Sashe 19
Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adede lokacin Yafuto daga dakinsa yayi masifar kyau cikin uniform dinsu na sojoji,kamar kullum yar qaramar bindiga tana soke a aljihun wandon sa nabaya,tun kafin yasako qafarsa kan Stairs yaji wani qamshin girki yadaki hancinsa,Mawahib kwata kwata bataji futowar sa,tasaka mopper akan stairs din zata fara gogewa taji alamun takun mutum,bata tsammaci ganinsa ba hakan yasa tanajin takun ta zabura cikin tsoro,hakan yasa santsi ya dauketa zata zube a wajan,kamar wasa tajita acikin jikinsa, shi kansa baisan menene ya fusgeshi ba harya tareta daga faduwar da zatayi,Mawahib kuwa cikin tsoro taqi bude idonta, kawai jira take yasaketa tafadi a wajan kamar yanda yayi abaya.
Batare da tunanin komai ba Captain yatsaida ta, saida yaga ta tsaya da qafafunta sannan yasake ta, yazo ya ra6a ta gefenta zai fice daga falon,fuska babu alamun wasa yace"kikula"
Abinda yace da'ita Kenan yakama handle din qofar falon zai fice,Mawahib dabata gama dawowa daidai ba daga tsananin mamakinsa, ganin zai fita cikin sauri tace"ina kwana?"
Baice da'ita uffan ba yabude qofar falon,tasake bin bayansa da kallo tace"break fast..."
Kai tsaye yace"no"
Daga haka ko waiwayen ta baiyi ba yafice cikin sauri,Sai dirin motarsa taji alamun yafice daga gidan.
Tasaki ajiyar zuciya tayi sauri ta qarasa aikin datake, sannan ta hau Sama tayi wanka,ganin baya gidan yasa tasaka wata yar 6ingilar Riga marar hannu,gaba daya tsawon rigar Iya gwiwar ta tatsaya, tawuce ta bararraje a dinning tafara yin break fast dinta cikin kwanciyar hankali tanaci tana danna waya,tunda tazo gidan yaune Karon farko data ta6a girki,kullum batada aiki saicin lemo da biscuit,shiyasa taci abincin sosai,tatashi takoma sama tasako zumbulelen hijabi akan rigar jikinta, hijabin dogo ne har qasa,ta dauki sauran abincin data rage takaiwa megadinsu maisuna David,bayan tagaidashi ta bashi abincin,cikin girmamawa ya kar6a,saitayi mamakin yanda yake bata girma kamar wata matar wani, harta tafi David yana binta da kallo yana sake jinjina wa oga Aryan akan yanda ya murji amarcinsa hankalinsa kwance(😲)
tunda sukazo gidan shida Madam kullum suna ciki saiyau yata6a ganin tafuto,ya tabbatar wannan yarinyar yanda ta keda kyannan Sai yanda tayi da oga Aryan.
Zuwansa wajan aiki da awa uku,suka shirya fita ganin wani daji zasuga yanayinsa kafin atura rundunar sojoji zuwa dajin.
Futowa sukai susu ukun suna tafiya zuwa ma'adanar Helicopter dinsu, ga wasu sojoji a bayansu kowa fuskarsa a daure kamar Wanda aka musu albishir da mutuwa.
Tun kafin su qarasa wajan helicopter din mai launin army green driver ya tadashi, babu wata-wata suka shige ciki duka su ukun.
Tunda suka shiga idon Captain Aryan yana waje,yana ganin yanayin yanda hanyar take,basu yi tafiya mai nisaba suka qaraso dajin mai cikeda duhuwa dakuma bishiyoyi.
Jirginsu bai sauka ba,kawai a'iya wajan yake zagaye.
Major Abdullahi ya Kalli Captain Aryan yace"Captain wannan ne dajin damuke tunanin yana cikeda yan bindiga"
Cikin zafin nama Captain Aryan yace"Okay sir..."
Colonel Abdul wahab yadora da fadin"dole Sai kunyi taka tsantsan dashi,kamar yanda labari yazo mana suma labari zaije musu zamu kawo musu hari"
Cikin biyaiya Captain Aryan yace"angama Sir"
Daga Nan suka Bawa driver umarnin Yajuya dasu.
Bayan sunkoma kai tsaye office dinsa yawuce yadauki takardar taswirar dajin yana sake qarewa wajan kallo ta yanda shida rukuninsa zasu cinmusu kafin yan bindigar su ankara.
Tsawon sati uku Captain Aryan yadauka yana sake horar da rukunun sojojinsa dayake aiki dasu, saboda dajin dazasu fuskanta, har zuwa wannan lokacin Mawahib kullum saita tashi da safe tagyara gidan tayi masa girki amma ko saudaya bai ta6aci ba,tun tanayi dashi hartazo ta daina tadinga dafa wa itada David Maigadi.
zaiji qamshi yacika gidan amma acewarsa bazaici jagwalgwalon taba.
Adede lokacin bikin Ashraf yazo,bai tafi da wuri ba kasancewar kullum yana bawa Yara horo, Sai ranar daurin auren yaje, tunda yaje kwata-kwata basu zaunaba shida Ashraf din,duk da bawani farinciki sukeda auren ba, hakan bai hanasu yin kyauba,farar shadda suka saka tareda babbar riga,komai iri daya sukasa, tundaga kan takalmi har hula da Agogo da links din dayake hannun rigar, babu Wanda yake gane waye angon a cikinsu,acikin masallacin suka zauna da sauran abokan su yan unguwa,har limamin unguwar yadaura auren Ashraf da Nabiha Akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalanba.
Basu samu shiga gidaba Sai can dare wajan qarfe goma da rabi zuwa lokacin mutanan gida baqi sunyi sauqi Sai Wanda baza'a rasaba,kai tsaye part din Mamy suka shiga,tana zaune tana kallo afalo taci kwalliya cikin leshi Riga da zani Sai walwali take kamar ba dare ba,falon nata tsaf Sai tashin qamshi yake,ita kadaice takeyin kallon, Sai baqi Yan kwana datayi yan'uwan mama Sadiya, suma Kuma suna dining tazuba musu abinci sunaci, tana ganin shigowar su Ashraf da Aryan ,cikin fara'ah tace"A a angwaye"
Ashraf yayi murmushi, atare suka hada baki suka gaisheta,Captain kuwa fuskarsa babu murmushi,daga gaisawar nan yayi qasa da kansa(😂)
Ashraf yace"Anty Mamy yunwa mukeji"
Mamy tayi murmushi tace"to bari insama muku wani abu sai akai muku daki,ahado muku da coffee ne?"
Ashraf yasake bata amsa yace"eh ahado"
Ta miqe tsaye zata wuce kitchen ta Kalli Captain Aryan da kansa yake qasa Koda wasa yaqi kallonta,cikin ranta tace Allah karimun waheedun yau nice nazama dodon Aryan,tun ranar da Mawahib takirata tana kuka Bata sakejin kansu ba kosun shirya kansu kokuma sunacan sunacin mutuncin juna oho musu,tace masa"Captain ya Abuja?"
Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace"Alhamdulillah"
Daga nan baisake cewa uffan ba.
Ashraf yace"Anty Mamy kicewa mama Sadiya Wanda suka raka yarinyar Nan su zauna su kwana tareda ita,zan kwanta anan tareda Aryan"
Cikin fahimta Mamy tace"to shikkenan bari in kawo muku abincin saina wuce part dinta Infada mata"
Captain Aryan yana jinsu,yana ganin shigewarta kitchen yatashi tsaye yace"tashi mutafi"
Ashraf yayi murmushi yatashi suka futo,part din Hajiya kilishi suka nufa tundaga bakin qofar falo sukejin hayaniyar mutane, alamun akwai sauran Wanda basu kwanta ba, Hakan yasa suka juyo suka koma cikin dakinsu, suna zuwa Ashraf ya kwashe da dariya yana qoqarin cire babbar rigarsa,ya Kalli Captain Aryan cikin dariya yace"wai Kai kunyar Anty Mamy kakene?"
Captain Aryan ya yatsina fuska yace"kunya Kuma?"
Ashraf yace"ni zaka rainawa wayo? tunda mukaje kayi kidis dakai kamar wani baqo,saini kadai nake mata magana "
Cikin damuwa Captain Aryan yace"niba kunyar ta nakeji ba"
Ashraf yace"kunya kakeji mana,kazo gaban surukarka, tun yanzu kana irin wannan kunyar idan kunfara amarci gidan zaka daina shigowa Kenan?"
Captain Aryan yadaure fuskarsa tareda girgiza kai yawuce toilet domin watsa ruwa,bayajin har abada wannan abun da Ashraf yake fada zai faru tsakanin shida wannan yarinyar, yana shige wa toilet adede lokacin Mamy takawo musu abincin sannan tayiwa Ashraf saida safe tafice daga dakin.
Sama Sama sukaci abincin sannan Ashraf ya kalli Aryan yace"kaga saqon dana turawa Mama Sadiya yanzu"
Yafadi haka yana bawa Captain Aryan waya.
Captain Aryan ya kar6i wayar yafara karanta saqon a fili kamar haka "Mama nasan Nabiha batason auren nan,Nima kuma kinsan hakane,to tasanar dani akwai Wanda take jira,Ina miki alqawari babu abinda zai samu Nabiha,bazan ta6a miki yarki ba,yanda kuka kawota haka zata auri Wanda takeso, daga Ashraf"
Captain Aryan yana gama karantawa yace"eh tura mata,dansu tabbatar wannan aure auren dasuka qulla mana babu inda zaije, ko Nima in turawa Anty Ma-my irinsa?"
Ashraf yace"karka tura,gara nawa hadin da sauqi akan Naka, kaifa ta ko'ina adaure kake, baka Isa kasaki yarinyar Anty Mamy ba, nidin de daba dogon mutunci nakeyi da Nabihan ba to zan'iya tura musu, tashi muje wajan Momy"
Haka suka nufi part din Hajiya kilishi.
Alokacin da Mama Sadiya taga saqon saitayi murmushi ta nunawa Mamy, itama ta karanta, Mamy tayi dariya tace"to bari mugani ayi Zaman auren, tunda kikaga haka da Aryan din sukai wannan shawarar, bazai turo ba sai Aryan yasani, duk su biyun zamu gauraya ne, dani suke zancen"
shabiyu saura,suka qarasa part dinsu, Alqali yana zaune afalo yana duba hisnul Muslim yaga shigowar su, Kai tsaye wajan sa suka nufa tun a wajan daurin aure rabon su dashi, kasancewar ko acikin duhu suke zai banbance su shiyasa Kai tsaye ya Kalli Ashraf cikin rashin wasa yace"mekake baka tafi gidanka ba?"
Cikin ladabi Ashraf yace"Daddy dama Naga akwai baqi a gidan ne dangin mamanta,shine nace su kwana tare Nima zan kwanta anan tareda Aryan"
Jin wannan bayanin nasa yasa ya gamsu,baisake cemasa komai ba Yajuya wajan Aryan yace"yaka baro iyalin naka?"
Captain Aryan yace"Lafiya kalau Daddy"
Alqali yace"babu damuwa deko?"
Kai tsaye yace"babu komai"
Alqali ya jinjina kansa sannan yace"Kariqe yarinyar nan amana,nasan babu Wanda yakeson auren acikin ku,amma karka duba wannan,Koda yaushe karka manta mahaifiyar ta ta rungume ku a lokacin da bakwa tareda taku mahaifiyar,saboda haka ko bayan raina karka kuskura kasani hannunta"
Lokaci daya jikin Captain yayi mugun sanyi,cikin sanyin jiki yace"to Daddy"
Alqali yace"zaku Iya tafiya"
Cikin sanyin jiki suka nufi dakin Hajiya kilishi,tana zaune adakin ita kadai tagama saka turaren wuta adakin Kenan, kasancewar ba'a Dade da gyara mata dakinba sakamakon baqi dasuka wuni adakin.
Zama sukai agefen gadon sukai shiru,Hajiya kilishi ta Kalle su tace"Lafiya?"
Ashraf yace"Momy ashe fishi kikeyi da Aryan"
Tajuyo ta Kalli Ashraf tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi, sakoka yayi agaba Kenan kazo Kamin duka saboda Ina fishi dashi?"
Cikin sauri Ashraf yace"Momy bahaka bane bafa...,kiyi haquri dan Allah,Kinga fa duk ya rame wallahi,ni rakoshi nayi yabaki haquri"
ya qarasa maganar yana zungurin qafar Aryan
Cikin sauri Aryan da yaji abinda Ashraf yamasa ya kalleta yace"Momy kiyi haquri idan nayi miki laifi kiyafemin,banajin dadi idan banji muryar kiba,fishin ki zaiyi tasiri akaina har hakan yashafi aikina"
Cikin 6acin rai kilishi tace"au cewa kake idanma Kamin laifi? Saboda angama shanyeka ko Babana? bazan ta6a Jin sauqin zuciyata ba harsai karabu da yarinyar Maryam,har abada bana fatan ace jinina yana auren jinin Maryam,karka sake Kiran wayata inde kasan baka saki yarinyar nan saki uku ba,naji dadi da Allah yasa ba haihuwa zakayi ba bare harka hada jini da wannan yarinyar...."
jin kalaman nata sunyi tsauri dayawa yasa Ashraf yafara hawaye, cikin sauri yafice yabar dakin.
Captain Aryan idanunsa suka kada sukai jajir amma shi baiyi kukan ba, cikin ladabi yace"to Momy zanyi yanda kikace,amma kiyi haquri kiyafemin"
Yana fadar haka Yafuto daga dakin nata jikinsa a mutuqar sanyaye,Alqali baya falon,Kai tsaye saiya wuce dakinsu,yana zuwa yaga Ashraf har lokacin yana goge hawaye,zama yayi kusa dashi cikin dauriya yace"wai kukan menene Ashraf?"