← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 112

Sashe 14

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna tayi kukan kura ta riko shi, amma sai nayi sauri na rike hannunta har ya samu ya zame ya fice da gudu, ai kuwa sai tayo kaina, na ruga sai dakin Baffa na rufe kofa ina leken ta taga. Tayi ta banbamin fada tana debe wa Sadauki albarka "bakin mugu mai bakar zuciya. Allah ya isan sa, idan ya dake ta ina ruwanka? Dan uwanta ne, kai kuma fa? Marar asali" tayi tayi dai babu wanda ya kula ta, ta tashi Mukhtar ta bashi ruwa ya wanke fuskarsa amma sai ya kasa fita wai tsoro yake kar Sadauki ya kuma kamashi a waje. Haka ya koma daki har sai da na fito nace "kayi tafiyarka, babu abinda zaiyi maka ai ya ramamin". Kuma haka ya fita a tsorace amma Sadauki yana kan mota ko kallonsa baiyi ba. Tun daga ranar ko kallon banza yaya Mukhtar bai kara yi min ba.

Yana daga al'adata kullum da daddare dakin Ummah nake zuwa inyi kallo. Inna ta hana amma sai Baffa ya daure min gindi yace "ai homework Sadauki yake koya mata a can din. In kuma kin iya sai ke kike yi mata a daki" Inna bata yi makaranta ba dan haka dole ta hakura. Yes, muna yin homework din in mun gama kuma muyi kallo muyi hira ko Ummah tayi mana tatsuniya. Inna dai ba'a san ranta ba. Wannan yasa ta dage sai data samo mana islamiyyar dare duk kuwa da cewa muna yin ta assuba sannan muyi ta yamma. Baffa yayi magana tace "ai ilimi baya yawa" haka ina ji ina gani kullum nake tafiya islamiyya da daddare. Ni raina baya son islamiyyar nan musamman saboda malaman akwai cin zali kullum zaka gansu suna yawo da doguwar bulala ni kuma babu abinda bana so irin a taba lafiya ta. Ga prefects suma da shegiyar mugunta. Kullum sai Sadauki ya tabbatar naje da wuri saboda kar a dake ni, in lokacin tashi yayi kuma shi zaije ya taho dani saboda kar wani ya tare ni a hanya yaci zalina.

Ranar nan sai na kasa bada hadda. Yasaiyadi ya ware mu ya kira monitan aji uku yace ya zane mu. Haka aka zazzabga min dorina a baya na, gurin ya tashi yayi rudu rudu. Tun da aka dake ni nake kuka har aka tashi Sadauki yazo tafiya dani. Ina fita kuwa na gaya masa duk abinda ya faru, yace in nuna masa wanda ya dake nin a nuna masa muka taho gida. Dama ranar laraba ne, ban san yadda akayi ba sai ranar assabar na tafi makaranta wata yar ajinmu ta tare ni a hanya tace "Diyam, wallahi kar ki je makaranta yau, ana nan an ciro bulalai ance yau sai an zane ki, wai yayanki Sadauki ya tare monitan daya dake ki rannan ya zane shi shida kaninsa. Wallahi yasaiyadi uku ne suke jiranki a makaranta" nan take cikina ya duri ruwa, na juya da sauri sai gida, ina shiga na lallaba na wuce dakin Inna na shige dakin Ummah, nayi sa'a itama bata nan tana dakin Baffa sai Sadauki yana kallo. Na dora hannu aka ina kuka na gaya masa abinda ya faru, yace "zauna. Kin daina zuwa islamiyyar daga yau. Ai ba jakarsu bace ke da zasu saka ki a gaba suna duka kamar ganga. Ina nan zaune a kusa dashi har Ummah ta dawo, ita ta dauka har na taso daga islamiyyar ne dan haka tace "Diyam ki tafi gurin innar ki kar tazo tana nemanki".

Washegari ina kallon Sadauki yana ta yan aiyukansa a saman rufin dakin Baffa, da Baffa yayi masa magana sai yace "Baffa zafi ake yi, hawa zanke yi sama ina shan iska da daddare" yana gama wa sai ya kira ni gefe yace min "idan Inna tace ki tafi islamiyya da daddare ki hau sama kiyi kwanciyarki" shikenan nayi graduating daga islamiyyar dare. Kullum da dare in lokacin islamiyya yayi sai in lallaba in hayewa ta sama inyi kwanciya ta akan katifar da Sadauki ya shimfida min. Daga baya sai Sadauki shima ya fara biyo ni, yazo muyi ta hirar mu muna dariya, ko kuma yazo mana da games din Chess, Watt ko ludo muyi tayin kayanmu. Amma duk kanin mu munsan cewa duk wanda ya juri zuwa rafi to kuwa tabbas watarana zai fasa tulunsa.
[1/12, 11:38 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forteen : My Boyfriend

Ina ajin karshe a primary Sadauki shi kuma yana ajin karshe a secondary. Mu nan wai muma mun girma a ajin mu sai ake yin irin soyayyar nan ta yarinta. Kowa da saurayinta, amma ni banda ni. Wannan abin yana kona min rai kullum ina ganin ana rubutowa kawayena love letter su karanta suyi replying amma ni babu wanda yake rubutomin.

Akwai seat mate dina lubabatu kuma itace headgirl, ita head boy din mu yake so, kuma dan rainin hankali ni yake bawa wasika in bata wai kunyarta yake jiba zai iya bata ba, ita ma kuma inta rubuta reply ni take bawa in bashi, su basu san haushi suke bani ba gabadayan su.

Ranar nan, ina koro yara aji an gama breakfast sai muka hadu dashi. Muka gaisa yana ta sosa keya ni kuma na fahimci me yake so na bata rai nace "kar ma ka tambaye ni, ni bansan inda take ba" yace "ni fa ba cewa nayi ina neman lubabatu ba, yanzu ba zamu gaisa ba sai kinyi tunanin wani abu?" Nayi gaba nace "oho dai, kai kasani" ya biyoni "dan Allah Halima kina ji ba? Ki ce mata bata bani amsar jiya ba fa" nayi kamar ban jishi ba nayi tafiyata. Bayan naje na zauna a aji na ganta tana ta faman zanen flower a jikin plain sheet, nayi tsaki nace "rashin aikin yi, wai soyayya? Yar karama dake har kin ita rubuta wa saurayi wasika. Allah ya sawake, kuma in baki daina ba sai naje gidan ku na fada" ta harare ni tace "Allah yaso ma dai ni wasika kawai nake rubutawa saurayi na, ke kuma fa? Da kullum kuke yawo ke da naki saurayin?" Nayi galala ina kallonta ina tunanin waye take nufin saurayi na, sai kuma nayi dariya nace "wai Sadauki kike nufi? Bafa saurayi na bane ba, yayana ne to" ta harare ni tace "in yayan ki ne to ya akayi ke fara shi baki? Kuma ai munsan ba babarku daya ba kuma baban ku ma ba daya ba" naji haushin maganar ta na dauki jakata na bar mata seat din na koma wani. Amma kuma sai maganar ta ta tsaya min a raina, wai Sadauki ne saurayina.

Ina nan zaune har aka tashi. Ana ta zuwa daukan dalibai sai ga wata sa'adatu yar A ta leko ta window tace da karfi "Halima Usman ki fito ga wannan saurayin naki yana nemanki" Lubabatu ta juyo tana yi min dariya ni kuma na kara kulewa, na dauki jakata na fita.

Kamar hadin baki sai gashi washegari muka je gidan Mama tare da Inna, muna ta harkokin mu dasu Rumaisa su Inna kuma suna hira, sai naji kamar sun ambaci sunan Sadauki sai na saurara ina jin abinda suke cewa. Inna tace "mtsw, Hafsa ba zaki gane abinda nake nufi ba, ni nake zaune da yaran nan ni kuma nake ganin abinda nake gani wallahi. Ina jin tsoro Hafsa. Bana son abinda nake gudu ya kasance" Mama tace "wai gani kike in sun girma zai iya cewa yana son aurenta?" Inna tace "sosai ma kuwa, ya riga ya shanye ta kamar yadda na fada miki, kuma alamu sun riga sun gama nunawa. Tsoro na Allah tsoro na kar ya furta abinda nake tunani saboda kinsan halin baban su, wallahi indai yaron nan yace yana son yarinyar nan bashi ita zaiyi" Mama tace "chafdi. Kice tsugunne bata kare ba kenan. Allah yaji kan inno, da tana raye wallahi da tuni ta fatattaki yaron nan daga gidan nan. Ni babban tashin hankali na shine rashin sanin asalin sa. Ga tambarin da uwarsa take dashi. Yanzu menene abinyi?" Mama tace "ni so nake kije ki kai maganar nan gidan Alhaji Babba, shi kadai ne zaiyi min maganin fitinar nan wallahi" Mama tace "wanne Alhaji Babba? Alhaji Babba ba zai iya yi miki maganin komai ba saboda kinsan halin mijinki ba lallai ne in Alhaji Babba ya gaya masa magana ya dauka ba. Ke dai addu'a zamuyi tayi, idan har Allah ya rubuta aure a tsakanin su to Allah ya daidaita lamarin" Inna tayi saurin girgiza kanta tace "babu, insha Allah babu, da wanne zanji? So kike zuciya ta ta buga?" Mama tace "ni Adda ba sanin yaron nan nayi sosai ba, gaya min, bayan rashin sanin ubansa da ba'ayi ba yana da wani aibun ne?" Inna ta bude bakinta ta rufe, ta kasa tuna wani laifi da Sadauki yayi mata wanda zata bayar da misali da shi.
Duk a cikin hirar su Inna kalma biyu ce ta tsaya min a raina. "So" da kuma "Sadauki" nayi ta kuya kalmomin a raina ina tunanin ma'anar su. Wai soyayya muke yi ni da Sadauki? Sai kawai naji wani excitement ya lullube ni. I can't wait in bawa Sadauki wannan labarin. Magrib tana yi inna ta ce mu nemo hijaban mu da takalman mu mu tafi gida "kunga yau na jawo muku kunyi fashin makarantar yamma, gwara mu tafi da wuri kar Diyam ta rasa ta daren itama" sannan ta bawa Mama labarin dalilin da yasa ta saka ni a islamiyyar dare. Mama tana ta dariya muka taho.
Chapter 14 · 0% Book details