← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 112

Sashe 27

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri na nufi inda muke zama in yazo, ji nake kamar inyi tsuntsuwa ko zanfi sauri. Tun daga nesa na hangoshi kuma na gane shi sannan naji dadin ganin sa sosai. He looks good, and that was all that matters to me a lokacin. Ina karasawa na lura da kayan jikinsa sababbi ne kuma masu kyau, he smells good too. Sai dai fuskarsa ce tayi betraying emotions dinsa dan idonsa ya fada ciki sosai kuma zagayen idonsa yayi baki alamun baya samun isashshen bacci. "Sadauki" na kira sunan sa da karyayyiyar murya, bai amsa ba sai murmushi da yayi min mai kokarin boye damuwarsa. Muka karasa zagayawa bayan dakin maigadi, Sadauki ya zauna akan ginin suckaway, wannan ya bani damar ganin gefen kansa inda akayi masa dinki. Na zauna nima a kusa dashi ina fuskantar sa kawai sai hawaye suka fara zarya a kumatu na, bai hanani kuka na ba sai ma ya miko min handkerchief dinsa na cigaba da kuka na, sai dana gama na share hawaye na sannan yace "dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ke din dama kuka baya miki wahala" nace "Allah yaji kan Baffa da Ummah" yace "ameen. Naje na kai musu ziyara kaburburan su. Suna kwance a sides din juna kuma ina fata da zaton suna aljanna a tare" sai naji dadi sosai a raina, dadin yadda naga ya dauki abin nima sai naji na samu courage din facing rayuwa a koya tazo min. Nace "kai kuma fa? Wanne hali kake ciki? A ina kake a zaune?" Yayi murmushi yace "ina gurin Alhaji Bukar (mutumin da yaya ladi take gurinsa) and they are treating me well, too well even. Ya gaya min cewa zai kaini gurin mahaifina, ya san shi ashe" na bude ido da baki "wow. Congratulations Sadauki, yaushe zaku je?" Ya girgiza kansa yace "I don't know. Ban san shi ba Diyam, bansan waye shi ba and for all I know zata iya yiwuwa ma bai san nayi existing ba, zai iya yayi denying dina yace ni ba dansa bane ba" Nace "amma ta yaya zaka sani in baka je ba? Nasan Sadauki na babu abinda yake tsoro just go kayi clearing doubt dinka and move on" ya gyada kai yana kallona yace "so I have your blessings kenan ko?" Nace "of cause you do".

Sai kuma na tambayeshi abinda yake raina tunda na ganshi "Sadauki me yasa kazo? Bayan abinda Inna ta tayi maka bayan yanzu babu Baffa kuma gashi ka samu wani mai rikon gashi kuma zaka je gurin babanka, me yasa kazo gurina? Ba ka gudun a wulakanta ka?" Ya dan bata rai yana kallona yace "me yasa ba zanzo ba to? For starters I love you, always have and always will. Na biyu duk abinda ya faru dani babu abu daya da yake laifinki dan haka baxanyi fushi dake akan abinda ba ke kika yi min ba. Na uku Baffa, a gurina darajar Baffa ta wuce in yi fushi da iyalinsa dan babu ransa, sannan........" Sai yayi shiru yana kallona, nace "sannan me?" Ya sauke idonsa kasa Yace "sannan lokacin da mukayi accident din, he looked at me straight in the eyes ya ce in wani abin ya same shi in kula daku ke da Asma'u".

Na sunkuyar da kaina inajin sabbin hawaye suna zubo min. Yace "amma bansan ta yadda zan iya kula daku ba Diyam, innar ku bata so na na sani, bansan ta yadda zan iya juyo da hankalinta ta soni ba tunda bansan abinda nayi mata wanda ya saka bata son nawa ba balle in daina. Diyam ina tsoron kar lokacin auren ki yayi in nema a hana ni akan dalilin da ni kaina ban sani ba, I don't think my heart can take that". Mun jima muna hirar yadda future dinmu zata kasance, sai daga baya yace "bara in tafi Diyam kar in jawo miki fada. I just want you to know cewa am okay, dan haka kema ya kamata ki rage wannan koke koken haka ki tsayar da hankalinki guri daya. And everything is going to be alright" nayi murmushi nace "ai na samu strength daga gurinka Sadauki, kayi sharing strength dinka dani" ya mike tsaye yana kallona yace "Aliyu shine sunan, Sadauki shine inkiyar, so ofcause am going to be alright". Muka yi sallama yana yi min alkawarin in sun saka ranar zuwa gurin babansa zai zo ya gaya min saboda inyi masa addu'a.

Shine a gaba ni ina binsa a baya, muna fitowa yayi hanyar gate ni kuma nayi hanyar cikin gida ina waigensa, a lokacin ne kuma aka budewa Alhaji Babba gate ya shigo gidan sukayi clear da Sadauki kafin Sadauki ya fita. Na kara sauri kafin yayi packing Ina jin bugun zuciyata yana karuwa amma ina kama handle din kofa naji muryar Alhaji Babba a baya na yace "Diyam, zo nan"

Not edited. In anga typos ayi hakuri Please.
[1/23, 10:35 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Four : Red Handed

Na juyo na ganshi a tsaye a gaban motarsa yana kallona, na dawo baya a zuciya ta ina karanto duk addu'ar da tazo bakina na durkusa a gabansa nace "gani Alhaji" ya nuna hanyar gate "waye wancan da na ganku tare?" Nayi shiru kaina a kasa "ya sunkuyo yace "ba'a koya miki in manya suna magana ba'a yin shiru a rabu dasu ba?" Na sake yin shiru ina jin hawaye yana taruwa a idona, ya kama kunnena ya murda, nayi kara na mike tsaye yace "waye wancan nace miki" cikin azaba nace "Sadauki ne" ya sake ni ya kwalla wa maigadi kira, baba audu ya taho dagudu ya durkusa a gabansa yace masa "wanene yace kake barin Æ´aÆ´an iska suna shigo min gida?" Dattijon ya kalle ni sannan yace "bansan baka so ya shigo ba Alhaji, da yake naga duk sanda tazo gidan nan yana zuwa gunta ne na dauka dan uwanku ne" Alhaji Babba yace "babu abinda ya hada mu dashi, daga yau in ka sake barinsa ya shigo gidan nan a bakin aikin ka. Ina fatan ka fahimta" yayi saurin gyada kai "na gane Alhaji, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba, ayi hakuri Alhaji".

Alhaji Babba ya juyo kaina yace "ke kuma muje gurin Amina ta gaya min idan da saninta kike shigo min da kattin banza cikin gida" na juya da sauri ina tafiya blindly, kafafuwana suna hardewa kamar zan fadi har na shiga dakin Inna na tarar da ita ita kadai da charbi a hannunta tana lazumi, ta dago tana kallona da mamaki "ke kuma lafiya kamar wadda aka koro? Me ya faru" ban bata amsa ba Alhaji Babba ya shigo dakin, ta mike da sauri dan hardly ne ka ganshi ya shigo cikin main gidan saboda part dinsa a waje yake. Yana nuna ni yace "kinsan Sadauki yana zuwa gurinta?" Ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta fara tafa hannu tana salati "Diyam? Yanzu sai da kika jajibo mana yaron nan har gidan nan? Wato duk abinda nake fada ta bayan kunnenki yake bi yake wucewa ko?" Yace "mai gadi yace min dama ya saba zuwa gurinta a duk sanda tazo gidan nan. Wato yar mitsitsiyarta da ita har ta fara jawo mana yaran banza marasa asali da tushe zuwa gida ko?" Inna tace "Alhaji kayi hakuri, anyi an gama insha Allah ba za'a sake ba. Yarinyar nan bata jin magana, babu yadda banyi da ita ba akan yaron nan tun kafin ta kai haka amma taki rabuwa dashi. Yadda kasan yadda Zainabu ta shanye marigayi haka shima yaron nan ya shanye Diyam" Yace "au kice min tafi ƙarfin ki kenan bata jin maganar ki" ya kuma kama kunnena, na saki karar azaba yace "ni in nayi magana ba'a tsallake ta a gidan nan, daga yau sai yau babu ke babu Sadauki" ya sake ni ya juya yana cewa "shi kuma duk sanda ya sake zuwa gidan nan sai ya gane bashi da wayo, sai na rufe shi naga wanda zai fito dashi, sai naga wanda ya tsaya masa a garin nan".

Bayan ya fita Inna ta bini da kallo ina rike da kunnena ina kuka, ta koma ta zauna a bakin gado tana kallona ina jiran ta dora daga inda Alhaji ya tsaya amma sai naji tayi tsaki tace "ba kya jin magana Diyam. Ke indai akan wannan yaron ne ba kyajin magana wallahi" ta dauke kai ta cigaba da jan charbin ta sai kuma tace "zo inga kunnen" na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline.

Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furicin da yayi akan sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amna gwara hakan akan abinda za'ayi masa in yazo din.
Chapter 27 · 0% Book details