← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 112

Sashe 55

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana zaune a bayan katon table din gaban sa, as majestic as ever, bai ko dago kai ya kalle ni ba yaci gaba da rubutu a takardar gabansa ni kuma ina tsaye sai daya gama sannan ya dago fuskarsa blank yace "welcome Madam, have a seat please" naji kamar in juya in fita daga office din, nayi nadamar dana sani banzo ba amma ina bukatar amsa, ina bukatar ji daga bakinsa cewa ya manta da first twenty years of his life. Na zauna a kan cussion chairs din da suke jere a office din. Ya mike tsaye, sai naga ya kara cika min ido da kwarjini da girma baki daya ya zagayo ya zauna a kujerar gaban table dinsa sannan yace "kince Alhaji Muhammadu ya turo ki akan wani negotiation, ina jinki" naji wani sabon bacin rai, ni na ma manta abinda ya kawo ni kenan, sai kawai hawate ya fara bin fuskata. Nace "abinda zaka ce ma kenan? Irin karbar da zakayi min kenan? Sadauki nice fa Diyam, how can you even......call me Madam?" Sai ya mike tsaye ya juya bayansa ya saka hannu a aljihu yace "menene sakon da Alhaji yace ki fada min?" Sai na mike na nufi kofa da sauri ina goge hawayen fuskata, bai ce min komai ba har naje na kama kokawa da kofa amma taki budewa, na juyo ina kallonsa sannan yace "ba'a fita daga office dina sai nayi wa mutum izni" sai na dawo da baya da sauri na dauki wasu magazines na motoci na jefa masa, na debo tarkacen files din kan table dinsa suma na yi ta dukansa dasu har takardun suka tarwatse a gurin amma ko motsawa baiyi ba, na durkusa a tsakiyar gurin na kama kuka sai ya dawo ya zauna akan kujera yace "menene sakon da zaki gaya min?" Sai dana gama kukana sannan na tashi na zauna na goge fuskata nace "why? Sadauki why? Me yasa kame treating dina haka?" Yace "ya kike tsammanin zanyi treating mayar employee na?" Nace "shikenan? Matsayina kenan? Matar employee dinka? Me yasa ka dauke shi aiki ma? A ina ka sami wannan kudin kuma? I need answers Sadauki, I need to talk to Sadauki not this Mr Abatcha" yace "zaki samu answers dinki in due time. Now me Alhaji Babba yace?" Na goge hawayena nace "nasan kasan bashi da kudi yanzu, bashi da kudin biyanka ko da kuwa kotun koli zaka kaishi, dan haka I think you are just wasting your time" yace "really? To tunda bashi da kudin biya na fili na da gadona sai ya shirya zuwa prison for it. Kullum takamarsa kenan, kullum maganar sa itace zai saka a rufe ni, lokacin yana da kudi ni kuma bani dashi. Ki je kiyi masa albishir da cewa the table have turned, yanzu nine zan rufe shi" na bude ido ina kallonsa nace "you don't really mean that, me zakayi da kudin? Me zakayi da filin Sadauki look at this" na fada ina nuna office din nasa "zaka iya siyan hundreds of wannan filin, kafi karfinsa yanzu" yace "Baffa ne ya siya min remember? I was suppose to build us a house a kan filin nan, gidan mu ni da ke da yayan mu remember?" Sai kuma ya mike ta sake juya bayansa yana kallon window. Mun jima a gaka sannan nace "kayi tunanin abinda Baffa zai so, Alhaji Babba yayansa ne uwa daya uba daya ba zai so ya ganku a court dakai dashi ba, ba zai so yaga ka rufe masa dan uwansa akan kudi ba" ya juyo yana kallona yace "kamar yadda ba zai so a cire ki daga makaranta exactly 40 days bayan rasuwar sa ayi miki aure ba, kamar yadda ba zai zo a siyar da abinda ya kwashe rayuwarsa yana building abar iyalinsa da hamma ba" sai yakuma juya wa sannan yace "kamar yadda ba zai so a raba mu ba" na runtse idona ina jin wound fin zuciyata yana dawowa sabo, kewar Baffa na tana lullube ni, mun jima haka sannan yace "tell Alhaji Babba nace yana da options guda biyu, na daya shine ya bar mana gidansa da yake ciki tunda shi kadai ne yanzu abinda ya rage masa, na biyu kuma shine ya tafi prison for the rest of abinda ya rage na rayuwarsa"

Na mike tsaye, "Sadauki, ubangiji ma yana son rama sharri da alkhairi, kamar yadda kayi wa inna, dan Allah ka bar maganar nan, Allah ma daya halicce mu muna yi masa laifi kullum amma idan muka durkusa muka roke shi gafara sai ya yafe mana" ya juyo yana kallona, his eyes shining, yace "then tell him yana da third option, yazo ya durkusa ya roke ni gafara, ya saka gwuiyoyinsa a kasa ya roke ni in yafe masa kamar yadda na saka guiwowina a kasa na roke shi ya bani aurenki ya hana ni, ya durkusa kamar yadda na durkusa na roke shi kar ya aura miki that monster he calls a son amma duk da haka ya aura miki shi. Yes, I want him to cry and beg kamar yadda nayi in yaso in naki hakura duk da yayi haka sai yaji shima irin yadda naji".

Sadauki yayi tsauri da yawa ko? Lol

Not edited
[2/14, 10:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Three : Heartless
Raina ya kara baci, ina mamakin anya kuwa wannan Sadauki nane? Sadaukin da na sani will never do that amma kuma sai nayi wani tunani. Yes, Sadauki yana da kirki da kyawun hali sosai amma bashi da yafiya, musamman idan akan abinda ya shafe ni ne Sadauki bai taba daga kafa ba ko da kuwa waye ya taba nin indai ba Inna ko Baffa ba, na tuno ranar daya doka wa yaya Mukhtar ball aka a gaban Inna. Sadauki bashi da tsoro ko kadan tun a lokacin da bashi da komai ma, ballantana kuma yanzu da yake da masu garin.

Nace "abinda kake so kenan? Abinda kake after kenan? Revenge?" Ya girgiza kai "this is not revenge, this is justice" nace "wanne justice din ne kuma wanda yafi wanda Allah ya riga yayi? Shin in kayi haka Sadauki ka gode wa Allah kenan? Kaga kuwa halin da Alhaji Babba yake ciki a yanzu? Ka kuma duba kaga halin da kai kake ciki a yanzu, kai kanka ka fada, the table have turned, menene kuma saura? Shin in ka yafe wa Alhaji Babba mai zai ragu daga jikin ka? Sai ma daraja da hakan zai kara maka a gurin ubangiji. Yanzu in ya siyar da gidansa ina zai kai iyalinsa?" ya bar inda yake tsaye ya zagawa gurin kujerar sa ya zauna yace "sai su dawo gidan ku ku zauna tare, ai naga kuna da bene, sai su zauna a sama ku kuma a kasa" na saki baki ina kallonsa sai ya danna wani button a jikin table din sai naga kofar dana shigo ta bude, ya kalle ni yace "goodbye, Diyam" na tsaya kawai ina kallonsa ina girgiza kai, I can't believe Sadauki yayi tauri har haka, sai na je na tsaya a gaban table dinsa nace "I don't like this Mr Abatcha da nake gani a gabana, I want my Sadauki back, I want my brother back" sai na juya da sauri na bar office din.

Ina jin matar nan ta waje tana yi min magana amma ban ma fahimci abinda tace ba ni dai na gyada mata kai kawai na fita da sauri. Da saurin kuma na karasa wajen gate na tari abin hawa na shiga muka tafi. Sai da muka bar gurin sannan na saki kukan da nake rikewa, ma dauka hawaye ne kadai nake yi bansan ya fito fili ba sai da naji drivern yace "yammata kiyi hakuri, komai na duniya mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba'ayi ba" a goge hawaye na ina jinjina maganar sa, watarana zanga kamar ba'ayi ba? Yaushe?

Sai dana je gida sannan nayi realizing wani abu guda daya, ni da na tafi gurin Sadauki da niyyar samun answers amma ban samu ko daya ba sai karin tambayoyi da na debo wa kaina. Na sani Alhaji Babba ya zalunce ni kuma ya zalunci Sadauki kuma har cikin raina ban damu ba in wani abin ya same shi a saboda abinda yayi, abinda na damu dashi shine Sadauki, I don't like this person he as turned to bana son wannan hanyar da yake tafiya a kai. Ni da zai aje duk wannan kudin nasa ya koma former Sadaukin da na sani da sai nafi jin dadi.

Na biya na dauko Subay'a sannan muka karasa gida. Muna zuwa na shiga daki na hada mana kayan mu ni da ita a akwati na chanza mata kaya muka fito. Mai gadi yace tafiya zakuyi ne haka Hajiya?" Nace "cikin gari zamu shiga baba iliya, sai Sunday zamu dawo" ya taro mana abin hawa ya saka mana kayan mu muka tafi Subay'a tana ta murna.
Chapter 55 · 0% Book details