← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 112

Sashe 58

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma'u ce ta raka shi ya bude dakin Ummah ya shiga, sannan ta dawo. Inna ta shigo tana kallona tace "kina jin Sadauki ba zaki fita ki gaishe shi ba?" Nace "baya son ganina inna. ganina a dakin ne fa yasa ya fasa shigowa". Inna tayi shiru kawai bata ce min komai ba ni kuwa zafin da nake ji a raina yasa na dauki kayan na koma cikin daki, amma sai na kasa cigaba da gyarawa na kwanta kawai. Ina kwancen ya dawo, ya leko yayi wa Inna sallama sai ta ce yazo tana son magana dashi. Ya shigo palon ya zauna tace "Sadauki. Ni dai kam bansan wanne kalamai wanda yayi laifi irin wanda nayi maka zai yi amfani dashi gurin rokon gafarar wanda yayi wa lafin ba. Na cutar da kai Sadauki iyakacin cutarwa kuma duk a bisa son zuciyata ba wai dan kayi min wani laifi ba. Amma a karshe sai ya kasance ni din dai nice a wahale. In kace ma ba zaka yafe min ba Sadauki bazan ji haushi ba saboda na cancanci koma menene zakayi min. Amma abinda na sani shine nayi nadama, Sadauki dan Allah...." Sai ya dakatar da ita yace "Inna na yafe miki ai, da ban yafe miki ba Inna ba zaki ganni a dakin nan ba. Maganar ta wuce tsakanin mu har abada" sai Inna ta kama yi masa godiya, har ya sake mikewa zai fita sai ta kira Asma'u, sai kawai zuciyata ta raya min in leka su, naje ta jikin labule ina lekawa sai naga ta kamo hannun Asma'u ta saka a cikin na Sadauki tace

"na hana ka auren Diyam a lokacin da kiyayyar ka ta rufe min ido, amma yanzu ga Asma'u na baka, duk abinda yayi Diyam shi yayi Asma'u har kamanninsu iri daya ne, ina fatan zaka karba kuma wannan zai wanke maka zuciyarka"

Na juya ina dafe kirjina kamar mai kokarin gana zuciyata fadowa kasa. Idanuwana kamar zasu baro mazauninsu ina girgiza kaina a hankali ina cewa "no, no, no" amma sai naga Sadauki yayi murmushi, sai ya cire hannun Asma'u daga nasa ya mayar wa da inna yace "Inna na gode da wannan babbar kyauta da kika yi min, kuma da gaske wannan kyautar ta wanke min zuciyata sosai amma kiyi hakuri bazan iya karba ba. Zuciyata Diyam take so ba kamannin Diyam ko asalinta ba, in na karbi Asma'u banyi mata adalci ba saboda zan tilasta mata zama dani alhalin zuciyata bata tare da ita. Kiyi hakuri idan ban kyauta miki ba amma hakan shine zaifi mana alkhairi a gani na".

Na saki labulen na zauna a gurin ina juya lamarin a kaina. He refused Asma'u, sweet teenage Asma'u, yana claiming that his heart belongs to me, how can that be? Bayan ni kuma I belong to someone else?

Sai yamma muka koma gida, daga nan kuma muka cigaba da lonely rayuwar mu nida Subay'a. Duk da ina kokarin ganin na rage tunanin Sadauki amma kullum tamkar kara min shi akeyi.

Two weeks after that akazo aka raba gidan Alhaji Babba. Aka ja katanga tun daga part dinsa har zuwa bakin gate, sai ya kasance part din nasa da filin compound din dayake gaban part din har zuwa dakin maigadi da gate din gidan duk na sadauki ne. Main house din kuma da sauran abinda ya rage na compound shi kuma na Alhaji Babba, amma ko gate basu dashi dan haka sai katanga suka fasa ake shiga gidan, ko kudin da za'a sayi kofa a saka babu.

Ba'ayi sati dayin haka ba dakunan Alhaji Babba suka zama dakunan kaji, Sadauki ya cika katon palon Alhaji da kuma two bedrooms dinsa da kajin gidan gona, broilers da layers. Compound din kuma akayi katuwar rumfa aka zuba raguna da tinkiyoyi, dakin maigadi kuma ya saka masu kular masa dasu.

Alhaji Babba kuma ya koma cikin gida, dakin da Inna ta zauna nan ya dawo da zama. Washegarin da aka zuba dabbobin da sassafe murja ta kira ni "Diyam wallahi yau bamuyi bacci ba a gidan nan. Yadda muka ga rana haka muka ga dare wallahi, ragunan nan tun magrib suka fara koke koke har garin Allah ya waye sannan kuma kaji suka dauki nasu suma. Ni dai gidan ki zan taho in taya ki zama kafin hamma ya dawo ya kore ni" nace ta taho babu komai. Sai kuma naji babu dadi a raina. Murya, Hajiya Yalwati da sauran yayan Alhaji Babba basuyi wa Sadauki komai ba amma har dasu ake paying. Isn't Sadauki taking this too far? Bayan gudun daukan alhakin wanda baiji ba bai kuma gani ba?

Da dare Sadauki yaje gidan mu. Ya gaishe da Inna sai yace da Asma'u. "Yar Asama kina son gidan gona?" Tace "gidan gona kuma hamma?" Sai ya ajiye mata takardu yace "gashi nan na baki kyauta. Duk karshen wata za'ake kayo miki kudin da aka samu a ciki" Asma'u sai murna da tsalle, yayinda Inna ta saki baki ta kasa magana.

Yana tafiya Asma'u ta kira ni tana son bani labari amma maganar ta kasa fitowa dan murna. Nace "kinga ki nutsu ki fada min, me ya faru?" Tace "hamma Sadauki ya bani kyautar gidan gonar sa da yayi a gidan Alhaji Babba" cikin mamaki nace "what?" Sai ta mikawa Inna tayi min confirming maganar. Har da sunan ta da komai a jikin takardun.

Na kira shi da niyyar yi masa godiya amma shiru wayar bata shiga kamar kullum. Nayi tsaki na yar da wayar feeling very frustrated sai kuma na dawo na sake dauka na tura masa message "ina yiwa Asma'u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka" na tura sannan na zauna rike da wayar a hannu ina jiran reply. Can sai gashi ya shigo. Three words

"You are welcome".

Nayi tsaki ina jin haushin sa, amma bansan dalilin da yasa nake jin haushin nasa ba.

Bayawa ko? Sorry, busy weekend
[2/16, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Five: Fauziyya

Murja tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba'a cigaba da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace "wallahi Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa samarin nan ina dasu, kuma duk wanda nacewa ya turo a cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi ba mu auren mu ke so kawai" na jinjina maganar nace "amma biki fa? Gara fa?" Tace "wannan kuma mijin ki zaki yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana. Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi abincin biki da shi" nayi dariya nace "kai murja, hadda sharri kuma?" Tace "wallahi ba sharri bane ba kayan da yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin su. Amma ya bar alhajin da yar shara".

Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su ya kira ni ya zazzage min bala'i. Bance masa komai ba har ya gama sannan nace "ni dai bani na kar zomon ba, ni ratayar ma ba'a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya gansu ba" ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya.

Tun ana gobe zai dawo yakira yagaya min "ke yanzu ko dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba. Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai kin tana de ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo" sai naji ma abin ya bani dariya nace "duk wanda ka gama samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar Diyam?" Bai musa ba yace "naki special ne. Da gaske nayi missing dinki fa" sai na kashe kawai. A raina ina jin inama yayi zamansa a can kar ya dawo?

Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe da taji tantakwashi. Na hada masa lemom kankana. Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa ya kaimu airport ni da Subay'a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai dai suje da Subay'a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana na gida nayi kwanciya ta a kan gado.

Ina jinsu suka zo, kawai naji wani bacin rai ya sauko min nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay'a ta shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo min kaya da jirgi da mota" nace "kice kin gode, sannan kice masa ga abinci nan a dining" ta fita na koma nayi kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune ina kallonsa shima yana kallona, ya kara fari har da kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace "shikenan? Babu oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan welcome back hug ba zai samu ba?" Nace "na dafa maka abinci, nace maka sannu da zuwa sai menene kuma?" Ya saki hannun Subay'a ya hawo kan gadon sai nayi sauyi na sauka na fita na bar musu dakin.
Chapter 58 · 0% Book details