Sashe 106
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Seventy Five : Maiduguri
Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din mota a waje, sannan ta ruga daki da gudu tayi refreshing. Tana cikin saka kaya Murjanatu ta shigo dakin tana kallon ta tace "wai sai yanzu kike shiryawa?" Diyam tace "da wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da zanyi amfani dasu tun a gida" Murjanatu ta shiga ta fito da karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ya dauko hijab dinta tana checking contents din handbag dinta sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta rataya. Suna saukowa Murjanatu tace "baku da abinci a gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci yunwa nake ji" Diyam tace "nima yunwar nake ji, in kin samu nima ina so".
A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin maneman Murjanatu suna magana, ya dora jallabiya akan shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha yazo ya karbi jakar hannun Murjanatu ya je ya saka a mota, Murjanatu tana kallon Sadauki tayi wa Diyam rada tace "baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa masa?" Diyam tana dariya tace "kakan bleaching ba bleaching ba" amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he seems kamar ya kasa daina murmushi.
Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace "to ya isa haka, shiga mota" ya nuna Murjanatu yace "kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?" Almustapha yace "kaji masu mata, muma dai mun kusa zuwa gurin" Sadauki yace "kun kusa, amma baku zo ba. Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma yanzu kana baya na" duk suka yi dariya, sannan su biyun suka shiga mota.
Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, sai ya mika hannu ya kama nata, tace "zamu tafi" yace "Allah ya kiyaye hanya. I will be on the next flight insha Allah. Take care of yourself for me kinji? Sai nazo anjima" tayi murmushi tana gyada kai, sai kuma tayi É—age on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata hijab dinta ya manna mata kiss a palm dinta sannan ya rufe mata kofa.
Suna jan mota Murjanatu tace "I will pretend kamar banga komai ba" Diyam ta harare ta tace "to ai dama babu abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi". Suna zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying maman su Murjanatu sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa.
Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda akayi musu a airport, tun daga motocin da Diyam taga sun zo daukan su harda motar security, Diyam ta kara tabbatar wa lallai É—an Umar Mustapha Abatcha ta aura. Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da gidajen kakanni, iyaye da ya'ya. Gidan baban Sadauki a ciki yake, uncles uncles dinsa duk suna ciki, da kuma cousins dinsa da sukayi aure. Ko wanne gida ka gani a cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar kudi daga aljihunsa dan akwai su din.
Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Murjanatu ta ja ta suka tafi part dinsu su yammatan gidan wanda shi a kansa ma gida guda ne. Murjanatu tana ta tsokanar ta "wallahi in kika ce kunya zaki ringa ji ko? To wallahi a gidan nan sai an kusa mayar dake tababbiya" Diyam tayi murmushi, amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba.
Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan, sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta jawo jakar kayanta zata saka sai Sa'adatu tace "Mama fa ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting" Diyam tayi godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu in yaso in an jima sai ta saka nata. Aka kawo mata kayan ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za'a dan buda mata. Nan take Sa'adatu tayi waya aka zo aka karba kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi. Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta, in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da dankwalin shaddar sannan ta saka bungles na danyen gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi ta rike clutch golden brown nan take ta fito a matsayin Mrs Aliyu Abatcha. Bayan suma su Murjanatu sun gama shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda Diyam tana zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din tayi.
Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki, kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu, kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba.
Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe ba wai anan ne za'ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka ko kuma family meetings. Sai da akayi la'asar sannan aka fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da Sa'adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace "wow" Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta. Nan take ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun dazu da suka tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply
"Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa ce?"
"Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but not directly"
"To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki godewa Allah Diyam dan yayi miki komai"
"Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the body.
Imojin heart mai beating
"I love you so much my husband"
"I love you more, my wife".
Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi. Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba'a tashi daga event din ba sai daaka fara kiran magrib.
Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo yake yi mata dan haka akan sallayar da tayi magrib anan ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su suka amsa mata da fara'a suka yi ta tsokanar ta tana rufe fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner mai kyau ta bata a matsayin gift sannan tayi musu sallama Mama ta tafi ta raka ta. Bayan Mama ta dawo ne sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma dabaru irin na zaman aure, wadansu maganar sai Diyam taji sunyi mata nauyi da yawa amma kuma duk tana ganewa kuma tana dauka. In dai Sadauki ne, she can and will do anything for him.