Sashe 40
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar wata laraba, Saghir ya dawo kamar yadda ya saba dawowa ni kuma na zuba abinci na kai masa kamar kullum. Ina shiga dakin naji wannan familiar warin dan haka na tabbatar yau ma a bugensa yake. Na ganshi a kwance daga shi sai singlet da gajeren wando yayi dai dai akan gado, na lallaba na ajiye abincin na juya zan fita kenan sai ganinsa nayi a gaba na yana kallona kasa kasa fuskarsa da murmushi, sannan cikin irin voice din da bazan manta ba yace "wai ke kullum sai ki shigo min daki kina wani lallabawa a tsorace kamar dakin dodo, ko ni dodo ne?" Ban bashi amsa ba na chanja hanya sai naji ya damko hannuna ta cikin hijab dina ya dawo dani baya, na fara kokarin ture shi nace "don't touch me" ya maimaita cikin kwaikwayon muryata "don't touch me, shikenan dai kullum don't touch me sai kace wani abin tabawar ne a jikin nata, bayan bata da komai haka aka kawo ta gidan nan, kirjin ma sai dana mammatso su sannan suka fito" naji hawaye yana bin fuskata, na ture shi na bude kofa da sauri na fita palo amma kafin inyi nisa ya kuma kamo hijab dina da karfi ya finciko ni baya, naji bayana ya amsa da karfi na saki kara. Ya zare hijab din yana cewa "ke dai kiyi ta yawo da wannan dogon abin, ke ko zafi ba kya ji?" Na sakar masa hijab din na durkusa a kasa saboda bayana da naji ya kasa mikewa straight, Sai kuma idonsa ya sauka kan dogon gashina da ya zubo har saman bayana ya bude ido yace "well well well, what do we have here. I always have a thing for mata masu dogon gashi" sai ya nannade hannunsa a cikin gashina ya dago ni tsaye da gashin, naji tamkar fatar kan gabaki daya yake cirewa, ba shiri na saki bayana dana rike na kama kaina na saki kara. Ban kuma jin abinda yake cewa ba saboda azaba sai jin muryar uwani nayi tana cewa "Saghir baka da hankali? Ka sake ta mana, baka ganin halin da take ciki?" Sai kuma ya sake ni, uwani tayi saurin rike ni muka bishi da kallo ya tafi dakinsa yana harhada hanya.
Uwani ta kama ni ta kaini dakina tana yi min sannu. Na durkusa a kasa inajin kaina kamar zai tsage da baya na shima ya rike. Sai naga ta dauko wayarta tana waya amma bana jin me take cewa na dai ji ta ambaci sunana da sunan Saghir. Daga nan baccin azaba ya dauke ni. Sanda na farka cikin dare ni kadai ce a dakin a kwance a kan gado, wani irin mugun ciwon baya ne ya tashe ni nakasa mikewa ma tsaye ballantana in fito in nemi taimakon wani, haka nayi ta murkususu ni kadai akan gado ina karanto duk adduoin da suka zo bakina. Ban samu bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.
Sai da gari ya fara haske sannan na lallaba na tashi nayi sallah, nayi azkar sannan na kuma kwanciya akan sallayar na sake komawa wani baccin. Lokacin dana sake farkawa sai naji ciwon kan ya lafa sosai sai bayan ne har yanzu amma shima ba kamar cikin dare ba. Na fito na duba agogo naga 20:32, nasan already Saghir ya fita dan haka na sauko kasa gurin uwani. A zaune na same ta da jakar kayanta a gabanta ga mayafinta a kusa da ita. Na tsaya ina kallon ta nace "wannan kayan kuma fa? Wanki zaki bayar?" Tace min "zauna Diyam" na zauna a kusa da ita tace "dazu da sassafe mijinki ya shigo nan, yazo ya same ni ya kare min zagi tas wai ni munafuka ce na hada shi da mahaifiyarsa. Yace min in fita in bar masa gidan sa kar ya dawo ya same ni" na mike tsaye zan fara masifa "lallai ma Saghir din nan, yanzu ke din zai yiwa wannan rashin kunyar?" Tace "ni dai abinda nasan nayi shine jiya da naga yana neman halaka ki na kira uwarsa, ni kuma abinda yasa na kira ta shine naga halin da kike ciki wai ko za'a zo a kaiki asibiti ko kuma a turo ma'aikaciyar lafiya ta duba ki, ni bansan me ta kira shi tace masa ba shine yazo yayi min wannan diban albarkar" nace "kira hajiyan to sai mu gaya mata abinda yayi, ita zata san abinda zata yi akai" tace "hmmm. Ai yana fita ita din na kirawo, tunda tun farko ai ita ce tace inzo in zauna din, amma dana gaya mata abinda yace sai cewa tayi in tafi can gidan kawai tunda yace baya son zama na anan din. Tace zata samo wata ta turo miki take kula dake" naji raina ya kara baci, hawaye yana bin fuskata nace "wannan wacce irin rayuwa ce, yanzu ace mutum babu yadda za'ayi yayi abu ba daidai ba a gyara masa sai ya zama laifi. Yanzu jiyan da ace ba kyanan Allah ne kadai yasan abinda zaiyi min. Ni ba zan zauna ba uwani, kina tafiya nima binki zanyi, bazan zan zauna ya kashe ni ba" uwani tace "a'a, ba zaki bini ba Diyam, ina tafiya dake cewa za'ayi nazo na kashe miki aure. Ni dai yanzu in naje zan gayawa mahaifiyar ki halin da kike ciki, itace take da hakkin zuwa ta tafi dake".
Ina ji ina gani uwani ta dauki jakarta ta fita, na raka ta har bakin gate ina hawaye tayi sallama da mai gadi wanda har sun saba dashi sosai, na tsaya ina kallonta har tayi nisa sannan na dawo cikin gida na rufe kofa. Na kwanta akan kujera ina tunanin wannan wacce irin kaddara ce ta hau kaina, wacce irin tarbiyya Saghir zai yiwa yayan mu bayan shi kansa ba tarbiyyar ce dashi ba? Ina nan kwance dai har yunwa ta kamani na tashi na shiga kitchen sai na tarar ashe uwani ta ajiye min dumamen tuwon jiya dan tasan ina so. Na dauko na dawo palo na zauna ina ci kawai naji ciwon bayan ya dawo and this time yafi na dare karfi. Yayi ya lafa ya sake dawowa kamar bayana zai rabu da jikina. A haka azahar ta same ni, la'asar ma tazo, sai dari ya fara duhu. A lokacin ciwon bayan ya hade har da cikina da mara ta. Na lallaba na koma sama ina tunanin wannan wanne irin ciwo ne haka tunda ni dai cikina ai bai isa haihuwa ba ballantana inyi tunanin ko nakuda ce. Bayan nayi sallar magrib ne kuma sai na kasa kofa tashi daga kan sallaya ta saboda azabar ciwo, ban taba addu'ar ganin Saghir ba sai a wannan rana na ringa addu'ar Allah yasa ya dawo da wuri ya kaini asibiti, wannan wanne irin ciwo ne haka? Ga yunwa dan tun tuwon safe ban kuma cin komai ba, ga babu waya a hannuna ballantana in kira in nemi taimako.
Shiru shiru babu Saghir babu labarin sa tun ina duba agogo har na daina. Sai kuma kamar daga sama naji tsayuwar motarsa, na daddafa da kyar na mike amma ina tsayuwa sai naji kamar an bude famfo ruwa yana fita ta kasana, nace na shiga uku ni Diyam fitsari nake a tsaye ko me?
Tun daga yanayin yadda yayi packing nasan cewa yau ma ba kalau yake ba, ina jin motsin shigowar sa palo sannan naji ya hawo sama, sai dai banji ya bude dakinsa ba. Na jima ina tattaro karfina sannan na fara bin bango na fita daga dakin. A palon sama na same shi, ya cire rigarsa ya jefar a gefe, ya kure ac ya kwanta a kan carpet. Da rarrafe na karasa inda yake nayi masa magana "Saghir, Saghir" shiru, na dan jijjiga shi, nan ma babu alamar motsi a tare dashi. Da daga hannunsa naji ya saki. Banbancinsa da gawa shine kawai shi yana numfashi. Na fara kuka "hamma Saghir ka taimaka min zan mutu, wayyo Sadauki" amma da wani ciwon ya sake tahowa sai na nemi kukan na rasa. Lallai wani abin yafi gaban kuka.
Na tuna da maigadi a waje dan haka nayi kokarin ganin ko zan iya zuwa gurinsa ya samo min taimako, duk da cewa ba makota ne damu ba. Amma tashi ya gagare ni, kamar kafafuwana sun daina aiki. Na durkusa na kankame kujera yayinda wani irin nishi wanda bazan iya rikewa ba tazo min, ina ji har dan jaririn ya fito daga jikina, na sauke wani numfashi jikina sharkaf da gumi duk da acn da take palon. Na saka hannu na dauko shi, the smallest most cutest baby dana taba gani a rayuwata. Komai nasa irin na babansa ne except dan karamin É—agaggen bakin sa da yake irin nawa, nayi murmushi ina jin sonsa for the first time yana huda zuciyata. But baya kuka, baya numfashi, aren't babies suppose to cry in aka haife su? Na jijjiga shi, "wake up little soldier" shiru, na dora bakina akan nasa ina hura masa iska irin yadda naga anayi a film amma shiru, na saka fingers dina guda biyu ina danna masa little kirjinsa shima shiru.
Wani ciwon ne ya sake dawo min, babu shiri na jawo rigar Saghir da ya ajiye na dora babyn akai na koma fagen fama har na haifi dan uwansa. Na dauko shi shima ina kallon fuskarsa, kamarsu daya da dan uwansa kamar an tsaga kara. Na dan jijjiga shi da dan saurin karfin daya rage min sai naga yayi motsi ya danyi kuka kadan sai kuma yayi shiru. Na ajiye shi kusa da dan uwansa ina feeling very dizzy, a lokacin ne na lura da jinin da yake malala akan tiles din palon. Na koma na kwanta kusa dasu a ina kallonsu. And it occurred to me that karshen rayuwata kenan, sai naji dadi saboda ina ganin nayi shahada na samu kyakykyawan karshe, my only regret a lokacin shine mutuwa without seeing Sadauki again.
Not edited
[2/3, 9:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: â¤ï¸ DIYAM â¤ï¸
By
Maman Maama
Episode Thirty Four : My Savior 2