← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 112

Sashe 64

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fauziyya ta zame ta zauna. Ni kuma sai na juya nayi hanyar sama. Kabir yace "Diyam ki kira gida ki fada. Maybe Alhaji yana da wani a sama wanda zai saka a fito dashi" na gyada masa kai kawai na wuce. Ina zuwa daki na karasa hada kayana na fito na wuce Fauziyya a palo ta zabga tagumi na je na dauko Subay'a na dawo na sake wuceta. Na shirya Subay'a sannan muka sauko tare da akwatin kayan mu. Fauziyya ta tashi tsaye tana kallon mu tace "ina zuwa haka?" Nace "gida" bata kuma cewa komai ba har muka fita. Mai gadi yayi min sannu da jiki sannan ya taya mu da kaya muka tari abin hawa muka tafi.

Inna tana ganina da akwati tace "lafiya" na ajiye kayan hannu na sannan na gaishe ta, bata amsa ba tace "lfy nace? Lafiya na ganki da tsakar ranar nan da akwati?" Na sunkuyar da kaina nace "Inna na gama auren Saghir" ta saka salati, "shi Saghir din ne ya turo ki gida ko kuma ke kika yi ra'ayin kin gama aurensa kika taho gida? Dama igiyar auren a hannun ki take?" Na girgiza kai nace "Inna Saghir fa...." Tace "Saghir me? Saghir din yanzu ai bana da bane ba. Kika zauna da wancan Saghir din ma ballantana wannan da kowa ya tabbatar ya chanja. Dama tun randa Sadauki yazo nan da maganar aurensa naga yadda kikayi nasan in ba sa'a akayi ba sai kin fito da wata maganar kuma" naji hawaye ya fara bin fuskata, nace "Inna ba a kan Sadauki na taho gida ba, tsakani na da Saghir ne, ni ba zan koma gidan sa ba Inna. Dan Allah karki mayar dani" tace "ina Saghir din?" Na share hawaye na nace "yana police station" ta sake wani salatin "me ya faru? Me yake yi a can?" Nace "Sadauki ne ya rufe shi." Ta mike tace "kuma kika ce ba'a kan Sadauki bane ba. kira min Sadauki yanzu yanzun nan" nace "na baro wayata a can gidan. Kuma ma ba daukan wayata yake yi ba" ta kwalla kiran Asma'u. Tana zuwa tace mata "kira min Sadauki da wayarki" Asma'u tana kallo na da alamar tambaya ta dauko wayarta ta danna kira ta saka a speaker. Har ta gama ringing bai dauka ba sannan ta sake kira shima shiru. Sai kuma gashi ya kira. Ta dauka tasa a speaker naji muryar sa yace "Yar Asama ya akayi?" Tace "Inna ce tace in kira ka. Gata" Inna tace "Sadauki me ya hada ka da mijin Diyam har ka rufe shi?" Yayi shiru, ni kaina sai da nayi mamakin karfin halin Inna. Sai ta ce "tazo gida yanzu tace wai ka kama Saghir ka rufe shi" ya sake yin shiru sannan yace "ita Diyam din ce ta kawo kara ta akan na rufe mata miji?" Nayi saurin girgiza kai zanyi magana Inna ta harare ni tace "eh fa, shine nayi mamaki nace me ya hada ku?" Yace "a ce wa Diyam tayi hakuri, za'a fito mata da mijinta gobe in Allah ya kai mu" sai ya katse wayar.

Na saka sabon kuka "Inna yanzu haushi na fa zaiji yace na kawo kararsa" Inna tace "na sani ai. Haka nake so saboda ki fita harkarsa ki barshi yayi aurensa kema ki zauna ki rike naki auren". [2/21, 12:53 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Nine : The Utterance

Inna taga ta kanta a gurin jama'a jiya. Duk inda na shiga kowa kokawa yake yi da abinda Inna tayi. But to me, laifin Inna a yanzu guda daya ne, rashin sauraron Diyam kafin ta yanke hukunci bawai hada Diyam da tayi da Sadauki ba. Wannan kuma shine halin kusan 70% na northern mothers. Kullum su dai burinsu shine yarsu ta zauna a gidan mijinta kar ta kashe auren ta dawo gida ta zauna a gabansu. But what if the marriage is not working? What if she is buying her ticket to hell fire instead of paradise a cikin auren?

And Saghir, Saghir yayi laifuffuka da dama a baya but a yanzu laifinsa shine dukan Diyam. Nothing, nothing gives a husband the right to hit his wife. Duk kuma namijin da yake dukan matarsa to ba mijin aure bane ba, ballantana mata mai ciki? Hmmm

Then Sadauki. Na lura Sadauki ya zama shafaffe da mai a gurin readers, sam basa ganin laifinsa komai yayi daidai ne dan ina jin few mutane ne naga sunyi comment akan laifin Sadauki. Sadauki is rather rude and very authoritative. Ba shi da right din da zai sa a rufe Saghir, yes Saghir yazo gurin aiki drunk kuma ya fadi maganganu wadanda babu wanda ya gane in banda shi Sadauki da ake magana a kansa. Abinda ya kamata Sadauki yayi shine yasa ka security su fitar dashi waje, in ya ga dama ya hada masa da takardar kora daga aiki. But bashi da right din kaishi station a rufe shi kuma wai without bail, saboda yana da kudi?

Let's continue

Na rufe fuskata ina girgiza kaina da sauri. "Inna kar kiyi min haka dan Allah. Inna ki tsaya ki saurare ni ki fahimce ni kar ki mayar dani gidan Saghir in na koma wallahi mutuwa zanyi" tace "da baki mutu ba shekara da shekaru sai yanzu da Sadauki zaiyi aure shine zaki mutu?" Sai ta mike zata shige daki nima na mike da sauri na rike hannunta da hannu na daya dayan kuma na daga mara ta da shi nace "Inna nayi bari jiya" sai ta juyo tana kallo na ido a bude, ta taba fuskata da hannunta tace "bari Diyam? Ya akayi kika san bari ne kinje asibiti?" Na gyada kaina nace "naje Inna, su suka tabbatar min da cikin jikina ya fita Inna. Saghir ya fitar min dashi" ta dan bata rai cikin rashin fahimta tace "Saghir? Ta yaya Saghir zai fitar miki da ciki?" Nace "dukana yayi Inna, dukana Saghir yayi ya buga ni da jikin bene ya kashe min baby na, kamar yadda shaye shayensa ya jawo mutuwar yan biyu".

Sai ta kama hannuna muka zauna tace "Diyam, kin tabbatar abinda kike gaya min gaskiya ne? Me ya hada ki da Saghir har ya dake ki haka?" Na shafa fuskata sai itama ta saka hannu ta taba fuskar tawa, side din da Saghir ya mare ni, na dan yamutsa fuska alamar zafi sai naga idonta ya kawo kwalla amma sai tayi sauri ta mayar da ita. Tace "me ya haÉ—a ku nace" sai na bata labarin messages din Sadauki. Tana girgiza kai tace "me yasa? Me yasa zaki ajiye sakon Sadauki a wayar ki har mijinki ya gani bayan kuma kinsan yasan tsakanin ki da Sadaukin" nace "inna na fada miki menene a cikin sakon nan, babu wata kalma ko daya data kauce hanya a ciki kuma in na goge su ai kamar bani da gaskiya kenan. Ina son Sadauki na sani, amma Allah ne shaidata cewa ko sau daya ban taba tunanin yin sabon Allah da Sadauki ba. Kuma ke kece shaida, Sadaukin nan tamkar dodanniya haka nake a gurinsa, ko kallon inda nake baya yi. Shi dai ya zarge ni ne saboda shi din yasan shi mai laifi ne, abinda yake cikin tasa wayar idanuwa ma ba zasu iya gani ballantana hankali ya dauka" Inna tace "akan wannan maganar ne Sadauki ya sa aka kama shi?" Nace "ni ban sani ba, amma ina jin akanta din ne. Ya dai fita a fusace yace sai ya wulakanta Sadauki, tun daga nan kuma bai dawo ba sai da safe Kabiru abokinsa yazo yace mana yana hannun yan sanda" Inna tayi shiru tana tunani sannan tace "yace za'a sake shi gobe, Allah ya kaimu goben, ya fito sai yazo yayi bayanin dalilin da yasa ya dake ki. Kar ki goge messages din ki barsu saboda shaida a gani cewa babu abin duka a cikin su".

Sai naji raina yayi min wani irin dadi, babu abinda yafi dadi irin a fahimce ka babu kuma abinda yafi ciwo irin ace kana da gaskiya amma a hana ka tsarawa ballantana a fahimce ka. Ina ma dai iyaye zasu ke bawa yayansu wannan damar? A fahimci kowa sai a hada both parties ayi wa kowa fada dai dai da laifinsa? Ba wai ace da mace ki komaki cigaba da hakuri ba tare da ko murya an daga wa shi namijin da yake maltreating dinta ba, wannan tamkar ana ce masa ka cigaba da maltreating dinta ne.

Amma dana fara tunanin abinda zai iya faruwa gobe sai naji duk hankali na ya kuma tashi. Nasan halin Saghir sosai nasan zai iya jujjuya maganar gabaki daya ta koma laifina kuma na tabbatar iyayen mu musamman mazan bayansa zasu bi, musamman in nayi la'akari da irin kiyayyar su ga Sadauki, da kuma soyayyar da suka san ina yiwa Sadauki, tabbas komai Saghir ya gaya musu yarda zasuyi. Ni kuma ba yardar su ko rashin yardar su ce problem dina ba a'a tirsasani in koma gidan Saghir shine problem dina. Na gama auren Saghir, ba zan koma gidan Saghir ba. Wannan is my decision. Ni a yanzu auren Sadauki ko rashin auren Sadauki ko shi kansa Sadaukin basa gabana. Abinda yake gabana shine rabuwa da Saghir.

Inna tace inje in kwanta in huta a daki. Na tashi na shiga ina jin Asma'u tane cewa "Inna amma ba za'a mayar da Adda gidan can ba ko?" Inna tayi shiru bata ce komai ba. Na kwanta kawai sai hawaye ya fara zubo min ina lissafin abin da zanyi in akace sai na koma. A ciki har da guduwa na lissafa amma inna gudu inje ina? Yan uwan uwata dai sune yan uwan ubana sune kuma yan uwan mijina. Sai kawai na yanke shawarar in aka matsa min akan in koma gidan Saghir to zan gudu gurin Sadauki, inje in tuna masa da amanar da Baffa ya bar masa ta kula damu, sannan in tuna masa cewa ni ma fa yar Baffa ce ba wai Asma'u ce kadai yarsa ba. In kuma roke shi daya shige min gaba in kai karar Saghir court alkali ya raba auren mu. Yes, wannan shine abinda zanyi.
Chapter 64 · 0% Book details