← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 112

Sashe 15

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna zuwa gida sallar isha nayi kawai na saka hijab dina na dauki jakar islamiyya ta, Inna ta bani kudi wai ko zanga yara suna siyan wani abu. Nayi mata sallama na fita amma ina fita sai nayi hanyar kofa kamar na tafi sai nacire takalmana na dawo da baya na zagaya ta kofar dakin Baffa na hare saman bene. Ina zuwa na zubar da takalma na a gefe na cire hijab dina na ninke dan kar yayi squeezing na kwanta rigingine na rufe idona ina jin dadin iskar da take kadawa a gurin. Na jima a haka ni ba bacci ba ba kuma ido biyu ba. Sai naji a jikina kamar ana kallona. Nayi murmushi na bude idona a hankali na sauke su a cikin na Sadauki daya zauna ya saka ni a gaba ya zuba tagumi yana kallona cikin hasken farin wata. Yayi murmushin daya bayyana kyawawan jerarrun hakoransa Yace "wato kinji dadin iska ko? Shine har da bacci?" Nayi dariya kawai, nace masa "ya garage din yau, mota nawa ka gyara yau?" Ya bata rai yace "daya" nace "kawai?" Yace "kinsan irin lalacewar da motar nan tayi kuwa?" Nan ya fara bani labarin irin parts na motar da suka lalace da irin yadda ya gyara su, ni kuma nayi shiru ina sauraronsa duk kuwa da cewa ba ganewa nake yi ba, sai daya gama sannan yace "to ya gidan Maman" nace "lafiya lau" sai kuma na bata rai nace "ina sweet dina?" Yayi murmushi ya saka hannu a aljihu ya dauko alawar splash guda biyu ya miko min, na karba nayi masa godiya sai kuma na bare daya na mika masa dayar kuma na jefa a baki. Sai ya zagaya bayan pillow na shima ya kwanta rigingine ya dora kansa akan pillown da nake kwance akai, sai ya kasance shi a kasa yake ba'a kan katifar da nake ba. Yayi shiru kamar bacci yakeyi amma ni nasan ba bacci yake yi ba, nasan kallon sky yake yi kamar yadda nima nakeyi.

Can kuma sai naji yace "Diyam? Yau sky tayi kyau sosai" nayi murmushi ina kallon yadda wata ya cika very full, ga stars ba adadi sun cika sararin samaniya. Sai na juya nayi rub da ciki na tallafe fuskata da hannayena, wannan yasa dankwali na ya zame saboda santsin gashi, gashin ya zubo a fuskar Sadauki, ya saka hannu ya tattare su gefe yana kallona, direct nace masa "Sadauki wai kai saurayi na ne?" Sai ya kware da alawar da yake sha, ya mike zaune yana tari yana bubbuga kirjinsa sannan ya kalle ni da mamaki yace "what?" Na daga kafada nace "nima haka naji ana cewa" ya kwanta rub da ciki irin yadda nayi yayi tagumi da hannayen sa yana kallona fuskarsa cike da mamaki yace "a ina kika ji ana fada?" Na bashi labarin abinda ya faru a school, ya ja hancina har yanzu da dariya a fuskarsa yace "ke kuma me kika ce? Are you my girlfriend?" Na juya na koma rigingine nace "oho" yace "oho? Baki sani ba?" Nace "eh, to kaga ai kai baka rubuta min letter da kalaman soyayya" yayi dariya sai kuma ya rufe bakin sa dan kar ajiyo dariyar tasa daga waje yace "kalaman soyayya Diyam? Naga ta kaina ni Aliyu, Diyam a ina kika san kalaman soyayya?" Nace "a makaranta mana. Ka ga lubabatu headgirl din mu to head boy ne saurayinta, kuma kullum sai ya rubuto mata letter ya bani na bata" yace "ohh, wato abinda kuke yi kenan ko? Head boy saurayin headgirl, ke kuma assistant head girl ke ce budurwar assistant head boy ko?" Nace "lah, ni me zanyi da wannan kazamin?" Ya koma ya kwanta, sannan yace "to ni yanzu me zanyi kenan in ina so in zama saurayinki?" Na daga kafada nace "wasika zaka rubuto min" yace "to ni ban iya ba, ki koya min" nace "kaga, plain sheet zaka samu, sai kayi zanen flowers da pencil, sai kazo ka zana heart da arrow yayi crossing heart din ka rubuta sunan ka a sama nawa a kasa, sai ka rubuta I love You Diyam a saman takardar, a ciki kuma sai ka rubuta min kalaman soyayya shikenan" yayi murmushi mai sauti yace "to ni ai ban iya kalaman soyayyar ba" na bata rai nace "ni ma ban iya ba ai" muka yi shiru gaba-daya muna kallon sky. Can sai naji yace "Diyam. Look at the stars, kinga yawansu ko? To zabi daya wadda kike ganin a idonki kamar tafi sauran dukka haske. Concentrate on it kiyi ta kallonta ita kadai ki manta da sauran, ki saka a ranki kamar babu sauran kowanne star a sky din nan sai wannan wadda kike kallo. A hankali zaki ga sauran sunyi disappearing, zaki ga ba kya ganin komai asararin samaniya sai wannan star din guda daya" nayi exactly yadda yace, sai naga komai ya bace a idona sai star guda daya, yace "do you get it Diyam?" Na gyada kaina da sauri ina murmushi, yace "to haka nake ganin ki a idona, ke kadai kike haske a duniya ta, duk sauran mutane da duhu nake ganin su. You are the only star in my sky" nayi murmushi na maimaita "You Are the only star in my sky" yace "that's right. Ki rike wannan a ranki, ko mai tsanani, komai shudewar zamani, ke kadai ke zaki kasance a raina har gaban abadan" nayi dariya nace "wallahi ka iya ashe. Yayi dadi sosai" yace "to shikenan na zama saurayinki?" Sai kawai naji wata kunya ta lullube ni, nayi sauri na rufe idona da hannayena guda biyu, yace "au wai kunyata kike ji kuma? Bude idon ki gani" na makale kafada, yace "kinga wani abu" nace "naki wayon" sai yakama hannu na da niyyar bude fuskar ni kuma sai na tashi da gudu na fara sauka daga stairs, shaf na manta da cewa buya nayi, na manta cewa gudun makaranta nayi, sai da naji muryarsa a bayana yace "Diyam!!, Come back!!" A daidai lokacin ne kuma idona ya fada cikin na Inna a tsaye a tsakar gida da tray din tea a hannunta. Muka tsaya muna kallon kallo, cike da mamaki tace "Diyam?" Adaidai lokacin da Sadauki yayi appearing a bayana. Ta saki trayn hannunta ya fadi cike da karar data jawo hankalin Baffa da Ummah suka fito a tare kowa daga dakinsa.

Writing.....
[1/13, 9:22 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Fifteen: Baffa

Cikin hanzari Inna ta juya ta koma daki, baya yi second uku ba sai gata ta fito da sharfadediyar dorinar da ta siyo ta ajiye danyi min barazana a duk lokacin dana ki jin maganarta. Da sauri na zagaya na koma bayan Sadauki, na kusa fuskata a bayansa zuciya ta tana aiyana min cewa yau kwanana ya kare, na tabbatar da cewa yana iya jin bugun zuciya ta a bayansa. Cikin tsananin zafin rai Inna ta karaso inda muke tsaye amma sai Sadauki ya sake tura ni baya ya hadani da jikin bango shi kuma ya tokare ni da jikinsa. Nan Inna ta fara dukansa da iyakacin karfinta da wannan dorinar ta hannunta amma ko gezau baiyi ba, shi kawai kokarinsa shine ya kare duk dukan kar wani ya sameni.

Sai da dorinar hannunta ta kakkarye sannan ta yar da ita ta shiga kitchen ta dauko muciyar tuwo, a lokacin ne Baffa yayi sauri ya rike hannunta, sai kuma ta saka kuka tadora fuskarta a kafadar Baffa. Sai kuma yaja hannunta a hankali ya shige da ita zuwa dakinta. Umma ce ta taho itama zuwa inda muke tsaye ta sauke kyakykyawan mari a kuncin Sadauki, kafin ya dago kai ta kuma marin daya side din sannan kuma cikin sassarfa ta wuce dakinta, Sadauki ya bita da sauri yana kiran sunanta "Ummah ta, Ummah ta. Ummah dan Allah kiyi hakuri". Sai ya kasance an barni ni kadai a tsakar gidan. Na durkushe a gurin ina jin kafafuwana suna rawa, sai kuma na dafa bango na mike da niyyar komawa sama in dauko kayana, a lokacin Baffa ya fito daga dakin Inna, nayi saurin komawa na dunkule a guri daya ina cewa "wayyo Allah Baffa kayi hakuri. Na tuba, bazan sake kin zuwa islamiyya ba" yazo ya tsaya a gaba na ya miko min hannunsa yace "zo uwata" na sake ja da baya, ya kama hannuna yace "zo Diyam, ba dukan ki zanyi ba, magana zamuyi kawai" na mike a darare amma sai naga yayi min murmushi.

Dakin sa ya jani muka tafi, ya zaunar dani akan kujera sannan shima ya zauna a kusa dani yana kallon yadda jikina yake karkarwa yace "share hawayenki ki daina kuka, ni ba dukanki zanyi ba kuma bazan bari innar ki ta dake ki ba in dai har kika gaya min gaskiya. In kuwa kika yi min karya, zan zaneki sannan bazan hana innar ki dukan ki ba kuma sauran ke da Allah, kinsan baya son mai karya ballantana mai yiwa iyayensa karya" na gyada kai ina jin dadi a raina tunda yace ba za'a dake ni ba sai in nayi karya, ni kuwa yadda nake ji da jikin nan nawa me zai saka inyi karya? Yace "me yasa innarki ta tura ki islamiyya kika ki zuwa kika buya?" Na share hawayen tunowa da laifi na na islamiyya sannan nace "dukana za'ayi in naje" yace "me kika yi zasu dake ki?" Na bashi labarin abinda Sadauki yayiwa monitan aji uku. Ya jinjina kai yace "to me yasa da akayi haka baki zo kin gaya min ko kumako gayawa innarki ta gaya min in yaso ni sai inje makarantar in basu hakuri shi kuma Sadauki inyi masa fada ba?" Na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna ina tambayar kaina me yasa? Ni da abin ya faru ma it never occurred to me cewa in gaya wa inna, in na gaya mata gani nake fada zata yi min ko kuma ma ta dake ni, besides, bana so ayi wa Sadauki fada akan me yasa ya daki wancan yaron.
Chapter 15 · 0% Book details