← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 68

Sashe 63

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mawahib tace"tosu Yaya Captain me sukaci? banji motsin suba ko sun fita ne?"
Nabiha tace" nakira Sweet yacemin sun fita, duk inda sukaje saisu ci abincin acan,naso in tashi dawuri inyi mana wani abun amma idona yacika da bacci,dama kuma ga gajiyar hanya data wajan walima,kawai sainayi bacci na, dana tashi naga bayanan kawai saina dafa mana Iya ni dake, Shima yaja musu basuyi break fast agidaba tunda shine ya hanani bacci jiya,amma aida zan tashi inyi mana wani abun dawuri"

Cikin sauri Mawahib ta kalleta tana tunani kode tajiyo Yaya Captain itama? Amma bata tambaye ta ba saitace"kema baki kwanta dawuri ba?"

Nabiha tayi murmushi tace"Yaya Ashraf ne ya hanani,amma yanda nagaji naso inyi bacci na"

Mawahib tazuba tea tafara Sha tace"toya za'ai sai haquri,jiya haka mukai da Yaya Captain nahanashi komai nace muyi bacci"

Nabiha tayi murmushi tace"nikam ban hana shi ba,kuma Koda wasa banyi kuskuren rufe masa baki ba, dade ace Aryan dina ya girma ne dole zan dauki mataki akan hakan, amma yanzu Kinga Aida saura,Mawahib a rayuwar Nan banajin akwai abinda nasan cewa zaisa Yaya Ashraf yaji dadi banyi masa Shiba, saboda shi din kamar kyautar Allah ce agareni,tun bansan menene soba nake qaunar sa,alokacin hankalinsa yana Kanki, hakan yasa nayi haquri ban baiyana ba naci gaba da Addu'ah, daga qarshe Kinga na mallakeshi, to mutumin dana tashi da soyaiyar sa, ban ta6a tsammanin zan sameshi ba, kuma sama taka na sameshi, tayaya ne zan hana shi jin dadin sa? ko a gidanmu barin sa nake yayi abinda yaso"

Mawahib ta ajiye cup dinta tagyara zama tace"Nabiha? Wai kina nufin dama duk yawan tambaya ta dakike yaushe Yaya Ashraf zai dawo dama sonsa kike? Amma meyasa baki fadamin ba?"

Kai tsaye Nabiha tace" saboda shi din dan'uwana ne, dole zan tayashi son abinda yake so, ke yakeso alokacin, dani dake kuma duka abu gudane Mawahib, shiyasa nake qoqarin Cusa miki ra'ayinsa"

Mawahib tace"nikam bansan wacce irin soyaiya Yan gidanku suke nunamin ba Nabiha, amma haqiqa kunmin komai, yanzu saboda farincikina saiki sadaukar min danaki farincikin?"

Nabiha tace"to ba gashi naga sakamakon sadaukar war danayi mikin ba?"

Mawahib ta karyi bread tace"kenifa dama nafada miki bana sonsa, bare kuma Yaya Captain da bana saka shi a lissafi, amma gashi Nima cikin hukuncin ubangiji Allah yadora min masifar qaunar Yaya Captain, yanda nakeji araina Nabiha, idan babu Aryan, to babu Mawahib"

Gaba dayansu suka sa dariya, Nabiha takira musu mutanan Saudia ta vedio call suna magana dasu harda Mawahib din, sun dade suna Waya sannan sukai sallama suka kashe

Mutara zuwa gobe🙏🏻

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki

Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/20, 10:13 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB

Sis Uzaimat
Mlm murja
Nana Asma'u ab
Sis Asma'u
Rahma delight
Fatima Baban
Fatima iddah
Salma
Ameeeeenah
Sis firdaus(writer)
Mai mahamane kagana
Sis nmera
Sis Ummi ❤️
Maman hunai
Amina Bamu
Mom Asas
Maimunat Muhammad
Umaima
Aisha musa
Mabaruka
Deeja@rh
Bilkisu saulawa
Bintu abyher
Haly jasheru
Nazifa
Fatima Abdullahi
Ummu Maryam
Bilkisu bej
Mrs Adam yar la6e😜
Ruqayya a kawu takwarar Mawahib
Mmn yzeed
Sadiya Bala zakr
Ruqayya maje
HauwaBima
Ummu Irfan
Amina kabir
Hafsat iliyasu
'yar malama me bibiyar shahaab da alama tafi tsoron bindiga akan hukumar efcc.

Bazaku qareba fa,duk wadda batada sunan taba zata gani a next page, Ina Alfahri daku💃🏼

Su Yaya Ashraf basu dawo gidan ba sai bayan azahar, alokacin Nabiha tagama yimusu girki sun sake wanka sun shirya tsaf cikin kyakykywar shiga, Mawahib doguwar riga ce ajikinta ta leshi me fadi, yayinda Nabiha tasaka riga da siket, lil Aryan yana wajan Mawahib tana wasa dashi,zama su Captain sukai a falon suna cigaba da tattauna maganar data shafi aikinsu.

Nabiha ce ta gabatar musu da abinci, yayinda Mawahib tatashi ta zauna tana dan yatsina fuska saboda yanda taji cikinta yana dan mata motsi kadan kadan.

Cikin kulawa Captain ya kalleta yace"babu matsala deko?"

Kallonsa tayi cikin soyaiya tace"babu komai, Ina lafiya"

Tare sukaci abincin gaba dayansu,bayan sun gama sukaci gaba da firarsu kad'an kad'an, saide Captain Aryan wayarsa ce a hannunsa yana turowa Mawahib kalamai tana karantawa, Nabiha sai ganinta tayi tana murmushi ita kadai.

Washegari Monday su Ashraf suka shirya suka tafi, har Airport su Mawahib suka kaisu,bayan sun dawo suka biya shopping sannan suka dawo gida.

Tun daga wajan mota yadauketa, yayinda ta saqalo hannunta ta wuyansa, har falo yakaita ya kwantar da'ita, sannan yakoma yadauko kayan dasuka siyo awajan shopping, dawowa yayi wajanta ya zauna aqasa, yayinda take kwance akan kujera yace"akwai abinda kike buqata kuma?"

Cikin kulawa tadora hannunta akan fuskarsa tace"bana buqatar komai Baby,kai kadai kamaye min gurbin duk wani abu dazan buqata"

Kansa ya gyada mata batare da yayi magana ba, ya shafa cikinta yace"dazu Naga kina runtse ido bakyajin komai yanzu?"

Cikin sauri tace" a a banajin komai"

Zama ya gyara yadora kansa akan kujerar datake zaune yayinda hannunta yake shafa lallausar sumar kansa.

Tsawon sati biyu Kenan kusan kullum Mawahib sai taji cikin yana yawan yimata motsi, ko bacci take haka zata farka, amma ganin abun baiyi mata tsananin ba yasa tayi shiru bata fada masa ba, haka sukaci gaba da kulawa da cikinsu hankali kwance, suna kuma Addu'ah Allah ya sauketa lafiya, har su Mamy suka dawo daga Saudia, basuje musu sannu da zuwa ba saita waya suka musu saboda Mawahib tayi nauyi sosai.

Washegari da safe bayan sungama break fast yana shirin fita aiki yaga tana yatsina fuska, cikin kulawa ya kalleta yace" babu matsala deko?"

Kafin tabashi amsa taji cikinta yayi wata irin juyawa, cikin azaba tafara yarfe hannu tace"cikina"

Arikice yadora hannunsa akan cikin yace"ciwo yake miki? me kike ji?"

idonta ta runtse tace"jinake yana juyawa"

Zaro idonsa yayi yace"juyawa?"
Bai jira amsar taba ya dauketa sai Mota, asbitin datake ganin likita nan yakaita,suna zuwa kuwa likitan sa ya hadasu dawata doctor mace, cikin kulawa ta duba Mawahib sannan tace zata mata scanning, Captain Aryan yana zaune agefen gadon da Mawahib ta kwanta hannunsa yana kanta yana shafa wa gabansa faduwa kawai yake tunda yaji tace ciki yana juyawa.

scanning din aka fara idon Captain da Mawahib yana kan Dr. suna kallonta, juyowa tayi ta kallesu tace"masha Allah, baby's dinku suna cikin qoshin lafiya,bawata matsala bane juyawar datakeji suna motsi ne"

Cikin sauri Mawahib tazaro idonta tareda bude baki, Captain Aryan kuwa zama ya gyara cikin farinciki yace"Dr. naji kamar kince Baby's"

Cikin farinciki ta kallesu tace"emana,yanbiyu ne acikinta ai,haba kukuwa bakuga cikin da girma ba? gashi ku kalla kuga yanda suke motsi"

Cikin sauri suka kai idonsu wajan,Mawahib tazubawa tv ido tana kallon wannan abubuwan duka acikinta suke,? ahankali tashafa cikinta, saide atsora ce take da batun yanbiyun Nan.

Captain Aryan Yasaki murmushi yace"wallahi yanbiyu ne, Alhamdulillah, Allah nagode ma,yanzu Dr. wacce shawara zaki sake bamu akan wannan cikin, banaso baby's dina su samu matsala, kuma Ina tausayin maman su, ko tashi zatayi saita runtse idonta"

Dr. tayi murmushi cikin ranta tace yau nahadu da dan soyaiya, tajuyo ta fuskance su tace"wannna tausayin daka fada kuwa dole zaka rageshi ka dinga tilasta mata kullum ta dinga motsa jiki saboda cikin nata ya girma,hakan zai taimaka mata wajan sauqin naquda,tadena zama haka kawai yanada kyau ta dinga motsa jikinta koda yaushe, sannan ahankali zata daina jin ciwon motsin harta saba daga Nan Har zuwa ranar dazata haihu, idan basa motsin ai akwai damuwa"

Cikin gamsuwa yace"Insha Allah Dr. zamu kiyaye"

Dr. tajuya ta kalli Mawahib tace"Maman twins bakya magana,ko bakya murna da ganin yaranki?"

Cikin sanyin jiki tace"Dr. mata ne?"

Dr. tajuya tasake dubawa sannan tace"maza ne, saide bamusan Yaya Allah zaiyi hukuncinsa ba, amma anan de abinda nagani dukansu maza ne"

Kallon photon yaran tasake yi tace"kuma zan'iya haifar Yara biyu?"

Likita tayi murmushi tace"idan kikai Addu'ah fiyeda biyu ma saiki ga kin haifa, komai yana wajan Allah"

Daga nan sukai shirin tafiya amma har lokacin jikin Mawahib bai rage sanyi ba, suna futowa sukai sallama da dayan likitan daya hadasu da matar data musu scanning sannan suka futo hannunta cikin nasa, adede lokacin aka wuce da wata mata akan gado Ana tura ta da uban ciki da alama naquda take, Mawahib tana ganinta saita fashe da kuka tashafa cikinta.

Captain Aryan yajata ya sakata a Mota sannan ya rufe yaja suka bar asbitin, har sukai nisa a hanya bata daina kukaba,cikin damuwa yataka birki yaja yatsaya sannan ya juyo ya kalleta yace"Honey kode bakya so nane yanzu?"

Cikin kuka ta dago ta kalleshi tace" dole kace bana sonka mana tunda natsaya kamin ciki gashinan kana gani ana mutuwa awajan haihuwa,idan na mutu ba shikkenan kahuta ba"(😂)

Murmushi yasaki yakama hannunta yariqe yana ganin yanda hawaye suke gudu a fuskarta yace"tunda akace yanbiyu zamu haifa naga hankalinki yatashi, waye yace miki ana mutuwa a haihuwa? Momy ta mutu ne? bakiga gashi ta haife mu kuma gashinan har yanzu da ranta ba? duk wanda kikaga yamutu kwanan sa ne yaqare Honey"

Wani hawayen ne yasake zubo mata tace"to meyasa zaka min cikin yanbiyu, bayan Nabiha ta fadamin guda daya ma qafar mutum daya lahira daya tana duniya"

Hannunta yasaki yasake matsowa yariqe fuskarta yace"Honey toni tayaya zansan namiki cikin yanbiyu ko dan daya? idan Allah yayi kowacce haihuwa yanbiyu zaki dinga haifomin Yaya zanyi ni?"

Tanajin haka tasake fashewa da kuka, ahankali yasaka harshensa yafara lashe mata hawayen tundaga kumatunta har idonta, sannan yahade bakinsu waje daya, saide har lokacin hawayen take zubarwa, ahankali yadago kansa ya kalleta sannan yazare bakinsa daga nata yace"menene matsalar kuma?"

Cikin kuka tace"ni tsoron haihuwa nake"

Cikin kwantar da hankali yace"zaki haihu lafiya kinji? insha Allah Allah yana tare damu yanda Momy ta haife mu lafiya nida Ash kema haka zaki haifomin sababbin Ashraf da Aryan kinji?"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta goge hawayen idonta,yasake kallonta yace" shikkenan komai yawuce?"

Dago idonta tayi ta kalli wata bishiyar mangoro agefensu reshen bishiyar duk ya sakko qasa, tace" ni mangoro zansha"

Cikin sauri yace"shikkenan muje Super market kidebi duk yanda ya miki"

Cikin shagwa6a tace"ni wannan danyen nakeso"
Chapter 63 · 0% Book details