← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 68

Sashe 6

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba yace"A a Ruqayya,yaushe kukai hutun ai baki gama hutawa ba,sannan ga yayanku yazo d'azu da yamma, kowa yana gida,bai kamata kitafi ba,ni kinyi masa murna ne akan karramawar daya samu?"

Wani irin qullutun taqaici ne yakama Mawahib,yanzu saboda Allah dan Yaya Captain yazo sai ahanata tafiya hutu maiduguri?
Cikin kwanciyar hankali ta shimfidawa Abbannata qarya tace"eh dazu mungaisa nayi masa ala sanya Alkhairi"

Tana rufe baki, aka turo qofar part din nasu aka shigo,wani irin qamshi mai dadi yadaki hancin Mawahib,sanin datayi cewa irin qamshin dazu ne, hakanne ya tabbatar mata da cewa Yaya Captain ne, hakanne yasa koda wasa batayi kuskuren dago kanta ba,cikin sallama suka shigo falon,dukansu su biyun sanye sukeda wando three quarter, da riga marar hannu alamun kayan shan is'ka ne a jikinsu tunna yamma,gaba daya sai suka saje suka zama abu d'aya,saide fuskar mutum daya data kasance babu wasa akanta.

Mawahib tayi mutuwar zaune kamar ruwa ya cinyeta,saika rantse bata cikin falon.
Cikin farinciki Mamy tace"yan samari"

Captain yad'ora hannunsa akan daya daga cikin kujerun falon yace"Anty Ma-my...."

yakira sunanta a rarrabe,cikin murmushi tace"Captain"

Yaya Ashraf yace"Anty Mamy akwai sauran kunun madarar nan na dazu?"

Mamy tace"akwai, yana dinning bari in dauko muku"
Tafadi hakan tana kokarin tashi, Abba ya Kalle ta yace"yakamata kiyiwa 'ya'yanki fad'an ajiye iyali Maryam"

Mamy takawo musu kunun madarar wanda yaji kwakwa aciki har lokacin da zafinsa,tazuba musu a cup tabawa kowa,ta zauna a kujera tana fadin"to gasunan de Alhaji,inajin saimun fara tallarsu a yanar gizo"

Adede lokacin Yaya Nabil yakira wayar Mawahib,a hankali tasaki wata irin ajiyar zuciya,dama atakure take a wajan,idan tatuna maganar Nabiha datake cewa Yaya Ashraf yana sonta, tasake tunawa da kato6arar datayiwa Yaya Captain dazu, gaba daya saitajita atakure, a hankali tamiqe tanufi hanyar dakinta,Captain Aryan yana shan kunun madara yad'ago da manyan idonsa a hankali yabita da kallo,karaf idonsa ya sauka akan hips dinta,cikin sauri yad'auke kansa.

Shikuwa Yaya Ashraf kasa daina kallonta yayi, har saida yaga ta shige dakinta tareda rufowa.

Mamy tayi ajiyar zuciya ganin Mawahib tabar wajan,gaba dayansu tana lura dasu yanda suka bi yarinyar da kallo, musanman Ashraf da tun shigowar su ya kafeta dawani irin kallo,to shikuma Captain Aryan kallon na menene? a hankali gabanta yafara faduwa,amma data tuna da maganar Nabil, saitaji hankalin ta ya kwanta harta sake sukaita firarsu.

Sun dade a part din Mamy sannan suka tafi dakin su,Ashraf yafara gyara musu lafiyaiyen gadon su,Captain yana danna wayarsa,d'ayar wayar tasa ce tayi qara, yadauka yana magana a hankali kamar da mace yake magana,Ashraf yayi tunanin Captain din yayi sabuwar budurwa ne, a hankali yadago yana kallon sa saiyaji yana cewa"A a bamu da irin wannan bindigar,idan zaka shigar da bayanan ka rubuta muna buqatar irinta,musanman saboda sababbin ma'aikata wanda zasu kar6i horo ok?"

Daga dayan 6angaren aka amsa masa, sannan ya ajiye wayar.
Ashraf yace"bansan yau zaka shigo gari ba, da nasa yaran nan sun gyara mana dakin,duk yayi datti wallahi"

Hankalinsa yana kan waya yace"nima bansan zan taho ba,kawai nagaji ne,kuma inason ganinka kaida Momy, shiyasa kawai nataho,toko muje gidanka mu kwana tareda wad'ancen sojojin?"

Ashraf yace"Rigima boy kenan....babu matsala mu kwanta kawai gobe saisu gyara mana,wai kasan yarinyar nan Zulaihat kuwa har yanzu tana nan tanata nacin kirana?"

Captain ya ajiye wayar hannunsa yace"karabu da'ita kawai,dan nima ganin farko danayi mata naji tamin..."(😲)

Ashraf yace"but... tabani tausayi, tana kuka tana tambayata meyasa zan yaudareta?"

Cikin rashin damuwa Captain yace"toya zatayi? Kashareta kawai kanemi wata"

Ashraf ya zauna abakin gadon ya kalli Captain yace"amma kasan idan nasake yin wata budurwar kace kana sonta saika raina kanka?"

Captain yace"to idan aka dace Ina sonta ya zakayi? zamu auri mace d'aya ne?"

Ashraf yadauki fillo yadora a cinyarsa sannan yace"wai kai baka ga Mawahib bane?"

Saida ya yatsina fuskarsa sannan yace"wace hakan?"(😲)

Ashraf yayi masa wata irin harara sannan yace"Mawahib d'in Anty Mamy mana"

Cikin rashin kula Captain yace "Oh..."

Ashraf yace"kamarya oh.....? wai kana nufin har yanzu kana nan kanaqin yarinyar nan?,ko saboda Anty Mamy yakamata kadena nunawa 'yarta qiyaiya...."

Cikin damuwa ya lumshe idonsa yabude sannan yace"Bansan jin maganar marar kunyar yarinyar nan Ash...,at all ma nibata gabana,ni maqiyin qasata shine maqiyina ba wannan qwailar ba...."(🙊😳😱)

(cin mutunci😲Captain mungode)

Mawahib littafin kudi ne,zaki biya naira 500 kacal,ki karanta abinki cikin kwanciyar hankali,sayan nagari maida kudi gida 💃🏼

Zaki turo 500 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

Idan kina buqatar a tallata miki hajarki a Facebook page dinmu,da whtspp,da status,farkon shafi ko tsakiya,ko qarshan shafi, duka akan farashi me sauqi,ki tuntu6eni ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: 💗MAWAHIB💗
(Hot luv)

Writing By Amnah El Yaqoub

5&6

Please🙏🏻kuyi Subscribe YouTube Channel dina,za'a fara dora muku Audio Novel's👇🏻
https://youtube.com/@Amnahelyaqoubnovels

____

Bayan tagama abinda take bata dawo gidanba saida ta daidaici lokacin dawowar Mamy daga Asbiti yayi, sannan itama tadawo gidan, gashin nan nata kuwa yasha gyara sai qyalli yake,jikinta yayi sumul dashi kamar ka latsa jini yafuto, koda ta nunawa Mamy gyaran da'aka mata koda wasa bata fad'a mata yanda sukai da Hajiya Kilishi ba.

Washegari da daddare suna zaune afalo gaba dayansu,Mawahib tana sanye cikin kayan bacci riga da wando mai santsi,wandon dogone har qasa, sai 'yar qaramar riga, tayafa dan qaramin mayafi a jikinta,amma kana Iya hango yanda sumar gashinta ta kwanta a goshinta.

Abba ya ajiye cup din hannunsa mai daukeda fruit salat, yad'auki remote yana canja channel tareda fadin"dazu su Yaya Ibrahim suka tafi Abuja,sunyi min magana kozan samu zuwa to ayyuka sunmin yawa a office shiyasa nima ban bisu ba,yauce ranar da za'a karrama su ARYAN,yana d'aya daga cikin wanda shugaban qasa zai karrama su saboda qwazonsu a wajan aiki"

Mawahib dake danna wayarta tayi shiru tana Jin abinda Abbanta yake fad'a,a wannan baqin halin na Yaya Captain tarasa yanda akai harya samu yashiga jikin manya gashi hardashi za'a karrama.

Cikin murna taji Abbanta yana fadin"Alhamdulillah Maryam kinga ma gashi suna nunawa a wannan tashar"

Cikin farinciki Mamy Tace"masha Allah,aikam gasunan,Alhamdulillah, Allah yasanya Alkhairi"

Cikin Jin dad'i Abba yace"ni gaba d'ayama sainaga Mawahib tana juyewa tana yin kama dashi,da idon,da hancin, da bakin,gaba daya na Captain Aryan ta d'auko"

Yajuya ya Kalli Mawahib da hankalinta yake kan waya ko inda TV take bata kalla ba,yace"koba hakaba 'yanmatan Abba?"

Ahankali tasaki wani murmushi mai kamada yaqe...
Sai a lokacin ta kalli tv,idonta ya sauka a kansa,kamar kullum yana nan da kyansa,kwantaccen sajen daya zagaye bakinsa irinna Yaya Ashraf yasake qawata farar fuskarsa kamar balarabe,jan lips dinsa d'an qarami mai mutuqar laushi sai sheqi yake kamar ya shafa musu lipstick,fuskar nan tasa ad'aure kana gani kasan babu wasa kamar ma baya farinciki da karramawar da akayi masa,yana tsaye qyam ya qame waje d'aya,ga shugaban qasa da kansa yana sake gyara masa rank dinsa,ga manya manyan sojoji daga gefe kowa ya qame a tsaye, saida shugaban qasa yagama gyara masa rigarsa,sannan shikuma yasara masa,sannan aka fadi irin jajircewar dayake akan aikinsa, tareda kyautar kudi Naira million arba'in,anan aka buqaci daya daga cikin familynsa yazo su kar6i kyautar tare,kai tsaye Alqali yatura Ashraf,cikin nutsuwa Yaya Ashraf yataka yaje gaban Aryan din suka kar6i kyautar tare,bama sai anyiwa mutane bayani ba,ana ganin ashraf wanda basu san cewa Captain Aryan 'yanbiyu neba, yau kam sun sani,tsirarun 'yanmata wanda suka samu damar zuwa wajan taron lokaci daya kallon su yakoma wajan Ashraf da Captain Aryan,kowa mamaki yake dama wannan miskilin Sojan 'yanbiyu ne?

Mawahib tagama qarewa Captain Aryan kallo, taga babu wata kama dasuke kamar yanda Abbanta yafada, banda fari dayake dashi irinnata ita bataga wani abun birgewa a wajan Yaya Captain ba bare har taji dadi dan ance suna kama.

Ganin yanda sauran sojoji suke qara girmama shi kamar wani nagaske,hakan yasa Mawahib taji wani irin baqin ciki,sai yanzu ne tagane dalilin zuwan Yaya Ashraf gida,a hankali tatashi ta wuce dakinta.

Abba yabi Mawahib da kallo harta shige dakinta,yajuyo ya kalli Mamy yace"madam ya kamata fa asamawa Ruqayya qanne,naga tatafi daki kamar tana fishi,kuma nasan ba fishi take ba, kawai shagwa6a take ji ba'a tafi da'ita wajan taron nan na yayansu ba,shiyasa tatafi d'aki"(🙊)

Mamy tayi murmushi batace komai ba,shima Abba yayi dariya yace"emanah,tana ganin itace qarama a gidan shiyasa take shagwa6a son ranta,inda tanada qanne ai zata rage shagwa6ar"

Mamy tayi murmushi tace"Alhaji kenan,babu wani shagwa6a ita tasan meyake damunta"

Cikin jin dadi yabi ilahirin jikinta dawani irin mayen kallo sannan yace"Allah koh?"

Itama murmushin tasake yi batace dashi uffan ba,saboda tasan ma'anar kallon dayake binta dashi(🙈)

Washegari Hajiya kilishi ce ta kar6i girki,a qa'ida kuma inde itace tayi girki babu wanda take kaiwa part dinsa,saide kowa yaje yadauka,saboda itace babba,Mawahib bataje ta d'auko musu nasu abincin ba,saboda Mamy tana wajan aiki,shima Abba yafita bai dawo ba,ita kadai ce kuma ba yunwa take ji ba, tun safe aketa sallama a gidan,ana zuwa anayi wa Hajiya kilishi murnar karramawar da Captain Aryan yasamu,sai hayaniya akeyi, tana kwance afalonsu tana chat da Yaya Nabil,wani d'an kawunta dake maiduguri tana jiyo surutun mutane kala kala,bata fita d'aukar abincin ba saida taji hayaniyar mutane ta ragu a lokacin itama tagama chat d'inta,rana tayi sanyi, sannan ta futo,tana sanye cikin doguwar riga marar hannu,yadin rigar yanada laushi, daga gaban rigar anyi mata ado da baqin leshi,sai dan qaramin mayafi data d'ora akanta,babu kowa atsakar gidan,kai tsaye ta wuce kitchen tad'auko nasu abincin,futowar ta kenan daga kitchen din adede lokacin Hajiya kilishi tafuto daga part d'inta itada wata babbar mace da alama qawarta ce, cikin ladabi ta rissina tace"Momy Ina wunin ku"

Hajiya kilishi ta amsa a taqaice tace"lafiya"

Ita kuma d'ayar cikin murmushi ta amsa tana bin Mawahib da kallo harta shige part dinsu, saida taga shigewar Mawahib sannan ta maida kallonta wajan Hajiya kilishi tace"Matar Alqali,Ina kuka samo 'yar kyakykywar yarinya haka?"

Hajiya kilishi tace"Hajiya Mariya baki ganeta bane?"

Wadda aka kira da Hajiya Mariya tace"ina zansan wannan yarinyar? duk zuwan danake bana ganinta,anya anan gidan take kuwa? Kina ganin yarinya jajir da'ita kamar wankan inji? Kiduba kiga wannan uban diri kamar ita tayi kanta,badan da 'yanbiyun samarinki a gidan ba aida nayiwa Farouq d'ina kamu..."
Chapter 6 · 0% Book details