← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 68

Sashe 20

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawayen idonsa yagoge gaba daya sannan yace"toya zakayi? Ya sukeso kayi? shi Daddy yace karka saketa,ita tace saika saketa saki uku,yanzu saboda Mawahib har Momy zatayi alfahri da rashin haihuwar ka saboda karka hada jini da'ita? Ni bazan iyajin wannan fadan nataba,zuciyata saita buga"

Ya qarasa maganar wani Hawayen yana zubo masa,Captain Aryan ganin Ashraf da gaske de kukan yake hakan yasa yadaure yazo kusa dashi yafara cewa "kayi shiru mana,aini bana kukan,kamar mace kana kuka Ashraf to waye zai lallashi Amarya bayan sati daya?"(🙈🙊😂)

Cikin sauri Ashraf yadauki fillo yadoka masa shikuma yana dariya,dahaka yayi nasarar lallashin Ashraf harsukai warware kamar babu abinda yafaru.

Washegari da yamma yayi shirin komawa Abuja,sunyi kyau sosai cikin baqin yadi Mai tsadar gaske,Sai hasken fatarsu yasake futowa sosai,kana ganinsu kaga angwaye,kafin yatafi sukaje wajan Hajiya kilishi,Ashraf Sai dauke Kai yake, suna gaisheta ya kawar da kansa gefe saboda abunda yafaru jiya da daddare.

Cikin sanyin jiki Captain yace"Momy zan wuce kimin Addu'ah"

Daqyar tabude baki kamar bataso tace"Allah ya tsare hanya"

Cikin sanyi jiki yace"Amin"
Yasaka hannu a aljihun rigarsa ajiye mata damin kudi guda biyu, sannan yasake bata haquri,suka futo daga dakin.

a gurguje Ashraf ya rakashi part din Mamy,ta dauko masa wata gumba dataji hadi irinna Yan maiduguri tasaka acikin baqar leda ta bashi tace yakaiwa Mawahib,cikin ladabi ya kar6a da hannu biyu,saida yaga tajuya sannan ya ajiye mata kudi dami daya akan kujera daga Nan suka futo.

abakin get ya hadu da iyayen nasa maza,yayi musu sallama, Alqali yasake jinjina masa akan ya riqe Mawahib da kyau, sannan suka shiga Mota da Ashraf yakaishi Airport shikuma yajuyo gida.

Sai qarfe shida na yamma yasauka a Abuja, suna Sauka Ana Kiran sallar magrib.

David yana ganin dawowar oga Captain yayi sauri yabude masa get cikin rawar sauri, saboda yasan yau bai kwana agidaba.

Matar gidan kuwa batasan baya nanba,idan yana nan dinma Sai suyi kwana da kwanaki basu haduba, shiyasa yanzun ma Batasan cewa yaje kano ya kwana ba,Kuma suma yan gidan babu Wanda yace mata Yaya Captain yazo gida.

Yana Bude falon nasu wani qamshi mai dadi na turaren wuta da air freshener yadaki hancinsa,qamshin yamasa dadi hakan yasa ya lumshe idonsa sannan yabude kai tsaye yahaye Sama ya shige dakinsa, zubewa yayi akan gadon sa yana maida gajiya,saida yahuta sosai sannan yakira Yan gida Yafada musu yasauka,fridge din dake cikin dakin yabude yadauki ruwa yasha sannan yaje yayi wanka yadauro alwala yazo yagabatar da sallah sannan ya zauna yana azkhar.

Yadade a zaune har wajan qarfe tara nadare sannan yatashi yacire farar jallabiyar jikinsa yasaka rigar bacci doguwa kalar dark blue,rigar iyakar tsawonta gwiwar sa,daga gaban rigar abude take kana Iya hango gashin dake kwance a faffadan qirjinsa.

Yana kwanciya akan gadon yaga ledar da Anty Mamy ta bashi yakaiwa Mawahib,dan qaramin tsaki yasaki yatashi ya dauko ledar batareda yadamu daganin menene aciki ba,Yafuto daga dakinsa yanufi dakinta

Adede lokacin tafuto daga wanka, kasancewar tasan baya ta6a shigowa dakinta hakan yasa taqi rufe dakin da key,ta tsaya a gaban mirror tana shafa humra ajikinta.

Sauke towel din dake jikinta tayi yayi qasa gaba dayansa,surar jikinta da dukkan dirin jikinta ya bayyana muraran batada komai ajikinta, ta dauki turare spray tana feshe duka jikinta dashi, adede lokacin yaturo qofar dakin zuciyarsa daya yashigo(🙆🏻‍♀️😳🙈)

Idonsa bai sauka a ko'inaba Sai akanta,gabansa yayi wata irin faduwa,a zahiri, Kuma agabansa, bai ta6a ganin mace babu kaya ba Sai yau.

Idonsa qyam akan nashanunta Wanda suke atsaye cif,ya Kalli bajajjan hips dinta cikin ransa yace"yahaka?, dama natane? dama jikinta ne ba cuko ba?"
zai Iya cewa akaf tarihin rayuwarsa bai ta6a ganin yarinya me qananun shekaru dakyan jiki kamar taba.

Lokaci daya yaji wani abu zirrrr tundaga qwaqwalwar sa har zuwa tafin qafarsa,duk saiya nemi jarumtarsa yarasa, Sai jikinsa yafara rawa.

Mawahib tana dago kanta ta ganshi a tsaye,lokaci daya tasaki wani irin ihu ta tsugunna qasa tareda wawuro towel din data jefar aqasa tarufe jikinta dashi,tuni hawaye suka 6alle mata afuska,ta qudundune a waje daya tana raskar kuka.

Kukan tane yasa yagama dawowa hayyacinsa, cikin sauri ya ajiye mata ledar a wajan, Yajuya yafice daga dakin cikin sauri.

Yana zuwa dakinsa Yafada kan gado yana maida numfashi kamar Wanda yayi gudu.

Lumshe idonsa yayi tareda dora hannu akan sumar kansa yashafa sumar zuwa fuskarsa, haushin kansa yakeji meyakaishi? meya aikata haka? Wanne kallo yarinyar nan zata dinga masa?

Cikin sauri yaja bargo yarufe jikinsa dashi har kansa, ya Runtse idonsa tareda karanto addu'ar bacci,cikin ikon Allah bacci ya dauke shi,saide ko awa biyu cikakke baiyi ba yafara ganinta cikin baccinsa a'irin wannan yanayin daya ganta dazu.

Cikin taqaici yatashi yazauna tareda sakin wani irin dogon tsaki, afili yace"a a, waiya haka ne?"

Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Mrs Usman✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻

Cikin kuka Mawahib tafara tirjewa tana kiran sunan Mamy, har zuwa wannan lokacin Mamy kanta yana dafe da hannunta, saide ruwan hawaye dayake gangarowa har zuwa tsintsiyar hannunta, tanan ne zaka fahimci kuka take,shikkenan komai yaqare, yau Mawahib dinta ce ta auri dan Yaya kilishi,Ma'aruf ya cuceta duniya da lahira, Abba yayi murmushi yazo saitin kunnanta yace"Maryan shikuma wannan ikon Allahn yaya zakiyi dashi kenan?"

bai jira amsar ta ba yajuya yabi bayan Mawahib da Captain Aryan,Captain dayake riqeda hannun Mawahib tana masa ihun kuka jiyaje kamar yadauketa da mari(🙆🏻‍♀️)

Alhaji Isah yayi sauri ya tarar dasu,kai tsaye yabude musu mota yakira driver yace"zoka kaisu Airport"

Mawahib tanajin maganar Abban ta ta qwace hannunta daga cikin na Captain tatafi da gudu ta rungume Alhaji Isa cikin kuka tace"Abba banaso,dan Allah Abba karka bari yatafi dani,zan mutu Abba"

Alhaji Isah yayi murmushin qarfin hali yaja hannunta yasakata cikin mota, sannan yakama hannun Aryan da idanunsa sukai jajir shima yasaka shi a motar sannan ya rufe musu motar yajuya cikin gida yanajin zuciyarsa tana karyewa saboda kukan Mawahib din

Acan dakin Hajiya kilishi kuwa,Alhaji Ma'aruf yajuya ya kalli Mamy yace"Maryam meyake faruwa ne?"

Mamy batace dashi uffan ba tajuya tatafi part dinta idonnan nata yayi jajir saboda kuka.

Alqali ya kalli kilishi cikin daure fuska yace"wuce daki"

Haka ta wuce daki saikace mahaukaciya, tayaya ne tanaji tana gani za'a bawa Aryan Mawahib,Aryan din dataci buri akansa shine za'a hadashi da wannan tantiriyar yarinyar dabata da aiki Sai nunawa mutanan gari jikinta,inde tanada iko akan Aryan tosaiya saki wannan yarinyar.

Alqali yanemi waje ya zauna sannan ya kalli Alhaji Ma'aruf da Ashraf dasuke tsaye yace"duk ku zauna"

Bayan sun zauna ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"Alhaji Maryam acikin gidannan take,sannan mutumin dakuke waya dashi akan maganar auren nan shine mijin ta,wato Alhaji bazamu kira abinda kayi amatsayin kuskure ba,abinda kayi ka kyauta, kuma muma kahutar damu, saboda mu a wajan mu da Ashraf da Aryan duk dayane,kaga wannan yaron dayake zaune?"

Yafadi hakan yana nuna Ashraf, Alhaji Ma'aruf yajuya ya kalli Ashraf sannan yace"naganshi Alhaji,amma yanaga haka? yanaga kamar wancen dayan? kode yanbiyu ne Alhaji?"

Alqali yace"yanbiyu ne,kuma dukansu 'ya'yanane, wannan shine Ashraf, shine babba,sai Captain Aryan shine qarami,yanzu haka zaman da kaga munyi anan da wannan goro dakake gani nasaka ranar Ashraf ne da Mawahib,Captain Aryan kuma muka yanke shawarar zamu hadashi da yar'uwarsa Asalamiyya,to shine shida dan'uwan nasa suka samemu da wannan maganar cewa kayi masa aure kaji dalilin dayasa muka kiraka domin musake tabbatar wa da abinda suka fada mana,tunda muke da Maryam bata ta6a nuna mana mahaifin Mawahib ba,tun bayanda yan tashin hankali suka faru abaya har Allah yasa aka samu saki a tsakanin ta da mijinta tabar gidannan tsawon wasu shekaru daga baya kuma Allah yayi zata dawo gidannan Isah yaje aka sake daura musu aure, sai muka ganta da wannan yarinya, muka kar6i yarinya muka riqeta da hannu bibbiyu,saboda mun yarda da Maryam mun tabbatar bazata haifi yarinya bata hanyar aure ba,ita bata kawo mana uban yarinya ba,muma Kuma bamu tambayeta ba,to abinda yake faruwa anan gidan shine iyayen yaran Nan mata basa jituwa,hakanne yasa muka dage kan hada auren Ashraf da Mawahib domin asamu sasanto a tsakanin su,to ashe Kai kariga kabata Captain Aryan,amma duk da hakan babu matsala,suje Allah yabasu zaman lafiya da zuri'ah tagari"

Gaba daya falon aka amsa da "Amin"

Alhaji Ma'aruf yace"ikon Allah,lalle ubangiji yayi hukuncin sa anan,to Allah yabasu Zaman lafiya,amma ni idan Naga wannan dinma ai Sai in dauka Captain Aryan dinne"
Ya qarasa maganar yana kallon Ashraf.

Alqali yayi murmushi yace"haka suke,tun suna yara ba'a cika banbance suba"

Alhaji sammani wakilin Asalamiyya yace"to yanzu Alhaji, Ina maganar saka ranar Asalamiyya da Aryan ta tsaya?"

Kai tsaye Alqali yace"Sammani tunda wannan abu yafaru, Ina ganin abar maganar Asalamiyya agefe, idan Captain ya zauna da matarsa sunga halin juna, yaji yanada ra'ayin qara aure,idan har Asalamiyya din tamasa saiyazo su daidai ta idan har zuwa lokacin batayi aure ba"

Alhaji Sammani yayi qasa da Kai cikin ladabi yace"to ai ranka yadade atawa shawarar Ina ganin mezai hana Ashraf yamaye gurbin dan'uwansa Captain Aryan,kamar yanda Shima Captain din qaddara tasa yamaye gurbin Ashraf?"

Alqali yace"da nayi wannan tunanin,to daga baya saina yanke shawarar Shima Ashraf din zan hadashi aure da qanwarsa NABIHA"

Jikin Alhaji sammani yayi sanyi, gashi babu damar dazai kushe Nabiha, kokuma yayi musu da Alqali tunda ga mahaifinta nan a zaune,cikin danne damuwar sa yace"eh hakane,hakanma ai yayi,to Allah yasanya Alkhairi,Allah yabasu Zaman lafiya gaba daya, mu bari muwuce"

Alqali yace"Allah ya maida ku gida lafiya"
Chapter 20 · 0% Book details