Sashe 96
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
as her husband yana saka ta murmusawa. Suna rabuwa da Bassam ta kira Sadauki ta bashi labarin dawowar Bassam. Wannan shine dai dai saboda boye boye shi yake kawo zargi in a relationship. Kamar wasa sai ga Bassam ya kawo wa Diyam Humairah har gida. Sai Diyam taga cewa ashe duk abinda take tunani a game da Humairah ba haka bane ba, na farko she is young, dan Diyam tana ganinta ta san cewa ta girme ta. Ko kuma dan tana da baby face ne? Da suka zauna suka fara hira sai ta fahimci tana da saukin kai sosai da kuma addini. Ta karbi babyn da yake hannun Humairah tana yaba kyawunsa tace "masha Allah, ya sunansa?" Humairah tace "Abubakar, Ayman ake ce masa" Diyam tayi murmushi tana tuna mitar da Bassam ya taba yi akan cycling suna daya within a family. Amma ai honor ne ko? Kowa yana burin ya haihu yayi wa iyayensa takwara. Nan da nan Diyam ta dauko zani ta goya Ayman, tana tuna sanda Subay'a take jaririya. Wannan yasa Humairah ta kara sakin jikinta saboda hausawa sunce mai É—a wawa ne. Sun jima suna hira, suka yi hirar similarities dinsu sannan suka yi hirar differences dinsu, a take kowacce a cikin su ta fahimci cewa tayi kawa. Tare suka shirya abinci sannan suka zauna suka ci a plate daya, suna cikin ci Murjanatu ta shigo tayi joining dinsu itama. A nan ne take bawa Humairah labarin cewa an kusa auren Diyam da yayanta, sai kuma hirar ta koma kan hidindimun aure da kuma zamantakewa ta aure har sai da Murjanatu ta mike tace "wannan hirar tafi karfina kar kuje ku kona ni tun kafin in tafasa". Komai ya tafi normal har Diyam ta kammala exams dinta, a cikin lokacin sau biyu Sadauki yana zuwa Oxford Diyam tana koro shi Nigeria saboda tace karatu yake hanata yi in dai yana can din. A dole ya hakura ya dawo Nigeria amma da sharadin cewa kullum zasuyi video call sau biyu. Ranar da zata dawo Nigeria Sadauki ne yace zaije ya dauko ta, amma sai ya gaya wa Asma'u ta shirya Subay'a su tafi tare. Subay'a kam murna take tayi ta kasa rufe bakinta saboda farin cikin zata ga mommyn ta, dan haka bata damu bama da wate zasu tafi tare dashi. Shi ya fito da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga sannan ya zagaya ya zauna yana tsokanar ta "Subis yanzu duk wannan kwalliyar ta mommy ce? Dama ashe kin iya kwalliya haka shine ni ba kya yi min sai mommy ko?" Ta sunkuyar da kanta tace "bani nayi ba ai, aunty Asma'u ce tayi min" yace "to gaya min, me kika tanadarwa mommy?" Ta bude hannu tace "babu komai, ai ni bani da kudi" yace "to me kike so ki siya mata" tayi shiru sannan tace "sweets" yayi murmushi "wato kin san ta da shan sweet ko?" Sai tayi shiru bata ce komai ba. Yace "kina so in kai ki ki siyo mata?" Ta gyada kai kawai, sai yace "a'a, in dai kina so to sai kinyi magana da baki ba da kai ba. In kuma baki yi ba bazan siya miki ba" tace "ina so" yace "to sai kin fadi sunana tukunna. Ya sunana" a hankali tace "uncle Aliyu" yayi murmushi ya shafa kanta yace "good girl". Suka biya ta mall suka ciko leda da kayan zaki sannan suka karasa airport. A airport din sai yaga duk walwalar data fara dazu ta ragu, tayi shiru kamar mai shirin yin kuka, sai ya durkusa a gabanta yace "menene kuma? Ba kya murnar ganin Mommy? Ko in kira ta a waya ince mata ta koma ba kya son zuwanta?" Sai tayi sauri ta girgiza kai, yace "to me kike so?" Tace "rannan da muka zo nan da mommy, sai police suka zo suka tafi da Daddy na kuma har yanzu basu dawo min dashi ba" sai hawaye suka zubo daga idonta ta dago tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta sake cewa "mommy tace zaka fito min dashi ko?" Ya saka hannu ya share mata hawayen fuskarta yace "daddyn ki zai fito little girl. I promise you" sai kuma yayi murmushi yace "amma sai kinyi min wani alkawari, promise me daga yau mun zama friends" ya fada yana mika mata dan karamin finger dinsa, ta goge hawayen fuskarta ta saka nata karamin finger din a ciki sannan ta gyada kai tana murmushi. Ya daga ta masa ya dora ta akan kafadarsa yace "now, let's wait for your mommy". Diyam tana fitowa ta hango su, and seeing them smiling together ya saka taji wani irin joy a zuciyarta marar misaltuwa, tana kallonsa ya sauke Subay'a kasa ita kuma ta taho da gudu gurinta sai ta durkusa ta bude mata hannayenta ta shige zuwa kirjinta ta rungume ta taba ajjiyar zuciyar dadi, ta dago fuskarta tayi kissing goshinta tace "I miss you so much little girl" Subay'a tace "I miss you too mommy". Ya karaso ya tsaya a kansu yace "na gane matsayi na" ta mike tana kokarin daukan Subay'a yace "ke! Careful kar kisa a daga min biki" ta harare shi tace "wato bikinka ne a gaban ka ko?" Yace "a yanzu, yes" Subay'a tace "uncle bikinka za'ayi?" Ta fara tsalle, "zanje gidan ka inga amaryarka" ya daga ta sama yace "karki damu, kece yar zaman daki". Daga airport basu yi cikin gari ba sai suka dauki wata hanya daban. Diyam tace "ina zamu je?" Bai kalleta ba yace "kawunan ku zanje in siyar" tayi dariya "ni kaina yafi karfin babarbare ya siyar" ya kalleta yace "siya na nawa kuma? Sai ya kalli Subay'a ta mirror yace "kinci sa'a we have company" ta murguda masa baki, yace "ki cigaba, ba dai rashin kunya ba, akwai ranar kin dillanci". Titin bypass suka hau sannan suka shiga unguwa uku, suka sauka daga babban titi suka shiga wani layi sannan yayi packing a gaban wani gida yace "Mrs Abatcha, welcome to your home" ta bude vaki tana kallon gidan sa yake gabanta sannan tace "wow" yayi murmushi yace "shall we?" Kafin ta bada amsa Subay'a ta bude motar ta fita da sauri tana cewa "uncle gidanka ne wannan?" Ya fito yana cewa "gidan mu ne princess, ni da mommyn ki da ke" sai ta kwasa a guje ta kama gate din tana cewa "Mommy ki kira inna kice ta aiko min da kayana" Diyam da Sadauki suka yi dariya a tare. Malam iliyasu ya fito yana bude musu gate. Diyam ta kalleshi sannan ta kalli Sadauki shi kuma ya daga mata kafada yana murmushi. Sai ta juya tana amsa gaisuwar da malam iliyasu yake yi mata amma bata ce masa komai ba sannan suka taka da kafa suka shiga gidan. Tsayawa bayyana tsari da kyawun gidan zai tsawaita labarin mu amma dai tabbas Moon construction company sun kure adakar su a wannan gidan. Daki daki suka bi a nutse Sadauki yana yi mata bayanin komai kuma tana neman gyaranta in akwai amma ita bata jin akwai wani gyara da za'ayi a wannan tsararren gidan. Bayan sun gama sun fito ne suka zagaya baya gurin wani dan karamin gurin shakatawa mai lullube da grass carpet da kuma madaidaicin swimming pool mai dan karen kyau wanda ganinsa kawai ya isa ya saka mutum yaji yana son yin wanka. Suka zauna a wasu daga kuherun gurin ita kuma Subay'a ta bazama tana zagaya gurin a kuje. Diyam tace "amma gidan nan yayi kyau, irin sosai din nan fa" yayi murmushi yace "am glad you like it. It will be our Kano home insha Allah. Zamu yi wani a Maiduguri saboda muke sauka in munje, and for Oxford we have to get a bigger apartment dan wanda kuke ciki yanzu yayi mana kadan". Sai ta dauko wasu takardu ya mika mata sannan ya gyara zama yana kallonta. Ta karanta ta kuma karantawa, ta fahimci cewa wata yarjejeniya ce signed by Aliyu Umar Abatcha cewa ya yafewa Saghir Muhammad Kollere kudaden sa daya satar masa. Akwai saka hannun lawyers dinsa, akwai saka hannun alkalin da yayi waccan shari'ar sannan akwai saka hannun Saghir. A kasan inda Saghir ya saka hannun ya rubuta "thank you". Ta dago da sauri tana kallon Sadauki, sai kuma ta kasa magana. Yaushe Sadauki yayi wannan shawarar? Shin hakan yana nufin Saghir ya fito ko kuwa bai fito ba? Jin bata ce komai ba yasa yace "lokacin da Saghir ya fada min wannan maganar a kanki ba rufe shi nayi niyyar yi ba, zuciyata abinda take gaya min shine in kama shi inyi ta dukansa har sai ya daina numfashi sannan in kaishi daji in ajiye shi dabbobi su cinye shi da rai" ya danyi dariya ganin kallon da take yi masa yace "babu irin imagination din da bana yi that's why I decided to set a trap for him and luck him up, a hakan zaiyi paying for what he did and he will be out of my reach yadda bazan yi masa lahanin da duk zamuyi dana sani ba. I didn't know his friend will set him up for drugs. Niyyata shine a lokacin da naji zuciyata tayi sauki a kansa sai in yafe masa ya fito but as fate have it ba wannan ne kadai case dinsa ba, so, har yanzu yana can kamar yadda alkali ya fada har sai an samu nasarar kama abokin nasa kuma sai abokin ya karbi laifin shi ya bashi ajjiyar drugs din" Diyam ta gyada kanta tana kallon Subay'a da take wasa a can nesa dasu sannan take murya can kasa "thank you. Mun gode Allah ya kara arziki" baice komai ba shima yana kallon Subay'a sai zuwa can yace "zanyi kokarin ganin ya fito, dan Subay'a taji dadi. But bazan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata daga farko, ruwansa ne yayi hankali ruwansa ne kuma yayi akasin hakan. Na riga nayi magana da Ahmad, duk da dai kamar baya goyon bayan fito da Saghir din but yace zai taimaka min, matsalar shine su iyayen Kabir din sunki vada goyon baya su fadi inda dan nasu yake" ya juyo yana kallonta yace "naso ya fito kafin auren mu, naso yazo ayi dashi dan anan ne zan tabbatar da nadamarsa