Sashe 25
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi in gaya muku, daga zuwanta da yaron nan ya dauki son duniya ya dora akansa, komai Sadauki komai Sadauki, ni na dauka ko rashin haihuwa ne ya saka haka amma sai gashi bayan na haifa masa yaya har biyu amma sadaukin nan dai ya fiye masa duk su biyun. To in ba asiri ko maita ba me zai jawo haka? A ce agolan da aka haifa a wani gidan koma a wani titin ne oho, tunda babu wanda yasan ubansa amma ace yafi yayanda mutum ya haifa da cikin sa? Ai shari'a tsakani na da zainabu sai a lahira za'a karasa ta. Tun yaron nan yana dan mitsitsinsa aka fara bashi mota a gidan nan, kullum 'sadauki zo ka kaini guri kaza, Sadauki zo muje guri kaza' nayi magana amma a banza tunda dama ni ba jin magana ta yake yi ba. Shine ranar nan yace "Sadauki zoka kaini Taura mu dauko Diyam' to gashi nan bai kaishi taura ba ya kaishi lahira" naji kaina ya sara, ina so in tashi in gaya mata cewa ba Sadauki ne yake driving a ranar ba amma nasan ba yarda zata yi kuma zata tambayeni wa ya gaya min.
Wata ta tambayeta "to ina yaron yake yanzu?" Tace "yana asibiti yana karbar magani, kinsan irinsu bada wuri suke mutuwa ba" sai na tashi tsam na wuce su na shiga daki. I can't take sunan sadauki da sunan mutuwa a sentence daya, not now da nake ganin ya samu sauki sosai. Not now da nake ganin nafi bukatar safiye da koyaushe.
Washegari akayi sadakar bakwai. Jama'a sun taru sosai bangaren Baffa da na Ummah, ga kuma makota da abokan arziki. Yaya ladi ma da sassafe tazo ta bude dakin Ummah inda mutanen su suka zauna. Ana gama yin adduoi aka yi sadaka sai kuma kowa ya fara watsewa, har yan Kollere ma duk sun gama shirin su ana gama wa suka yi sallama suka dauki hanya. Muma kuma sai Inna ta fara hada mana kaya amma ni sai na koma na zauna a tsakar gida na takure a guri daya ina sheshshekar kuka. Yanzu shikenan barin gidan mu zamuyi? Gidan da aka haife mu muka tashi a ciki, me yada zamu barshi mu koma gidan wasu mu zauna a karo? Bayan muna da rufin asirin mu. Ina kallo aka fara fita da kayan mu ana zubawa a motar da Alhaji Babba ya aiko da ita.
A lokacin ne kuma ya shigo. Kansa still a nade da bandage hannunsa kuma sanye da carnula. Ya tsaya yana rike da kofa for support idanuwansa a kaina, na mike nima ina kallonsa ina hango tsantsar tashin hankali a idonsa. Ko ba'a gaya min ba nasan ya sani. "Ina Ummah?" Ya tambaye ni da wata irin murya, sai na fara sheshshekar kuka na kasa ce masa komai. A lokacin ne Inna ta fito da wani akwati a hannunta ta ajiye tana kallonsa tace "sun sallamo ka kenan, dama yanzu nake tunanin yadda za'ayi a fitar maka da kayanka zamu rufe gida" ya kalleta kawai sannan ya sake mayar da dubansa kaina yana kallon yadda nake kuka babu sauti, hawaye wani na korar wani. Sai ga yaya ladi ta shigo afujajan, tana ganin shi ta sauke ajjiyar zuciya "yanzu shine ka fito daga asibitin ka taho nan Aliyu?" Kallo daya yayi mata sai ta saka kuka itama.
Na tafi a hankali har inda yake tsaye na rike hannayensa a nawa, sai kuma na dora kaina a kirjinsa a hankali nace "Sadauki Ummah ta tafi ta barmu, Baffa ma ya tafi ya barmu, sun mutu Sadauki ba zamu sake ganin su ba. Mu dasu sai dai muyi musu addu'a kuma sai kuma a lahira in munje muma"
Baice min komai ba bai kuma yi magana ba amma ina jiyo yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata bar jikinsa, ya saka hannu ya ture ni daga jikinsa ya fara tafiya kamar zai tafi dakin Ummah sai kuma ya juyo, yayi kamar zai fadi na tafi zan rike shi sai ya dakatar dani da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kirjinsa dashi. Ya dan jima a haka sannan ya sake straightening ya doshi hanyar waje, da sauri ni da yaya ladi muka rufa masa baya muna kiransa amma sai Ummah ta damko rigata a dawo dani baya "in kika bar gidan nan sai na kakkarya ki" ta harari waje "muma duk marayun ne, mun rasa iyayen mu kuma mun hakura".
Sai daga baya na fahimci ashe wasu kawayen Ummah ne suka je duba shi a asibiti shine suka yi masa gaisuwa, basu san cewa bai sani ba, shine ya gudo daga asibitin ya taho gida dan ya tabbatar. Ni dai a bangare na zan iya cewa tunda akayi rasuwar nan banyi kuka mai yawa irin na ranar nan ba dan a tsakar gida na zauna nayi tayin abu na, ina kukan tausayin kaina ina kuma kukan tausayin Sadauki. Menene makomar mu ? Menene makomar soyayyar mu? Babu wanda ya kula ni sai Asma'u da take makale dani tana taya ni kukan itama.
Can naji Inna tana cewa "su kenan kayan sun kare, in muna bukatar wani abu ko Diyam sai tazo ta daukar mana tunda babu nisa" Mama tazo ta tashe mu ni da Asma'u "ku daina kuka kunji? Ai ba barin gidan kuka yi ba gaba-daya zaku dawo in innar ku ta gama takaba" na gyada mata kai kawai. Muna ji muna kallo aka tisa keyar mu zuwa waje aka rufe gidan, a raina ina tunanin kayan Sadauki fa? Kayan Ummah fa? Ai bamu kadai muke da gidan ba tunda dai a tunani na Ummah tana da gado dan haka Sadauki ma yana da gado kenan.
Ina shiga mota kamar ance in kalli side sai na hangoshi a tsaye a jikin bishiyar da take opposite gidan mu, hannayensa a rungume a kirjinsa, idanunsa a cikin nawa. Nayi kamar zan fita sai Inna ta tura ni ciki ta shigo ta rufe kofa. Driver kuma ya tayar da mota muka tafi. Na juya waiwaya baya ina hangoshi ya matso tsakiyar layin mu yana kallon motar mu har muka sha kwana na daina ganinsa. Na juyo idona ya sauka akan dashboard din motar, agogo na kalla,time 3:15 date 25th August and it occurred to me cewa yau ne ranar Birthday dinsa, a yau ya cika shekaru ashirin cif a duniya. So young and so alone. Sai na rufe fuskata da hannayena ina sake wani sabon kukan.[1/22, 11:13 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: â? DIYAM â?
By
Maman Maama
Episode Twenty Three : Shared Strength
Assalamu alaikum wa rahmatullah
Ina neman afuwar wadanda littafin Diyam ya saka kuka a kwana biyun nan, ina rubutu ne dan in faranta muku badan in bakanta muku ba. Amma ina so ku sani ita rayuwa is full of ups and downs dole sai ansha wuya sannan za'a sha dadi. Ina so duk sanda kuke karatu ku saka a ranku cewa kirkirarren labari ne, non of this happened in real life duk da cewa zai iya faruwan. But labarin Diyam kirkirarren labari ne.
Daki ne aka bamu a gidan Alhaji Babba, dakin a babban palon gidan yake. Ciki daya ne da banÉ—aki mai dauke da gado da wardrobe a ciki, asalin dakin an yi shine saboda baki in sunzo daga Kollere anan suke dauka amma sauran matan gidan kowa in tayi baki to part dinta suke tafiya. Muna zuwa matan gidan duk suka firfito harda Hajiya Babba da kanta, aka zauna a palo ana ta kara yiwa juna gaisuwa da kuma jajanta abinda ya faru sannan aka saka yan aiki suka kara gyara mana dakin aka kai mana kayan mu can sai kuma kowa ya watse ya bar mu mu kadai.
Nina fara tashi na shiga dakin da aka bamu ina kare masa kallo, babu laifi yana da girma kuma da toilet a ciki amma kuma it doesn't change the fact that aro aka bamu, aron kuma da nia ganina bama bukata. Na tuna yawan dakunan da suke gidan mu, Inna daki biyu da palo, Ummah daki biyu da palo sannan ga dakin Baffa ciki da palo ga kuma dakin waje, amma wai duk mun ajiye su mun dawo daki daya mun zauna da sunan taimako, taimakon me? In taimaka mana za'ayi ni a ganina ai food stuff ya kamata ake kai mana can gidan mu kamar monthly haka ko duk sanda aka samu dama, ko ake bamu kudi muna siyan abin bukatun mu da kan mu amma ba gurin zama muke bukata ba. Kuma ko kudin ne ma ni aganina zamu iya kula da kan mu ba sai mun dogara da kowa na. Yes, Baffa ya mutu amma bai bar mu fakirai ba, ya bar garejin sa da yake running for over twenty years, zamu iya cigaba da running kayan mu da kan mu, Sadauki can do that tunda yasan komai dashi ake komai kuma duk costomers din Baffa sun san shi.
Ni a ganina da mun yi zaman mu a gidan mu mun dora Sadauki akan komai kuma nasam as hard working and dedicated as he is zai iya yin komai. Ya cigaba da zamansa a gidan for security tunda za'a ce ba zamu zauna mu kadai babu namiji ba, in ma kuma Inna bata son zamansa a cikin gidan tana ganin ba muharramin mu bane ba zai iya zama a dakin waje ai, kuma yadda yake da kwarjini din nan babu wanda zai kawo mana raini a unguwa. Sadauki yana da gado a gidan da garejin, so it will be a mutual relationship wanda ni nake ganin mu zamu fi benefitting akan sadauki.
Ina ta tunanina har Inna ta shigo tana ta jera mana kayan mu a wardrobe din dakin, Asma'u tana tayata tana kuma mitar cewa wardrobe din tayi mana kadan sai dai mu bar wasu kayan a cikin akwati. Bayan sun gama na tashi na sake goggoge dakin na wanke toilet na jera mana toiletries dinmu da kuma kayan shafe shafen mu, sannan nayo wanka da alwala nazo nayi sallah tare da jera adduoin neman nasara akan Inna in samu ta saurare ni ta kuma yadda da shawara ta.