← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 112

Sashe 112

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A lissafin Sadauki so yayi in sun bar Nigeria su fara tafiya Canada suyi kwana biyu tukunna, amma Diyam ta tubure masa ita bata son zuwa, ya gane abinda yasa bata so, ita kunya take ji ake ganin ta da ciki. Yayi dariya "to wai ke banda abinki, ni fa banga abin kunya anan ba, kowa ma fa yana yi" ta juya masa baya tana kallon Subay'a a cikin swimming pool tace "kuma kawai sai in je gidan inyi ta yawo da ciki suna kallona?" yace "baiwar Allah, idan baki je da ciki ba in kika haihu dai ai dole zasu ganki da dan ko? Ko shima cewa zaki yi ba ke kika haifa ba?" Tace "ai kuwa in naje gidan da baby to har in bar garin ba zan dauke shi ba" ya rike baki "to waye zaiyi feeding dinsa?" Tace "sai ya sha madara" ya kwanta akan camp bed din da yake zaune akai ya rufe ido yace "you are impossible Diyam, ke fulatancin kamar a kanki ya kare" ya sake cewa "kiyi addu'a to, kar a saka bikin su fanna kafin ki haihu, sai muga yadda zakiyi da cikin a gurin biki" tayi saurin cewa "Allah ya kiyaye, insha Allah sai na haihu". Sai ta jawo kujerar da take kai kusa dashi tayi tagumi tana kallon sa, ya bude ido yana kallon ta yace "what?" A hankali tace "I want to kiss you, kuma Subay'a tana kallon mu" yace "ohh, a wannan bangaren kam kin ajiye fulatancin ko?" Sai kuma ta rufe ido tana dariya.

Addu'ar Diyam dai bata karbu ba, dan suna komawa makaranta aka saka ranar bikin su Sa'adatu kuma wata biyu kadai aka saka, meaning cikin Diyam yana da wata takwas kenan za'ayi bikin. A dole Diyam ta taho Maiduguri lokacin bikin da katoton cikinta, Sadauki yana ta yi mata dariya amma sai ta maze da shiga harkokin bikinta sosai ta rike role dinta na matsayin babbar yaya. Da ita akayi shawarar komai, da ita aka sayi komai, wani abun ma in ana nema sai Mama tace azo wajen Diyam.

Su Inna da Mama da Asma'u ma duk sunzo gurin bikin sun kuma Kawo wa amaren gift sosai har sai da Maman su Murjanatu tace "kayan nan anya basu yi yawa ba Amina?"

Aka daura aure aka kai amare gidajen su. Sa'adatu ta auri Aminu an kaita Abuja. Falmata kuma Saifullahi mutumin Kano amma mazaunin Canada dan haka can zasu koma, Fanna kuma ta auri cousin dinta Al-mustapha zasu zauna anan Maiduguri amma zata zauna a gurin su Diyam ta karasa karatun ta.

Bayan su Diyam sun koma England sai hankalinsu kuma ya koma kan haihuwa, Sadauki yana ta rawar kai, duk zuwa asibiti tare suke yi idan kuwa yaga namiji ne zai duba ta sai ya ja abarsa su bar asibitin. Twins ne kamar yadda Sadauki yake ta addu'a. Diyam tayi tunani sai taga cewa ba zata iya tuno yadda haihuwa take ba tunda bata yi labor a haihuwar Subay'a ba, haihuwar twins kuwa ba zata iya tuna yadda abin ya kasance ba dan haka sai ta shiga maternity classes, anan ta fahimci komai ta kuma yi browsing wasu abubuwan ta sake fahimta.

Abinda take tsoro guda daya shine shigar Sadauki gurinta in tana labor, tasan kuma za'a bashi option din shiga kuma tasan zai shiga din. Sannan tasan in dai ya shiga sai ya hargitsa daga ita har me karbar haihuwar kuma in yaga wahalar da ake sha a gurin haihuwa sai sunyi rigima kafin ya barta ta samu wani cikin. Ta kuma san yadda yake son yaya, dan haka ta yanke shawarar yi masa dabara yadda ba zata haihu a gabansa ba saboda ta haifa masa yaya as many as yadda Allah ya basu.

Ranar data fara jin alamar labor da daddare sai taki nunawa Sadauki, da safe kuma sai tayi pretending as if bacci take yi har ya gama shiryawa a hankali dan kar ya tashe ta, ya zo yayi mata kiss ya fita. Sai bayan fitarsa sannan ta tashi ta dauko jakar tafiya asibitin ta wadda already ta riga ta shirya ta ta kuma yi driving kanta zuwa asibitin. Sai da taje suka aunata suka kuma tabbatar mata da cewa haihuwa zata yi sannan suka bata daki suka kuma nemi su kira mijinta amma ta hana su tace sai ta haihu tukuna.

Ta sha wahala ba kadan ba, Sadauki ya sha kira kamar sunan sa zai kare ta kuma yi nadamar kin gaya masa dan da yana kusa ko ganin sa in tayi zata ji dadi. A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifi namiji first, sai data huta sannan labor ya sake dawowa ta haifi mace. Ana miko mata su taga fuskar babansu amma fatarta, sai dai namijin bai kai macen haske ba.

Sai da aka gama garata aka kuma gyara babies din ta kuma danyi bacci kadan ta huta sannan tace su kira shi. 30 minutes after kiran nasa sai gashi ya shigo asibitin hakan yasa Diyam ta tabbatar da cewa yayi breaking every traffic rule a hanya saboda sanin nisan asibitin daga office dinsa.

A rikice ya bude kofar dakin da aka nuna masa ya shiga. A tsaye ya ganta a gaban window ta juya masa baya. T-shirt dinsa ce a jikinta, wadda ta kawo mata har zuwa rabin cinyarta, gashin kanta a barbaje wani ya sauka a bayanta wasu akan kafadun ta wasu kuma sun zubo kan kirjinta. "Diyam" ya fada cikin sarkewar murya. Ta juyo tana kallonsa, hannunta rike da jariri tana rocking a hankali, fuskarta da faffadan murmushi. Ya karaso cikin sassarfa ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yace "don't you ever do that to me again" ta kwantar da kanta akan kirjinsa tace "am sorry my Lion. Bana son in tayar maka da hankali ne" yace "kinsan tashin hankali da naji kuwa? Kinsan da yadda nazo asibitin nan kuwa? I tot karya suke yi min da suka ce lafiyar ki kalau, I tot ba zaki iya haihuwa ba tare da ni ba" tace "I missed you sosai, nayi ta kiran sunanka" ya danyi dariya yana dago fuskarta da hannun sa daya, taji kunya ta mayar da fuskar kasa.

Ta zaunar dashi akan kujerar da take dakin ta mika masa babyn hannunta, ya dan leka cikin diaper dinsa fuskarsa kamar zata yage dan murmushi. Ta dauko dayar da take bacci a kan gadon su ta mika masa itama. Ya rike su hannu bibbiyu inya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan ya kasa tantance wanne yafi kyau a cikin su. Yayi musu addu'a. Tana tsaye a gabansu tana kallon su sai ta fara buga kafa cikin shagwaba, ya dago kai yana kallon ta cikin alamar tambaya sai tace "ni a ina zan zauna, sun tare min gurin zama na" ya daga babies din da sauri yace "zo ki zauna akan cinya" ta tafi ta zauna tana karbar daya, ta rike ta da hannun ta daya dayan hannun kuma ta zagayo wuyansa dashi. Sun jima a haka suna kallon kyautar da Allah yayi musu sannan yace "Baffa ne da Ummah. Baki ga yadda suke ta kokarin rike hannun juna ba?" Diyam tayi dariya tace "babu ruwana sai na gaya wa Inna" yayi murmushi yace "so kike ta biyo ni da muciya?" Sukayi dariya a tare. Sai ta kwantar da kanta a wuyansa shi kuma yayi kissing forehead dinta tare da sauke ajjiyar zuciya. A hankali yace

"ALHAMDULILLAH"

Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya. Allah ya kara salati ga fiyayyen halitta (SAW) Allah kuma yasa muna da rabon ganin sa baki daya.

Godiya ga fans dina wanda na sani da wanda ban sani ba a duk inda suke, alkhairi ya kai muku har dakunan ku, ina sonku sosai da sosai, idan babu ku to kuwa tabbas babu ni.

#MyWattpadpeople, thank you for all the votes, the comments and the encouragement.

#MamanMaamaNovels na Facebook ina godiya da soyayyar da kuke nuna min a duk books dina, ina ji daku sosai mazan ku da matan ku.

#MamanMaamaNovels groups 1,2,3,4,5 na WhatsApp, ina ji daku tamkar nama daya a miya. Allahu ya bar kauna.

The ladies at #Shatuuskingdom, #zaurenBiebeeIsa, #KDM soldiers, #ZeenatNovel, #SameenaAliyuNovels, da sauran groups din da nake ciki da wadanda ma bana ciki, ina godiya kwarai da gaske. Allahu ya bar zumunci.

Zaku sake ji na da wani labarin, amma banan kusa ba, maybe sai 1-1-2021 maybe kuma kafin nan. In kuma babu rabo to Allah ya hada fuskokin mu a aljannatul Firdaus. Allahumma ameen.

Please pray for me a duk sanda labarin mutuwa ta ya riske ku.

ILYSM.
Chapter 112 · 0% Book details