← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 112

Sashe 51

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina nan kwance kawai naji an hawo saman sai aka bude dakin, Saghir ya shigo fuskarsa kamar zaiyi kuka "Diyam? Me yasa ne wai ke kullum burinki kiga na tozarta a duniya, why?" Na tashi zaune ina girgiza kaina nace "me nayi kuma?" Yace "tuwo. For God's sake tuwo Diyam zaki yi wa wannan mutumin da bana jin ya taba cin sa? Ko ni ba cin tuwo nake yi ba kuma kin sani" nace "cewa yayi ba zai ci ba?" Yace "to ni ina zan iya bashi? Kin san da yadda nayi convincing dinsa ya shigo kuwa kuma kawai sai inkai masa tuwo?" Na tashi na zura jihab dina na fita ya biyo ni a baya.

Yana facing stairs, wannan yasa ina fara sauka na ganshi amma shi kansa yana kasa yana daddanna wayar hannunsa. Na dauke ido na daga fuskarta ina kallon gefe nace cikin wata muryar da naji kamar ba tawa ba "Barka da zuwa" ya dago kai, kallo daya sannan ya mayar da ganinsa kan wayarsa yace "Barka kadai Madam. Ya gida?" Still with the Madam, na fada a raina and my heart hurts. Ban amsa ba na mike naje dining na duba na tabbatar komai yana nan yadda ya kamata sannan na dawo na tsaya ina kallon Saghir da yake ta kokarin yi masa hira nace "ga abinci a table Ko nan za'a kawo muku?" Sadauki ya mike da sauri yace "thank you, zamu ci a can din. Ni am fine ma really, maigidan ki yace sai nazo naci, so I guess I will just have a taste and go" sai kuma ya tafi dining area da sauri Saghir ya bishi a baya, yana zuwa ya dauki plate zaiyi serving kansa sai plate din ya zame daga hannunsa ya fado ya tarwatse, and I noticed that his hand was shaking. Saghir ya kwalla min kira "zo da sauri ki gyara gurin nan" amma kafin in karasa Sadauki ya bar gurin da sauri yayi hanyar waje, Saghir ya kalleni da alamar tambaya na daga masa kafada, sai kuma ya bishi wajen.

Na tsaya da tarin abinci a gaba na ina kallon kofa, so the mask has fallen, my Sadauki is still in there kawai duk pretence ne.

Ina tsaye Saghir ya dawo yace "get a basket ki zuva warmers din a ciki, he is taking it away" naje na dauko na hada masa komai har drink din na rufe, Saghir ya karba yana cewa "Allah yasa ma yaci, wannan mutumi kamar aljanu ne dashi".
[2/12, 6:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty One: A Stranger in the Dark

Ina jinsu suka fita daga gidan, and some parts of me went with them.

A juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na koma sama nayi alwala na gabatar da sallar isha sannan na kai kuka na gurin ubangiji na. Bayan na gama nayi shirin bacci na zauna akan gado ina jujjuya waya ta a hannuna, I wish zan iya sanin halin da Sadauki yake ciki, I can't even begin to imagine in dai har son da yake yi min ya kai wanda nake ji a raina a game dashi to kuma tabbas da nice zuciyata bugawa zata yi in fadi in mutu. It hurts so much to meet him bayan shekaru da yawa and not be able to talk to him, to ina ga shi kuma da yake kallona a matsayin matar wani?

Ina nan zaune naji shigowar Saghir, ya jima a kasa sannan ya hawo sama, nayi tsammanin dakinsa zai wuce kamar kullum amma sai naji ya turo kofar dakina ya shigo da tray a hannunsa ya ajiye akan side table ya zauna a kusa dani yana janyo table din gaban mu. "Sarkin yan tuwo gashi nan na debo miki, ko ba zaki ci ba?" Na zuba a plate ina cewa "Nagode" sai naga ya dauko chokali shima nace "au zakaci ne? Bayan baka cin tuwo?" Yace "albarka ta zan saka miki" murmushi kawai nayi zuciyata tana ayyana min abinda yake ransa. Sai da muka gama ci na kwashe kayan na mayar kasa na taho da ruwa da zuba masa a cup na mika masa ni kuma na zauna ina sha a robar ruwan. Sai dana gama na juya naga ya tsatstsare ni da ido kuma nasan irin wannan kallon but not today, I just can't.

Sai na mike zan bar gurin yasa hannu da yawo dani kan gadon, ya jawo ni jikinsa yana mammatsa min kafadu na amma sai nayi saurin ture hannunsa dan ji nake kamar wanda yake doramin garwashin wuta a jiki, kafin in matsa ya saka hannunsa biyu ya juyo dani ina facing dinsa ya jawo fuskata dai dai tasa yana kokarin hada bakin mu, nayi saurin juyar da kaina nace "Please stop, bana so" amma yaki hakura, na fara ture shi kuma yana jawo ni kamar dai yadda muka saba yi duk sanda yazo da bukatar sa, ganin yafi karfina yasa na fara kuka shabe shabe da hawaye ina rokonsa akan ya kyaleni amma yaki, can kuma sai ya sake ni da karfi ya hankada ni baya ya mike tsaye yana kallona da idonsa da fuskarsa da duk suka yi ja saboda bacin rai yace "nagaji, nagaji, nagaji Diyam nagaji. Yaushe ne wai zaki daina guduna? Yaushe ne zamu mori auren mu ni da ke? Tunda akayi auren nan shekara bakwai Diyam in na zauna zan iya lissafa miki adadin lokutan da kika bari na kusance ki suma kuma babu wanda kika kawo kanki kuma babu wanda kika karbe ni cikin son ranki. Ni fa mutum ne, inada jini da tsoka a jikina ina bukatar kulawar matata amma ke na fahimci da dutse akayi taki halittar. Kullum ina bawa kaina hakuri ina ganin kamar zaki dawo hayyacinki amma kin ki, ni Saghir ni da mata suke rubibi na a waje har kawo min kansu suke yi amma ni ne matata take guduna. Na gaji wallahi. Hakuri na ya kai bango" na sauko daga gadon ina goge hawaye na nace "then let me go, mu daina daukan alhakin juna haka nan, auren nan tun farko da aka yi shi ni da kai bama so, igiyar nan a hannunka take, ka saki igiyar ni da kai mu huta da kunan zuciya" sai ya tsaya yana kallo na yace "haka kika ce? To tsaya kiji, lokacin da akayi auren nan ni kaina banyi niyyar zama dake ba wallahi, after what happened on our first night I thought in na sake ki ban kyauta miki ba, nayi niyyar in rufa miki asiri in cigaba da zama dake a haka ina tunanin with time zaki soni. Amma har yanzu kinki sona, kina ganin kamar ban isa ba ko something like that, ni kuma nasan babu macen da ta isa tace bata sona, in na sake ki Diyam kamar kinyi winning a kaina kin nuna min ban isa ba, which is something I won't agree to. Kin san me? Nasan maganin ki. Aure zanyi. I will let you watch as a lady wadda bata kaiki komai ba take away your husband ta marar dani dan lelenta nima in mayar da ita yar lelena a gaban ki, maybe wannan shi zai nuna miki worth dina ki dawo cikin sense dinki" na mike na rike rigarsa cikin rarraunar murya nace "Saghir, ni ban hana ka aure ba, ni ba zan ma damu dan kayi aure ba ka auri duk matar da kake so Saghir but please ni ma ka barni in koma gurin wanda nake so" yace "ohh, wai dama har yanzu baki hakura da yaron nan ba, dama a saboda shi ne kike tayi min wannan wulakancin? Yaron da aka ce min babu wanda yasan inda yake watakila ma ya zama dan shaye shaye ko dan fashi amma ke shi kike so when you already have me?" Nace "so guda daya ne Saghir, kuma Sadauki naje yi wa shi" ya warce rigarsa daga hannuna yace "then you will rot here. Ke da Sadauki sai a mafarki" ya juya ya fita ya barni. Na jingina kaina da jikin bango ina jujjuya kan, sai kuma na zame na kwanta a gurin akan dandaryar tiles. Ina ji hadari ya hado aka fara ruwan sama mai karfi, tiles din dana ke kai ya dauki sanyi amma na kasa tashi ballantana in koma gado in lulluba, ji nake jikin nawa bashi da wani amfani dan haka lullube shima bashi da amfani. Anan assuba ta same ni, sai da akayi assalatu sannan na tashi da jan kafa na shiga toilet na dauro alwala na gabatar da sallah ina kara kai kuka na a gurin ubangiji na dan nasan shi kadai ne zai iya yi min magani, nasan yana gani na yana kuma jina kuma nasan bai manta dani ba dan yafi kowa sona.

A ranar na tashi da mummunar mura da tari, kuma nasan hakan yana da dangantaka da kwanan da nayi akan tiles. Na shirya Subay'a da kyar, na sha magani na kwanta daga nan kuma sai zazzaɓi ya rufe ni. Daga nan sai ciwo, zazzaɓi ciwon kai mura da tari amma Saghir ko leko inda nake baiyi ba ballantana yaga halin da nake ciki duk kuwa da cewa na tura subay'a ta gaya masa yafi a kirga. A haka nayi ta ciwo na, da kansa yake shirya subay'a ya kaita school kuma ya dauko ta yasiyo musu abinci suci kayansu. Ni kuwa sai naji yunwa tana neman illata ni zan tashi insha tea in koma. Har na kwana biyar a haka.
Chapter 51 · 0% Book details