← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 68

Sashe 36

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mawahib tabi kayan jikinta da kallo taga rigar da fadinta sosai,kokadan bata nuna shape din mutum,menene aibun shigar?
ganin babu damar tambaya hakan yasa batayi masa musu ba tatashi takoma dakinta tasaka wata rigar,tafuto,tana zuwa falon taga baya nan,cikin sauri tafuto zuwa compound din gidan, yana tsaye yana waya ajikin motarsa,tunda tafuto Yaqare mata kallo tana Sanye cikin dogon hijab jalbab har qasa,baka ganin rigar data saka, tasaka glass medan fadi jan duhu a fuskarta, tariqe Jakarta a hannunta na dama, kasancewar ta fara tas, Sai glass din yayi mata kyau yasake qawata fuskarta,tana zuwa kusa dashi ya janye idonsa daga kanta, sannan yakashe wayar yabude mata motar da kansa,Mawahib ta qame awajan, tana tunanin kansa ya budewa Mota kokuma ita ya budewa?, kallonta kawai yayi, sannan yajuya yakoma dayan side din yabude yashiga, daga kallon da yayi mata anan ta fahimci cewa yana nufin tashiga, shiyasa cikin sauri tashige sannan tarufe motar suka tafi, David Sai daga musu hannu yake.

Suna daukan hanya batare daya kalleta ba yace"cire glass dinnan"

Cikin sauri tasaka hannunta tacire, tabude Jakarta tasaka shi aciki, babu wanda yasake magana a cikinsu, har sukaje wajan wankin kai, wanda ita de batasan inane ba, shine ya kaita da kansa, suna tsaya tabude zata fita,taji yace"qarshan number Anty Ma-my"

Cikin sauri ta juyo ta kalleshi saitaga atm dinsa yake bata,tana so tace masa akwai kudi a Jakarta to amma tana shakka ganin yanda yahade fuskarsa, babu musu ta kar6a sannan tace"thanks"

"idan kingama kikirani"

Kallonsa tayi sannan tace"to"
tafuto tarufe masa motar, sannan tashige wajan, tana jujjuya atm din nasa a hannunta tana tunani ,qarshan number Mamy ne pin dinsa? wacce irin shaquwa cene a tsakanin sa da Mamy?
Saida yaga shigewarta sannan yaja motar yana fatan ace Karta sake maida wannan glass din idonta saboda ba qaramin kyau yamata ba.
Ta dade awajan sosai kasancewar gashin nata yanada yawa,kuma saida aka mata harda fulawa ta baqin lalle a hannunta, sannan tabasu atm din suka cire kudin su,ana gama wanke mata lallen takira wayar Mamy bayan sun gaisa zuciyarta daya tace"Mamy dan turomin number Yaya Captain,naje wajan wankin kai yace idan nagama nakira shi"

Mamy tayi shiruuuu tana tunani,mata ce take tambaya aturo mata number mijin ta wai yaran nan anya Zaman nan nasu kuwa babu gyara? kina zaune da miji wata da watanni amma bakida number sa wacce irin rayuwa ce wannan?ajiyar zuciya tayi, cikin ranta tace akwai matsala, da sauran gyara,a fili saitace "to bari inturo miki,kingama ne yanzun?"

Tace"eh nagama,inaso na koma da wuri saboda baquwarki da kikace zatazo Kuma Kinga har azahar tayi"

Mamy tace"to shikkenan Allah Yakiyaye hanya"

takashe waya tatura mata number Captain,sannan takira qawarta Hajiya Saudat,bayan sun gaisa Hajiya Saudat tace"yanzu nake shirin kiranki dama, ki turomin address din gidan zanfita yanzu"

Mamy tayi ajiyar zuciya tace"Sister Saudat akwai matsala,Zaman yarinyar nan taki akwai gyara, idan kinje inaso kisha cikinta sosai tafada miki duk abinda yake faruwa Sai kiyi settling komai,Ina aiko mata maganin mata tana tambaya ta maganin menene, sannan yanzu haka da'ita nagama magana tana tambaya ta number mijin..."

Sister Saudat tace"haba sister Maryam,to tayaya zakibarta haka bazaki kirani da wuri ba Kuma yarinya tana zaune a'irin wannan garin, gari garin 'yan boko Kuma mijin ta me yawan fita salon yaje yagano wata a waje?"

Cikin damuwa Mamy tace"Saudat bazaki gane ba, naci buri sosai akan auren Mawahib,nabaki labarin yanda auren ya kasance de,a yanda na tsara maiduguri naso turata duk su koya mata komai ayi mata gyaran jiki kamar ma wata biyu,to komai yazo a baibai, Ma'aruf ya ruguza min komai"

Sister Saudat tace"to shikkenan, yanzu de ki kwantar da hankalinki,zanje gidan ai, duk yanda ake ciki zakijini"

Daga nan sukai sallama tareda kashe wayar.

******

Wani soja ne yazo ya dauketa ya maida ta gida, tana zuwa tacire hijabin jikinta tafara qoqarin girkawa baquwar tata abinci,bata gama ba Sai yamma, saboda tahada harda girkin Captain tayi komai gaba daya,tayi wanka ta zauna afalon kenan, David yashigo yasanar da'ita tanada baquwa,ta bashi umarnin yashigo da'ita,saida yakawo ta har falo sannan Yajuya, Mawahib tatareda cikin farinciki,sister Saudat ta rungumeta tana kallon tsarin gidan nasu cikin ranta tana yabon kyan gidan, zama sukai a kujera Mawahib ta gabatar mata da abincin da tayi mata tareda lemuka da ruwan sha,ta kunna musu kallo sunayi, sister Saudat tadage tana kallon duk da ba ma'abociyar kallon bace,amma dan Mawahib din tasake da'ita yasa tasaka kallon agaba sunayi suna fira kad'an kad'an har yamma,saida taga Mawahib din tasaki jiki da'ita sannan tace"karatu yafara nisa Kuma gashi Captain yagudo dake Abuja"

Cikin murmushi tace"A a baiyi nisa ba,ai yanzu ne zamu shiga level 200"

Sister Saudat ta jinjina kanta sannan tace"hakane fa,to amma ai zai barki Kici gaba da karatun ko?"

Tace"bansani ba wallahi,ban ta6a yimasa maganar ba"

kafin sister Saudat tayi magana Captain yashigo falon,gaba dayansu qofar suka kalla,Mawahib tana ganinsa tayi qasa da kanta, tace"sannu da zuwa"

bai amsa mataba ya tsugunna cikin ladabi yacewa sister Saudat"sannu da zuwa,barka da yamma"

Cikin farinciki tace"yawwa sannu da zuwa,ya aiki?"

Kansa a qasa yace"Alhmdulillah"

Daga nan yatashi yawuce sama,Sis Saudat ta bishi da kallo cikin ranta tana fadin lalle 'yar tasu tayi dacen miji irin wanda kowacce mace take burin samu.

Mawahib tadago kanta taci gaba da kallo ko inda Captain yake bata kalla ba, cikin mamaki sister Saudat tace"bazakibi mijin naki bane?"

Zaro idonta tayi sannan tace" la'ila...aibana zuwa"

Sis Saudat ta jinjina kanta sannan tace"Meyasa?"

Mawahib tace"ai agida ma bayaso muna zuwa dakinsu,nikuma tsoro nakeji"

Cikin shan ciki Sister Saudat tace"eh Kuma hakane,dole Kiji tsoro,babu dadi ka takura wa mutum,amma idan yanason wani abu fa yakuke?"

Mawahib tace"ai girki ne kawai,idan nayi masa na ajiye masa shikkenan,zaizo yaci,girkin ma da bayaci, shine Mamy tace inci gaba dayi masa"

Sister Saudat ta zubawa Mawahib ido tanajin komai, tace"amma duk dadin girkin ki bayaci? yanzu yanaci sosai ko?"

Tace"yanaci yanzu,idan yaci zai fita wajan aiki"

Sis Saudat tace"to idan yadawo yana sake fita ne? kokuma zama kukeyi agida?"

Tace"wataran yana fita,amma ba sosai ba,nide dakina nake tafiya inyi bacci shikuma yana aiki a falo"

Sis Saudat ta Zaro ido tace"bacci?"

Mawahib tace"eh,saboda nagaji,kullum sainayi gyaran gida da girki"

Sis Saudat ta kalleta ayanda tadanji zancen nata ta fahimci abubuwa dayawa,cikin sigar dabara tace"to yanzu kitashi kije dakinsa kiji koda abinda yake buqata, Kinga yadawo daga wajan aiki,Kuma Ina zaune afalon,bazai Iya futowa yazo yazauna ba, kije kiyi masa sannu da zuwa idan akwai abinda yakeso sai kizo kikai masa"

Mawahib tace"to"
Sannan tatafi sama cikin ranta tana mamakin wannan baquwa,Kuma daga zance saita turata dakin Yaya Captain?
to taje ta masa me?

Sis Saudat tabi bayan Mawahib da kallo ta girgiza kanta,da alama girman qashi ne da'ita kawai,amma batada wayo,tuni matan bariki zasu Iya qwace mata mijin...

tana zuwa bakin qofar dakin takama handle din dakin ahankali tatura tashiga a karo na biyu tunda tazo gidan,wani irin sanyin esi da daddadan qamshi ya daki hancinta,adede lokacin ya futo daga toilet yasaka hannunsa biyu yana gyara sumar kansa,murdaddan jikinsa ya baiyana sai sheqi fatarsa take,tana ganinsa tayi sauri tajuya baya tareda runtse idonta tana jiran taji saukar duka kamar yanda yata6a cewa zai daketa lokacin dataje dakinsu.

Kallonta yayi,yana mamakin zuwanta dakin, ahankali yatako yazo dab da'ita,kamar zai rungumota tabaya,yadan karkatar da kansa dede kunnanta cikin rada yace"lafiya?"

Cikin sauri ta girgiza masa kanta,jitake zaiyi mata masifa saitaji sa6anin haka,saima magana daya mata cikin rad'a.
ganin batason hada ido dashi ne yasa yajuya yazauna abakin gadon sannan yace"bani mai"

rikicewa tayi,cikin sauri tajuya wajan mirror ta dauko masa wani mai batasani ba shi yake shafawa koba shi bane, ta qarasa wajansa kanta aqasa taqi kallonsa tace"gashi"

Kallon fuskarta yayi yaga idonta a runtse,da alama a rikice take,wani dan qaramin murmushi yayi cikin jin dadi yasake cewa "bani kayana"

Cikin sauri tasake juyawa tabude Wadrob din tarasa wanne kaya zata bashi?
ganin yamma ce Kuma tasan yafi saka kayan shan is'ka saita dauko masa qananun kaya,ta bashi, yana kar6a tayi sauri zata fice daga dakin taji yace"zonan"

gabanta ne yafadi,mekuma zata masa?
Ahankali tajuya taqarasa wajansa ta tsaya kanta aqasa tana wasa da hannunta, kamar wasa taji ya fuzgota saigata d'are d'are akan cinyarsa,idonta ta runtse hannunta na hagu ta dorashi akan qirjinsa da fatar jikinsa tayi sanyi sosai, kallonta yayi yaga idonta a runtse,dan qaramin bakinta Sai motsi yake amma takasa magana,meyasa ne wasu lokutan take tsorace dashi? ya kamata ace yafara qoqarin cire mata wannan tsoron nasa, hannunta dayake kan qirjinsa ya kalla ahankali yasaka hannunsa ya janye hannun nata,sannan zubawa fulawar hannunta ido yafara murza hannun, wani iri Mawahib tafara ji ajikinta, wani irin yanayi wanda tunda take bata ta6a Jin irin wannan yanayin ba,amma idonta a runtse yake har lokacin,daina murza mata hannun yayi,cikin sigar rad'a yace"yaushe aka miki wannan abun?"

Sarai tasan da zanen lallan hannunta yake,batareda tabude idon ba tace"awajan wanke kai"

Cikin wata irin murya qasa qasa kamar meyin rad'a yace"shine baki nunamin ba? i luv it..."

Yafadi haka sannan yakai hannun saman lips dinsa,ya lumshe idonsa yasakar mata wani irin kiss

Cikin sauri tabude idonta ta kalleshi,a lokacin shima yabude idonsa suka zubawa juna ido tsawon yan sakwanni,cikin ranta take mamaki dama yana lura da wannan abun?
cikin sauri tafara motsa wa zata bar jikinsa, bai hanata ba yabarta tatashi,saide tana zuwa bakin qofar dakin tun kafin tabude taji yace"wait.."

Cak taja ta tsaya awajan,amma koda wasa batayi kuskuren juyowa ta kalleshi ba, tashi yayi yasaka kayansa, yafesa turare sannan yatako yazo wajanta,kudi yabata me yawa yace"kibata tasha mai"

Kanta ta gyada masa sannan tace"to Allah yasaka da Alkhairi"

Yaji dadin addu'ar data masa,baice da'ita komai ba, yakamo hannunta suka futo, saida sukazo falon qasa sannan yasaki hannunta yafice daga gidan gaba daya

Sister Saudat taga yanda yaruqo hannun Mawahib din amma saita maze ta nuna bata gansu ba har Mawahib kusa da'ita tazauna, tana zama taji tana wani qamshin turaren daban,tayi murmushi cikin jin dadi da alama akwai abinda yafaru,taji dadin hakan sosai,Mawahib tabata kudin tace"gashi yace kisha mai"

Sister Saudat takalli wannan uban kudi cikin ranta tafara tunani irin wannan kudi haka ai dole nema ta hurewa yarinyar nan kunne Shima yaga canji(🙊)
Chapter 36 · 0% Book details