← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 112

Sashe 100

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Friday, da wuri Humairah tazo gidan, hakan ba karamin faranta ran Diyam yayi ba. Suka hadu da Rumaisa, Rufaida, su Murjanatu da kuma Asma'u. A ranar Kasusu (yan uwan ango) suka zo gari, gidan Alhaji Bukar suka sauka, daga nan kuma suka taho gidan su Diyam kawo kayan gaisuwar uwar amarya. Set guda akayo wa Inna na kaya tamkar wanda aka hado mata lefe, sai kuma kayan kunshi iri iri wadansu ma ko sunan su su Inna basu taba ji ba. Su kuma anan gidan suka hada musu goma sha tara ta arziki na nau ikan kayan ciye ciye, fura da nono kam ba'a maganar ta saboda tambarin su na fulani, sai gurasa ita kuma shedar su kanawa ne, sai kuma sauran abinciccika da kala kalar nama da drinks har sai da suka ci suka bari suka kuma yi takeaway. Da zasu tafi suke tsokanar su Sa'adatu "wato dan kunyi yaya shine kuka tare anan? To sai ku bita har gidan mijin kuyi mata zaman daki" Asma'u tayi saurin cewa "nice yar zaman daki ai".

Daga nan kuma sai aka fara shirye-shiryen wushe-wushe (bangajiya). A gurin taro na Meena event center anyi decorating gurin da traditional costume na barebari. Falmata, wadda take registered beautician ita ce ta zauna ta tsarawa Diyam kwalliya sannan suka nannade ta da flowery laffaya mai kalolin red and blue. Su kuma yammatan duk sunyi kwalliyar blue shadda da akayiwa dinkin riga three quarters da skirt, sai kuma suka yafa jan mayafi. Duk abinda suke yi Diyam tana jin sune kawai, amma ita hankalinta yafi tafiya ne akan murnar yau zata ga Sadauki, dan rabonta da ganin sa tun ranar Monday daya tafi Maiduguri zai taya Papa shirye shiryen saukar bakinsa da zasu zo daurin aure.

Bayan magrib motoci suka zo akayi ta diban mutane ana kai su, kowa cewa yake yi zaije saboda kowa yana son yaga wannan al'ada ta barebari sannan kuma kowa yana son cin dadi. Lol

Sai da aka gama kwasar mutane saura Diyam da yammatan ta sannan Sadauki yazo daukan ta. Aka kawo kuma wata motar da zata dauki kawayenta. Ya kira ta yace ta fito su tafi, ai kuwa duk su fanna suka taho rakiya da kuma tsegumi. Suka hango motar daya zo da ita, tun daga motar suka fahimci cewa yau a shiryen sa yake, Al- Mustapha ne a seat din driver, kuma dama yana daga cikin samarin Murjanatu dan haka ta bude seat din kusa dashi ta zauna. Diyam kuma aka bude mata baya inda Sadauki yake zaune ta shiga ta zauna kusa dashi aka rufe kofar. Adama ta zagaya side din da yake tayi knocking window, ya sauke glass yana kallon ta yace "ya akayi?" Tace "yaya Aliyu dan Allah in shigo? In zauna a tsakiyar ku kaga waccan motar kamar ba zata ishe mu ba" ta karashe maganar tana kokarin yin dariya, bai ce mata komai ba sai tayi winding up glass din yana murmushi yace "yaran nan so suke su mayar dani kakan......" Sai kuma maganar ta makale ya kasa kammalawa saboda juyo wa da yayi suka hada ido da Diyam da take kallon sa saboda kyawun da yayi mata ko kuma maybe dan bata saba ganin sa da manyan kaya bane ba?. Bakin sa ya motsa a hankali amma Diyam bata ji mai yace ba, sai ta tambayeshi. Yace "tasbihi nake yi ga Allah, mahaliccin kyawawan surori" ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta sai yabi hannun da kallo, idanunsa suka sauka akan tsararren kunshin da yake kwance akan farar fatarta. Yace "wadda tayi kunshin nan ko nawa aka biya ta taci kudinta" Diyam tayi masa fari da ido tace "harda kitso tayi min" yace "may I see it?" Ta makale kafada tace "not today" yace "gobe ne dai kadai ta rage min. Amma ban sani ba ko zan kai goben? Dan wannan abin da kike min da ido bana jin zai barni in yi bacci yau" dariya suka ji Murjanatu tayi daga gaba, Sadauki ya kalle ta yace "ko kiyi shiru ko kuma a sauke ki ki hau napep" Al-mustapha ya dan waigo yace "amarya, ni ko gaisawa ma ba'a bari munyi dake ba" Sadauki yace "hey! Juya ka kalli gabanka, don't go about looking at something that is not yours" Murjanatu tace "an fara, yau zanga yadda za'ayi wannan taron" Sadauki yace "kinyi shiru ne ko kuma ayi packing ki fita?" Al-Mustapha yace "in ka sauke ta sai dai ka zagayo ka ja motar ka da kanka" Diyam dai tana jinsu tana ta murmushi. Ita kanta tasan tayi kyau kuma tasan yau za'ayi rigima da Sadauki duk kuwa da cewa komai nata a rufe yake fuskarta da hannayenta ne kawai a bude.

Suna packing ya miko mata hannu yana murmushi, ta makale kafada sai ya langwabe kai yace "Please" sai ta saka hannunta a cikin nasa, ya juya hannun sannan ya saka fingers dinsa a tsakankanin nata yana kallon yadda hannayen nasu suka yi kyau sosai together, perfect match for each other, kamar dama a haka aka halicce su.

Suka fita suka jera a tare suka tafi gurin da aka tanada saboda su, Diyam idanuwanta a kasa tana jin tsananin kunyar mutanen gurin. Tun daga bakin mota ake turara su da turaren wuta iri iri masu kamshi kala kala har suka je suka zauna sannan aka sake zagaye su da turarukan wuta. Nan take aka fara gabatar da shagali wanda ita Diyam ba fahimta take yi sosai ba saboda hannun da yake rike da nata kuma tayi dabarar kwacewa ta kasa. Ga kuma idanuwa guda biyu a kanta suna kallon duk wani motsi nata. Ta dan kalle shi tace "hey.......stop looking at me like that" ya daga gira yace "ko? Saboda me? Baki san ni maye bane ba? Ko baki da labari?" tayi murmushi tace "kar ka bari Inna taji ka" yace "am serious fa, kin dauka wasa nake yi ko? Ina tausaya miki ranar da zaki fahimci a inda tawa maitar take" ta sake kokarin karbar hannunta ta kasa. Yace "wannan hannun tunda kika bani shi kuma ya zama nawa, sai sanda nayi niyya zan baki aron sa" ta sake cewa "ni ka daina kallo na" ya bata rai yace "ba fa ke nake kallo ba, lips dinki nake kalla wondering what they taste like" taji kamar zata nutse a gurin, tace "wayyo Ummah".

Anyi rawa sosai, rawar barebari, yan'uwa da abokan Sadauki ne suka fara yi sai kuma na Diyam sukayi joining dinsu suna koya, sai kuma suka koya musu suma irin tasu rawar ta fulani. Amma Diyam ko motawa daga seat dinta Sadauki bai bari tayi ba ballantana ta saka ran yin rawa. Duk wanda yazo gurin su daukan hoto kuwa indai namiji ne to Sadauki zai ce masa "zagayo ta side dina" sai suyi dariya gaba daya. And Diyam wondered, anya kuwa Sadauki zai barta ta koma school?

Sai after 11 suka tashi, shima dan dare yayi ne ba wai dan sun gaji ba. Da kyar Sadauki ya bar Diyam ta shiga gida, shi ji yake kamar su yi ta zama a mota har gari ya waye, gani yake kamar gobe ba zata yi ba.

A ranar duk su biyun babu wanda yayi bacci. Kwanciya suka yi da wayoyinsu a kunnuwansu suna bitar rayuwar su, yarintarsu, rabuwarsu, da kuma sake haduwarsu. Diyam ta bashi labarin sanda take lekensa ta window lokacin da Saghir ya kawo shi gidan su. Yace "ohhhh, ashe shi yasa naji kamar zan fadi, ashe idanuwa ne suka yi min yawa". Sai da dare ya raba sannan suka yi shawarar gabatar da salloli da addu'ar neman alkhairi a cikin sabuwar rayuwar da zasu shiga gobe. A kan sallayinsu suka karasa kwana. Sai da suka yi sallar asuba sannan Diyam ta kwanta, amma kuma ba wai bacci tayi ba likimo kawai tayi tana jin su Humairah dasu Murjanatu suna ta hirarrakin su suna dariya har gari ya waye. Bata tashi ba sai da Hannatu Sokoto ta zo ta tashe ta tana cewa "gwara da kikayi baccin ai, shi bacci yana kara fito da kyawun mutum" sai ta ajiye mata special dahuwar kazar da tayo mata daga gida, ta zauna ta cinye tas sannan ta kora da tsumin maman fareeda (07033742833), tana ci suna hirar su da Humairah suna kuma jiyo hayaniya a tsakar gida maza suna ta shirye-shiryen tafiya daurin aure. A lokacin Bassam ya kira Humairah ya gaya mata ya shigo gari amma ya zarce venue din daurin auren, Alfurqan Mosque.

Kafin ta gama Hannatu Sokoto ta shirya mata ruwan wanka dan haka ta shiga tayi wanka tafito, tana zama a gaban mirror message din Sadauki ya shigo wayarta.

Dear Mrs Abatcha
Alhamdulillah. I am now yours and you are mine.
Signed
Mrs Abatcha

Ai mun gama ko?
[3/24, 10:36 PM] +234 703 589 5826: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventy Two & Three : A Perfectly Perfect Night

I was thinking about covid-19. Sai nake ganin da ace al'ummar duniya duk sun sani kuma sun bi umarnin fiyayyen halitta (S.A.W) a inda yake cewa idan annoba tazo guri, wanda yake ciki kar ya fita wanda kuma yake waje kar ya shiga, da an bi haka da cutar bata kai matsayin da take a yanzu ba.

Chinese basu san wannan umarnin na annabi ba, amma mu munsani dan haka me yasa mu ba zamu bi ba dan dakushe yaduwar cutar?
Stay safe
Stay at home

Hannatu Sokoto da muka yi magana a last episode wata member ce ta group dina na WhatsApp, amma bata gyaran jiki, na saka sunanta ne kawai to honor her and for fun.
But Maman Fareeda is real, duk mai so zata iya kiranta.
Chapter 100 · 0% Book details