← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 68

Sashe 43

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunyi wani irin bacci me dadi wanda su kansu basusan tsawon lokacin da suka dauka suna baccin ba,koda wasa basuji kiran sallar farko ba,haka lokacin da aka shiga sallah a masallatai ma basujiba,aka idar basu jiba,saida gari yayi haske sannan Mawahib tafarka,ahankali tafara bude idonta harta budeshi gaba daya tas a fuskarshi,baccinsa yake hankali kwance har lokacin,ahankali tafara qoqarin tashi ganin gari har yayi haske,motsin tane yasa shima yafarka, yana bude idonsa yasauke shi akanta,ahankali yasaka hannunsa yashafa gashinta,idonsa yana kanta sannan yashafa fuskarta yace"jiya kinyi kuka,kanki yana miki ciwone muje asbiti?"

Ahankali ta girgiza kanta Sannan tayi qasa da idonta,ta yunqura zata tashi yasaka hannunsa ya riqeta baice da'ita komai ba kawai kallonta yake,kasa kallonsa tayi, ahankali tace"lokacin sallah yawuce fa"

Agogon dakin ya kallah sannan yatashi, itama tatashi tana gyara gaban rigar ta,Sannan tasake gyara gashinta daya barbazu, duk yana kallonta, saida yasake qarewa shigar tata kallo, cikin ransa yana fadin fine girl, sannan yasauko daga gadon ya shige toilet.

Cikin sauri itama tafice daga dakin takoma dakinta.

Bayan ta idar da sallah babu abinda tayi, kawai saukowa tayi tafara qoqarin hada masa abinda zaici kafin yafita aiki.

saboda tasan ya makara wajan fita aiki saita hada masa iya tea da bread sai wainar qwai,taqara dafa jallop din soyaiyar taliya 'yar kad'an tadora masa da soyaiyan naman kaza agefe,tana jera abincin a dining yafuto cikin uniform dinsu yana tafiya yana kallon agogon hannunsa, baiyi tunanin harta gama abinci ba adan qaramin lokaci haka,kai tsaye wajanta ya qarasa yadora hannunsa akan kujerar dining din cikin girmamawa yace mata "Ina kwana?"

Kallonsa tayi cikin mamaki,Allah yaso ba'acikin mutane yake mata wannan gaisuwar ba,sai mutane suyi tunanin wani abun take masa,babba dashi amma shine yake fara gaishe ta,cikin kulawa ta amsa masa, sannan tazuba masa jallop din taliya wadda taji kayan ganye dasu carrot tatura masa gabansa,ya Kalli taliyar yahadiye wani irin saliva,sannan yaja kujerar baya yazauna yasaka fork yafara ci yana lumshe idonsa,tana daga tsayen tana satar kallonsa yanda yake lumshe ido, da alama abincin yayi masa dadi amma miskilanci bazai barshi yayaba mata ba,wainar qwan tasake tura masa gabansa, tabude bread ta dauko slide hudu ta ajiye, sannan tabude flasks tazuba shayi tahada masa shi yayi kauri, sannan tabar wajan takoma kitchen,gyara kitchen din tayi, tafuto cikin sauri zata fara gyaran falon yataso daga dining din, taku uku yayi zuwa hudu yasaka hannunsa ya fuzgota tafada jikinsa,baice da'ita komai ba yadauketa cak yawuce dining din, bai mata mazauni a ko'inaba sai akan cinyarsa,cikin sauri ta kalleshi tace"yaya Captain zan gyara kitchen..."

Cikin sauri yagirgiza mata kai yace"bakya gajiya ne?kici abinci first"

Kafin tayi wata maganar yafara bata abincin a bakinta,ya 6ata lokaci sosai wajan bata abincin,yana bata tea wayarsa tafara ringing,dauka yayi batare da yayi magana ba, daga dayan 6angaren akace"Captain Aryan lafiya jiya baka shigo office ba, yauma shiru"

Saida yabata tea din sannan ya Kalli wayar yace"Captain Habib Ina hanya"

Captain Habib yayi murmushi yakashe wayar.

Saida ya tabbatar ta qoshi,sannan yadauki tissue yana goge mata bakinta, Mawahib tayi zugud'um tana kallon ikon Allah,gaba daya al'amarin yaya Captain daure mata kai yake,yakamata tayi waya da Nabiha,saboda abun nasa yawuce tunanin ta,tana cikin wannan tunanin taji yasakar mata kiss a wuyanta,cikin sigar rada yace"kiyi haquri akan abinda yafaru jiya,zan fita,ki kulamin da kanki...."

Gabanta ne yayi wata irin faduwa rasss!
lokaci daya Yaya Nabil yafado mata,shine yake fada mata wannan kalaman,tasan cewa shikuma soyaiya suke, amma Yaya Captain fa?

Kanta ne ya daure,harya ajiyeta zai fita jikinta a Sanyaye yake,tasan de yayi mata magana, amma batasan meyace ba harya fita,yana fita ta zauna jagwab a kujera tareda dafe kanta.

Bayan yarage ayyukan office yadauki wayarsa yakira Hajiya kilishi,saida yayi mata 5 missed call bata dauka ba, ya lumshe idonsa tareda ajiye wayar, akwai babban qalubale acikin rayuwar aurensa, yarasa tayaya zai warware wannan matsalar, sai yaushe ne Momy zata sauko tadaina fishi dashi?
Yaya zaiyi da ransa? Ashe haka Ashraf yaji lokacin dayake qoqarin fahimtar dashi irin soyaiyar dayake yiwa Mawahib?
haqiqa soyaiyar Mawahib kamar jarabawa ce da ubangiji yayi masa, Koda wasa bai ta6a tunanin cewa shi Aryan zai so Mawahib ba, soyaiya ma mai tsanani kamar wannan,baya tunanin akwai wani abu wanda bazai Iya sadaukar mata dashiba, ciki harda ransa,agefe guda ga Momy tanaso yasake ta, idan yasake ta Yaya zaiyi da soyayyar ta?

wayarsa yadauka yakira Ashraf,bayan yadauka cikin damuwa yace"Ashraf yaya zanyi da matsalar Momy ne?,bata daukan wayata, dama ranta ya6aci,kuma zuwanmu gida bayan umarnin data bani hakan yasa tasake yin fishi dani,narasa yanda zanyi da raina,idan nasaketa yaya zanyi da soyayyar ta Ash? tayaya zan fadawa Momy soyaiyar yarinyar nan tasa bana gane komai?"

Ashraf yayi murmushi yace"dan soyaiya,ya'isa haka"

"Ashraf bazaka ganeba,idan Ina tareda ita manta komai nake wallahi,ciki harda kaina, ina mantawa dani ko waye gaba daya sai inzama kamar yaro sai yanda tayi dani"

Ashraf yace"ka kwantar da hankalin ka,Momy fa tana sonmu,zata huce,amma wai ya ake ciki ne? kafada mata kana sonta kuwa?"

Dan qaramin tsaki yasaki"nakasa fada mata,bazan iyaba,koda nayi niyar fada mata saitamin kwarjini,bansan Yaya zanyi ba"

Ashraf ya kwashe da dariya yace"serious.... Aryan, wai kaine kake tsoron mace? kaga karka bani kunya,qanina yafi qarfin kowacce irin mace,kayimin alqawari yau zaka fada mata"

Cikin sauri yace"amma Ash..."

Dasauri Shima Ashraf din ya dakatar dashi yace" no,banason jin komai,kafada mata,na tabbatar dole zata kar6i soyaiyar qanina,saboda kyakykywan saurayi ne"

Captain Aryan yayi murmushi yace"naji,niba saika zigani ba,nayima alqawari"

Suna sallama yasaki wata irin ajiyar zuciya me nauyi yanajin kamar yasauke wani tarin kaya me nauyi daga kansa.

Bayan tagama gyara gidan ko'ina yayi tas ciki harda dakinsa, ta kunna turaren wuta,gida yadauki qamshi.

tayi wanka tafuto falon ta dauko ice-cream tasa agabanta amma takasa sha, abubuwan da Yaya Captain yake mata shine yake damunta,dole de yakamata ace takira Nabiha.

Wayarta ta dauka tadokawa Nabiha kira,alokacin tana zaune tasaka taura da magarya agabanta tanataci, dauka tayi tace"mutanan Abuja"

Mawahib tace"meciki,ya Babyn mu?"

Nabiha tace"gashinan lafiya kalau,yakike kwana biyu Ina Yaya Captain"

"yana lafiya Nabiha,ke kinsan meyake faruwa? Shekaran jiya Asalamiyya takira Yaya Captain,lokacin muna breakfast, to inaga saboda ya ganni ne shiyasa bai dauki kiranta ba,jiya da daddare ma wajan shadaya dawani abu tasake kiransa,na dauka nayi mata magana,qarshe de baqin ciki yasa na kashe wayar,shima gashi duk narasa gane kansa,sai wasu abubuwa yakemin kamar ba Yaya Captain ba"

Nabiha tace"aina fada miki, kece kikaqi yarda, amma tun kafin kuzo ranar da akai tashin hankalin nan nabaki shawara,haba Mawahib wacece wata Asalamiyya, mezata fada miki? abinda take dashi kema kinada shi saide ma ki nuna mata wani abun, amma idan kika tsaya kallon ruwa kina gani kwado zai miki qafa, kija mijinki ajikin ki,saboda tun ranar da'aka ce yasakeki yaqi sakin ki na tabbatar Yaya Captain sonki yake, inba haka ba ke kina ganin akwai me sauya Yaya Captain ne? Kinde San halinsa babu me Iya masa sai Allah, banda yana sonki babu abinda zai hana a ranar yacika umarnin mahaifiyar sa,saboda haka kidinga kiyaye wa da Asalamiyyan Nan, ni daga ita har Momy kilishi tsoro suke bani"

Cikin sanyin jiki Mawahib tace"to shikkenan Nabiha,saimun sake magana"

Tana kashe wayar takira Mamy suka gaisa, tasake kiran Abba suka gaisa sannan takira babanta na kebbi, ta ajiye wayar tayi shiru tafada duniyar tunani, meza tayi dan tasaka Yaya Captain aranta kodan ta watsawa Hajiya kilishi qasa a'ido?
To amma da gaske ne maganar Nabiha Yaya Captain sonta yake?
Idan sonta yake Yaya zatayi da qiyaiyar Hajiya kilishi?
Ta wani Fannin gara ace karma yafara sonta, saboda idan de har yana sonta to ita ya kuntowa ruwa, ta tabbatar mahaifiyar sa bazata ta6a sonta ba.

Ajiyar zuciya tasaki tabude ice-cream din tasha dan kad'an taji duk yafita daga ranta danhaka tamaida shi fridge.

Qarfe uku na yamma tashiga kitchen tadafa musu jallop din cous cous ta yaiyanka hanta aciki,sannan tahada lemon ginger,tayi musu farfesun jan nama d'an kad'an, tawuce sama tasake wanka tasaka riga da wandon jeans,tadawo falo tayi zamanta tana chatting.

Har aka kira sallar magrib tana wajan sannan takoma sama domin yin sallah,Captain Aryan bai dawo da wuri ba kasancewar baitafi aiki da wuri ba, Kuma jiya baije ba,bai dawo gidan da wuri ba sai da yatsaya awaje yayi sallar ishai'i sannan yashigo gidan, alokacin tana dakinta bataji shigowar saba,daya shigo falon yaji wani irin qamshi yadakeshi, ya lumshe idonsa sannan ya Kalli dining saboda wata irin yunwa yakeji Kuma yaqicin komai kawai girkin matarsa zaici, cikin sauri ya haye sama anan yaga irin gyaran data yiwa dakin nasa,sai yau yasake tabbatar wa duk gyaran namiji idan mace tayi nata dole kaga banbanci,wanka yashige yafuto yayi shafa, sannan yafeshe jikinsa da turare, yasaka kayan bacci, yafuto daga dakin nasa, adede lokacin itama tafuto daga dakinta tana Sanye cikin daya daga cikin kayan da sister Saudat takawo mata,tana ganinsa gabanta yafadi tayi turus ta tsaya abakin qofa, tayi tunanin baya gidan shiyasa tafuto da wannan shigar tana so tayi sauri taci abinci saita gudu dakinta ta kwanta.

Captain Aryan kuwa qamewa yayi awajan yazuba mata ido kamar yau yafara ganinta,numfashinsa ne yafara sauyawa lokacin da idonsa yasauka akan farar fatar jikinta wadda take wani irin sheqi,gabansa yafara faduwa kamar yau yafara ganinta,rigar Iya karta Rabin cinyarta,tanada hannun brezia sannan qirjin rigar akwai breast cup dan qarami wanda madedetan nashanunta suka cika breast cup din har suna futowa waje,shara-shara ce rigar babu abinda baya gani hatta dan pant dinta na rigar shima yana ganinsa,haka kan nipples dinta ma yana ganinsu, tahade gashinta waje daya ta daura ribon kalar kayan,wani irin yanayi ne mewuyar sha'ani yake fuzgarsa,fatan sa kawai yajita a jikinsa,cikin sauri tajuya zata koma dakinta,baisan lokacin daya fuzgota ba,batayi masauqi a ko'inaba sai a faffadan qirjinsa, tanajin yanda yake fitar da wani irin numfashi kamar wanda yayi tseren gudu,yanda yayi mata kyakykywar runguma a jikinsa hakan yasa yayi mata runfa da faffadan qirjinsa,yadora hancinsa akan wuyanta yana shaqar qamshin jikinta,gabanta yafara faduwa Ganin kamar besan meyake ba yasa cikin sauri tafara qoqarin raba jikinta da nasa,lokaci daya yayi saurin daidaita kansa,cikin shaqaqqiyar murya yace"muje nabaki abinci?"
Chapter 43 · 0% Book details