← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 68

Sashe 65

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri yatashi daga kan cinyarta yana goge hawayen idonsa, sannan ya qarasa kan gadon ya kalli yaran masha Allah ba qananu bane,suna baccinsu cikin kwanciyar hankali suna nema su kashe masa mata, bai dauke suba, yakama hannun Mawahib yariqe sannan ya shafa kanta yadora bakinsa akan goshinta yayi kissing dinta, cikin kunnanta yarada mata "Allah yayi miki Albarka Honey"

Yasaka hannunsa yana sake goge hawayen idonsa, Mamy tayi murmushi tatashi tafice,tana fadin "bari inje in bugawa Yan maiduguri waya Infada musu"

Mama Sadiya ma tatashi tafita, Hajiya kilishi kuwa wayarta ta dauka takira Alqali yana dauka tafara fada masa, sannan itama tabar dakin, Captain Aryan yana jiyota daga falo tana buge bugen waya tana fadawa mutane.

Shida kansa yakira Ashraf yafada masa, inda Ashraf din yabashi tabbacin yau zai baro wajan aikinsa yazo yaga yaran shima, Mama Sadiya kuwa itace ta fadawa Nabiha.

Ta dade tana bacci yayinda Captain Aryan yana zaune agefe yana aikin kallonsu itada yaran yanajin wani irin farinciki aransa wai ita da yaran duka nasa ne,kallon yaran yake tundaga kan yatsun qafarsu iri dayane babu banbanci, kamar de shida Ashraf, ahankali yasake jin wani hawayen yana zubo masa, yasaka dan yatsansa ya goge, sannan ya sunkuya yayi kissing dinsu, yasake komawa gefen Mawahib.

Nabiha ce tashigo dakin cikin farinciki tana ganin Mawahib tana bacci saita fara takowa a hankali dan karta tasheta, yaran tafara kalla ta sunkuya ta dinga kissing dinsu cikin farinciki sannan ta gaida Captain Aryan daya kafa yatsare yaqi zuwa ko'ina, sannan tafuto daga dakin.

Nabiha tana fita bayan minti talatin Mawahib ta farka, ahankali tafara bude idonta harta gama bude shi fes a kansa, hannunta yana cikin nasa, cikin kulawa ya sunkuya yayi kissing dinta sannan yace"Sannu Honey,Allah yayi miki Albarka..."

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace"Yaya Captain..."

Cikin sauri yace"Honey yau ba Baby?"

Bakinta taturo gaba tace"nadena haihuwa"

Hawayen tausayin tane yazubo daga idonsa,ahankali tasaka hannu ta share masa hawayen, cikin hawayen yace"nima bazan bari kisake haihuwa ba, wannan ma sun'isa,wahalar tayi yawa,nayi tunanin mutuwa zakiyi, kingansu nan ban dauke su ba,nabari saikin tashi mu dauki yaranmu da kanmu atare"

Fuskarsa ta shafa tayi murmushi tayunqura tatashi daqyar, yayi sauri yasaka mata fillo a bayanta, sannan yadauko yaran yadora mata su ajikinta gaba dayansu, sannan ya hadasu ya rungume su wani sabon hawayen yana sake zubo masa.

Kallon Yara take tanajin yanda take tsantsar qaunar su acikin ranta, ahankali ta kalleshi tace"wana fara haifa?"

Cikin sauri ya nuna mata nafarkon,ta sunkuya ta sumbaceshi, ta sumbaci dayan ma tace" Allah yayi musu albarka"

Hawayensa ya share yace"Amin"

Dago kanta tayi tasake kallonsa,ganin yana share guntun hawaye hakan yasa ahankali ta dora harshanta akan fuskarsa ta share masa hawayen tas, kamar yanda yake mata, Mamy ce tashigo dakin cikin sauri Captain Aryan yayi baya tareda sosa qeyarsa.

Mamy bata nuna musu komai ba ta qaraso gadon ta zauna tana qoqarin daukar yaran daga cinyar Mawahib tace"wai har yanzu basu tashi daga baccin bane?"

Mawahib tace"basu tashi ba"

Mamy tadan jijjigasu tace"maza kutashi ba bacci kukazo yiba,baccin awa nawa zakuyi, kutashi gasu Yaya khaleed can afalo sunzo suga abokan su"

Hajiya kilishi ce tashigo dakin da tuwon dawa miyar kuka wadda taji Jan nama aciki, sai man shanu da'aka zuba akan tuwon dakuma kunun kanwa, mama Sadiya ma tashigo da farfesun nama duk suka ajiye mata, Hajiya kilishi takalli Mamy tace"wai har yanzu basu tashi bane?"

Mamy tace"gasunan sun kama ido sun rufe sunata bacci ko tsoron ganin mu suke oho"

Hajiya kilishi tace"tashe su"(😂)

Babu musu Mamy tafara tashin su.
Hajiya kilishi ta juya ta kalli Mama Sadiya tace"Sadiya kice su Alhaji su shigo mana,su shigo kawai"

Adede lokacin kuwa Mamy tatashi yaran, nan da nan kuwa suka fara kuka, Captain Aryan ya kallesu cikin jin dadi ya sunkuya yayiwa Mawahib rada yace"kinji kukan su"

Murmushi tayi tanajin dadi aranta.

Adede lokacin Alqali da Abba, da Alhaji khaleed suka shigo dakin,har rige rigen daukan yaran suke saboda farinciki,Alqali ya dinga kallonsu sai suka tuna masa da shekarun baya lokacin da kilishi ta haifa masa yanbiyunsa.
Hajiya kilishi takalli Mawahib tace"sauko kici tuwo saiki basu susha"

Mawahib tace"Momy ni banason tuwo"

Captain yayi sauri ya kalleta yace"yau kuma?"

Mama Sadiya tace"dama ai cikin ne yasa take cin tuwon shiyasa ga yaran nan masha Allah 6ul 6ul dasu kamar ba haihuwar farko ba"

Captain Aryan yayi kasa da kansa yana tunanin maganar Mama Sadiya cikin ransa yana fatan Allah yasa iya cin tuwon tadaina banda daya abun 🙊🙈

Hajiya kilishi tace"tuwo ai dole ne Mawahib,idan kikaci tuwon kika Sha kunun kanwar nan yanzu yanzu ruwan nono zaizo, suma yaran saisu samu abinci"

Badan taso ba tatashi daqyar ta sauko sai taji cikinta sakayau kamar an debe mata komai haka tafara cin tuwon ahankali tana tunanin yanda take masifar son tuwo kafin ta haihu amma yanzu tuwon ne bataso, taci tuwon daidai misali sannan tafara shan kunun kanwa,Alqali yayiwa yaran Addu'ah,yabasu ruwan zam-zam sukasha, sannan ya kalli hajiya kilishi yace"Kilishi yanzu kinsamu sabin angwaye ba Zaman lafiya"

Momy kilishi tace"A a bana wannan auren, ba nayi Sam Alhaji,Ina mazaje anan tunda suka zo suke aikin bacci"

Alhaji khaleed yace"A a Yaya baza'a yi hakaba"

Hajiya kilishi tace"tun yaushe?"

Dukansu dariya sukai, Nabiha tashigo dakin tana sake kunna turaren wuta.

Daga nan su Alqali suka fita, Nabiha ma tasake fita taje takawo mata fruit, sannan ta zauna tana mata sannu.

Saida taci ta qoshi Mamy tahado mata tea me shegen kauri shima tasha, sannan Hajiya kilishi ta kalli Captain Aryan tace"bata su tabasu susha"

Ahankali yadauki guda daya yabata, ta kar6eshi, Hajiya kilishi ta fice, Mamy ma ta dauke sauran kwanunkan da Mawahib tagama cin abinci tace"Nabiha zo muje ki kawo wa Captain abinci"

Nabiha tatashi tabi bayanta, Hajiya kilishi ta kalli Mamy cikin jin dadi yanda take kula da yaranta,Koda bata Raye ta tabbatar Mamy zata kula mata da yaranta, gashi de yazo tundaga Abuja babu wanda yayi tunanin bashi wani abun yaci, ciki harda ita, sai Mamyn ce tayi tunanin bashi.

Captain Aryan yana ganin ficewarsu ya matso da daya yaron a hannunsa ya kalli Wanda yake hannun Mawahib sannan ya kalleta yace"kibashi mana"

Ahankali tazuge zif din rigar ta tafuto da nonon ko brezia babu tafara bashi, Captain Aryan ya kalli breast din yanda suka sake cika yahadiye wani irin Saliva yana kallonsu da birge wa, ahankali ta runtse idonta tace"yanasha da zafi Yaya Captain"

Cikin sauri yace"Honey wai bazaki dena cewa Yaya Captain dinnan ba?"

Kallonsa tayi cikin wata irin hararar soyaiya, cikin shagwa6a tace"to ba Kaine kasa Ina zaman zamana yaranka sukazo suna neman kasheni ba, gashi yanzu suna shamin abu da zafi"

Murmushi yayi cikin jin dadi yace"zaki daina jin zafin Honey,kiyi haquri please muntuba"

Kallonsa tayi tace"Allah da zafi"

Cikin kulawa yace"sorry,basu ahankali to"

Haka ta daure taci gaba da basu duk da zafin datake ji.

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

Sai yamma Ashraf yadawo, kai tsaye suka dauke yaran shida Captain Aryan suka futo falo dasu wajan Hajiya kilishi, Mawahib kuma suka barta da Nabiha adakin,Ashraf yasake qarewa yaran kallo yace"Momy wannan ne babba,saboda haka shine Ashraf"

Cikin sauri Captain Aryan yace"inji waye? saboda Kaine babba kuma yanzu ma saika za6i babban kace shine Ashraf?, to bazai iyu ba, suma suna girma haka babban zai iyo halin ka ya dinga cewa shine gaba da Aryan, saboda haka na sauya, yanzu Aryan ne babba, Ashraf qarami"

Hajiya kilishi tace"Dan Allah sai yaushe zaku girma kudena musu akan waye babba waye qarami? Akan yayan naku ma saikun gwada halinku?, to duk ku barsu, uwarsu saita za6a da kanta waye zai zama babba waye qarami"(😂)

Wannan furucin natane yasa sukai shiru tunda tabarwa uwar yaran wuqa da nama a hannunta.

tunda akai haihuwar duk wasu masu zuwa barka anan falon Hajiya kilishi suke ganin yaran, Mawahib kuma tana cikin dakin tana hutawa, saide in yunwa suke ji sai Nabiha takawo mata su susha.

Kwanan ta uku da haihuwa Alhaji Ma'aruf yazo yaga yaran, bai hadu da Mamy ba alokacin tana wajan aiki,duk wata kulawa data dace Hajiya kilishi tana bawa Mawahib,koda yaushe tana sakata tana zama acikin ruwan dumi saboda dinkin da'aka mata, tsakanin ta da yara saide in suna jin yunwa kawai, da rana haka zasu wuni suna bacci, da daddare kuma su hana Mawahib da Hajiya kilishi bacci da kukan su.

Ana gobe suna suna zaune da Hajiya kilishi da Mamy da Mama Sadiya dukansu adakin Hajiya kilishin,Mawahib taci kwalliyar ta cikin riga da siket na leshi tayi kyau sosai duk da dare ne,ruwan tea takesha Abba yashigo dakin yadauki yaran Wanda idonsu yake qur akan hasken dakin, cikin kulawa Abba yace"suna tayaku fira kenan"

Hajiya kilishi tace"wadannan? lumbu lumbu kenan, Ana jimawa zasu fara kuka kamar wanda ake zigasu, daya yana fara kuka Shima dayan zai farka yafara har tausayi uwar tasu take bani,haka zan yi juyi inganta daram a zaune tana faman jijjigasu, to sai in dauki daya in tayata Nima, amma bama bacci wallahi, nikuma lokacin danayi goyon su Ashraf bahaka nayi ba, kalau muke bacci"

Abba yace"toku dinga hanasu baccin da rana mana Yaya"

Hajiya kilishi tace"ana musu wanka ma idonsu a rufe yake, saide in wankan yayi wanka shine zasu farka,amma wannan kukan nasu yayi yawa, kamar hadin baki Yara kudinga ihun kuka cikin dare"

Kafin Abba yabata amsa megadinsu yadoko sallama yafara ajiye wasu hadaddun akwatuna agabansu, mamaki ya kama su, kafin suyi magana Ashraf da Aryan ma sun shigo da wasu, wasa wasa saida suka ajiye akwatuna guda goma, na yara shida, kowa uku uku, na Mawahib kuma guda hudu.
Chapter 65 · 0% Book details