← Book details Mawahib Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 68

Sashe 41

Mawahib Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan tawuce dakinsa tafara dube dube,can ta hango wata farar leda, tana dubawa taga magungunan aciki masu yawa, mamaki ya kamata, me Yaya Captain yake da wannan magungunan?
bashida lafiya ne?
Hannu tasa acikin ledar ta dauki guda daya taduba tagani,ta6e bakinta tayi ganin bata fahimci maganin kona menene ba, tafuto tarufe dakin sannan takawo masa,takoma kitchen tadauko masa ruwa takawo masa,bata tashi daga wajan ba tana satar kallonsa saida yasha Kala kalar magani sunkai guda biyar, sannan tadauko ledar tawuce sama.

Har qarfe shadaya da rabi nadare idonta biyu batayi bacci ba,sai yanzu ne abubuwan da Yaya Captain yake mata suke sake dawo mata arai, meyasa yake mata haka?
yaudara ce kokuma yan'uwan taka?
tasan cewa de soyaiya kam babu ita, Yaya Captain bazai ta6a sontaba, to amma meyasa yake qoqarin ganin ya faranta mata a kwanakin nan?

Wayarta dake silent tayi haske alamun shigowar saqo,cikin mamaki ta kallo agogon wayar taga qarfe shabiyu na dare,waye zai mata saqo,?
Number data gani ce tasa gabanta faduwa,a fili ta furta Yaya Captain?
saqon tabude taga yaturo mata "kin kwanta ne?"

Cikin mamaki tace anya lafiya kuwa?
bai ta6a turo mata saqo ba, Kuma a'irin wannan lokacin.

Acan dakin Captain kuwa a zaune yake a gadon yasaka wayarsa a gabansa yana jira ta masa reply,bazai Iya Samun nutsuwar bacci ba sai yaji daga gareta, yanason su dinga fira ta wayar ko yasamu bacci ya daukeshi.

Saqo ne yashigo, cikin sauri ya rarumi wayar zai duba saqon, bai bude ba saida ya kwanta sannan yabude yaga taturo masa "no,but zan kwanta yanzu"

mezaice mata Kuma?
Bawani surutu suke yiba,shibe Iya zance ba, da Ashraf nede saita gaji, to amma shi mezaice yanzu?

Cikin jin haushin rashin surutun sa yayi mata replay da "Ok sweet dream nd take care of yourself...."

Wayar yazubawa ido yana jira ko zata ce masa wani abu, shiru shiru bata turo masa komai ba, haka ya haqura shima yakife wayar tashi sannan ya lumshe idonsa yafara karanta Addu'ah ta bacci.

Washegari sassafe tatashi tayi ayyukan komai ta ajiye masa breakfast takoma sama ta kwanta takoma bacci, saboda tasan yau Monday zai fita aiki da wuri.

Captain kuwa yana dawowa daga wajan motsa jiki kawai wanka yayi,yafuto yaci abinci yazauna afalon yana shan magungunan sa yana kallo kad'an kad'an,yau babu inda zai fita yariga yanemi excuse,har qarfe goma na safe bata futo ba, yayi mamaki sosai,yadade yana falon har wajan goma da rabi, sannan yakashe kallon yadauki fillon kujera guda daya yadora a cikinsa ya rungume shi, sannan ya lumshe idonsa yafara bacci.

Mawahib bata tashi farkawa ba sai wajan qarfe goma shadaya na safe,tayi wata irin miqa sannan tawuce toilet tayi wanka a nutse,tashirya cikin riga da wando tasaka hula akanta,riga da wandon sunada dan fadi tasake acikin kayan sosai,haka yadin kayan yanada santsi amma ba sosai ba,qasa ta sauko domin cin abinci, batayi tunanin yana falon ba,tana zuwa saitayi turus ta tsaya tana kallonsa,tayi sauri taduba wayarta taga de yau Monday,amma yata ganshi a kwance anan?
tajuya gefe taga magungunan sa awajan, ta tuna jiya ma yace tabashi maganin zaisha,Kuma Bayan ta kwanta yamata text yana tambaya ko tayi bacci to Kode bashida lafiya ne?
Ko ciwon ne yasa yaqi fita aiki shida baya wasa akan zuwa wajan aiki?
Kokuma jikin nasa ne yatashi shiyasa yake tambayar ta a text yana nufin idan bata wani abu taje ta taimaka masa?
Shi miskilancinsa yamasa yawa, bazai futo fili yafadi abinda yakeso ba,to amma kuma aiyace mata ta kwanta tayi bacci medadi.

Matsowa tayi kusada kujerar dayake kwance,takai hannunta zataji jikinsa koda zafi,saitayi sauri ta janye hannunta tafasa, ta kalli tulin magungunan dasuke gefe tasan cewa ba kalau ba, matso da fuskarta tayi dab da tashi fuskar ko zataji jikinsa da d'umi.

Captain Aryan yana jinta tun lokacin datazo wajan yafarka saboda qamshin ta daya shaqa, yanajin qamshin turaren yafarka amma bai bude idonsa ba,yanda yaji numfashinta yana sauka a fuskarsa sai hakan yake qoqarin jefashi awani irin yanayi, Mawahib kuwa da taji bataji wata alama ta zafi ba saita dago kanta kad'an, tamaida kallonta kan kyakykywar fuskarsa,zallar kyansa take gani,jan lips dinsa ta kalla tafara tunani, Yaya Captain yanada kyau sosai, amma tarasa meyasa takasa jin sonsa aranta kamar yanda sauran mutane suke sonsa.

Ajiyar zuciya tasauke zata tashi tawuce kitchen,Captain Aryan dayaji zatabar kusa dashi cikin sauri ya fuzgota tafado jikinsa,cikin tsoro tasaki wata yar qaramar qara,cikin sauri yasaka hannunsa ya rufe mata bakinta sannan yazubawa fuskarta ido yana kallonta,itama shi take kallo,fuskarsa da bacci da rashin bacci koda yaushe haka take babu fara'ah, cikin muryarsa tame bacci yace"me kike kallo?"

girgiza kanta tayi sannan ta janye hannunsa daga bakinta tace"dama....dama..damafa nayi tunanin bakada lafiya ne,shin...shine"
saitayi shiru takasa qarasawa,ta sunkuyar da kanta qasa tana kallon yanda tayi male male akan jikinsa kamar tasamu katifa.

Wani irin dan qaramin murmushi yayi,har zaice shine daga tunanin rashin lafiya kika tsaya kina qaremin kallo,? to kuma sai yayi shiru yashareta,idonsa ya lumshe sannan yabude ya kalleta yace"lafiyata kalau,karki yi girki yau,idan kingama abinda kike,qarfe biyu zamu fita"

Cikin sauri ta daga masa kanta, sannan tafara kokarin tashi daga jikinsa,yanda take motsa jikinta anasa hakan yasa yayi saurin lumshe idonsa yanajin wani irin dadi,fatansa daya, Allah yasa idan sun fita ya'iya kallon idonta ya bayyana mata abinda yake cikin ransa ko zai samu ta yafe masa takuma amshi soyaiyar sa.

yanajin tatashi,shima yatashi yayi sama saboda daga haduwar nan tasu tasashi cikin yanayin da bazai Iya tunkaran masallaci batare da wanka ba(🙈)

kamar yanda yafada qarfe biyu daidai suka fita,yau wankan laffaya tayi,baqar laffaya ce me adon stones,kasancewar ta fara hakan yasa laffayar tayi mata kyau sosai,shikuma yasaka manyan kaya na shadda, saide baisaka babbar riga akai ba,bata ta6a ganinsa da manyan kaya a Abuja ba,kullum saide qananu kamar ba bahaushen mutum ba,amota babu wanda yake magana,Mawahib tana tunanin yau Kuma inane zasuje dahar yaqi zuwa aiki saboda fitar tasu?
shikuma yana tunanin yanda zai fada mata yanda yakejin ta acikin ransa.

wani wajan cin abinci sukaje,wajan yahadu sosai an qawatashi Iya qawatuwa,babu kowa awajan,haka duk kujerun dasuke wajan iya kujera daya ce aka shirya shirya abinci da lemuka akai, hakan ya tabbatar mata wajan yakama gaba daya kenan, Captain Aryan ya Kalli ko'ina yaga tsarin yamasa kamar yanda sukai magana dasu ta Email,wajan zaman suka qarasa yaja mata kujera ta zauna sannan shima yazauna,kallonsa tayi taga yanata walwala,dakansa yatashi yafara zuba mata komai, cikin sauri tace"yaya Captain kabarshi zan zuba dakai...."
Kafin ta qarasa cewa dakaina,yadora hannunsa akan qaramin lips dinta yace"shiiiit"

Babu musu tayi shiru,shine yazuba mata komai yatura mata gabanta, sannan shima yazuba,d'aya daga cikin ma'aikacin wajan yazo cikin ladabi yace"yalla6ai akwai abunda kuke buqata aqaro ne?"

Hannu kawai Captain yadaga masa alamun cewa babu komai, cikin girmamawa yajuya yabasu waje.

Abincin sukaci cikin nutsuwa,har yanzu Mawahib tana tunani aranta meyasa yau suka futo cin abinci?
ko natane bashida dadi?
gaba daya mamakin sa yagama kashe ta,gaba daya gani take kamar an sauya mata shi.

Sun dade dagama cin abincin harta yi tunanin ko wani yake jira,saita ga yatashi yadawo kusada ita ya zauna,cikin sauri ta kalleshi,bai damu da kallon nataba yakama hannayenta duka biyun yariqe, sannan ya Kalli qwayar idonta yace" I'm sorry"

Cikin mamaki Mawahib ta kalleshi sai rarraba idanuwa take,cikin rawar murya tace"for what...?"

Yakalli qwayar idonta sannan ya sassauta murya tace"for everything...,kiyafemin,nasan nayi miki laifi abaya,ba daya ba, ba biyu ba,kuma kina kallo na da wannan abun aranki, amma na kar6i laifi na,na kar6i kuskure na,inaso kiyafemin please..."

Jikin Mawahib yayi wani irin sanyi,meyasa Yaya Captain yake mata wannan abubuwan ne?
waye ya sauya shi?
bazata Iya qin yafe masaba,duk da ba soyayya ce a tsakanin suba yanzu zaman nasu yafi na baya,yana kokarin kyautata mata,kallonsa tayi, cikin sanyin jiki tace"nayafe ma Yaya Captain"

Cikin sauri yace"are you sure?"

Murmushi tasaki tace"very sure"

Idonsa ya lumshe yana hamdala aransa,saura Kuma batun soyaiya,but kar tayi tunanin saboda soyayyar sane yasa yanemi yafiyar ta,yanemi yafiyar tane saboda yafara wanke kansa a wajanta,hakan yasa ya haqura bai fada mata cewa yana sonta ba,Mawahib ta Kalli idonsa taga bakinsa yana motsi kamar yanason yafadi wani abu, har lokacin hannunta yana cikin nasa hannun,yadago kansa ya kalleta yace"muje gida?"

Cikin sauri ta daga masa kanta,dama atakure take awajan,takasa sakewa har yanzu, tarasa dalilin sa na neman wannan yafiyar, amma dole zata tambayi Nabiha.

Hannunta cikin nasa suka futo daga wajan,yabude mata mota tashiga sannan yashiga yaja suka dauki hanyar gida.

basu qarasa gida ba sai qarfe hudu da kwata, hakan yasa yana ajiyeta yajuya yatafi masallaci,itama sallah tayi, tacire laffayar jikinta ta watsa ruwa, sannan tasaka yar qaramar riga tafuto falon qasa,saitake jin ranta fes, kamar ansauke mata wani abu data dade yana damunta, hakan yasa tashiga kitchen ta dauko robar ice-cream guda daya tayi zamanta afalon tafara Sha,Yaya Captain bai dawo ba sai wajan qarfe biyar,yana zuwa yaganta afalon tabaje tana shan ice-cream yayi murmushi yawuce sama, ko banza tunda yanemi yafiyar ta yasan hakan yayi tasiri sosai tunda gashi harta Iya fara zama afalon duk da tasan yana gida zai Iya shigowa kowanne lokaci,amma ahakan tazauna bata gudu daki ta kulle kanta ba, hakan ya nuna tafara dan sakewa dashi.

Qananun kaya yasaka yafice motsa jiki,bata bar falon ba saida taji anfara kiran sallar magrib, tatashi tayi sama,ta gabatar da sallah sannan tabude qur'ani tana karantawa har zuwa lokacin sallar isha'i.

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼
Chapter 41 · 0% Book details