← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 112

Sashe 45

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da assuba na tashi kamar kullum, na cire hannayensa daga kaina na mike ina kallonsa yana ta sharar baccinsa, ban tashe shi ba tunda ni dai dama ban taba jinsa ya fita masallaci ba, na tafi dakina na shiga toilet na kunna wa kaina shower wai ko zata sanyaya min zuciya, inna wanke jiki na sai in sake wanke wa in sake wanke gani nake kamar duk Saghir dinne a mammanne a jikina, ji nake ina ma ace zan iya cire fatar jikina in sake wata wadda Saghir bai taba ba? Nayo wanka na na fito na saka doguwar riga ta hijab nayi sallah ina addu'a Allah ya kawo min karshen auren nan, sai kuma na chanja nace idan auren shine mafi alkhairi a gare ni Allah ya cire min Sadauki daga zuciyata ya shiryar da Saghir ya saka min sonsa a raina. Ko da banso shi ba at least in rage tsanarsa hakan zai dan rage min zafin da nake ji a zuciyata.

Ina nan kan sallayata har gari yayi haske rana ta fito, sai naji an bude kofar dakin da nake, na juya ina kallon Saghir daya dau wanka yasa gayunsa kamar kullum sai kamshi yake, ya tako har tsakiyar dakin da takalmin sa a kafarsa yace min "ki zo ki bani breakfast zan fita" na dauke kaina gefe saboda wani takaici da ganinsa ya saka min nace "ka kawo abin breakfast din ne?" Yace "ki duba dakina akwai kayan tea sai ki hada min tea, akwai kuma kwai a kitchen sai ki soya min" daga haka ya fita, na tashi nayi abinda yace na kawo masa palon sama yana zaune yana kallo, na zauna ina kallonsa har ya gama ya karkade jikinsa zai tashi nace "mu kuma fa? Me zamu ci" ya tsaya yana kallona yace "babu abinci a store?" Nace "ka ajiye ne?" Yace "bana son maganar banza in babu kawai kice min babu" nace "ai ka fini sanin babun" yace "ku sha tean mana to, kafin lokacin abincin rana ai zan dawo" yayi hanyar waje nace "in baka dawo ba nima zanyi Allah ya isa" sai kawai ya juyo ya kalleni yayi murmushi ya fita.

Bai dawo ba din kuwa. Haka na samu wata guntuwar shinkafa a store muka dafa fara dama uwani tayo guzurin yaji muka ci da mai da yaji. Bai dawo ba sai dare, daren ma sai bayan mun kwanta kuma nasan maybe yayi hakan ne dan kar inyi masa mitar bai ciyar dani ba. Da safe ina kasa muna gyaran gida sai gashi ya sauko, ya leka wajeya kira mai gadi sai naga sun hau sama tare ya bashi akwati ya sauko dashi kuma daga ganin akwatin nasan da kaya a ciki, akwatin cikin kayan lefe nane. Nabi mai gadin da kallo har ya fita sannan na hau saman muka hadu dashi yana kokarin saukowa nace "wancan kamar kayana naga an fita dasu, ko dai ido na ne?" Bai kalle ni ba yace "aro na dauka, zan siya miki wasu idan wadansu kudina da nake jira sun zo" nace "ko aron ne ai ana tambayar mutum kafin a dauki aron kayansa, kuma ni ban bayar da aron ba a dawo min da abi na" yace "ta yaya zamu zauna da kaya cikin akwati alhalin store din abincin mu babu komai? Ai ba kyauta nace ki bani ba aro ne kuma zan biya ki kin dai san ni ba talaka ba ne ba ko?" Kafin in bashi amsa ya fice. Na shiga dakina na tarar duk ya hargitsa min kaya, kusan duk kayan lefe na masu tsadar ya dauke. Bakin ciki ya kama ni kawai sai na zauna ina kuka, sai na tambayi kaina, wai yaushe ne zanyi farin ciki ni kam, yaushe ne zanyi murmushi, irin geniun smile din nan mai zuwa har zuci.

Ya siyo mana kayan abinci sosai, ya kuma bani 10k ya ce kudin cefane "saura kuma a karar dasu da wuri ace min babu" sauran kudin kuma bansan me yayi dasu ba.

Kwana biyu bayan nan, tunda rana naga yana tayi min fara'a sai nasha jinin jikina, da dare ina kwance a daki sai gashi ya bude kofa ya shigo nayi sauri na rufe idona dama fitila a kashe take, yace "Diyam, Diyam" nayi banza na rabu dashi. Sai ya hawo kan gado na sai nayi juyi na fara munsharin karya, irin wannan munsharin mai kamar kakin majina, sai yayi tsaki ya tashi ya fita. Na gyara kwanciya ta a raina nace "sai dai kaje ka rungumi pillow bani ba" and that got me thinking, this is his second attempt a kaina a cikin sati daya da dawowa ta, amma wancan karon wata na bakwai a gidan sa tun randa yayi raping dina bai kuma kallata da wannan maganar ba, menene ya chanza yanzu? Sai nayi realising cewa da yana da kudi yanzu bashi dasu, meaning da yana iya siya a waje yanzu ba zai iya siya ba, wato wannan shine dalilinsa na yarda da dawowa ta irin ga banza ta fadi dinnan ko? Ni kuma indai haka ne bazan yarda ba sai nasan yadda nayi na karbar wa kaina yanci. Sai kuma nayi mamakin kaina yadda nayi realizing Saghir yana neman mata amma ko a jikina wai an tsikari kakkausa, ko kadan banji raina ya baci ba alhalin ko a yanzu da nake matar wani in nayi imagining Sadauki da budurwa ba karamin baci raina yake yi ba ballantana inyi imagining dinsa yayi aure. I can only imagine yadda Sadauki yake ji a ransa a yanzu da make matar wani, har na haihu dawani. Ko ya yake ji? Ko ya yake coping?

Washegari ya tashi yana ta fushi, ni ko kallo bai ishe ni ba. Zai fita yace "zanyi baki anjima, abokaina ne manyan mutane ne sun takura wai sai sunzo sun ganki. Please don't embarrass me, kiyi musu abinci kuma kiyi shiga mai kyau kisa kayan da zasu kara miki girma". Bai jima da tafiya ba dai sai gashi ya dawo da kaji wai duk ayi musu. Mukayi abinci ni da uwani muka jera a dining, muka gyara gida tsaf yana ta kamshi na tafi sama nayi wanka na saka wata doguwar riga ta atamfa, dama ba kwalliya nake yi ba, na saka hijab nayi sallah ina zaune akan sallaya ya shigo yace "gasu sunzo, kuma please ki cire wannan dogon abin" ya juya ya koma, na tsaya ina tunanin menene dogon abin, doguwar rigar ko kuma hijab din?

Na tashi na gyara hijab dina na bishi, suna zaune a palon kasa kusan su biyar duk irin sa, yayan masu kudi masu ji da kansu. Na zauna a hannun kujera na gaishe su suka amsa, suna tsokana ta wai amaryar da ake boyewa, ina kallon Saghir yana ta harara ta nayi kamar ban ganshi ba sai cewa yayi "kin zo kin zauna kin saka mutane a gaba, ba zaki tashi ki kawo musu ruwa ba?" Na fahimci lallai so yake ya dizga ni a gaban abokan sa ya nuna musu ba sona yake yi ba, ni kuwa bai san yadda nake jin haushinsa yafi yadda yake jin nawa ba. Na mike sai cewa yayi "au ina miki magana ba zaki tsaya ki gama ji ba sai ki wani tashi ko?" Na dawo da baya na tsaya a gabansa nace "wanne daga ciki kake so Saghir? In tsaya kayi min fadan ne sai in kawo musu ruwan ko kuma in tafi in kawo musu ruwan sai kayi min fadan which one will you like first". Kusan gaba-daya suka kwashe da dariya. Ya kasa cewa komai ya tsaya yana kallona, sai na daga kafada nace "abinci yana kan dining, you can serve them in ka gama fadan" na juya nayi hayewata sama. Ni kaina nasan na gama da Saghir, amma kuma shi ya jawo wa kansa, me yasa zaiyi tunanin bara ya wulakanta ni a gaban abokan sa? Ko yana ganin hakan zai kara masa class ne a cikin su.

Ina nan zaune naji fitarsu a motoci sai kuma naji yana hawowa, nasan zuwa zaiyi mu yita amma sai naji bana jin tsoronsa, ya shigo har dakina ya karaso gabana ya tsaya, kawai sai jin saukar mari nayi a fuskata, saboda karfin marin har saida na daina gani for some seconds sannan ya sauke min a daya side din. Sai da naji taste din jini a bakina. Ya nuna ni da dan yatsa "ke har kin isa ki ce zaki gaya min magana a gaban abokaina, me kika dauki kanki ne? Wallahi ki bini a hankali Diyam in ba haka ba watarana sai na kai gawarki gida" Ya juya ya fita.

Na rike fuskata na zauna a bakin gado, bazan iya tuna sanda aka taba marina ba, to ni waye ma mai dukana in banda inna itama kuma mostly a kafa take dukana. Hawaye ya fara bin kuncina ina lissafa irin abinda zai faru da ace da ne wani yayi min wannan marin a gaban Sadauki. Nice kuka har magrib ina tayi, daga yin Sallah kuma sai zazzaɓi mai zafi ya rufe ni. Uwani ta hawo taji ni shiru sai ta tarar bana jin dadi sai ta zauna a waje na har saida Saghir ya dawo sannan ta sauka.
Chapter 45 · 0% Book details