← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 112

Sashe 111

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saghir ya juyo yana kallon Subay'a, yana kallo Sadauki ya kama hannunta ya bude mata kofa ta shiga mota sannan shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da pregnant Diyam. Yayi sauri ya rintse idonsa tare da dafe kansa yana jin hawaye yana zuwa idonsa. Bai dauka har yanzu Diyam tana da gurbi a zuciyarsa irin haka ba, ya dauka ba zaiji komai ba inya ganta musamman saboda kokarin da mr Abatcha yayi masa, amma ita zuciya bata da linzami dole ya ja baya dasu ya daina ganinsu, ko kuma abinda yaji din yana da alaka da yadda Diyam din ta zama? Irin kyawu da cikar halittar da tayi? Wai hakan na nufin da ace ya kula da ita tsahon shekarun da suka yi a tare da irin haka zata zama kuma maybe da zata so shi? Lallai gaskiyar hausawa da suka ce tun ranar gini tun ranar zane, shi kuwa nasan ginin ya bushe dole sai dai ya hakura da zanen ko kuma ta sake sabon gini, sabon ginin wata rayuwar.

But with who? Wannan wata tambaya ce for another time. Maganar da Subay'a ta fada ta dawo masa zuciyarsa "zan kawo maka ziyara gidan ka" wanne gidan? Shi fa yanzu ko gidan kansa ba shi da shi, wayake ma maganar gida, shi ko kwandala bashi da ita. Bashi da komai sai freedom dinsa, kuma ya dauki freedom din nasa ya zama another chance at life. Chance din kuma da insha Allah zai yi amfani dashi sosai yadda har sai mutane sunyi mamakinsa. Yadda har sai iyayensa sunyi alfahari da shi. Iyayen da a wancan lokacin ya wofantar ya wulakanta, abinda yake tunanin shine dalilin zuwansa inda yaje ba wai Diyam ba.

Maganar mai napep ce ta dawo dashi hankalinsa, yace "yallabai munzo" ya leko dakansa yana kallon gurin yace "nan ne?" Mai napep yace "nan dai yayi min kwatance, yace jaen layin shago tara, gashi nan kuma har mun kusa fita daga layin tunda mun fara hango diga. Sai dai ka sauka ka tambaya" Saghir ya sauka yana kallon gurin, not that bad. Mai adaidaitan ya miko masa dari biyar yace "dubu biyu ya bani, ga dari biyar ka sha ruwa kai ma" Saghir ya karba harda yi masa godiya sannan ya tafi gurin wasu mutane su uku da ya hango a kasan bishiya ya gaishe su yace "dan Allah tambaya nake yi, gidan Alhaji Babba, bai dade da dawowa unguwar nan ba" duk suka ce basu sani ba, yayi gaba ya cigaba da tambaya amma babu wanda ya sani sai ya juyo ya fara retracing ta inda suka shigo yana yi yana tambaya, ga rana gashi dama jikin sa duk babu karfi.

Da kyar ya samu wanda yace "inda akayi biki watannin baya?" Da sauri Saghir yace "eh" sai aka hada shi da yaro suka koma can inda ya baro, suka je har gaban wani gida sannan yaron ya nuna masa ya juya. Ya tsaya yana kallon gidan, a tsahon rayuwarsa bai taba tsammanin duniya zata yi juyawar da har nan gidan zai koma shine gidan baban shi ba, gidan ma kuma gidan haya, gidan hayar ma kuma Diyam ce ta ke biya masa.

Ya shiga soro yayi sallama, Hajiya ya hango ta fito daga wani guri daya ga kamar kitchen tana amsa sallamar hannunta rike da wuka tana goye da wani yaron da bai sani ba a bayanta. Ta yarda wukar tana kiran sunan Alhaji, Alhaji ya fito, Hajiya yalwati ta fito, sai ga yaran gidan suma sun fito daga wani daki duk suna binsa da ido. Shi ya karasa shigowa, ya tafi gaban mahaifinsa ya durkusa amma sai ya kasa gaishe shi sai kuka ya kwace masa. Alhaji ya sunkuya gabansa ya jawo shi jikinsa ya rungume shi shima yana hawayen yace "bansan yau zasu fito da kai ba Saghir, da ko ba zan iya zuwa da kaina ba da sai in gaya wa mahaifiyarka ta je ko ta tura aje a taho da kai" Saghir ya goge hawayen sa yace "Mr Abatcha ne yaje ai, dashi da Diyam da Subay'a" ya fada yana jin dacin zuciyar dazu yana dawo masa. Alhaji yace "madallah dasu. Allah yayi musu albarka ya jikan Usman".

Nan fa gida ya rude da murnar dawowar Saghir, dan ma yanzu duk yaran babu saura kadan. Hajiya Babba ce ta kama shi ta kaishi daki, Hajiya yalwati kuma ta dora masa ruwan wanka, alhaji kuma ya aika a siyo masa nama da lemo kafin a gama abinci. Babu laifi suna cikin rufin asirin su duk da cewa alhaji har yau bai kuma gwada kasuwanci ba amma matansa suna yan sana'o'in su sannan yayansa mata da suke aikin gwamnati suna kokari gurin taimaka musu sosai, haka ma surukan gidan lokaci zuwa lokaci suna aiko musu da kayan abinci ko kuma suttura.

A dakin Hajiya ya huta, naman da Alhaji ya siyo masa sannan yayi wanka ya chanja kaya zuwa wanda Hajiya ta ajiye masa akan gado. Sai ta kunto yaron bayanta ta mika masa. Kallo daya yayi masa yasan waye, sai kawai ya ajiye shi a gabansa ya sunkuyar da kai, tace "sunan babanku ne dashi, Jawad ake ce masa" yaron ya rarrafa da sauri yabi bayan Hajiya yana kuka alamar bai san shi ba.

Dakin da yake soro, wanda kuma yake da kofa a waje shi dama Alh yasa aka gyara tun sanda yaji labarin dawowar Saghir gida. Aka shimfida carpet aka saka katifa, wardrobe, da kuma standing pan. Nan ne ya koma dakin Saghir.

Kwanan Saghir biyar ya warware, duk da dai babu inda yake fita sai yan'uwa da suke ta zuwa yi masa murna. Inna ma tazo ita da Asma'u da Subay'a, suka kuma bar Subay'a anan tayi weekend tare da mahaifinta da kakannin ta. A ranar ne Alhaji ya kira shi dakinsa. Suka zauna sai ya dauko wata leda ya miko masa, Saghir ya karba ya bude sai yaga kudi a ciki, ya zaro ido "Alhaji kudi ai, kudin menene wannan?" Alhaji yace "kudi na ne, sauran kudin gida na ne da kuma abinda na samu daga gadon Usman, su nake ta ajjiye dasu da niyyar duk ranar da ubangiji ya sake baka dama a rayuwa ya saka ka fito daga prison nima zan sake baka dama in baka su kayi jari" Saghir yayi saurin girgiza kansa hawaye yana bin idonsa yace "Alhaji kar kayi haka, ka bani kudi sau ba adadi ina salwantar wa, kai ma kana bukatar kudin nan alhaji, kana da iyali kaima. Ka rike kudinka alhaji ka kula da kanka da matanka da kanne na" Alhaji yace "da wanne karfin Saghir? Ni ai tawa ta kare, karfi na ya kare, dan haka kai na dora wa wannan nauyin ka juya wannan kudin ka kula da kanka sannan ka kula dani da iyayenka da kannenka, kuma ka cigaba da kula dasu ko bayan rai na ne".

Saghir ya karbi kudin ya rike yana jin nauyi a zuciyarsa "anya kuwa akwai soyayya sama data iyaye?"

Alhaji yace "akwai kuma wata magana da nake so muyi. Ina so ka kawo karshen rashin jituwar da take tsakani na da danuwana, ina son ka auri Suwaiba" ya dago kai yana kallonsa, Alhaji ya gyada kai yace "ta inda ake hawa tanan ake sauka. Tunda kuka bata dan haka ku zaku gyara". Sai Saghir yaji Fauziyya ta fado masa a ransa. Bayan ya bata takardarta sun rabu, daga baya sai ta koma tana gaya masa cewa tana da cikinsa, ta kuma ce zata haifi cikin za kuma ta jira shi as long as bata samu miji ba har ya fito sannan kuma yana da sha'awar mayar da ita. Bayan ta haihu kuma ta kai masa babyn ya gani. And after seeing Subay'a rike da hannun Sadauki, baya jin zai kuma barin wata yar tasa a wani gidan. Dan haka indai Fauziyya bata yi aure ba to sai dai ya hada su ita da Suwaiba.

Wata daya bayan nan Diyam tazo yi musu sallama zata koma Oxford, England. Washegarin zuwanta kuma alert ya shigo masa. Ya bude ido yana kallon kudin cike da mamaki ya tafi da sauri ya nunawa Alhaji. Alhaji yayi murmushi yace "Diyam ta gaya min jiya, kudin da Kabir ya gudu dasu ne aka dawo maka dasu. Zabi kuma ya rage naka kasan me zaka yi dasu".

Abinda Saghir ya fara yi shine ya dauki kudin da Alhaji ya bashi ya sayi gida madaidaici amma me kyau. Ba shine ya tare a gidan ba, Alhaji Babba da iyalin sa ne suka tare. Sai kuma ya sayi karamin fili a kusa da gidan a matsayin nasa "sai in zauna a kusa daku yadda zanfi jin dadin kulawa daku" next sai yaje har gidan Kawu Isa ya durkusa ya bashi hakuri sannan ya nemi ya bashi auren Suwaiba. Sai kuma ya tafi gidan su Fauziyya itama ya nemi auren ta. Amma duk kan su yace sai shekara mai zuwa idan ya samu nutsuwa sosai.

Daga nan sai ya tafi kantin kwari, tsofaffin shagunan Alhaji wadanda wuta ta cinye babu komai sai ginin, shima ginin duk ya mutu an sace kwanukan. Cikin kwanaki kadan ya tayar da ginin su, yayi komai ya saro kayan duk da yasan Alhaji yana siyarwa ada da kuma kayan da yasan zamani ya zo dasu ya zuba a ciki. Sannan ya nemo tsofaffin yaran Alhaji wadanda suke kular masa da shagunan a da ya dawo dasu dan su suka san kan kasuwa, shi kuma ya zauna cikinsu dan shima ya fahimci harkar.

Watanni kadan abubuwa suka warware wa Saghir, ya hada kudin neman aure ya kai gida biyu aka saka masa rana watanni takwas masu zuwa za'ayi duk a tare, sannan kuma ya fara ginin gidan sa a hankali. Gidan da yake da yakinin zai zamanto tushen sabuwar rayuwa a gurin sa.

****************************
Chapter 111 · 0% Book details