← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 68

Sashe 39

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga dakin Nusaiba tajata gefen gado suka zauna, tatashi ta dauko mata wani magani sannan tadawo kusa da'ita ta zauna tabata maganin tace"nasan idan sundawo ba lalle su barmu musake ba,kiyi amfani da wannan maganin nasan zakiji dadinsa,tunda yanzu de nasan Captain ya maidake yar gari,kidinga sakawa a yogurt kinasha, zaisa jikinki yayi fresh sosai,amma kuma saikin sake daurewa,idan kuka hadu da oga ba sauqi, duk da nasan cewa matan sojoji muna qoqari,suna nuna mana qarfi kamar sun manta cewa mudin ba sojoji bane"

Atare suka saka dariya saide ita Mawahib dariyar yaqe take,gaba daya bata cikin nutsuwar ta,Nusaiba tace"shiga kiyo alwalar to,bari in Shimfida miki darduma"

Mawahib tace"to nagode"
ta ajiye maganin kusada agogon ta, Sannan tashige toilet, tana shiga ta jingina da jikin qofar toilet din, gumi yana sake futo mata a goshinta,lumshe idonta tayi amma wannan abun na Yaya Captain take gani, cikin sauri tabude idonta, maganar Nusaiba tadawo mata cikin ranta,idan ta fahimceta maganin mata tabata,kenan dama Mamy ma maganin mata take aiko mata dashi Kenan?
Shine tadage tuquru tanasha jitake abun arziqi ne?
wato kowa burinsa tasha maganin mata Yaya Captain yaji dadi kowa sonsa yake babu wanda zai lura da cewa shiba sonta yakeba, ita ba sonsa take ba,ajiyar zuciya tasaki tafara zuba ruwa a fuskarsa harta samu nutsuwar ta tadawo, sannan tayi tsarki ta daura alwala tafuto tatada kabbarar sallah.

falon suka dawo suka zauna har lokacin su Captain basu dawo ba, bata daura dankwalin taba sai mayafin data yafa har kanta, mufid yana hannunta tana wasa dashi Sai qyalqyala dariya suke,tana son yara kasancewar gidansu basuda qananun yara,duk da tana tuna abinda yafaru a tsakanin su da Yaya Captain hakan bai hana ta sake suna wasa da Yaron ba,adede lokacin suka dawo daga masallaci, hannunsa yana zube cikin aljihun wandon sa, fuskarsa kamar kullum tana daure,tun daga bakin qofar falon yazuba musu ido itada yaron yana kallonsu,sun birgeshi sosai kamar ya dauketa itada yaron sutafi gidansu ko zai samu yadinga ganin wannan kyakykywar dariyar tata kullum(🙈)

Har suka zauna a kujera Mawahib bata dago kanta ta Kalle su ba,tanata wasanta da mufid,Nusaiba data gama zuba musu abinci ta kalleta tace"Mawahib kinason yara,kema zaki haifi naki,may be ma naki Yaron yafi mufid kyau da fari tunda mijinki fari ne kema haka, kokuma ki haifo mana 'yanbiyu, tunda shima 'yanbiyu ne"

Captain Aryan daya faracin abinci ya saci kallonta,saiyaga tayiwa mufid kiss a goshi sannan tace"banason farin yaro"

Wani irin murmushin gefen baki yayi,batare da kowa yasani ba,matarda taga abu duk ta rikice tana tsoro jikinta yana rawa itace hartake da za6i akan yaron dazata haifa, a wannan tsoron nata tayaya ma zata saki jiki harta samu yaron? .

Captain Habib yayi dariya yace"to saide in dangi dan naku zai iyo,amma iyayensa de duka gakunan farare ne"

Murmushi tayi dan kadan bata sake cewa komai ba,har suka gama cin abincin,basu sake zaman awa dayaba,Captain yace zasu wuce,badan sun soba haka suka musu rakiya har Mota, Nusaiba Sai rada take yiwa Mawahib akan kartayi wasa da wannan maganin,daga nan sukai sallama maigadi yabude musu get suka fita.

tunda suka dauki hanya babu wanda yace da dan'uwan sa uffan, Mawahib gaba daya hankalin ta tamaida kan window tana kallon yanayin garin,ahankali yajuyo ya kalleta yaga kokadan taqi kallon inda yake,dan qaramin murmushi yasaki baice da'ita komai ba,suna zuwa gida tabude motar tafuce tanufi gida sai sauri take kamar zata tashi sama, kallonta yayi yasaki wani irin numfashi tareda zuba hannunsa cikin aljihun wandon sa yabi bayanta ahankali.

har zuwa dare Mawahib bata yarda tahadu da Captain ba,shima bai takura mata ba ya qyaleta,saide har zuwa dare yana tunani akan matsalar haihuwar sa,idan yatuna zuwa gidan Captain Habib dasuka yi,saiya dinga ganinta a'idon zuciyarsa itada wannan yaron,bai ta6a jin yanason haihuwa ba sai yau din dayaga yaron yamata kyau,bai ta6a jin ciwon rashin lafiyar sa ta tsinkakken maniyi ba sai yau,yaga alama tabbas tanason yara, yakamata ace yabata nata Babyn itama saita dinga wasa dashi, bai fargaba saida yakai kusan qarfe biyu nadare yana tunani, ajiyar zuciya yasaki yatashi yawuce toilet yayi alwala yazo yafara nafilfili, yadade yana Addu'ah yana roqon Allah yakarkato masa hankalin matarsa kansa,Allah yabasu zaman lafiya da zuri'ah tagari,Allah ya daidai ta tsakanin mahaifiyar sa dakuma matarsa, Allah yasa koba yanzu ba, watarana mahaifiyar sa taso matarsa kamar yanda take sonsa,saida yagama shafa Addu'ah sannan sannan yadauki wayarsa yasake turawa Hajiya kilishi saqon ban haquri da neman yafiya, sannan yayi addu'ar bacci ya kwanta.

Washegari sassafe yayi wanka yafice yabar gidan,kai tsaye Maitama general hospital yaje,bayan yayi duk abinda yadace yasamu ganin doctor,saida suka sake yimasa wasu gwaje gwajen, sannan likitan yayi masa rubuce rubuce akan katin sa yabashi katin sannan yace"kanemi wannan magungunan yanzu yanzu,sannan karka yi wasa da shansu,inde kana shansu bisa qa'ida insha Allah cikin qanqanin lokaci sperm din zai koma daidai kamar yanda yake ada,but karage cin abu me maiqo, sannan dazaran kafara amfani da maganin saika sanar dani yaya kake ganin yanayin sperm din, idan da yiyuwar asauya magani sai asauya ma wani"

Cikin gamsuwa Captain Aryan yabashi hannu suka sake gaisawa, sannan sukai exchange din number,yafuto daga office din,kai tsaye magungunan yaje ya siya sannan ya futo daga asbitin yabude motarsa ya ajiye maganin,shima yashiga yaja motar yanufi gida.

50/50,Ali yaga Ali 😂🙈
(Captain de ya lalla6o neman magani dakansa 😂🤣)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub ✍🏻
[7/13, 5:41 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Banji dadin yanda wasunku suke fitar min da littafi naba, ada har Ina murna Ina cewa Allah yahadani da fan's din MAWAHIB yan amanah,asheni bahaka bane nice nake yaudaran kaina,wasu writer's din idan suna novel har sha'awa suke bani saboda bazaka ta6a ganin littafin su yana yawo ba,amma ni bansan meyasa akemin hakaba, littafin nan na kudi ne,kudi kukasa kuka siya, meyasa bazakubar duk wanda yakeso Shima yasiya da kansa ba? kusa aranku idan kune kuka hana kanku bacci, kuka hana kanku sukuni,domin ganin kun farantawa masoyan ku rai kawai sai kuka ga littafin ku yana yawo a group zakuji dadi?
nasan wasu daga cikinku sunsan yanda typing yake,yanda typing yake da wahala idan Marubuciya tace Allah ya'isah billahillazi sai Allah yasaka mata, kullum posting biyu nakeyi saboda kada kudinga jira muyi muyi mugama kowa hankalinsa ya kwanta amma jiya jiya Ina posting cikin mintuna qalilan sai gashi Har kun fitar min dashi, group fa ba mutum dayane aciki ba, wani group dinma yatara sama da mutum 600 menene ribarki idan kin fitar dashi ne? Bafa komai zasu miki ba watama saide tace miki 't' wato tnx, tun farko saida nace idan kinsan cewa zaki sai littafi nane danki dinga fitar min dashi to nahadaki da girman Allah karki siya, bana buqatar kudin ki, ni aganina ko 100 ce dani gara in fadawa mutum inaso, idan ya siyar min shikkenan in karanta cikin kwanciyar hankali yafi ace anbarni da Allah, masu cewa Wai idan ba'a share nasa tayaya ne wasu zasu gani su siya Toni nagode da wannan share din, Iya free page din danayi posting Wanda suka gani suka siya sun Isa, Allah yayi masa albarka, ko a addinin musulunci ciniki babu dole, idan kin siya Mawahib ne danki fitar min dashi kiyi left, zan miki transfer din kudin ki 🙏🏻
[7/13, 5:41 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

yana komawa gida ya ajiye ledar aqasan carpet din falo ya kwanta akan doguwar kujera yakira wayar Ashraf.

Alokacin suna zaune afalonsu yadora Nabiha akan cinyarsa hannunsa yana cikin rigarta yana shafa cikinta wanda yafara dan tasawa kad'an.
Daukan wayar yayi, daga 6angaren Captain yafara magana qasa qasa kamar yanda yasaba yace"Ash naje naga doctor yanzu"

Ashraf yayi murmushi,yadora hancinsa akan qirjin Nabiha yana goga mata dogon hancinsa irinna Aryan sannan yace"kayarda da magana ta kenan,yanzu za'a fara fafatawa"

Idonsa ya lumshe sannan ya budesu a hankali yace"bahaka bane Ash...,kawai naga tana son Baby ne"

Ashraf yayi murmushi yace"kafada mata kuwa?"

Cikin sauri yace"nakasa Ashraf,nikaina kunyar kaina nakeji,bansan Yaya zan tunkareta da maganar ba"

Ashraf ya lumshe idonsa yace"meyake damunka ne?kacire komai aranka kayi abinda yadace"

Cikin sanyin jiki yace"Okay ,jarababbe sai anjima"

Ashraf ya Kalli wayar da sauri yana murmushi bayan yaji Captain din yakashe wayar,hakan yana nufin yagane da Nabiha yake tare kenan.

Yana kashe wayar yashiga email din wani gidan abinci yana magana dasu,daga dakinta tafuto tayi kwalliya tana sanye cikin doguwar riga ta atamfa fitet gown,daurin dankwalin nata yayi mata kyau sosai,tana qarasowa falon ta ganshi a kwance yana danna waya,qarasowa tayi ahankali tana zuwa kusa dashi qamshin ta yanayi masa sallama, kallon fuskarsa tayi wadda babu fara'ah kamar kullum, sannan ta janye idonta ahankali saboda karsu hada ido,tace"Ya Captain Ina kwana?"

Kallonta yake cikin wani irin shauqi,yana qarewa shigar jikinta kallo a taqaice yace"kin tashi lafiya?"

Mamaki ya kamata,yau Kuma salon gaisuwar tasa kenan,tasaba Koda yaushe saide yace mata lafiya, a taqaice.

Kanta aqasa tace"akwai breakfast"

wayar hannunsa ya ajiye sannan yatashi yace"Okay"

dining suka qarasa,yadora hannunsa akan kujera yana tsaye, itama daga tsayen tafara zuba musu abinda tadafa,kallonta yake cikin zuciyarsa yana yaba irin nutsuwar yarinyar,harta gama zubawa ta ajiye masa agabansa,itama ta ajiye nata agabanta,abincin ya dauka yabar inda yake yadawo kujerar kusa da ita ya zauna har jikinsu yana haduwa dana juna,ta kalleshi ta gefen idonta,sannan ta dauki fork tafara cin arish din dake gabanta ahankali,kad'an kad'an tanajin gabanta yana faduwa amma saita dake,babu wanda yayi magana duka su biyun,saida suka kusa gamawa batare daya kalleta ba yace"ya tsoron jiya?"

Lokaci daya Mawahib ta qware, tafara tari,meyake damun Yaya Captain ne?
tasamu tafara mantawa shikuma yana qoqarin tuno mata da wannan tashin hankalin.
Chapter 39 · 0% Book details