← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 112

Sashe 86

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ahmad Muhammad" a ina nasan wannan sunan? Na dago kai muka hada ido da Sadauki sai na tuno inda nasan sunan and everything become clear to me. Ahmad Muhammad shine babban abokin Sadauki wanda suka taba zuwa min visiting makaranta tare, Ahmad Muhammad da yace bashi da buri irin yaga ya zama commissioner of police dan ya kama yan iskan gari ya rufe su a cell. That Ahmad Muhammad. Sai na tuno da kamun Saghir na farko, lokacin da aka je bail dinsa akace wai commissioner yace kar a bada bail dinsa. Sai nayi realising cewa Sadauki yana playing Kawu Isa ne, wato ya dauke shi ya kaishi office din abokin sa sun hadu sun ninke shi a bai bai da maganar cewa suna iyakacin kokarin su bayan kuma babu wani kokarin da suke yi. And I realized with a sinking feeling that Sadauki bashi da niyyar fito da Saghir.

"Ahmad Muhammad" na maimaita a fili. Duk suka juyo suna kallona sai muka hada ido da Sadauki a take kuma na fahimci cewa ya gane cewa na gane abokin sa ne. Nace "shekara biyar ko? Allah ya nuna mana shekara biyar din. Kawu kuyi hakuri kuyi min afuwa ku barni in tafi karatu, kafin shekara biyar din na dawo insha Allah. A lokacin in Saghir din ya fito sai ayi maganar auren".

Gaba-daya suka yo kaina da fada, har bama na jin abinda suke cewa ni kuwa na sunkuyar da kaina. Su basu san cewa decision din yafi yi min zafi a kansu ba amma dole ce ra saka ni. Sadauki bashi da niyyar fito Saghir bana jin kyma zai fito dashi ko da kuwa bayan na aure shi dinne. Option dina daya a lokacin shine inyi relying da son da yake min in hana shi cikar burinsa na aure na har sai ya warware daurin dayi da hannunsa.

Fada suke tayi min har saida Sadauki ya koma basu hakuri, inna kamar zata dake ni tana cewa "ya fasa auren naki to, aurensa zaiyi ya rabu dake. Yarinya sai shegen taurin kai" Aunty Fatima tace "ikon Allah, wai kamar ba Diyam din da take ta kuka an raba ta da Sadauki ba ce ba, yanzu kuma ita ake cewa ta auri Sadauki tana ki"

Ni kuma bana son in bayyana musu gaskiyar laifuffukan Sadauki saboda bana son in bata shi a wajensu. Gwara ni in dauki laifin shi kuma ya zauna fes.

Washegari da safe Sadauki ya kira ni a waya. Da kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka dan inji me zai ce min sai yace "Oxford din ce kenan" na danyi tunani. I need a break gaskiya, from Sadauki and from my family. Maybe in nayi nesa da Sadauki zaifi tabbatar wa cewa da gaske nake maybe rashina yayi breaking dinsa. Sadauki loves me, and that love shi nake relying on. Nace "Yes, Oxford din ce" ya danyi shiru sannan yace "na gaya miki tuntuni, I can't do abinda kike fada. Ki bar maganar Saghir, he deserves halin da yake ciki" nace "deserves? Sadauki Allah ne fa kadai yasan waye yayi deserving kaza wate baiyi ba, Allah ne kadai yake judging mutane akan laifuffukan su ba wai mu bil'adama masu tarin laifuffuka ba, Saghir yayi laifuffuka na sani, Alhaji Babba ma haka, amma Allah shi zaiyi judging dinsu bamu ba. Me yasa ba zamu zamanto masu yafiya ba saboda muma Allah ya yafe mana?" Sai yace "Allah yana judging wadansu ta hanyar wadansu. Wanne department din za'ayi miki applying for?" Nayi shiru. I had been thinking about that for years na kasa tsayar da shawara sai a ranar da Saghir ya bani takarda ta, a ranar da na samu freedom dina, a ranar ne na yanke shawarar abinda zan karanta. Law.

"Law" na fada masa. Yace "wow. But why law" nace "nayi tunani, kusan duk abinda ya same ni a rayuwa, tun daga auren dolen da akayi min har zamana a gidan sa da rabuwar mu ta farko da karbar Subay'a da yayi da farko. Duk wadannan sun faru ne saboda abu guda daya. Saboda rashin sanin yancin kaina da banyi ba. Alhaji Babba a both musulunci da kuma a dokar kasa bashi da right din yi min auren dole. Ko da mahaifin daya haife ni ne bashi da wannan right din sai dai zan iya yi masa biyayya dan in samu lada amma ina da option din cewa 'no'. Zaman da nayi a gidan Saghir, wahalhalun da nasha wadanda suka yi kokarin lalata both rayuwata ta duniya da kuma ta lahira duk sun faru ne a saboda bansan yancin kai na ba balle in nemi rabuwa da Saghir, both matsayi na na musulma da kuma matsayina na yar Nigeria sun bani yancin zabin wanda nake so in zauna dashi a matsayin mijina, na tuna rabuwar mu ta farko lokacin da ya dauke Subay'a ya tafi da ita da irin halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashinta, shima wannan duk ya faru ne saboda bansan yancina ba, ba kuma ni da courage din fighting for my right dan shari'a ni ta bawa rikon Æ´ata, ko da mutuwa nayi rikon Subay'a baya hannun Saghir sai dai a bawa Inna, wannan itace Shari'a ta gaskiya. Amma rashin sanin yancin kai da matan hausawan mu suke fama dashi shi yasa ake tauye musu islamic and constitutional rights dinsu"

"Wannan shi yasa nayi deciding in karanta law, dan in samu damar tsayawa duk wata yarinyar da iyayenta ko marikanta zasu tursasa ta gurin auren wanda bata so, dan in tsayawa duk wata matar auren da take zaune da abusive husband kuma take son rabuwa dashi, dan in tsaya in tabbatar iyaye mata sun samu right dinsu da ubangiji da kansa ya basu na karbar rikon yayayensu a lokacin rabuwar aure ko kuma lokacin mutuwar miji. Wannan shine zai zama role dina a society"

Yace "Masha Allah. I am very proud of you Diyam. Kuma ki sani ina tare dake tun daga farko har karshe".

Na fahimci cewa Sadauki shi ko a jikinsa da nayi suspending auren mu nace sai na gama karatu. Shi dai kawai in dai Saghir zai cigaba da zama a prison shikenan. Da nayi kokarin yi masa complain cewa bama so nake tunda bai damu da aurena ko rashin aurena ba sai yace "you have no idea how much I want to marry you. This is just a phase we are going through. Am sure zaki chanja mind dinki along the way, in ma baki chanja ba I will wait har ki gama din ki dawo".

Wato ni ina depending on son da yake yi min cewa zai sauko ya chanja shawara ya fito da Saghir saboda muyi aure shi kuma yana depending on son da nakeyi masa yana saka ran zan sauko in bar maganar Saghir muyi aure. Ni dashi aga wanda zai fasa.

Ya gama nema mana admission, kuma mun samu successfully. Anan na fahimci cewa su ba yearly suke bada admission ba kamar in batches suke yi kuma mu namu session din zai fara ne January. Daga nan kuma sai ya shirya ya tafi yaje yayi one week a can ya dawo yace "all set, an samo muku apartment a kusa da school din an kuma ajiye muku mota saboda zirga-zirga. Abinda ya rage miki shine koyan driving" shi ya koya min, ya ajiye duk harkokinsa yake zuwa yana dauka na muna fita koyon mota kuma cikin kankanin lokaci na iya sosai. Zamu yi ta hirar mu amma da zarar nayi masa maganar Saghir zai dauke wuta in ba hakuri na bayar da kuma to sai dai mu dawo gida ranar ba za'ayi koyon motar ba.

Shi yayi min komai na harkar student's visa, muka je Abuja ni da shi da Asma'u. A embassy na UK na hadu da Judith itama tana neman student's visa, daga gaisawa naji yarinyar ta kwanta min muka yi ta hira har na fahimci scholarship ta samu daga program na African Initiative for Governance kuma session din karatun mu zai fara tare ne. Sai na roki Sadauki ya karbar mana visar tare da ita sannan kuma nace mata in mun hadu a can tazo mu zauna tare a apartment din mu.

Bayan everything ya zama set kuma sai na ji duk jikina yayi sanyi. Naji bana son rabuwa da gida, da Inna da Subay'a da Asma'u. Bana son rabuwa da Sadauki. Inna nasamu wadda har lokacin bata daina fushi dani ba akan kin auren Sadauki, nayi mata bayanin manufa ta akan hakan, na nuna mata nima bawai hakan naso ba sai dai hakan nake ganin shine dai dai, sai ta dan sauko, ta saka min albarka sannan tayi min nasiha a game da zaman da zanyi a can.
Chapter 86 · 0% Book details