← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 68

Sashe 54

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya kilishi data lura Mawahib bata motsi cikin sauri tatashi tafara kiran Sunanta tace"Mawahib!"

Taji shiru, tasaka hannunta duka biyu tafara jijjigata cikin rawar murya wadda take gab da fashewa da kuka tace"Mawahib!!"

tagado ta kalli Alqali da Abba dasuke shirin fita tace"Alhaji kuzo ku duba kar itama mu rasata"

(So Sad 😭)

(matan sojoji Allah yakare muku mazajenku,🤲🏻,Wanda suka rasa mazajensu ubangiji Allah yabasu haqurin rashin su,🤲🏻😭)

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/18, 5:57 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 78*

Abba ne yasunkuya ya tatta6a fuskarta yana kiran sunanta "Ruqayya! Ruqayya bude idonki"

Shirun da yaji ne yasa yata6a qirjinta yaji bugun Zuciyarta yana nan, sannan yace"suma tayi"

Ya kalli Mamy ko zata bata wani taimakon yaga Mamy sai faman kuka take ko kallon Mawahib dinma batayi ba.
Ya kalli Ashraf yace"bamu ruwa Ashraf"

Tashi yayi fuskarsa tana tsiyayar da hawaye yaje fridge yadauko gorar ruwa guda daya yabawa Abba, yakar6a tareda budewa yazuba a hannunsa sannan ya shafa mata dan kadan a fuskarta, amma bata farfado ba.
Hajiya kilishi tace"mutafi asbiti kawai"

Mama Sadiya da Alhaji khaleed ne suka shigo falon, Mama Sadiya sai kuka take tana salati.

Gaba daya itada Mamy sai suka sa duka mutanan falon kuka,amma abun mamaki Hajiya kilishi har yanzu batayi kuka ba,idonta de yana cike tab da qwalla, kuma tana magana kanajin muryarta tana rawa alamun tana dab da fashewa da kuka.

Abba ya kalli Ashraf yace"karomin wani ruwan"

Ashraf yasake bude gorar zai zuba masa ruwan, wayarsa ta dauki qara alamun kira yashigo, cikin sauri yaduba wayar,gabansa ne yayi wata mummunar faduwa a fili yace"Aryan...."

Cikin sauri Mamy tadago kanta ta kalleshi,Mama Sadiya datake goge idonta ta dankwalin kanta itama ta dakata duk suka zuba masa ido,Alqali ya kalli Ashraf daya qame a tsaye yakasa daukar wayar, yatashi yakar6i wayar, yana fadin"ina tunanin mutuwar zasu fada mana"

Yadauki wayar yazauna a kujera sannan yasaka wayar a speaker yace"Assalamu Alaikum"

Daga can 6angaren cikin muryar nan tasa me aji yace"Ash...."

Cikin sauri Alqali yatashi tsaye yace"Aryan...Aryan kana jina? kaine kake magana ko kunnuwana ne?"

Murmushi yayi yace"nine Daddy...."

Lokaci daya fuskar jama'ar falon ta washe,Hajiya kilishi tasaki wata irin ajiyar zuciya,sai alokacin wani irin hawaye yazubo mata.
Mamy tafara goge hawayen idonta tana murmushi,kowa ya matsu abashi wayar, kafin Alqali yayi magana Alhaji khaleed yace"Aryan yanzu mukaji labarin mutuwar ka,kaganmu nan hankalin kowa yatashi iyayenka sai kuka suke"

Cikin mamaki yace"Uncle mutuwa kuma? rumors ne kawai,babu wanda yarasu acikin mu,basu gama tantance labari bane suke yad'ashi"

Alhaji Isah yace"Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah abun godiya.... Yanzu kana Ina? yaushe zaka taho? kokuma de mu muzo gaba dayanmu muganka ko hankalin mu zai sake kwanciya?"

Captain Aryan yayi murmushi yace"Uncle yau zan taho gida komin dare insha Allah,yanzu haka muna Abuja shiyasa nasamu damar kiranku,munfuto wajan network"

Abba yace"to Alhamdulillah,ubangiji Allah yakawo ku lafiya Aryan,Allah yatsare ku"

Ya amsa masa da "Amin" sannan yace"Ashraf...."

Alqali yayi sauri yabawa Ashraf wayar,Ashraf dayake goge hawayen idonsa na farinciki ya kar6i wayar yace"Aryan"

Captain yayi dan qaramin murmushi jin Ashraf din kuka yake,danya kwantar masa da hankali yace"Whare is my wife...?"

Ashraf ya goge hawayen idonsa sannan ya kalli Mawahib dahar lokacin take kwance bata farfadoba,yasake goge hawayen idonsa danya kwantar masa da hankali yace" She's sleeping..."

Ajiyar zuciya Captain yasauke me nauyi sannan yace"kakula min da'ita kafin nazo itada Momy, saina qaraso"

Ashraf yace"to Aryan"

Gaba daya falon sai bakin kowa yabude, falo yadauki surutu,Hajiya kilishi tasake goge idonta ta kalli Mamy tace"Maryam tunda kinji labarin dannaki yana raye zoki duba tawa yarinyar"

Dariya suka saki gaba dayansu,ta taso takarbi gorar ruwan da Ashraf yakawo tabude bakin robar ta kwara mata,cikin sauri Mawahib tasaki wani irin numfashi tareda jan numfashi,Mamy ta kamota ta rungume ta ajikinta,ahankali tafara bude idonta harta budeshi ras,tana ganin mutanan falon ta tuno abinda yafaru,cikin d'acin zuciya tasaki wani irin kuka tace"Mamy da gaske yaya Captain yatafi yabarni?,meyasa saida yabari nafara sonsa zai tafi yabarni? meyasa mutuwa bata daukemu tareba,? Mamy nima mutuwa zanyi..."

Cikin lallashi Mamy tace" Mawahib Captain yana nan,bai mutu ba,yana nan da ransa yanzu muka gama waya dashi"

Hawayen idonta ta goge tace"Mamy dan karna mutu shiyasa kika fadi haka ko? da idona nagani ance yamutu"

Ashraf yayi sauri yakira Aryan,bugu daya yadauka yace"Aryan ga Mawahib tana so taji muryarka"

Yafadi haka tareda bawa Mamy wayar,daga can 6angaren Captain Aryan da beyi tunanin a speaker aka saka wayar ba, cikin sigar soyaiya yace"Baby bakya kewata ko...?"

tanajin haka ta kalli wayar da sauri,sannan ta kalli Mamy,cikin sauri ta 6oye fuskarta ajikin Mamy, Mamy tayi murmushi tabawa Ashraf wayarsa, Ashraf yafice daga falon da wayar a kunnansa.

Alqali yayi murmushi ya kalli Mawahib yace"shikkenan kuka yaqare ko Mawahib?"

Cikin sauri ta juya bayanta anan taga duka iyayen nasu maza da kowa da kowa na gidan duk suna falon,cikin sauri tacire jikinta daga na Mamy tatafi dakinta da gudu cikeda kunya(🙈)

kan gadonta tafada tasaki wani irin murmushin farinciki,fillo taja ta rungume a qirjinta tana sakin murmushi ita kadai, cikin sauri tatashi tafada toilet tayi wanka wanda ta dade batayi irinsa ba, sannan ta dauro alwala tazo tafara gabatar da sallar nafila tana sake yiwa Allah godia daya dawo mata da mijinta gida lafiya.

mutane suna jin labarin nasarar su Captain aka fara sallama a gidan ana yiwa mutanan gidan barka.
Su Daddy kuwa suna idar da sallah suka wuce wajan limamai suna sake yimusu godia akan irin taimakon dasuka basu na Addu'ah.

Ashraf kuwa gida yawuce yadauko Nabiha suka dawo gida.
tun yamma Mamy da Mama Sadiya suka shiga kitchen tare suka fara gabatar da abincin da za'a tar6i Captain Aryan,Nabiha kuwa tana wajan Mawahib sai tsiya take mata.

Zuwa magrib su Mamy suka gama komai, Hajiya kilishi tace"sukai komai da komai part dinta ahadu acan gaba daya aci abincin"

can suka kai abincin tareda taimakon Mawahib da Nabiha, Mawahib gaba daya hankalin ta ya karkata kan bakin get,gani take kamar bazai dawo ba,bayan sungama jera komai a part din Hajiya kilishi compound suka dawo gaba dayansu kowa ya zauna a kujerun roba dasuke tsakar gidan nasu.
Amma Mawahib a tsaye take takasa zama,tana daga tsaye ta dora hannunta akafadar Nabiha, tayi kwalliyarta madedeciya tana sanye cikin riga da siket na leshi, har dare suna Compound din gidan,mazajen gidan su Daddy harsun shigo gida kai tsaye sukace wuce part din Hajiya kilishi.

Mamy ta kalli Abba tace"Alhaji bai qaraso bane har yanzu?"

Abba yace"sun sauka tun dazu,Ashraf yaje dauko shi"
Mawahib tanajin haka tayi wata irin asirtacciyar ajiyar zuciya,ta sunkuyar da kanta.

Ko minti ashirin ba'a yi da shigowar su Daddy ba,Yaya Ashraf yashigo sannan Yaya Captain,yana Sanye cikin uniform dinsu na sojoji,Mawahib tana ganoshi ta saki ihun murna tatafi da gudu ta rungume shi(🙈🙊🙆🏻‍♀️)

Ihun dasu Abba suka jiyo yasa suka futo anan sukaga Mawahib rungume da Captain Aryan.
Sosai ta rungume shi kwata kwata ta manta da wata aba kunya,murmushi yasaki shima baiyi wata wata ba yadora hannunsa akan hips dinta ya rungume ta sosai yana sakin ajiyar zuciya,hawaye take na farinciki ta dora kanta akan faffadan qirjinsa tayi luf tana zubar da hawaye, cikin kuka ta dago ta kalleshi tace"ina sonkaaaa!! ".
Wani irin farinciki ya kama Captain, Murmushi yasaki sannan yadan sunkuya daidai tsawonta yadora bakinsa akan kunnanta cikin sigar rad'a yace"I miss you...,kiyi shiru mana,bagashi nadawo ba?"

Cikin hawayen tadago kanta ta kalleshi sannan takai masa wani irin dukan soyaiya a qirjinsa.

Cikin sauri Mamy dataga alamar kamar sun manta iyayensu suna wajan tayi gyaran murya tace"sannu da zuwa Captain"(😂)

Ahankali yasaki Mawahib ya qaraso cikin gidan yana dan sosa qeyarsa, ya kalli iyayen nasu da duka fuskarsu ta cika da farinciki, sannan ya tsugunna yasake sosa qeyarsa ya gaida su, cikin farinciki suka amsa, Hajiya kilishi data cika da farinciki ta kalleshi tace"Baba nah? aikasan yanda ake rubuta takardar barin aiki ko?"

Alqali yayi murmushi yace"kai taso muje kayi wanka muci abinci kowa da kowa kai yake jira"

Cikin kunya yatashi suka wuce part din Hajiya kilishi,acan yayi wanka sannan Ashraf yakawo masa kayansa yasaka,suka futo falon hannunsa cikin na Ashraf,dukansu suna zaune a dining kowa jiransa yake, yana zuwa kuwa suka zauna shida Ashraf, Nabiha tana gefen Ashraf, Mawahib kuma tana kusada Mama Sadiya, Hajiya kilishi tana daya gefen nata, sun sakata a tsakiyar su,Mamy ce tazubawa kowa abinci,saida tafara zubawa mazan sannan iyayensu mata saikuma su yara, abinci aka faraci Alqali yana kallon kowa yanajin dadi aransa,ranar dayake fata yake buri yau gata tazo, Allah yahada masa kan iyalansa gaba daya, babu tashin hankali babu fitina, ko yanzu yafadi yamutu yasan cewa bai bar baya daqura ba.

Captain Aryan yanacin abincin yana satar kallon Mawahib,ita kuwa qin dagowa tayi ta kalleshi kasancewar tana fuskantar sane, gata ga Hajiya kilishi Ina ita Ina rashin kunya agefen suruka?

idan tabiye masa babu abinda bazai faru ba,tundashi bazai Iya daina kallonta ba togara ita tadan nutsu.

Qare mata kallo yake ganin tarame sosai tafada, saide fari data qara,jiyake kamar ya janyota jikinsa,cin abincin nan dayake jinsa yake kamar akan qaya yake.
Ashraf daya ga gaba daya hankalin Captain yana kan Mawahib yaturo qafarsa ta qasan table din ya zungureshi.

Sai alokacin yadawo hayyacinsa,yaci gaba dacin abincin har suka kammala gaba daya,yar fira sukai cikin farinciki kowa yaana tofa albarkacin bakinsa har wajan qarfe goma nadare sannan Mama Sadiya da Alhaji khaleed sukai musu sallama suka tafi Part dinsu, Nabiha ma tatashi tabi bayan Mamanta.

Sannan Mamy da Abba ma sukai musu sallama suka tafi,cikin nutsuwa itama Mawahib tabi bayan iyayenta tanajin yanda idon Yaya Captain yake yawo ajikinta,amma bazai iyu ta zaunaba dole zasu barsu da iyayensu ko zasu tattauna wata maganar.
Chapter 54 · 0% Book details