← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 112

Sashe 110

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba'a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, Nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?" Diyam ta gyada kai, yace "ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir ba kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za'a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money. Yau sai gashi ya dawo, can You believe ge got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa"

"Nayi submitting record din to Ahmad, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama kabir, and Saghir is coming out latest next week".

Not edited. Ayi hakuri da typos.❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventy Eight and Nine : Finale

Sai da Diyam ta gama da Sadauki sannan ta zauna ta kira Inna ta gaya mata labarin zancen fitowar Saghir. Inna tayi murna sosai tace "Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah yasa karshen wahalar sa kenan shi kuma Sadauki Allah ya saka masa da alkhairi" Diyam tace "ameen Inna" tace "bari in kira gidan Alhaji Babba inyi masu albishir". A ranar zance ya zagaya family, zuwa washegari yab uwa suka fara kiran Diyam suna confirming "da gaske Saghir zai fito?".

Ranar da aka kama Kabir kuwa Hajiya Babba har gidan Diyam ta zo tayi mata godiya ita da sister dinta, hawaye fal idonta, tana ta bata hakuri dan gane da rashin kyautawar da suka yi mata a baya. Diyam ta cika su da abin arziki kuma ta nuna musu babu komai ai yiwa kai ne. Sun so ganin Sadauki suyi masa godiya amma yaki fitowa yace ace musu babu komai.

Ranar da Saghir zai fito, Friday kenan, a ranar Sadauki yace da Diyam ta shirya tare zasu je. Daga gidan su gidan Inna suka fara zuwa suka dauki Subay'a sannan sannan suka tafi prison din. Suka yi packing a tsallake, Sadauki yace musu su zauna a mota ya shiga shi kadai. Bayan ya tafi Subay'a tace "Mommy nan prison ce ai" Diyam tace "eh" "inda Daddy na yake" "eh" "to Mommy mu shiga mana muhe mu ganshi" "a'a ba shiga zamuyi ba Subay'a" "to Mommy mai uncle ya shiga zaiyi a ciki?" Sai kuma ta bude ido ta ja numfashi tace "zuwa yayi ya fito dashi, dama ya gaya min zai fito dashi, Mommy ki bude min kofa inje gurin su" Diyam ta rike hannunta, sai kuma tayi murmushi tace "Subay'a uncle zuwa yayi ya fito da Daddy, amma kiyi zamanki a mota tunda uncle bai ce ki fito ba, yanzu zaki gansu sun fito tare". Subay'a ta hakura bata fita daga mota ba amma kuma bata zauna ba, in ta leka ta waccan window din sai ta dawo ta leka ta wannan, in kuma taga motsi a bakin kofar gurin sai ta fara tsalle sai taga basu bane ba. Daga baya data gaji sai ta kwanta a backseat tana kuka wai sunki fitowa.

At last sai gasu sun fito. Sadauki ne fara fitowa tare da wadansu mutum biyu wadanda Diyam ta gane a matsayin lawyers dinsa. Sai kuma Saghir ya fito tare da wani wanda ya tsaya yana ta yi masa bayanai har su Sadauki suka karaso mota. Mutanen suka yi masa sallama suka tafi sannan wancan ma yayi wa Saghir sallama ya tafi.

Diyam ta zauna tana kallon shi ta cikin motar. Yayi baki sosai, ya kuma rame sosai, amma wannan kyawun yana nan sai dai babu gayun, kuma shekaru sun fito sosai a fuskarsa harda strings of furfura a gashin sa. Ta gane kayan jikinsa, sune kayan da yake sanye dasu ranar da aka kamashi a airport, she can remember yadda ya fito daga arrivals cikin yana taku dai dai yana jin duniya duk a tafin kafarsa ga kyakykyawar Fauziyya a gefensa but yanzu da ta kalle shi bata ga komai daga cikin characters din wancan Saghir din ba. He looked calm and very different.

Sadauki ne yayi knocking a tagar da Subay'a take, ta dago tana kallonsa sai yace "Subis ga Daddy nan" ta mike da sauri ta kalli kofar prison din, tana hangoshi sai ta kama kokawa da handle din motar sai Diyam ta bude mata central lock tana dariya. Ai kuwa nan take ta bude ta fice daga motar a guje, Diyam ma ta bude ta fito tana cewa "careful Subay'a akwai titi fa". Daga tsallake Saghir ya hango fitowar ta, ya kuma lura da yadda tayo kan titi da gudu dan haka sai shima ya taho da sauri gurin ta zuciyarsa tana bugawa. A tsakiyar titi suka hadu, ya daga ta sama amma sai ya kasa juyi da ita ya sauke ta yana haki yace "kinyi girma Subay'a, Daddy kuma bashi da karfi" sai ta rungume ƙafafuwan sa tana murmushi.

Ya kamo hannunta suka karasa tsallako titin zuwa inda su Diyam suke a tsaye. Unintentionally hannun Diyam ya sauka akan cikinta tana kallon Saghir, sai taga ya kalli cikin sai kuma tayi sauri ta dauke hannun tana sunkuyar da kanta. Yayi murmushin takaici Yace "amarya" sai ta gaishe shi ya amsa yace "a sake min godiya gurin Mr Abatcha. Na goge sosai Allah ya bar zumunci" ta gyada kai a hankali tace ameen tana kallon Sadauki wanda yake ta danne danne a waya kamar baya jin me suke cewa. Sai ta kalli Saghir tace "congratulations. Allah ya kiyaye gaba" daga haka ta bude mota ta koma ciki. Sadauki ya dago kansa yana kallon Saghir ya nuna masa mota yace "Bismillah, sai mu ajiye ka a gida ko?" Sai Saghir ya kalli Diyam, ya hadiye wani daci a ransa ya girgiza kai yace "no, thank you. Kar in takura muku maybe akwai inda zaku je. Bara in hau napep kawai" Sadauki ya daga kafada kawai, sai ya tare masa napep din ya kuma biya kudi sannan ya yi wa mai adaidaitan kwatancen sabon gidan Alhaji Babba, tunda Saghir din bai sani ba.

Saghir yace da Subay'a "zaki bini gidan Alhaji?" Ga mamakin su sai ta kalli su Diyam ta kuma kallonsa sannan ta girgiza kai tace "no, Aunty Asma'u tace yau Uncle Bassam zai zo, kuma na bashi sakon abubuwan da zai taho min dasu in zai zo, ka ga kar yazo bai same ni ba" Sadauki ya bude ido yace "Subis akwai zarar magana sai kace wata babba" Saghir yayi murmushi yana kallon inda Diyam take yace "gado tayi ai". Har adaidaitan zai ja sai Subay'a tace "Daddy zan kawo maka ziyara gidan ka".

In silence suka bar gurin kowa yana lissafe lissafe a zuciyarsa. Sai can sannan Sadauki yace "ba zan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata. Bana son drama, nafi sonsa a nesa damu" bata ce komai ba, ya cigaba "amma zanyi masa komari ya samu kudin sa na gurin Kabir" Diyam tayi sauri ta kalle shi tace "kudin ka dai, ai kudinka ne" ya girgiza kai yace "nayi signing takarda cewa na bar masa kudina daya dauka, so legally yanzu kudin sa ne ba nawa ba. I have already talk to my lawyers, za'a siyar da kadarorin Kabir maybe za'a samu part of kudin amma nasan ba za'a samu gaba daya ba" Diyam taji dadi sosai a ranta tana yabawa kyawun zuciyar Sadauki, kamar yadda ya taba fada mata shi fire ne da ice, duk da wadda kazo dashi za'a tarye ka.

Tayi masa godiya sosai sannan yace "kin san wani abu? Ni da Saghir are alot alike" ta bude ido dan ita bata ga hadin su ba bayan kasancewar su musulmai kuma half fulani tace "ta yaya?" Yace "kinga ni da shi duk only sons ne a gurin iyayen mu. Kuma iyayen mu suna son mu sosai sannan sun nuna mana soyayya in their own different ways. Duk kanin mu iyayen mu sun bamu kudi, the only difference is yadda muka yi da kudin da suka bamu. Sannan kuma duk muna sonki" ya fada yana kallon ta, tayi saurin girgiza kanta tace "he doesn't" yace "he does. I saw it in his eyes yanzu da yana kallon ki"

Tayi saurin kawar da maganar ta hanyar cewa "kuma duk ku biyun kuna da kanwa mai suna Murja" yayi dariya yace "ni kanwa ta Murjanatu sunan ta ba Murja ba, kuma ni nafi shi son kanwa ta" tace "ita kuma duk duniya gani take yi kafi kowa kinta" and they laughed together.

*************************
Chapter 110 · 0% Book details