yanada kyau, ki janyo hankalin mijinki kanki...."

Cikin sauri Mawahib tace"amma Nabiha kina ganin hakan zai iyu?,ance ana musu allura karnaje allurar sojojinsa tatashi akaina,Yaya Captain nefa kina ganin...."

Kafin ta qarasa magana cikin sauri Nabiha ta katse ta,tace"nasan Yaya Captain ne,shi Yaya Captain din waliyi ne?,kikama shi, kokuma kibarwa sauran mata...."

Tana fadar haka ta kashe wayarta,Mawahib tazubawa wayar ido tana tunani Anya zata Iya?🤔

(Nabiha da alama akwai wani tsohon qulli tsakaninki da Captain shiyasa kika bada wannan shawara,...😂)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/11, 9:36 AM] AMINA KABIR CAPS: Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki.

Tunani tafara acikin shawarar da Nabiha tabata babu ta yarwa,to amma tayaya ne zatayi hakan bayan bata sonsa sannan kuma baijata ajikin dazata sake dashi harta Iya yimasa wani abu ba?
tabbas dan hakin dakai raina shine tsone maka ido,idan bata damu da kiran da Asalamiyya take masaba tabbas wataran zata jita acikin gidannan amatsayin matar sa.

Ahankali tasaki ajiyar zuciya,tazuro qafafunta qasa, sannan tatashi tsaye tafuto daga dakin,ahankali take sakkowa tayi tunanin har zuwa wannan lokacin wayar yake,saita hangeshi da computer agabansa idonsa yanakan computer yana aiki,tun kafin ta qaraso qamshin turarenta yagame falon,idonsa ne yake fuzgarsa ya kalleta, amma kuma yakasa,wasu takardu yake gani da'aka turo masa su ta email dinsa,saide yana karantawa ne kawai, amma baya fahimtar komai, tana zuwa falon taga babu plate din dayaci abincin, tajuya ta wuce kitchen anan taga yakawo matasu duka ya ajiye,mamaki ya kamata dama yana aiki?.

yanajin shigarta kitchen ya lumshe idonsa yabude, meyasa zuciyar sa take kwadaita masa son ganinta ne?

Ajiyar zuciya yasauke,cikin sauri kamar an tsikareshi yatashi yawuce kitchen din shima,yana shiga yaganta a tsaye tana goge abinda data zuba masa abinci da alama wanke su tayi,shigar jikinta ya kalla yaga tasauya wata zuwa kayan bacci ba shigar d'azu bace,ta nannande dogon gashinta abayanta,wata irin ajiyar zuciya yasauke saboda ganinta,kamar wanda yadad'e baisata a'idonsaba, tanajin ajiyar zuciya abayanta tajuya da sauri,yana ganin juyowarta shima yabude fridge zai dauko ruwa,Mawahib tazuba masa ido taga yana dube dube,Kuma shibe mata magana ba,ta tsaya sosai tana kallonsa yayinda shikuma yarasa mezai dauka sai dube dube yake, itace ta katse musu shirun tace"meza'a kawo?"

Cikin sauri ya kalleta sannan yadan kawar dakai gefe yace" ruwa"

Tace"to"

Sannan ta nufo fridge din,cikin sauri ya juya yafice zuwa falo, tana dubawa taga ga gorar ruwan nan dayawa amma Kuma taga shi Sai dube dube yake kamar baiga ruwan ba,amma ko marar gani ne yasaka hannu ya laluba zaiji ruwan,to tunanin meyake dayahanashi ganin ruwan? Wata zuciyar tace da'ita tunanin Asalamiyya (😂)

Girgiza kanta tayi sannan ta dauko masa ruwan tareda cup, tadawo falon ta zauna agefensa sannan ta bude ruwan ta zuba masa tace"gashi"

Idonsa yanakan computer yayi qarfin halin mazewa bai kalleta ba yace"thanks"

shiru sukai na wani lokaci ita tana kallo maganganun Nabiha suna mata yawo a kanta, shikuma yana karanta takardun cikin ransa yana mamakin zamanta.

Kuma kokadan yaqi kallonta,cikin zuciyarsa yanason ya kalleta saide Kuma yana kunyar hakan.

tana cikin kallon bacci ya dauketa kasancewar da wuri take kwanciya kullum saboda tashi sassafe datake yi, baisan tayi bacci awajan ba,saida yagama karance karancen sa, sannan ya rufe computer zai tashi, yana juyawa yaga ta dora kanta akan kujera tana bacci cikin kwanciyar hankali, mamaki ya kamashi, daga kallo Sai bacci?

Kasancewar falon nasu akwai haske sosai hakan yasa Yazuba mata ido yana qare wa halittarta kallo a Karon farko arayuwarsa, ajiyar zuciya yasaki yaharde hannunsa a qirjinsa,yabi bajajjan hips dinta da kallo duk da tana zaune,yamaida kallonsa zuwa ga madaidatan qirjinta Wanda babu brezia amma gasunan atsaye qyam,ya Kalli gashinta dayake da duhu sosai kamar na Mamy,nan take maganar Ashraf tafara dawo masa acikin ransa,(yarinyar tanada qira mai kyau)
tambayar kansa yafara meyasa yakeson yawan kallonta cikin kwanakin nan? meyasa yakejin sanyi acikin ransa duk lokacin daya jishi akusa da'ita?
Idonsa ya lumshe sannan ya motsa jan lips dinsa yanason yakira Sunanta tatashi amma yakasa,tunda yake da'ita bai ta6a Kiran sunan taba,daga ke,shikkenan saide Kuma yafadi maganar sa Kai tsaye batare daya Kira sunan nataba,yanzun mezai ce?

Ahankali yafara dukan kujerar sannan cikin murya qasa qasa yace"ke...,tashi"

Cikin baccinta taji kamar ana magana,saitayi juyi ta banqaro qirjinta tana so tajuya tagyara zamanta.
Cikin sauri ya kawar da kansa gefe,gabansa yafara faduwa yanajin yanayinsa yana son sauyawa.
Ahankali yafara kawo hannunsa jikinta,ya Runtse idonsa sannan yasaka dayan hannun ya dauketa cak yamiqe tsaye, Sai yajita shafal babu nauyi,cikin bacci tasake gyara kanta a faffadan qirjinsa tayi luf, yanda ta motsa kanta a qirjinsa hakan yasa gashinta data daure abaya ya kunce yazubo akan farin hannun Captain wanda yake cikeda gashi baqi,tsayawa yayi cak Yazuba mata ido yana kallonta,yasake gyara mata ruqon da yayi mata, garin gyaran ruqon hannunsa ya damqi hips dinta,lokaci daya yaji wani irin shock ya kamashi,ahankali cikin rashin kuzari yafara taka stairs din zuwa dakinta, da hannu daya ya riqeta, yasaka dayan hannun yabude dakin nata,wani irin qamshi mai dadi yadaki hancinsa,jin yariqeta da hannu daya saitaji kamar zata fadi hakan yasa tasaka duka hannunta tayi masa wata irin kyakykywar runguma (🙆🏻‍♀️)
Lokaci daya Captain ya kar6i saqon,nan take suka zube akan gadon nata,rabin jikinsa yafada kanta,jan lips dinsa yasauka akan dan qaramin pink lips dinta,cikin shagwa6a tabude idonta tanaso tayi kuka.

ganin zata masa kuka yasa nan take ya rikice,cikin sauri yadagata,gaba daya ya dimauce banda jikinsa dayake wata irin mahaukaciyar rawa,cikin sauri yace"Sorry, sorry okay? sleep...."

Nan take Mawahib ta wartsake daga baccin datake,gabanta yayi wata irin faduwa,cikin sauri tayi qasa da kanta cikin wata irin matsananciyar kunya,takasa hada ido dashi.
Cikin sauri Shima Yajuya yafice yabar dakin zuwa nasa dakin.

Yana zuwa dakinsa yazauna akan gado tareda dafe kansa da hannunsa(🤦🏻‍♂️)
meyasa tafarka? yasaka hannu yashafa lips dinsa, yanzu data ganshi tayaya zai Iya sake kallonta?.

Kwanciya yayi ko falon baisake komawa ba bare yadauko computer sa,daqyar yasamu bacci ya dauke shi sakamakon wata irin sha'awa data dameshi cikin dare,wadda tasa asubar fari yayi wanka sannan yagyara jikinsa yafita zuwa masallaci.

Bayan yadawo kawai wanka yashiga ya shirya, sannan yafice cikin sauri yabar gidan saboda kunyar hada ido dayake da'ita(😂)

Mawahib kuwa jikinta tagama qarewa kallo taga de babu alamun wani abu ajikinta,sannan tasamu nutsuwa takoma ta kwanta, saide baccin gaba daya ta nemeshi ta rasa,anya ba sauya Yaya Captain akayi ba? shine yadauke ta da hannunsa?

mamaki yahanata bacci da wuri, hakanne yasa ta makara bata tashi da wuri ba,saida gari yayi haske sannan tayi sallah, bata sake gigin komawa bacci ba,tayi azkar sannan tafuto tafara gyara gidan kamar yanda tasaba,ganin har qarfe tara na safe bataji motsin Yaya Captain ba hakan yasa ta leqa ta window anan taga babu motarsa guda daya, hakan ya tabbatar mata da cewa yafita aiki ne.

Tunda abun Nan yafaru Captain yafara qauracewa Mawahib,baya yarda su hadu kwata kwata,duk yanda zuciyarsa takeson ganinta haka yake faman yakice tunanin aransa,yanaji idan baiyi nesa da'ita ba wataran zai Iya tafka abun kunya, bayan kuma bada ita ya tsara hakan ba,ya tsara cin amarcinsa ne bayan yasamu wadda yakeso, cikin kwanakin aiki yasaka agaba kawai,idan zai fita Sai yaji babu motsin ta sannan zaiyi sauri Yafuto.

Anata 6angaren kuwa hakan bai dameta ba,saima sabuwar rayuwa data budewa kanta tana cin abinda takeso, tana shan abinda takeso, sannan tasaka kayan datake so tayita yin kallo, aikinta kenan, kusan satinsu biyar suna wannan halin 6oyewa junan.

Kamar kullum yauma bayan tagama girkin rana,saide ta makara bata gama da wuri ba,Sai wajan qarfe hudu na yamma sannan tagama,David mai gadi ta zubawa sannan tafuto Sanye cikin abaya mai launin pink, tun zuwanta gidan bata cika saka Abaya ba saboda dama tafi sakawa ne idan zata fita, Kuma Abuja tunda tazo ko nan da can bata fita ba,dankwalin abayar ta yana akanta,sannan ta dauko abincin tafuto zuwa compound din gidan.
Chapter 30 · 0% Book details