← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 112

Sashe 31

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da yamma Mama ta sake dawowa gidan. Inna ta tsara mata abinda dazu ya faru da Saghir. Mama tace "to dama ni abinda ya kawo ni shine in gaya miki in anjima Sadauki zai zo, ya sake kiran layi na yace min zasu zo shida dan uwan mahaifinsa da kuma Alhaji Bukar na garin nan. Abinda nake so ince miki shine dan Allah idan sunzo kema ki fito ki nuna cewa ba kya son hadin Diyam da Saghir, ki karbi Sadauki sau daya dai a rayuwarki ko dan yarki" Inna ta fara girgiza kai "na gaya miki Hafsa, kin sani kuma bana son yaron nan bana kaunarsa" Mama ta fara daukan zafi "Yanzu kinfi son ki hada Diyam da mutumin daya kalli cikin idonki ya gaya miki baya kaunar yarki akan wanda yake binki kamar zai lashi takalmin ki saboda ki bashi yarki? Wacce irin zuciya ce dake Adda?" Amma inna sai ta cigaba da girgiza kanta kawai.

Ni kuma jin maganar Mama sai naji hankalina gaba-daya ya koma kan Sadauki. Sadauki zaizo da gaske? Kuma tare da dan uwan babansa? Kenan ya ga babansa da gaske. Amma kuma har zuciya ta ina tsoron yadda zata kasance tsakanin su da Alhaji Babba.

Muna nan zaune kuwa sai ga kira a wayar Mama, ta amsa sai ta tashi tana saka hijab dinta tace "sun zo, bara inje" amma inna bata motsa ba, ni dai ina zaune ina jin jira, irin jiran da akuya take yi lokacin da aka kaita mayanka. Har wani daci daci nake ji a bakina.

Abinda ya faru a waje kuma shine; Mama ce da kanta ta shigo da Sadauki tare da wani mutum da zuka zo tare daga Maiduguri. Babban mutum ne sosai kuma kana ganinsa kaga babarbare harda tsagun su a fuskarsa. Sai kuma Alhaji Bukar wanda shine asalin wanda ya aurar da Zainabu. Suka shigo tayi musu iso har palon Alhaji Babba ba tare dashi Alhaji Babban yasan ko su waye ba ballantana abinda yake tafe dasu. Sai da yaga Sadauki sannan balli ya fara tashi yace a fitar masa dashi daga gidan sa. Mama ta roka dan Allah a tsaya a saurare su tunda dai suka taho kafa da kafa tun daga Maiduguri ai sun chanchanci a saurare su. Mutumin da hausa bata ishe shi sosai ba sai yana hadawa da turanci ya fara bayanin cewa mahaifin Sadauki ne ya turo shi yayi representing dinsa saboda shi baya kusa, gurin nemawa Sadauki auren Diyam kamar yadda shi Sadaukin ya nema. Nan take Alhaji Babba ya basu short ansa da cewa "ba za'a bashi dinba, kuma Diyam mun riga munyi mata miji. Na gama baku amsa ku tashi ku bar min gidana tun kafin in kira muku yan sanda" Alhaji Bukar yace "shikenan dai? Shikenan maganar 'yan sanda dai?" Alhaji Babba yace "ai gida na kuka shigo, dan haka duk abinda nace kunyi min ya zauna kenan" Alhaji Bukar yace "ai kai abinda baka sani ba shine, in kai baka rufe mu ba mu sai mu tufe ka kuma muga wanda zai tsaya maka ya fito da kai" Alhaji Babba yace "anji din, aure dai ba za'a bayar ba in kaji haushi kamar yadda kayiwa zainabu aure dan munki yarda Manu ya aureta to shima Sadauki ka daura masa aure gobe mu gani" Alhaji Bukar yace "tabbas nayi wa zainabu aure, aure kuma wanda manu baiyi irinsa ba, amma kuma da amincewar ta ba wai tilasta mata nayi ba kamar yadda kake da niyyar tilastawa marainiyar Allah ta auri lalataccen danka. Wallahi indai kayi mata wannan auren sai Allah ya kamaka da hakkinta tun a duniya ba sai kunje lahira ba". Ya mike tare da dayan mutumin daya ke ta mamaki yana tambayarsa dama haka mutanen suke? Anan kuma Aliyu ya girma?

Amma Sadauki sai yaki tashi daga inda yake a durkushe. Sai ya rarrafa gaban Alhaji Babba yace "Alhaji dan Allah, nasan nine ba kwaso na yarda kuma ba zaku aura min Diyam ba amma dan Allah, dan Allah Alhaji kar kuyi mata aure, in dai saboda nine to na hakura na janye neman aurenta please ku barta tayi karatunta, ku barta ta girma ta zabi wani da kanta" Alhaji Babba ya dauke kansa, Sadauki ya sake cewa "in kuma lallai sai kunyi mata aure please not Saghir, ga Mukhtar nan" ya fada yana nuna Mama, "ku aura mata Mukhtar indai har sai kunyi mata auren yanzu but please banda Saghir".

Alhaji Babba ya mike "kai a matsayin ka na waye zaka gaya mana wanda zamu aura mata da wanda ba zamu aura mata ba? To albishirin ka, Saghir din zamu aura mata kuma rana ita yau za'a daura auren idan kaji haushi kaje ka fada rijiya ka mutu".

Ina daki a kwance, na bude idona a hankali ina kallon dakin na lura Inna bata nan. Sai na tashi zaune haka kawai naji ina son in fita waje. Na fito palo sai naga Inna da amaryar Alhaji Babba a can gefe suna magana kasa kasa amma basu ganni ba, sai na wuce su na bude kofar palon na fita waje ina karewa compound din kallo, haka kawai naji zuciyata tana gaya min in tsaya anan wajen. Ban jima ba kuwa sai na hango su sun fito daga part din Alhaji Babba su hudu, manyan maza guda biyu da Mama sai kuma mutumin da ko cikin duhu na hango shi zan gane shi. Sadauki. Su biyun sauri suke yi shi kuma a hankali yake tafiya yana ta waige waige, sai kawai na sati handle din kofar na fita da gudu na tafi inda yake, tun daga nesa ya hango ni sai ya juyo ya bude min hannayensa ni kuma na wuce direct zuwa kirjinsa ya mayar da hannayen ya rufe. Na fashe da kuka ina kankame shi.

A hankali yace "shshshsh, ya isa haka kukan, stop crying please. Wai litre hawaye nawa zaki zubar ne a cikin wata daya?" Sama sama naki hayaniya a compound din amma sai nake ji kamar wani background noice ne akan maganar da Sadauki yake gaya min. "Be strong Diyam, you are stronger than this. Ki zama jaruma ki bude hannayenki ki karbi duk wata kaddara da Allah zai dora miki ki dauke ta a matsayin jarabawa, ki dauka cewa Allah yana jaraba ki ne dan yaga how strong are you for the blessings He plans a head for you. Ki sani cewa Allah yana tare dake a ko da yaushe, kuma ki saka a ranki cewa ni Sadauki zan kasance tare da ke a koda yaushe, this is my promise to you, I will be with you forever and ever, I will love you forever and ever. Always ki saka a ranki cewa an angle is watching over you. Always. No matter what happens and no matter how long"

Hayaniya ake yi sosai yayinda ni kuma nayi luf a kirjinsa ina jin kamar anan aka halicceni, ina jin muryar Inna "ba zaka shika ta ba? Maye" Alhaji Babba "kuyi ta dukansa har sai ya sakar mana 'yarmu" dan uwan baban Sadauki "kar wanda ya taba shi, wallahi duk wanda ya taba shi sai yayi nadama".

Lokaci daya kuma sai Sadauki ya sake ni, ya rike fuskata yana kallona idonsa cike da wani yanayin da ban taba gani ba and then without another word ya kama hanyar waje da sauri, ina jin Alhaji Babba yana bawa yaran gidan umarnin su dake shi amma sai naga kawai kaucewa suke suna bashi guri har ya fita. Ni nasan a wannan yanayin da yake ciki da wani ya taba shi da tabbas in bai kaishi lahira ba to kuwa zai kaishi asibiti.

Yana fita daga gidan naji wani nauyi a zuciyata, wani duhu ya mamaye idanuwana, sai kuma kafafuwana suka lankwashe na zube a gurin unconscious.

Hope ba kuyi kuka sosai ba. Lol.
Love you all.
Chears[1/27, 9:17 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Seven : Acceptance

Na bude idona a hankali ina kallon ceiling kamar mai son fahimtar yadda aka tsara shi. Kaina yayi min nauyi haka kirjina. Sheshshekar kukan da naji a kusa dani ce ta sakani waigawa ina kallon mai kukan, Asma'u, tayi sharkaf da hawaye da majina da gumi sai kukanta take yi bil hakki. Na tashi hannuna dafe da kaina nace "Asma'u?" Sai ta juyo da sauri ta rungume ni "Adda dan Allah kema karki mutu ki barni" na rungume ta ina dan jijjiga ta nace "bazan mutu ba kinji, ina nan tare dake" sai ta daho kai tana kallona tace "Adda wai Sadauki ya tafi da gaske? Inna tace wai ya tafi kuma ba zai kuma dawowa ba" naji gaba-daya abinda ya faru yana dawomin kaina kamar film, wani kuka ya taho min amma sai na rike shi a nace mata "zai dawo kinji Yar Asama (sunan da yake tsokanar ta dashi) zai dawo wata rana".
Chapter 31 · 0% Book details