← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 112

Sashe 19

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hutun da muka zo na third term din jss2, ina shiga palon Ummah hannuna rike da Asma'u da take ta murnar gani na, na tarar da akwati a ajjiye a kofar palo. Bayan na gaisheta nace "Inna wannan kayan fa?" Ta hade rai tace "naki ne, hutu zaki tafi" naji zuciyata ta buga nace "hutu Inna? Ban gama ganin ku ba fa ina zan tafi hutu kuma?" Ta harare ni tace "gidan Alhaji Babba zaki tafi, in muna son ganin ki mu zamu zo mu ganki" nayi ajjiyar zuciya a boye, dan dai sharada? Nasan Sadauki ko da adungure zai je ya ganni. Kwana na daya a gida na tafi sharada. Ni da Rumaisa ne zamu je muyi hutu a can yayin da Inna ta yi mana rakiya. Rumaisa tana ta murna saboda ita kam tana son zuwa gidan Alhaji Babba. Ni kuma ina yake saboda kar Inna ta harbo jirgina na plans din da mukayi da Sadauki.

Now, let's talk about Alhaji Babba da family dinsa.

Kamar yadda na fada Alhaji Babba shine babban yayan su Baffa, shi ya fara zuwa Kano neman kudi kuma a lokacin yafi dukkansu dukiya, dama baffan mu ne baya. Allah ya jarrabi Alhaji Babba da mugun son yaya maza sai kuma ya hana shi su, wannan yasa ya kasance mai aure aure duk a tunanin sa da burinsa hakan zai saka ya samu cikar muradinsa. Matarsa ta farko yar uwa ce daga Kollere, ya daya ta haifa masa Adda Zubaida, daga nan bata sake haihuwa ba sai ya auri Hajiya Babba wadda tashin farko ta haifa masa muradinsa na É—a namiji wanda muke kira da hamma Saghir. Hajiya Babba jinin sarautar kano ce, hamshakiyar macece mai mulki da izza wadda hatta kishiyoyinta inka gansu a gabanta zaka iya dauka cewa yaranta ne. Bayan shi ta sake haihuwar mata biyu, Aysha da Salma. Daga Hajiya Babba kuma sai Hajiya Yalwati wadda tafi duk sauran matan yawan yaya kuma wannan shine kadai abinda yake zaune da ita a gidan. Hajiya Yalwati kawar Inna ta ce dan haka duk sanda muka je gidan a dakinta muke zama, kuma nima saboda babbar kawata a gidan, Murja, yar Hajiya Yalwati ce dan haka nima na zama yar dakinta. That plus daga ni har Inna babu wanda yake iya jurar mulkin Hajiya Babba. Sauran vacant space din guda daya kuma na mai rabo ne, wannan ta shiga wannan ta fita.

Hamma Saghir shine da daya tilo da Allah ya bawa Alhaji Babba, dan haka zama bayyana cewa dan gata ne bata lokaci ne. An haife shi tun kafin Baffa na yasan zai auri Inna ballantana a haife ni, dan a lissafi ya bani shekaru goma sha shida da watanni. A kullum idan naji mata suna lissafa siffofin mijin da suke so su aura sai inga kamar lissafin kamannin hamma Saghir suke yi, fari, dogo, kyakykyawa, mai saje, marar son surutu, mai kudi, mai class blablabla. Hamma Saghir is all that and more. Labari ya zo min cewa makarantar da hamma Saghir yayi ma kanta daban take da ta sauran yaran gidan dan Alhaji Babba cewa yayi "a samo min makarantar da yayan masu kudi suke zuwa a garin nan, ita zan saka Saghiru" a haka yayi primary da secondary dinsa, sannan aka saka shi a buk yayi degree a economics ya fita da pass. Alhaji Babba yace "ba wani abu, dama an saka ka a makarantar ne saboda ka samu ilimin juya dukiya ba wai dan ka nemi aiki da takardun ka ba". Sai kuma Alhaji Babba yayi masa irin abinda Hardo yayi masa shima. Ya debi dukiya msi yawa ya bashi yace "tafi ka nemi arzikin ka" Saghir ya gyara zama yace "China zan tafi Alhaji, tunda can ne cibiyar kasuwanci ta duniya a yanzu. In naje sai in nemi Company in saka hannun jari a ciki. Maybe kafin shekara sai kaga nazo na bude nawa Companyn"

Haka ya shirya aljihu fal kudi ya tafi China, daga nan ba'a kara jin labarinsa ba har sai da ya shekara uku sannan sai gashi ya dawo daga shi sai jakar kayan sa yace "yan damfara na hadu dasu Alhaji, gaba daya kudina sun salwanta da kyar na tsira da kudin jirgi na dawo gida" Alhaji Babba yace "kasuwanci ya gaji haka dama, yau riba gobe faduwa hakan kuma ba zai saka mu karaya ba" sai ya debi wadandu kudaden ya kuma bashi, shi kuma ya karba yace "Dubai zan tafi wannan karon inke saro kaya ina aikowa dasu gurinku kuna siyar min". Wannan karon ma tunda ya tafi ba amo ba labari ko waya babu, amma sai iyayen suke boyewa kullum suna nuna kamar yanayi musu waya "abubuwa ne suka yi masa yawa amma yace yana gab da zuwa gida". Yazo gidan kuwa bayan shekara biyu, sai dai wannan karon ko akwatin kayansa bai dawo dashi ba ballantana kudi "Dubai bata karbe ni ba Alhaji. Kudi na gabaki daya sun salwanta ba bu abinda ya rage a hannu na" Alhaji Babba yace "kasuwanci bai karbe ka ba Saghiru. Dole sai mun zauna munyi maka adduoin neman sa'a sosai. Kuma ina kyautata zaton akwai nasara sosai a rayuwar ka shiyasa kake samun tangarda" Hajiya tace "musamman ma shi da yake da tarin makiya, gaskiya kam sai an hada da addu'a".

Bayan an gama rarraba wa malamai kudi sunyi adduoi, sai kuma Alhaji yace "gwara ka zauna a kasar nan saboda muke ganin abinda kake yi muna kuma baka shawara" amma sai Saghir yace "gaskiya Alhaji ko zan zauna a kasar nan to ba'a Kano ba, saboda anan an saka min ido dayawa". Haka rayuwa ta cigaba masa, yau yana wannan garin gobe yana wancan duk da sunan neman kudi, in kudin hannunsa sun kare ya dawo Kano ya karbi wadansu ya kara mai.

Tunda nake bazan iya cewa ga ranar da hamma Saghir yazo gidan mu ya gaishe da Baffa wanda yake kanin babansa ba ballantana Inna da take cousin din babansa kuma matar kanin babansa. Ni kaina ganin da nayi masa a duniya a lokacin bashi da yawa sai dai a jikin katon hoton sa dake kafe a main palon gidan.

A ranar da muka je gidan, kamar yadda muka saba, part din Hajiya yalwati muka fara zuwa muka ajiye kayayyakin mu muka huta sannan muka fita muka zagaya muka gaishe da sauran matan gidan. Bayan mun dawo palon Hajiya Yalwati ne Inna take tsokanar Murja "Murja ya na ganki a daki ne yau kamar matar kulle? Tunda muka zo gidan nan banga kin fita ko babban palo ba?" Hajiya Yalwati tace "uhmm ina zata fita taje, boss din su yana gidan? Tun safe nace musu suyi zamansu a daki kar wadda ta fita in ba haka ba sai kiga an dawo da kumburarriyar fuska ya kama su ya mara, komai akayi ai shi laifi ne a wajensa, magana ma mai karfi in sunyi cewa zaiyi sun hana shi bacci duk ya hada su yayi musu duka. Kuma ban isa inyi magana ba" Inna tace "wai Saghir kike nufi? Yazo garin kenan. Oh ni yaushe rabon da inga Saghir?" Kamar da hadin baki kuwa sai gashi ya shigo palon. Ya dafa kujera daga tsaye yace "Hajiya barka da gida" Hajiya Yalwati tayi yake tace "Barka kadai Saghir, anzo lafiya" yace shortly "lafiya lau" sai ya juya zai fita, Hajiya Yalwati tace "ga gwoggonka fa, gwoggo Aminan baffa Usman" ya dan juyo yana shafa kai yace "lah gwoggo ai ban lura ba. Ya gida? Ya Baffa?" Inna tayi murmushi tace "lafiya lau Saghir, ya kasuwa? Allah yayi jagora" yace "ameen" sannan ya fice ba tare daya ko kalli inda muke zaune ni da Rumaisa muna kokarin gaishe shi ba.

Yana fita Inna ta juya tana kallon Hajiya Yalwati tace "kai masha Allah. Saghir ya zama babban mutum sosai" Hajiya Yalwati ta tabe baki tace "eh fa. Yo mutumin da yake kokarin cika shekara talatin a duniya ai kuwa dole a kira shi da babba. Ni in dai gatan gaskiya kuke yi masa ma aure ya kamata kuyi masa maybe ko ya haifa muku jika namiji" Inna tayi dariya tana tafa hannu, Hajiya Yalwati tace"a'a to bai isa auren bane ba? Ko dai kuyi masa aure wallahi ko kuma ya dauko muku abin kunya dan duk abinda yake aikatawa a garuruwan da yake zuwa muna sane, in munyi magana kuma ace hassada muke yi masa" Inna ta watso mana harara ni da Rumaisa, sum sum muka tashi muka basu guri dan munsan ma'anar hararar.
Chapter 19 · 0% Book details