← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 112

Sashe 43

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina zama na kwantar da kaina na lumshe idanuwana ina tunanin ta inda zan fara neman Sadauki, I just want to see him koda bance masa komai ba. Naji ya tayar da motar, sai naji Inna tace "Yakasai zaka kai mu" nayi saurin bude ido na ina kallonta, a raina nace 'finally' Finally Inna ta yi breaking out of her shell zata yi flying, to kawai yace mata ya dauki hanyar gidan mu. Naji mun tsaya na kuma bude idona sai naga traffic light ce ta tsayar damu a gefen asibitin, na dan sauke glass din windown da nake saboda in sha iska tunda babu ac, kamar daga sama naji kamar an ambaci sunana da muryar da ba zan taba mantawa ba, nayi saurin dago kai amma sai naga su inna kamar basu ji kiran ba, and then I smelled him, wani unique smell wanda daga gurinsa kawai nake jin sa, nayi saurin kallon window na and there he was, Sadauki, yana tsaye da hannayensa cikin aljihunsa yana kallona da budaddun idanunsa. Yayi loosing weight sai naga kamar ya kara tsaho, fuskarsa da kansa suna bukatar aski. Na zauna kawai ina kallonsa as the time froze and my heart stopped. He just stood there looking at me, sai kuma na kwalla masa kira "Sadauki!!" Inna ta juyo a tsorace ta riko ni tana tambayata lafiya, na juyo na kalleta sannan na juya da niyyar nuna mata sadaukin dana gani but ge was gone, as if yayi vanishing.

Kuka nake iyakacin karfina ina kiran sunan Sadauki yayinda Inna ta rike ni take tofa min addu'a, Saghir kuma yana bala'i duk da bana jin abinda yake cewa nasan akan kiran sunan Sadauki da nake yi ne ni kuma ban daina ba.

Manage this please
[2/6, 10:06 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Six: Mother's Tears

Har muka je gida ina kuka na, though na daina yi da karfi sai ajjiyar zuciya nake yi. Ina jin Saghir yana cewa "wannan Sadauki dama naji ance dangin mayu ne, tunda kin kwallafa shi a ranki ba dole yake yi miki gizo ba? In kuma da gaske shi din kika gani Allah ya bashi sa'ar yi miki magana in nuna masa shi karamin dan iska ne" daga ni har inna ba wanda ya kula shi wanda hakan ya bani mamaki dan nasan inna bata wuce tayi in dai akan zagin Sadauki ne. A raina nace "kaji Saghir din nan da son a sani gaida uwar saurayi a kasuwa".

A kofar gidan mu yayi packing muka fito, na tsaya ina kallon gidan da yake holding so much memories, good memories, Inna ta dauko key a jakarta ta bude gidan ni kuma na dauko mana jakar mu zan wuce ciki naji Saghir yana cewa "anan zan barku ne naga kuna daukan kaya?" Ban kula shi ba sai Inna tace "eh" daga haka itama bata kara komai ba muka shiga cikin gidan.

Na tsaya a tsakar gida na jingina da bishiya ina karewa gidan kallo, ko ina yayi datti dukun dukun. Inna ta bude dakin ta ta shiga sai ta dauko key din dakin baffa shima tazo ta bude. Cikin dakunan basu yi datti sosai ba. Na zauna akan kujera ina tambayarta "Inna anan zamu zauna ko? Ba zamu koma gidan Alhaji Babba ba ko?" Eh kawai tace min sai ta dauki kayan shara ta tafi ta fara share dakin baffa. Na taso na biyo ta zan taya ta tace "ke da baki da lfy kiyi zamanki kawai" amma sai naki, tana share yana ni kuma ina karkade kurar kan furnitures, a haka muka gama gara cikin daki da palon sa, muka wanke toilet dinsa na palo sannan sai gasu Mama sunzo ita da yammatan ta da yake ranar weekend ne babu school, su suka karasa aikin tsakar gida da kitchen da garage. Dakunan umma kuma aka rufo su muka zauna a palon Baffa muka ci abincin da Mama ta taho mana dashi sannan Mama da Inna suka fita su kace zasu je gidan Alhaji Babba.

Bayan sun tafi ne Rumaisa take tambayata "Diyam, bani labarin yadda haihuwa take, naji Mama tana cewa kinyi kokari kin haifi yara biyu ke kadai babu taimako, ya kika ji?" Na girgiza kaina kawai, ni kadai nasan yadda naji, babu wanda zai gane kuma yadda naji din sai wanda ya tsinci kansa a irin hakin dana tsinki kaina. Ba kuma nayi wa Rumaisa fatan shiga halin da na tsinci kaina.

Sai bayan magrib su Inna suka dawo, sun debo duk kayan Inna da na Asma'u, amma duk naga rayukansu a bace suke daga dukkan alamu ba rabuwar arziki akayi ba. Asma'u ta shigo tana ta tsallen murnar dawowa gida, tace "Adda ina son gidan nan wallahi, nafi son muyi zaman mu anan dani dake da inna".

Washegari muka yi breakfast da yan kudaden da Mama ta bamu da zata tafi, bayan nan kuma sai Inna ta fita can sai gata ta dawo da dillaliya, suka shiga dakinta suna ta cinikin kaya ni dai ban bisu ba, daga baya matar ta fita sai gata ta dawo da maza suna ta jidon kayan dakin inna. Set din gadonta, set din kujerunta, kayan kallon ta kai hatta labulayenta sai da aka fita dasu. Katifar dakin mu ce kawai aka kawo nan dakin Baffa sai sauran tarkace kuma ta saka almajirai suka tattara ta zuba su a dakin soro. Sai aka share dakin kuma aka rufe shi. Naje na leka dakin Ummah ta taga naga yana nan yadda yake ko kayanta ba'a kwashe ba. Da daddare naga Inna ta zauna tana ta lissafin kudi.

Kafin sati ya zagayo mun samu tenants a gidan mu, sai akayi yar karamar katanga a tsakanin mu for privacy. Mata da miji ne da kananan yayansu guda biyu Iman da Saudat, da zasu tare sai sukayi fenti suka hada harda gurin mu suka yi mana. Matar mai kirki, irin masu son shiga mutanen nan ce dan tun da suka zo data gama abinda taje yi zata zagayo gurin mu muyi ta hira, in mijin ya siyo wa yayansa wani abu kuwa sai kiga ta dibo ta bawa Asma'u.

Kudin kayan da inna ta siyar, sai ga Mama tazo ta dauke ta suka fita sai gasu sun dawo da lodin kaya, tun daga kan shinkafa har zuwa ashana, sabulan wanka dana wanki kala kala, har da biscuits da sweets da bobo na yara, ta saka aka buga mata runfa daga gefe ta jibge kayan ni na dauka kayan amfanin mune har ina lissafin watannin da zamuyi muna amfani dasu sai naji ta tura Asma'u duk makotan mu ta gaya musu tana siyar da kaya. Kwanon shinkafa kanon fulawa, har gwangwani daya in kana so zata auna maka, manja man gyada barkono babu abinda Inna bata siyarwa. Ta mayar da Asma'u kuma former school dinta, da yake tsohuwar dalibar suce ba'a siya mata form da uniform ba kawai books aka siya mata sai kudin makaranta wanda a take Inna ta biya, Asma'u tana ta murna. Sai naji dadi dana bata wannan shawarar, na kuma ji dadi data dauka.

A bangare na kuwa tunda muka koma gida kullum sai wata makociyar mu ta shigo tayi min wankan jego, wankan runhu take yi min inyi ta kuka wai zafi amma ni kaina nasan inajin dadin wankan. Sosai na warware na dawo haiyacina karfina ya dawo jikina. Inna kullum tana diban kudi ta siyo min nama ta dafa minmai romo ta saka in chinye in shanye romon, ga tuwo zatayi min da dare da safe ta dumama min. Har addu'a nake Allah kar ya kawo karshen wannan zaman nawa. Amma ina....

Tunda muka zo gida babu wanda ya kara bibiyar mu a cikin yan uwanmu, Saghir ko mai kama dashi ban gani ba, hatta aunty Fatima bata zo ba sai mama ce kadai take ziyartaru tana duba lafiya ta. Ta gaya mana itama duk sun daina kulata kuma suna ta surutun wai dan karayar arziki ta samu Alhaji Babba shi yasa muka juya masa baya, bayan mu abinda yayi mana bayan rasuwar Baffa ya dauko mu ya rike mu ya aurar dani ga dansa mafi soyuwa a gurinsa amma duk bamu gani ba saboda mun zama butulu. Inna tace "Allah ai shi yasan abinda zuciyar bayinsa".

Sai da mukayi wata uku a haka, har na gama wanka duk da cewa na wata biyu akayi min. Ranar nan muna zaune da maman iman muna cin wake da shinkafa sai najiyo Inna tana waya, daga jin sunan data ambata nasan kiran daga Kollere ne, ai kuwa tana gama wa naga jikinta yayi sanyi tace min "Hardo ne. Yace yana neman mu duk a Kollere ranar asabar" tun daga nan naji duk wutar jikina ta dauke. Washegari kuwa dai zazzaɓi. Ranar asabar da assuba Mama tazo tare da driver suka dauke mu ni da Inna muka bar Asma'u a gurin maman Iman. A hanya nayi kwanciya ta a mota trying so hard not to think about what the outcome of the meeting might be.
Chapter 43 · 0% Book details