← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 112

Sashe 73

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari tun da wuri na tashi na shirya inna ma ta shirya tace gwara muje tare, muka bar Asma'u a gida muka tafi bompai amma muna zuwa muka tarar Hajiya Babba ta riga mu zuwa ita da wani kaninta. Idanunta sun kumbura alamar tayi kuka harta gode wa Allah. Muna shiga ta taho gurina da sauri "Diyam sharri yake masa wallahi, wallahi sharri yake yi masa ina yaron nan zai kai wadannan uban kudade?" Inna ta rike ta tana lallashinta ni kuma na karasa gurin desk officer din da yake on duty. Ya miko min wata takarda wacce take dauke da case statement na case din Saghir, a jiki naga bayanin cewa ya yi transfer din kudi ne daga account din company zuwa private account dinsa. Amount din dana gani sai daya saka kaina ya sara naji kamar zan fadi, mai Saghir yake tunani ne wai? A jiki kuma naga cewa Saghir din ya karbi laifinsa tun a jiyan da aka kawo shi dan haka har an fara shirin tura shi court. Na ajiye takardar nace da officer din "can I see him please" ya kalle ni da mamaki yace "are you sure? He went through some questioning so an dan sassama shi kadan" ya karasa yana grinning. Na juya na kalli inda Hajiya har yanzu take zaune tana kuka Inna tana rarrashinta. Nace "zan ganshi, amma ni kadai" sai ya miko min wani form yace in cike. Na karba na tafi gurin su Hajiya nace musu "sun hana ganinsa, gwara ku tafi gida kawai. Ni zan zauna in cike wasu takardu yanzu zan biyo ku" kamar ba zasu tafi ba sai kanin Hajiya wanda dama tunda muka zo naga yana ta nuna alamar ya gaji yace "in mun zauna ma babu abinda zasuyi mana fa, zasu iya wulakanta mu gwara mu koma gida sai asan yadda za'a bullowa lamarin" sai naci sa'a suka bishi suka tafi ni kuma na koma ciki na cike form din da aka bani, aka kaini wani daki na zauna ina jira, shiru shiru tun ina kallon agogo gar na fara zama frustrated ina jin tamkar na shekara a dakin sai aka bude kofa aka shigo.

Saghir ne, amma kamar ba Saghir ba. Daga shi sai singlet da gajeren wando, fuskarsa babu inda bai kumbura ba dan idanuwansa da kyar suke budewa. Sai kawai naji zuciyata ta karye na rufe baki na kama kuka. Officer din daya shigo dashi yace "na gaya miki ai" sai ya zaunar da Saghir akan benchi ya juya ya fita. Na tsaya kawai muna kallon kallo. Sai can yace cikin wata irin murya "kinzo ne dan ki sakani a gaba kiyi ta kallo kina cewa Allah ya kara ko kuma kinzo ki karasa aikin da tsohon saurayinki ya fara?"

Na zauna ina facing dinsa nace "Saghir me yasa ka daukar masa kudi? Why? In zaka dauki kudin kowa a duniya me yasa zaka taba na Sadauki bayan kasan abinda yake tsakanin ku?" Yace "menene a tsakanin mu din? Ke? Dan ke akayi min wannan abin na sani kuma yayi da dan halak. Sai na rama duk ranar da na bar gurin nan sai na chanja masa kamanni kamar yadda yasa aka chanja min nawa" na girgiza kai cike da takaici, he is still being arrogant, nace "ni so nake in tabbatar, ka daukar masa kudi ko ba ka daukar masa ba? Ina so insan gaskiyar maganar nan saboda in san ta inda zan bullo mata" ya dauke kai yace "I don't need your help. Kiyi tafiyar ki kawai. Ki je ki gaya masa cewa tarkon daya kafa ya kama shaho" na girgiza kaina a raina nace 'he have no idea how much trouble yake ciki' sai na bashi labarin case dinsa da yan drugs. And that broke him down.

Hannu biyu yasa ya dafe kansa, ya jima a haka sannan ya dago yana kallona yace "wannan duk yana cikin irin kiyayyar da kike yi min Diyam? Me yasa baki fada min ba kika barni na dawo kasar? Me yasa kika barni na fada tarkon da makiyana suka kafa min" naji tausayinsa har cikin raina, nace "Saghir, ko daya ba naki gaya maka ne saboda bana sonka ba, naki gaya maka ne saboda nasan in na gaya maka ba zaka dawo ba and that means trouble for Alhaji, wanda babanka ne shi mahaifi dan haka dawowarka yafi maka alkhairi akan kin dawowarka" yace "really? To case din Sadauki fa? Shima kamanin da yayi yafi min alkhairi akan rashin kamani? Waye ya gaya masa zan dawo da har yasa aka tare ni a airport?" Nace "duk abinda zan gaya maka ba lallai ka yarda ba. Amma duk da haka zan gaya maka. Bani da idea akan abinda ya faru tsakanin ka da Sadauki. Na san dai yana buying time for something but bansan menene ba. Kuma ina so kasan cewa zanyi iya kacin kokari na na ganin ka fita daga gurin nan but for that ina bukatar ka gaya min gaskiya. Ka dauki kudin Sadauki ko baka dauka ba? Drugs din da aka samu a dakin ka da motar ka, naka ne ko ba naka ne ba?"

Ya jima shiru kamar ba zaiyi magana ba sannan kuma sai ya danyi murmushi yace "that former boyfriend of yours is smart, na bashi credit anan. Tunda yaron nan ya dauke ni aiki, ina jin ma ai na taba gaya miki, babu aikin da nake yi. Sai ya dauki wani a matsayin assistant dina to duk aikin da ya taso shi ake bawa yake yi and I tot 'huta roro' tunda dai ana bani salary na mai kyau ai bani da problem. Shekara da shekaru, ko banje gurin aiki ba bani da matsala, I should have known tun a lokacin that something is off but ni ta constant monthly income dina nake yi. And then lokacin da na koma aiki, suddenly it was all work for me. A lokacin ne nasan ma how much money ne a cikin account din Company and it was a huge money. Kullum kudi suna shigowa wadansu suna fita, kudi masu yawa. Shi yayi tafiyar sa, and duk takardar da aka kawo zaiyi signing sai a kawo min ace yace inyi a maimakon sa. Duk kudin da za'a fitar ni za'a saka in fitar dasu haka duk kudin da za'a shigar. It was like cewa ake yi Saghir dauki kudin nan. And I saw my chance. Mutumin nan yaci amana ta yayi making fool of me for years, dan haka dole ce ta saka ni na cigaba da aiki under him saboda babu inda zanje in samu din. Dan haka sai na dauka as a revenge for what he did to me kuma dan in kafa kaina nima in daina aiki under him. Nasan zai gani amma kuma nasan yana tsoron kar in bata masa image dinsa with that scandal so I expected him to keep quiet. Da kudin na sayi gidan dana gaya miki na kuma saya mana motoci ni da ke da Fauziyya and I gave some part of the money to Kabir da niyyar zamu hada share muyi business tare. Sauran kuma dasu nayi wannan tafiyar wadansu kuma suna account dina da niyyar su zasu rike mu kafin business din da zan fara ya kankama".

A gyada kai, my mind already thinking ta yadda za'a harhado kan wadannan kudade. Ya cigaba:

"Drugs kuma, wadanda aka samu a daki na, a kasan gadona, ba nawa bane ba. You know I don't do drugs. Na Kabir ne ya bani ajjiya saboda yana da iyali karsu taba masa ni kuma tunda zanyi tafiya shine yace in ajiye masa, a mota ta kuma alcohol zasu samu".

Na gyada kai nace "so, where is Kabir now?" Ya daga kafada yace "ta yaya zan sani tunda ina nan a rufe?" Nace "but ta yaya akayi suka kai mamaye gidan ka?" Yace "I have no idea. Ask that smart boyfriend of yours maybe shi yana da idea".

Na mike tsaye nace "thanks for telling me the truth. Zan je gidan Alhaji zamu zauna muga ta yadda za'a bullowa lamarin. Insha Allah, you are getting out of here. Zamuyi reporting cewa stuffs din Kabir ne ba naka ba." Na juya zan fita sai yace "why?" Na juyo ina kallonsa nace "why?" Yace "why are you trying to help me bayan duk abinda nayi miki? I tot ke celebrating zakiyi ma cewa you are finally getting rid of me" nace "kamar yadda Hajiya ta gaya min rannan. Kai dan'uwa na ne, mijina, kuma uban yata".

Daga bompai gidan Alhaji Babba na koma, a can na same su harda inna duk sunyi jigum jigum har aunty Fatima itama tazo. Na zauna na lissafa musu tas abinda ya faru. Saghir dai ya dauki kudi ba sharri ne akayi masa ba, ya kuma admitting to ajiye drugs a gidan sa amma yace ba nasa bane ba na Kabir abokin sa ne.

Nan take Alhaji Babba ya dauko waya ya kira Alhaji Murtala mahaifin Kabir yana tambayarsa in yasan inda Kabir din yake amma sai yace shima nemansa yake yi bai san inda yake ba, ya dauka ma tare suka fita da Saghir, da yake duk halin daya ne. Nan fa hankalin Alhaji ya sake tashi. In ba'a samu Kabir ba Saghir ne a ruwa.

Out of the confusion na fita waje na zauna a compound. Sai na dauko wayata nakira Fauziyya. Tunda na ganta a airport sanda aka kama Saghir ban kuma waiwatarta ba kuma babu wanda ya kuma kiranta. Bugu biyu ta dauka. "Halima ya ake ciki?" Naji haushin da bata kirani taji ya ake ciki ba sai yanzu? Amma sai nayi mata bayanin duk abinda na fahimta da kuma halin da ake ciki a yanzu. Sai ta tabbatar min da cewa tabbas taga sanda ya ajiye drugs din a day to tafiyarsu yace ajjiya aka bashi but bata san menene ba a lokacin kuma bata san waye ya bashi ajjiyar ba. Sai na ce mata ta shirya ta taho gidan Alhaji itama ayi komai da ita.
Chapter 73 · 0% Book details