Sashe 98
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
By
Maman Maama
Episodes Seventy & Seventy One : The Wedding
The chance of you dying with COVID-19 is 1% while the chance of you dying anywhere anytime by any means by Allah's wish is 100%. Wanne ya kamata muji tsoro? Corona virus ko Allah? Then why the panic bayan mun yadda da kaddara munsan komai rubutacce ne?
Mafita kawai shine mu koma ga Allah mu rungumi Alqur'ani da Azkar, mu yawaita istigfari sannan kuma mu bi dokokin da ma'aikatan lafiya suka kafa.
Idan Allah ya riga ya rubuta cewa Corona virus itace sanadin mu muna rokon Allah ya karbi shahadar mu (mutuwar annoba shahada ce), idan kuma ba ita bace ba Allah ya bamu rayuwa mai albarka ya dawwamar damu cikin imani Ameen. Allah kuma ya kyautata karshen mu.
Diyam...............
Diyam taji dadi sosai a ranta. Tabbas ko da Sadauki bai fito da Saghir ba to kuwa yafe masa ma da yayi ya nuna cewa his stone hard heart is now soft. Yanzu ya yi part dinsa ya rage nasa kuma ya taimaka wa Saghir ko yaki duk ganin damarsa ne, taimakon yana da kyau sosai musamman saboda xuri'ar da aka riga aka hada, amma kuma ba wajibi bane ba. Dan haka ba zata sake yi masa magana ko kokarin tursasa shi zuwa haka ba dan in yayi din ya zamanto niyyarsa ta kyautata.
Tayi masa kyakykyawan murmushi tace "hakan ma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci" yace "Ameen, Mrs Abatcha" ta harare shi, "bana so" yace "okay, madam kike so?" Ta mike tsaye kamar zata yi kuka "bana so wallahi" ya mike shima yana mata dariya "gaya min to, me yasa ba kya so?" Tace "sai in ji na zama kamar wata katuwar ƙedara, wai Madam" yayi dariya sosai yana matsowa kusa da ita yace "to me kike so ince miki?" Ta juya ido tace "Diyam" yace "Sadiyam" tayi masa gwalo tace "sholoki" sai ta bar gurin da sauri ta tafi gurin Subay'a tana waigensa. Ya daga murya yace "zan kama ki ne ai, not now but on the 25th" bata waigo ta kalleshi ba but she blushed.
Wayarsa tayi kara ya duba sannan ya taho gurinsu yana cewa "time off, Inna ta gaji da jira tasa yar asama ta kira mu" Diyam ta mike straight tana cewa "Allah sarki inna ta, nima nayi missing dinta sosai" ta mika masa takardun hannunta suka tafi Subay'a tana ta fushi wai ita ta dauka sunzo kenan.
A kofar gida ya ajiye su yace bazai shiga ba. Subay'a ta fita da gudu tana ta dokin bawa Asma'u labarin sabon gidan da suka je. Diyam ta yi masa sallama zata fita kenan sai ya miko mata wani card ta karba tana dubawa taga credit card ne sai yace "ki dauki kudin da zaki bukata a ciki, ki kuma dauki na su Murja da kika yiwa alkawari" kafin tayi masa godiya sai yace "birth year din ki shine pin din" ta gyada kai tana murmushi, ta sake bude baki zata yi godiya yace "bana son ji. Ko ki fita ko kuma in tafi dake kuma bazan dawo dake ba sai dai a biyo ki da kayan ki".
Bata san tayi missing inna har haka ba sai da ta ganta tukunna, ta tafi da sauri ta rungume ta tana dariya, itama innar dariyar take yi amma sai ta ture ta tana cewa "kar ki karya ni" Asma'u ma ta kankame ta tana cewa "nayi missing dinki, sosai Adda ta" Diyam ta kalleta tace "oh, Asma'u kin kara girma fa. Inna wannan ai itama kamata yayi a hada bikinta da nasu Murja" Asma'u ta fara buga kafa tana cewa "shikenan zaki kunto min ruwa, dama inna kiris take jira ta dawo kaina" ta karashe maganar tana tafiya daki. Inna ta bita da kallo tana cewa "yayanki ne ya daure miki gindi ai, daga ke har shi kun tsaya kuna ruwan ido amma ace yarinya kamar ki har yanzu bata da saurayi?" Diyam dai tana tayi musu dariya saboda ta fahimci wanne yayan ake nufi, shi har yanzu kallon Asma'u yake kamar wata jaririya.
Diyam ta lura da chanji a gidan su, an bude part din Ummah an kwashe kayan ciki sannan an gyara shi amma ba'a zuba komai a ciki ba. Ta shiga daki tayi wanka ta shirya tayi sallah sannan ta dawo palo suka zauna cin abinci da Inna, Asma'u da Subay'a da take ta zuba mata hira tana kokarin bata labarin duk abinda akayi a gidan sanda bata nan. Sai Diyam taji tamkar gidan yafi ko ina dadin zama.
Bayan ta kwana biyu ta huta sai shirya da niyyar zagaya gidajen yan uwa ta gaishe su. Inna tace "sai kiyi musu sallama kuma dan ba lallai ne ki sake samun zuwa gurin su ba". Tare da Asma'u suka fita, gidan Alhaji Babba suka fara zuwa, wannan shine zuwan Diyam gidan na farko kuma taji dadin yadda taga gidan, ba kamar dai nasu nada ba amma kuma basa cikin kuntata. Babban abinda ya kara mata jin dadi shine ganin Alhaji Babba ya chanja sosai ya samu nutsuwa fuskarsa ta saki ta rage nuna damuwa. At last ya daina blaming makiya da sauran al'umma for his misfortune. Da fara'a sosai ya amsa gaisuwar tata har da tsokanar ta da cewa "munji ki shiru har ina tunanin ko sai dai kawai mu daura auren anan in yaso angon ya biki can?" Ta rufe fuskarta tana jin kunyarsa. Sai kuma yayi mata godiyar kudin haya data biya masa sannan ya dora da bayanin neman yafiya a bisa abubuwan rashin adalcin da yayi mata. Ta katse shi da sauri "Alhaji ni na yafe ai, tuntuni na yafe muku tun ma kafin mu rabu da Saghir. Komai ya wuce sai fatan Allah ya kara gyara mana zumuncin mu" yace "ameen" ya dora da "ina son kuma ki sake yi min godiya gurin yaron nan Aliyu. Satin daya wuce naje na gano Saghir kuma ya gaya min abinda yayi masa, ya gaya min ya yafe masa kudaden daya daukar masa" ya fada yana dauke hawaye da babban yatsan sa. "Kudade masu yawa amma yace ya bar masa su. Kuma yace min ya hada shi da lauyoyinsa zasu taimaka masa akan maganar kwayoyin nan. Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yaji kan mahaifiyarsa, matar da har ta mutu Allah bai bamu ikon neman yafiyarta ba".
Ta shiga dakin Hajiya ta dauki Muhammad, kyakykyawan yaro har ya warware yana ta shan madarar sa. Sai kuma ta shiga dakin Hajiya yalwati inda acan ne tafi dadewa suna ta hira da Murja da sauran yammatan, suna ta competition gurin farantawa Diyam.
A gidan Kawu Isa shima ya karbe ta sosai shi da iyalinsa. Sun jima suna hira yana tayi mata nasiha a game da aure, sai taga kamar wani chance ne ta samu na kokarin gyara tsakanin su da Alhaji Babba. Tace "Kawu, mu kuwa zamu ji dadi idan komai ya wuce tsakanin ka da Alhaji, kune iyayen mu, ta yaya zamuyi zumunci idan ku ba kwa yi?" Sai ya girgiza kansa yace "uwata shi zumunci yi min ne inyi maka, shi Alhaji Babba son kansa da son dansa ne ya jawo igiyar zumuncin sa da mutane duk ta gutsire. Ni fa wai kyautata wa ce na yiwa yaron nan na dauki yarinyar nan nace na bashi ita a daura musu aure saboda in gyara zumuncin da nayi tunanin kamar ya samu baraka, amma kinga sakayyar da ya saka min dashi. Dana je gurin uban na gaya masa ga abinda dansa yayi maimakon ya nuna alhinin sa kuma ya kira yaron nan ya nuna masa laifinsa sai ya shafawa idonsa toka yace shi ba dansa ne yayi ba, ko tambayar yaron ma fa baiyi ba. Yanzu gashi nan ya ga sakayya ai. Ni kuma gashi an barni da yarinya, ni ina ganin na kaita Kollere ta haihu a can ina tunanin kamar na rufe maganar ashe duk jama'a kowa ya sani. Jiya jiyan nan na fito daga masallacin unguwa naji ana maganar. Yanzu waye zai aureta da wannan tambarin? Menene makomar rayuwarta dana zuri'ar da zasu fito daga gareta?" Diyam tayi shiru tana tunani sai tace "Yanzu Kawu zaka hakura idan Saghir ya fito ya auri Suwaiba? Suka bude sabuwar rayuwa suka kuma rike dansu? Zaka yafe masa ka dawo da zumuncin ka da Alhaji?" Yayi shiru yana dan jujjuya kafa sai yace "yaushe Saghir din zai fito?" Diyam tace "very soon, insha Allah" sai yace "Allah ya fito dashi lafiya, abinda zasu yi shida mahaifinsa idan ya fito din shine zai zama tubalin cigaban alaka a tsakanin mu".
A cikin gidan sai Diyam taga bata ji dadin ganin Suwaiba ba duk ta rame, duk da cewa ita mai kiba ce amma yanzu duk ta sirance, farin ma ya ragu amma sai Diyam ta danganta hakan da haihuwar da tayi. Sai da Diyam tazo tafiya sannan Suwaiba ta biyo ta da niyyar rakata sai tace "Diyam kinga Jawad a gidan Alhaji?" Diyam ta gyada kai tana kallon ta, sai tayi murmushi kawai, anan Diyam ta fahimci problem din Suwaiba, kewar jaririnta take yi, sai tace "Diyam naga abban mu ya sakar miki fuska, dan Allah ko zakiyi masa magana ya karbo min Jawad" Diyam tayi shiru bata ce mata komai ba saboda ita dai ba zata iya wannan rashin kunyar ba. Sai dai kuma ta tausayawa Suwaiba saboda tasan zafin rabuwa da É—a musamman ma wannan da yake dan jaririn da ko nono ba'a barta ta bashi ba. But hausawa sunce idan bera da sata to kuwa daddawa ma tabbas da warinta. Tabbas Saghir yayi laifi amma kuma itama Suwaiba da akwai nata laifin da har ta bari dadin bakinsa da kyawun fuskarsa suka rude ta ta bude masa kafafuwanta yayi mata ciki. Abinda ta shuka ne itama take girba.