Sashe 32
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na gyara mata kwanciyar ta a jikina naja bargo na lullube mu tare, sai kuma na fara bitar abubuwan da suka wakana, na hango fuskar Sadauki a idona da irin bacin ran dana gani a idonsa, na tuno kalaman daya gayamin a kunnena. "Be strong" he said, but how can I be strong without him bayan shi din shine strength dina? Yace in bude hannayena in karbi duk wani abin da ya tunkaro ni but how can I do that bayan ya sabar min da kasance wa shield dina? Shi yake tsayawa a gabana ya kare ni daga duk wanda yayi niyyar zalintata, shi ya shagwaba ni inyi duk abinda nake so saboda ina takama ina da Sadauki. Yanzu banj da Sadauki kuma. I felt so exposed. So alone. So scared. Ji naui kamar duk mutanen duniya ne suka hada kansu suke nema su zalince ni. Suddenly sai naji duk duniyar ta ishe ni, to menene amfanin zama a cikinta? Me zan tsinta a cikin rayuwar indai har aka aura min wanda bana so aka ce in cigaba da zama dashi har karshen rayuwata? Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke kashe kansu saboda auren dole suka ji kafin su kashe kan nasu. Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke guduwa daga gaban iyayensu suke shiga duniya suke ji kafin su gudu din, ashe dai laifin su kadan ne, ashe dai tura su akayi zuwa limit din da shaidan ya kada musu gansar sa su kuma suka bishi.
Sai dare sannan na tashi na hada sallar magrib da isha saboda wani irin zazzaɓi da ciwon kai da nake yi. Ƙwaƙwalwa ta ta zama blank kamar babu komai a cikinta saboda na rasa wanne tunanin zanyi. Ni dai bana so in shiga duniya saboda I might end up never seeing Sadauki again tunda bansan inda zan same shi ba. Ba kuma naso in kashe kaina saboda nasan wuta zan tafi. Bani kuma da wanda zan kai kara gurinsa saboda su masu shirin yi min auren nan su ne dangin uwata kuma sune dangin ubana, dan Alhaji Babba a lokacin zan iya cewa shi yake juya kowa a family, saboda shi yake da naira. Sai na dora goshina a kasa na fara gayawa Allah, ina rokon sa ya sakamin ga duk wanda ya zalince ni, ina rokonsa kuma ya bani karfi da juriyar daukan duk wata kaddara daya rubuta min.
A kan sallayar na kwanta na lulluba da hijab dina, ina jin Inna ta shigo ta taba wuya na sai kuma ta fita, sai gasu sun dawo da Hajiya Yalwati da Murja, ina jin su suka kamani suka saka ni a mota sannan naji muna tafiya, na dago kai na kalli Hajiya yalwati data rungume ni a cinyar ta nace "Hajiya, dan Allah bana son auren hamma Saghir". A asibitin muna zuwa suka bamu gado, sunce temperature ta tayi sama da yawa dan haka sai na kwana a gurinsu for monitoring, suka yi min allurai ciki har dana bacci dan haka na samu nayi bacci amma cike da mafarkai. Cikin mafarkan da nayi harda wanda na ganni na soka wa hamma Saghir wuka a ciki.
Washegari aka sallamo ni tare da warning cewa jini na yana neman hawa, as young as I was. Muna dawowa gida Hajiya Yalwati ta zauna tana jera wa Inna bayanin likita Inna ta fara sharar hawaye tana cewa "ni in kuna wannan maganar sai inga kamar kuna dora min laifi ne, ni ya kuke so inyi ne wai? Ta yaya kuke tunanin zan je gurin Alhaji Babba in ce masa ba zai aurawa Saghir Diyam ba? Ta yaya? Ga Hafsa ma tayi fushi dani tunda ta tafi jiya har yau taki daukan wayata" Hajiya Yalwati tace "kamar yadda shi da matarsa suka so kansu suke neman hada Diyam da tantirin dansu kema haka zaki so taki yar kice ba za'ayi ba" Inna tace "yanzu zumunci har ya kai haka lalacewa? To ku ku gaya masa mana? Ku gaya masa Diyam tace bata so gashi har tana neman salwanta saboda haka" Hajiya Yalwati ta rike baki tace "ni asu wa? Ina magana cewa za'ayi kishi nake da bakin ciki".
Da rana sai ga abinci kala kala wai inji Hajiya Babba, ko kallon inda suke banyi ba. Ana jimawa sai gata tazo, tunda muka zo gidan ban taba ganinta a dakin ba sai yau. Ta zauna a bakin gado suna gaisawa da Inna sannan ta data jikina tace min "sannu Diyam" kai kawai na gyada mata, tace da Inna "ba zai wuce malaria ba fa, ita ake ta fama yanzu" Inna ta kauda kai tace "likita yace jininta ne yake neman hawa, hawan jini ne yake kokarin kamata" Hajiya Babba ta bude baki tace "hawan jini kuma? Wa likitan ya gayawa?" Inna ta ce "Hajiya Yalwati, ita ta kaita asibitin ai" Hajiya Babba tayi murmushi tace "hmmm, neman magana ne kawai irin na Hajiya Yalwati. Babu wani hawan jini ni na sani" sai kuma ta kauda maganar "kinga fita ma zanyi nace bara inzo in duba ta. Kinsan dazu da safe Alhaji ya siyasa Saghir gidan da zasu zauna, shine yanzu zanje in ga gidan sannan inyi lissafin duk kayayyakin da za'a siya. Wannan abu ai tuwona mai na ne. Kar kiji komai duk abinda ake yiwa yarinya na gata to za'a yiwa Diyam a dakinta. Ni da kaina zan siyo komai tun daga kayan daki har kitchen".
Tana fita Inna ta bita da harara tana magana kasa kasa. Sai kuma ta dauki waya ta kira zuwa can aka dauka ta fara magana "haba Hafsa, wai dame kike so inji ne, da mutuwar mijina ko da auren dolen da za'ayiwa Diyam ko kuma da fushin da kike yi dani? Yanzu Hajiya Babba take gaya min wai an bata kudi zata siyo wa Diyam kayan daki, saboda Allah bake da Fatima ya kamata kuyi wa Diyam siyayya ba? Wannan ai ba hurumin ta bane ba. Gaskiya kizo kije gurin Alhaji sai ki nuna masa kamar baki san maganar ba ki tambayeshi ya bayar da kudin kayan dakin Diyam zaki je ki siyo mata" sun jima suna ta mayar da magana sannan suka yi sallama.
Mama bata zo gidan ba sai washegari, shima tana zuwa tace "ni fa ba wannan maganar ce ta kawo ni ba, zuwa nayi in duba jikin Diyam. Su je suyi ta siya mata koma menene ba damuwa ta bace wannan. Ni damuwa ta shine in dauko yaron nan kafa da kafa in kawo shi har gidan nan amma a wulakanta su har dake a ciki, ni da ban shi nake yi ba dan Diyam nake yi. Kuma wallahi yadda naji takaicin abinda kukayi wa yaron nan ko wallahi da niyya nayi in bashi auren Rumaisa, dan dai kawai yace min a'a ne wallahi da sai dai kawai ki gansu tare da Rumaisa sai kuma inga yadda zaki yi da shi. Suma kuma yan uwansa suka ce a'a ba yanzu zasuyi masa aure ba wannan ma dan rana daya ya tayar da hankalinsa suma kuma ya tayar musu shi yasa suka taho nema masa". Haka ta gama fadanta ta tafi babu wanda ta gaisar a gidan.
Washegari na dan samu sauki babu laifi. Amma zuciyata babu sauki a tare da ita sai ma kara zafi da takeyi kamar ana hura min wuta a cikinta. Inna ta matsamin dole nayi wanka wanda rabona dashi tun ranar da Sadauki yazo gidan. Na fito daga toilet na tsaya a gaban mudubi ina kallon kaina. I can't believe how many things ne sukayi changing a rayuwata in just few weeks? Har yanzu fa ba'ayi arba'in din baffa da Ummah ba amma wai har mutane sun manta dasu, har an shafe babinsu an bude sabon babi na yiwa yarsa aure a shekara goma sha huÉ—u. Nayi wa yarsa auren da aka san inda ace yana da rai babu wanda ya isa ya ko tunkare shi da maganar danshi ba damuwa yayi da kudin mutum ba ballantana mutum yace ya daina bashi.
Ina cikin saka kaya ne naji hayaniya a palo har da guÉ—a, sai kuma gasu Murja nan sun shigo inda nake suna ta murna da dariya. "Amaryar Hamma" Salma autar Hajiya Babba wadda ba'a jima da bikinta ba ta fada. Sai kuma suka kwashe da dariya. Kusan duk yayan Alhaji Babba wadanda suke aure dama yammata da suke gidan duk suna nan. Na dauke kaina ba tare dana kula su ba na zauna ina daura dankwali na, "munga kaya masha Allah, kaya sunyi kyau, ko dan gidan gwamna ne iya kacin kayan lefen da za'a kawo kenan" naji wani suka a kirjina "lefe? Nawa?" Sai na kwanta a kan gado na rufe idona. Ina jin murja tace "ku bata so fa, kar ku saka ta kuka" Suwaiba tace "bata son wa? Hamman? Anya kuwa akwai macen da zata ce bata son hamma komai kyanta? Kunya ce dai kawai take ji amma babu ma zancen wai bata sonsa" Aysha tace "ni kam zan so inga yayanku, wow, Diyam kyau hamma kyau, in ina da ciki zanke zuwa gidan ku dan in haifi yaya kyawawa nima" na juya baya na jawo hijab dina na rufe fuskata a raina ina cewa 'ya'ya kuma? Ni da Saghir? Tabbas nasan me akeyi ake samun yayan but I will die first kafin in barshi ya taba ni. For I thought I belong to one, and one alone. Sadauki. Sai kawai tunanin matan da suke kashe mazajensu cikin dare yazo min and it didn't look so bad.
Adda Zubaida ce ta shigo ta kore su gaba-daya. "Manya manya daku kunzo kun saka yar karamar yarinya a gaba kuna tsokanar ta" Salma tace "yar karama ce amma ta kusa shiga layin manya" suka fice suna dariya. Adda Zubaida ta zauna a kusa dani ta dafa ni taji ina sheshshekar kuka tace "kiyi hakuri Diyam kinji? Kiyi fatan wannan hadin ya zamo miki alkhairi. Duk sanda kike bukatar wani abu ko wata shawara ki neme ni kinji? Karki dauka cewa ni yayar Saghir ce ki dauka cewa ni yayarki ce kinji" na gyada mata kai.