← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 112

Sashe 59

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na tarar da lodin kayansa a palo, na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana shirin wanka, na dauko abincin da nayi masa na kawo palon sama na ajiye sannan na koma kasa muka zuba ni da murja muna ci tace "ke ba zaki tafi gurin mijin ki ba ya dawo daga tafiya? Ke ana neman mijin ke kina wulakanta naki?" "Humm" kawai nace mata sai ga kira kuwa Subay'a tana yi min inzo inji Daddy. Yana zaune a kujera ya hade rai "ki zo ki zuba min abincin tunda ba zakiyi min wankan ba" bance komai ba na zuba masa na kawo table gabansa na ajiye masa. Yace "wai ke ciwon rashin magana ne ya same ki? Na fi so ina fada kina mayar min yafi dadi" nace "ba ciwon rashin magana bane ba, Æ´ata ce ta girma shi yasa nake shiru a gaban ta" yayi dariya yana kallon Subay'a data zauna ta zuba mana ido. Na juya zan koma kasa sai ji nayi yace "kai! Matar nan wani duwawu naga kina yi fa" nayi saurin kallon Subay'a naga tana dariya sai kawai na girgiza kai na tafi.

Muna kasan Subay'a ta jawo wani karamin akwati da kyar, murja ta tashi ta taimaka mata suka sauko dashi tana cewa "Mommy kinga kayan da Daddy ya siyo min" tana ta bubbuda wa, kayan sawa ne masu kyau da takalma, sai toys, murja tana ta yabawa, sai kuma Subay'a ta koma sama da gudu sai gata da karamar travelling bag mai kyau ta kawo min. "Inji Daddy, wai irin kayan da turawa suke sakawa ne ya siyo miki kema kike sakawa. Ki koma irin su" na bata rai nace "to sarkin surutu" na karba na ajiye, murja ta dan dake ni tace "tashi zaki yi kije kiyi godiya sosai" na mike na tafi amma sai nayi kwana na shiga dakina nayi kwanciya ta.

Sai bayan magrib ya shigo dakin yana kallona ina ninke sallaya yace "zan fita, zan tafi zance" na dauke kaina nace "ba gidan Alhaji ya kamata kaje ba? Ka gaishe su kuma kaga abinda aka yiwa gidan?" Sai kawai naga yayi murmushi yace "au kishi kike dan zanje zance ko?" Na zauna a bakin gado nace "Saghir, na riga na gaya maka tun kafin kayi tafiyar nan ni ko mata goma zaka aura ba zanyi kishin ka ba. Ni da son samu nane ma hudu nake so kayi, yadda zaka bani takarda ta in kara gaba" ya karasa shigowa yana cewa "wato kin ganshi ko? Alhaji ya tura ki kin ganshi ko? To bara kiji, in shi yake zuga kima ki gaya masa, auren ki yanzu na fara. In kinga na rabu dake to mutuwa nayi" ya juya ya fita.

Ranar da wuri na yiwa murja sallama na hau sama tana tsokana ta "wato miji yazo shine zaki tafi turaka ko?" Nayi dariya kawai na tafi, na shirya Subay'a na kwantar da ita sannan nima na shirya na rufe kofa ta nasa key nayi kwanciya ta. Cikin bacci naji karar wayata, na dauka na ga Saghir ne sai na saka ta a silent na juya na cigaba da bacci na, sai kuma naji shi yazo yana knocking, ko kallon kofar banyi ba har ya gaji yayi tafiyar sa. Da sassafe ya bar gidan, a raina nace "Allah ya raka taki gona".

Da yamma sai ga Mama tazo, ni na dauka zuwa tayi gani na sai da naji ta kama yi min fada sannan na fahimci Saghir ne ya kai kara ta. "Diyam me kike nema wa kanki? Kin manta abinda annabi ya fada cewa mata sunfi yawa a wuta? Kuma mafi yawansu sun shige ta ne sakamakon rashin bin aure? Abinda kike so kenan? Wuta kike so ki kai kanki? To wallahi ki nutsu kiyi wa kanki fada. Ganin Sadauki ya dawo ne zaki kuma dorawa kanki kulafucinsa ko? So kike a lahira shi Sadaukin da kike yi saboda shi idan ya aikata aiyukan alkhairi ya kasance a aljanna ke kuma kina wuta saboda shi?" Nace "Mama ni ba dan Sadauki bane ba, Sadaukin da ko kula ni baya yi?" Tace "to ya zaiyi ya kula ki? Matar aure ce fa ke. Ke ai har yanzu ba hankali ne ya ishe ki ba shi kuwa da hankalinsa. Saghir yace shi yana sonki, yana son zama dake, me yasa ke ba zaki so shi ba? Shima Sadaukin nan fa dole watarana aure zaiyi, yadda yake da kudin nan ma sai ki ga ya auri hudu a rana daya. In haka ta faru kuma ya zakiyi?.

Sai dare Saghir ya dawo gida. Yana shigowa palo murja ta gaishe shi ya hade rai yace "ki shirya gobe ki koma gida" tace to sai ya wuce sama. Murja ta kalleni pleadingly, ni kuma na daga mata kafada. Kamar bazan tashi ba musamman ganin ko kallon inda nake baiyi ba kuma dai sai na tashi na bi bayansa. Ina shiga dakinsa naga yana kokarin cire kaya sai na kama masa ya cire nayi hanging rigar sai yace "Mama tazo gidan nan kenan" na rike kugu nace "tunda ka kai kara ta ba dole tazo ba?" Ya zagayo hannayensa a waist dina yace "naga kina neman ki kaini lahira ne shi yasa na nemo taimakon gaggawa" ya shafa fuskata yace "you really are beautiful" na ture hannunsa nace "bararojin kuma?" Sai yayi dariya yace "wai baki manta ba, ai bararoji suna da kyau so it was a compliment" ya saka fuskarsa a cikin gashina yana shakar kamshinsa yace "tell me duk abinda kike so inyi miki" nace "ka bar murja ta cigaba da zama a gidan nan" yace "done. Sai kuma me?" Nayi shiru, yace yana zuge zip din rigata "ba zaki ce in fasa aure ba? Say it and it will be done" na sake shiru na rufe idona ina jin daci a bakina yace "kice 'hamma Saghir Please kar kayi min kishiya" bance komai ba ya daga ni ya dora akan gado, hawaye ya fara bin fuskata yace "kice hamma Saghir ina sonka" nayi shiru sai yayi ajjiyar zuciya yana hawowa gadon yace "watarana zaki fada, ina nan ina jira".

Ina kallon sa yana ta shirye shiryen sa, ni ko su inna ban gayawa zancen auren sa ba sai da suka ji daga gidan Alhaji Babba, Hajiya ta kira ni a waya "yanzu Diyam da gaske Saghir auren nan zaiyi? Shi yanzu kudin da zai kashe gurin auren ya bawa Alhaji su mana ko shago ya bude ya fara dan kasuwanci. Yanzu kina ganin kofar gidan nan ma da kyar Saghir ya saka ta shi ko a jikinsa ma wannan cin mutuncin da akayi wa gidan nan" "sai hakuri Hajiya" shine kawai abinda nace mata.

Har dani akaje aka kai lefe, aka saka rana akayi komai aka fara hidimar biki. Kowa sai mamaki na yake yi wai ni ko a jikina mijina zaiyi aure. Shi kuma Saghir kullum sai ya ce ince masa ya fasa aure ni kuma naki fada. Sai yayi fushi ya daina yi min magana sai kuma dan kansa ya sauko. Sadauki kuma bai kuma bi ta kaina ba, sai dai yakanje ya gaida Inna, kudin gidan gona kuwa account ya bude wa Asma'u ake zuba mata a ciki sai dai kawai su dauko suyi amfani da abinsu".

Satin bikin Saghir yana kamawa Hajiya ta kirani tace ita fa babu wani taro da zata yi, ni kuma sai nace zanyi walima ranar kawo amarya anan gidan Saghir, yadda kowa yazo in an kawo amarya sai ya ganta. Saghir yana ji ya fara fadan wai za'a bata masa gida. Ranar kafi suka zo suna ta daddaga hanci, na saka murja ta nuna musu spare dakin da yake sama suka ce "dama yace ba sai anyi mata komai ba ya saka komai a gidan, gadon ma da cewa yayi kar ayi mune muka ce sai anyi saboda kar a mata gori". Ina jinsu suna gulmar "wannan yar karamar yarinyar ce uwargida?".
Chapter 59 · 0% Book details