← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 112

Sashe 83

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina so ki fahimci cewa ban rufe Saghir dan in aure ki ba. Yes, I loved you, I love you and I will take your love with me to my grave but da ace zaman lafiya kuke yi da Saghir da babu abinda bazanyi ba dan ganin cewa zamanku ya dore a tare. I would have given everything in dai zakiyi farin ciki. But after na fahimci irin zaman da kuke yi, after what he said a gaba na ba tare dako digon nadama a muryarsa ba, after ke da kanki kin gaya min cewa ba kya son komawa gidansa then I won't let you. Yes, na barwa Saghir kudina intentionally saboda ina so ya dauka, saboda ina son in samu hujjar rufe shi yayi paying for abinda ya aikata. But I didn't force his hands. Shi yayi making decision din dauka da kansa. And that's what took him to prison bani ba".

"Yanzu na dawo gurinki Diyam. Ina neman aurenki bisa yardarki. Yes, nasan shekaru sunja ba lallai ne kina da feelings for me a yanzu ba. Amma ina so ki fada min abinda yake ranki, in kika karbi offer ta ta aure I will surely be the happiest man on earth, in kuma kika ki karba I will be heart broken maybe fiye ma da wancan karon but I will respect your wish. Bazan matsa miki ba ba kuma zan bari a matsa miki ba".

Ina jiran amsar ki.
[3/5, 10:12 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty One: The Decision

Nayi kokarin dago kaina in kalleshi amma na kasa, tun daya fara magana nake hawayen tausayin rayuwata da tasa, wani gurin kuma inyi murmushi ina jin soyayyar sa tana kara ninkuwa a zuciyata. A karshe sai na samu kaina da tambayar kaina. Shin tsakanin ni da Sadauki waye yafi son dan'uwansa?

But can I tell him that? Anya zan iya gaya masa cewa babu abinda ya ragu a zuciyata dangane da soyayyar sa sai ma karuwa da yayi. Sai jin murtarsa nayi a hankali yace "should I start crying? Ko kuma in durkusa a kan guiwa ta?" Na yi murmushi ina karasa goge sauran hawayen ido na, na bude baki sai maganar ta makale, sai kawai nasa hannayena na rufe fuskata. Ya kama dariya yana cewa "you must be kidding me. Yanzu ni in zauna in gama bude miki zuciyata amma ke sai ki rufe fuska? In ba zaki gaya min bama at least let me look at your eyes in karanto amsa ta a can" na girgiza kaina nace "I can't" yace "wait, wai kunya ta kike ji?" Na bude fuskata nasan "mu fulani kunya ce damu" yayi dariya yace "maybe kin manta, nima bafulatani ne" nace "half ba. Mun bar musu kuma" yace "ni ban yarda ba, ko bani da jinin fulani my heart is fulani. Zuciya kuma itace rayuwa" nayi murmushi ina tuna ranar daya fara fada min nice zuciyarsa a Taura. Yace "I still need to hear it. I need to hear you say you love me. In kika fada then I have tukuici for you. Happiness insha Allah, till eternity. Through thick and thin".

Ina sunkuyar da kaina kasa, murmushi a lips dina, ruwan hawaye a idona, nace "kalmar love can't even begin to describe yadda nake jinka a zuciyata. Sometimes ina jin soyayyar ka kamar tayi waya a kirjina Kamar zuciyata ta cika har tana zuba da sonka. Da sonka aka haife ni Sadauki kuma nasan da shi zan koma fa mahalicci na. Bana jin kalmomi zasu iya bayyana soyayya ta gare ka dan duk abinda na fada ji nake yi kamar yayi kadan" sai yayi sauri yace "okay, will you marry me? Please? Sai a nuna min soyayyar a aikace ko zan fi fahimta sosai" sai nayi saurin jan hijab dina na rufe fuskata saboda nauyin maganar sa da naji. Ban san me yasa yanzu nake jin tsananin kunyar Sadauki ba bayan kuma sanda nake karama bana ji kamar haka. Ina jinsa ya sake jawo kujerar sa kusa dani yace "Please say something Diyam. Am dying here".

Hayaniyar su Asma'u ce tasa na bude fuskata amma ban kalli inda yake ba sai na juya inda na jiyo muryoyinsu. Murjanatu tazo da sauri tana cewa "yaya, wallahi naga irin motar da kayi min alkawari as my birthday gift. Please, please yaya ka bar min ita" sai ya dafe kansa da hannu daya yace "zaki saka min ciwon kai Fanna. Please go and make the noice somewhere else" sai na mike tsaye nace "yauwa an kawo abinci, dama yunwa nake ji".

An jera mana abinci iri iri akan shimfidar da akayi mana akan grass carpet din gurin. Muka tafi mu uku muka fara saving kan mu muna ci muna hirarrakin mu amma hankali na tana kansa yana zaune har yanzu a inda muka zauna da waya a hannunsa. Naji shigowar text cikin waya ta sai na duba naga "Please ki ajiye abincin nan kizo mu karasa maganar mu" sai na juya na kalle shi nace "me za'a zubo maka?" Ya bata rai yace "am not hungry".

Anan mukayi sallolin mu, Murjanatu tana ta yi masa nacin mota sai yace ta bari sai birthday din nata. "Ke ba iya motar ma kika yi ba. In na baki me zaki yi da ita?" Tace "koya min zakayi ai" yace "ni bani da lokacin koya miki mota akwai driving schools ki shiga ki koya a can". Sai da magrib ta gabato sannan muka tafi gida. A hanya Asma'u da Murjanatu ne kawai suke ta hirarrakin su amma ni da Sadauki kowa yana hira ne da zuciyarsa. Ni ina rarrashin tawa ne akan ta yarda da hukuncina a kan Sadauki, ina gaya mata cewa hakan shine abinda ya kamata gare ni, gare shi ga Subay'a, ga kuma zuriar dazamu haifa in muna da rabo. But my heart was weeping tana ganin banyi mata adalci ba. Tana gaya min hukuncina ni zaifi affecting ba wai shi wanda nayi wa ba.

Muna zuwa gida yayi packing a kofar gida su Asma'u sukayi masa sallama suka fita, ina hango Subay'a ta fito da gudu sai kuma ta tsaya tana kallonsa sai ta juya ta koma gida. Ya juyo yana kallona, nasan maganar da zaiyi min kuma kirjina bugawa yake da karfi ina tattaro courage din amsa masa, yace "baki bani amsa ta ba Diyam. In kin amince min ina son zanje gurin Kawu Isa" na juyo ina kallonsa, ina tunanin irin smartness ne Sadauki. Gurin Kawu Isa. Yasan a yanzu in ya nemi aurena a gurin Kawu Isa da gudu zai bashi ko dan ya kara bakantawa Alhaji Babba rai tunda har yanzu basu shirya ba. Sai kuma nayi tunanin hakan da Kawu Isa zaiyi shi zai kara rusa yar guntuwar zumuntar da take tsakanin uncles dina guda biyu. Sai nace "ina son aurenka Sadauki. Zan iya cewa shine greatest burina a yanzu. But, ina son muyi shi akan dai dai. Ina son muyi shi ta yadda nan gaba ba zamu zo muna nadama ba" yace "nadama kuma? Akan me zamuyi nadama?" Nace "have you thought about maganar da mukayi ranar nan? Akan forgiveness?" Sai ya dauke kansa gefe yana kallon waje nace "nima da akayi wa laifin nan na yafe musu. And I felt good lokacin da na yafe din ji nayi tamkar na dauke wani abu ne mai nauyi daga zuciyata. Wannan feeling din shi nake yi maka kwadayi. And Subay'a, Æ´ata ce at the same time Æ´ar Saghir ce duk yadda bana son Saghir bazan taba cewa ba shine ya haife ta ba. She will come in between us ko da munyi auren ma she will never forget cewa kai ka rufe mata mahaifinta and that may affect me nima a gurinta zata iya tunanin da sani na akayi komai" yace cikin dacin murya "I didn't lock up her father. Shi yayi signing takarda da hannunsa babu wanda ya tilasta masa" nace "but intentionally ka bar masa ai. Kuma kudin ka ne. You can just walk to the court a yanzu kace ka yafe masa a d that will be all" ya girgiza kansa yace "you seem to be forgetting something. Ba kudina ne kadai yake rike da your precious Saghir a prison ba. Ko drygs din ma ni na daka masa a dakin sa?" Naji zafin kalmar 'precious Saghir' din daya fada amma nasan kishi ne yake yi, sai nace "ba kai ka saka masa ba. Abokinsa ne yayi framing dinsa amma yayi framing dinsa ne saboda ya samu damar guduwa da kudinka da Saghir ya dauka, so it circles back to you. Please Sadauki, you have the power, you can set him free. Saghir yayi nadama. I saw it in his eyes sanda naje gurinsa a prison" yace "nadama? Baki san hausawa sunce kowa ya tuba dan yuwa babu lada ba? Ko zaiyi nadama Saghir ba yanzu ba" nace "Sadauki, Saghir fa....." Sai ya daga min hannu yace "stop, Please stop mentioning his name" sai na fahimci wani abu. Duk maganar da nake Sadauki ba jina yake yi ba, kishi ya rufe masa ido gani yake yi kamar saboda ina son Saghir ne nake so ya fito da shi. Ban kuma cewa komai ba sai na dauki purse dina na bude kofa na fita. Ina jin yana kirana amma ban juyo ba duk kuwa da cewa ji nake tamkar tawa zuciyar tafi tashi jin zafin hakan.
Chapter 83 · 0% Book details